Da tarin fushi Binta ta koma gidanta, kamar tana shirin idan Mujahid yayi magana hata hadiye shi ta huta da baqin cikinsa.
Ta sha atisayen gwada kala-akalar rashin kirkin da zata yi masa wanda ko ya qi Allah sai ya sallame ta a ranar.
Shirinta bai ci ba don kuwa ya shigo da fuskar gabarsa da ya saba da ita qarfe biyar na yammacin ranar.
Yana shigowa ya haye kangon dakinsa, ta dinga kasa kunne tana jiran ya shigo wajenta da tsokanar da ya saba don ta haukace masa, amma sai ga shi bai shigo ba. Shiru-shiru. . .