Skip to content
Part 38 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Da tarin fushi Binta ta koma gidanta, kamar tana shirin idan Mujahid yayi magana hata hadiye shi ta huta da baqin cikinsa.

Ta sha atisayen gwada kala-akalar rashin kirkin da zata yi masa wanda ko ya qi Allah sai ya sallame ta a ranar.

Shirinta bai ci ba don kuwa ya shigo da fuskar gabarsa da ya saba da ita qarfe biyar na yammacin ranar.

Yana shigowa ya haye kangon  dakinsa, ta dinga kasa kunne tana jiran ya shigo wajenta da tsokanar da ya saba don ta haukace masa, amma sai ga shi bai shigo ba. Shiru-shiru har lokacin sallar magariba ya sakko da alwalarsa zai tafi masallaci. Ta miqe kenan zata shiga bandaki ta yo alwala ya leqo falon,

Suka yi wa juna kallon qurulla, Binta cike da nuna jin haushi, shi da boyayyar manufa. Ita ta fara kawar da kai da qaramin tsaki zata nufi waje abinta, ya taro ta, babu walwala a fuskarsa don haka ta ji ta kasa gardama,

“Yau kuma da nake shirin zuwa da babban al’amari zaki marabce ni da tsaki? Don Allah kina da hankali ke kuwa?”

Kamar dama bai tambaye ta don ta amsa ba, tana yamutse fuska shi yana amsa mata,

“Ina shakkar in kina da hankali”.

Da qyar ta qwaqwulo furuci ta yi cikin son zubar da hawaye,

“Kai da kake da hankali kuma kake riqe da mahaukaciya ai ka fi ni alamun hauka, Da ikon saki a hannuna yake na rantse maka da Allah in kai Sarki ne ba wai Mahaukaci ba da tuni na yi maka saki dari idan ana yi.”

Duk da fuskarsa babu walwala amma muryarsa ba ta nuna damuwa,

“To dama wa zai ba Mahaukaciya riqon igiyar aure? Ai ke da igiya sai dai in ta Gugan da zaki ja ruwa in na gaji da tabararki na mayar da ke qauye.”

Baqin ciki ya qara cika zuciyar Binta, sai ta kasa magana.

Suka dan yi shiru saboda ya jira ta yi magana ba ta tanka ba sai ya tafi maganarsa ta gaba,

“Ki yi wanka don Allah Malama zaki dan fi kyan gani, sannan ki dafa min shayi kafin na dawo, zan je in ga likitanki ya tsara mana yadda zamu rayu, na wuni yau cikin tunanin da yadda zan rayu da wannan mahaukaciyar mai kuma ciwon qanjamau, tsiya goma da ashirin wai shege da hauka.”

Yanzu kukanta ya fara zuwa,

“Ai ka fi tsiya Mujahid, tunda kai da hankalinka kake son rayuwa da mai tsiya goma da ashirin…”

Ya tare ta cikin halin ko in kula,

“Gaskiya na fi ki tsiya da na rakito sonki na manawa zuciyata, to amma ya zan yi da qaddara? Ita ke sabunta min sonki duk kwanan duniya, duk aibun da zaki zo da shi ba ya taba qara min tsanarki sai dai ya qara min sonki da fahimtar banzayen halayenki, amma in da so zabe yake ai kin san babu yadda za’a yi na zabo ki Binta…”.

Bai jira cewarta ba ya sa kai ya fice daga falon.

Nan ta yi tsaye ita ma lokaci guda ta fara shakkar anya ma kuwa Mujahid da ke kiranta Mahaukaciya ba shi ne mahaukacin ba? Tun da ya tsiri fara sonta yake maimaita mata kaifin son da yake mata amma kullum tsakaninsu babu abin arziqi sai baqar magana?

Ta yi wanka dai, amma ta qi dafa shayi tana zaune tana cika tana batsewa sai gashi ya dawo qarfe tara na dare daidai.

Ya shigo da wankansa yana ta faman zuba qamshi, ko inda yake Binta ba ta kalla ba saboda in ta kalla tana jin zuciyarta na barazanar fashewa.

Sai daga baya ta fahimci ya shigo da kayan qwalam ne dangin nama da na jiqa maqoshi yana samar musu wajen zama a farantai.

Ya shirya komai a tebur sannan ya juyo ya dube ta,

“Ina shayina?”

Ta qurawa Tb ido ta ba banza a jiyarsa, tana qunquni ba tare da ya ji abinda take fada ba, ana cikin haka sai ga tallan kamfanin Alhaji Ibrahim dinta tare da sako hotonsa a matsayin Manaja, komai ya dawo mata sabo, ta dinga tuno wahalar da ta dinga sha da Mujahid amma duk da haka sai da ya zame mata qarfen qafa ya zama mijinta, sannan ya yi nasarar ma ba zai bar zuciyarta da ciwon aurensa bisa dole kawai ba sai ya dinga bin ta da manya da qananan cutuka yana zoza mata a zuci.

Ya lura da halin da ta shiga, don haka ya taho a hankali gabanta ya tsaya yana duban Tb shi ma, fuskarsa da yanayin tausayi, sannan ya sake rakito alhinin duniyar nan ya dube ta da shi,

“Allah sarki Ibrahim, ke ma ya baki tausayi ko? Duk san da na tuna shi sai na ji tausayi, in dai irin yadda nake jin son ki a zuci kike jin nasa haqiqa yakamata duk safiya na dinga yi miki jajen rasa shi”

Binta ta shanye haushi, don ta san don ta ji shi Mujahid yayi maganarsa, duk da haka bai bar ta ba sai da ya sake jangwalo wani turin haushin ya tura mata, yana dariya ya ce,

“Amma fa dole ta wani bangaren na yi masa barka, da yanzu shi ya jangwali ciwonki ko? Gaskiya Allah ya rufa masa asiri, daga ganin lasar lebe ya ari qafar kare”

Kawai sai ta tashi ta bar masa falon, ya bi ta yana kira,

“Zo don Allah ki ba ni lambarsa na yi masa jaje.”

Ta qarasa daki da kuka, bai kuma fasa bin ta ba.

Ta kife bakin gado shi kuma ya zaro wayarsa,

“Ayya, na manta ma ina da lambarsa.”

Cikin sakan talatin sai ga Alhaji Ibrahim ya daga wayar, ko sallamarsa mujahid bai amsa ba ya shiga yi masa karadi,

“Abokina babu fada me ya kawo gaba? Na sha kiranka ba ka amsawa, kai kuma baka tare ni ka fada min laifin da na yi maka ba…”

Duk da Alhaji Ibrahim qullace yake da mujahid amma yayi mamakin jin cewa wai ya sha kiransa, murya a sarqe ya amsa masa,

“Gaskiya ban ga kiranka ba…”

Mujahid ya tare shi yana dariya,

“Akwai alamar hakan tunda dai gashi yanzu ka daga.”

Alhaji Ibrahim ya daure yayi tambayar da ke yunquro masa a maqoshi,

“Shin wai da gaske ne ka yi aure?”

Sai da ya zura wa Binta Ido sannan ya amsa cikin gadara,

‘Eh, na yi aure na auri Binta”

Alhaji Ibrahim ya saki nishi, zai yi magana ya kasa.

Mujahid ya sake magana cikin dare,

“Amma ka san na yi aure shi ne ko ka kira ni ka yi min jaje?”

Cikin rashin fahimta Alhaji Ibrahim ya ce,

“Jajen me zan yi maka? Jaje zan maka ko murna Mujahid?”

Kai tsaye Mujahid ya amsa,

‘Wai ai da na san cewa kai kadai ne ka san duk wanda aka aurawa Binta sai duniya ta yi masa Jaje, kai ka fara…”

Ba zato babu tsammani ya ga wayarsa a hannun Binta ta fizge tayi jifa da ita kan gado, yayi saroro yana kallonta tamkar shi fa bai yi komai ba, ya ce,

“To haukan ne ya tashi, a kira likita?”.

Ta kasa tankawa, takaici ya hana ta magana.

Shi da yake jin nishadin abinda yake faruwa ya sake kunno ta,

“Ba ki zaci abinda zan yi kenan ba ko? Ai haka nake, ina zaune da rigar Siliki irinki in ban zama kamar ke ba, zaki sha ni basilla”

Ta tsare shi da kallon da ke nuna da tana da dama sai ta tashi ta shaqe shi ta kashe, sannan ta loma baki ta sake hadiyewa.

Ya kada kafada da alamun ko in kula,

“Kin zaci yabonsa zan yi saboda kan sa’arsa na mun kasa ya ya siyar ya bar ni? Ko kin zaci waqe shi zan yi saboda jarumtar mun zuba tsere ya sha ya bar ni? A’a ki ce shi ne ma Antarun, Ko kowa na tsira daga zambona duk wanda ya bude qwanji don shiga tsakanina da ke ba zai tsira ba…”

Ta tare shi da kukanta,

“To dama tunda ni kaina ban tsira ba waye zai tsira? Ni dama ban taba sa rai da farin ciki a aurenka ba, saboda haka ko wacce qaddara ma ta zo qwallon kaina ta sami masauki, zan yi tawakkali”

Dariya ce ta yi mugun cika shi, kuma bai shirya yin ta ba, don haka ya je ya dau wayarsa yana kada kai ya matsa ya ba ta waje.

****

Kwanaki suka dinga shudewa cikin su uku babu mai jin dadin yadda suke wanzuwa, Mujahid dai qarfin hali kawai yake yana yaqe da nuna shi fa babu wani abu da zai damar masa rai, alhalin ya fi kowa damuwar, shi ne mara sa’ar son wadda ba ta sonsa,  tun yana qirga kwanakin da Binta zata gaji ta so shi har lissafin ya fara kubuce masa, ya dawo canki-cankin wai ma da shi mai auren wadda bata sonsa da kuma ita da ta auri wanda bata so wa ya fi wani takura da jin qunan zuciya? Duk dai amsar da ya samo ba ta sanyaya masa rai kamar yadda ba ta rage ko digo cikin son da yake wa Binta. Ya rasa irin son, ita kuma ta kasa tsayawa ta mora, shi kuma ya kasa damqa mata moron a haka don kar ta wulaqantar.

Amma ita a zatonta ita kadai ke shan uquba, ita aka garqame a wannan auren me kama da Keji, mara ko wacce irin walwala kama daga ta zuciya zuwa ta kulawa, har ma da ta aljihu idan ta kama, don tun da ta shigo ko kobo Mujahid bai taba dauka ya bata a matsayin hasafi na tsakanin miji da mata ba, hakazalika bai taba tambayarta abinda take so ko da a dangin abinci ne ya sauya mata da wanda ranta ke so ba, duk wadannan ba wai don ta rasa ba, don tana daukar albashi mai tsoka, A’a sai don kawai ita fa duk burin duniyar nan da ta ci a kan mijinta mai ‘yar banzar kula da ita ta so, ido a dukkan motsinta kuma mai bata da yawan lokacinsa, amma shi wannan babu komai tsakaninsu sai baqar magana, tamkar dama ya aureta ne don ya hukuntata da nuna mata shi fa ya qware a zambo da baqar magana.

Watarana ya tashi fuskarsa a bace sakamakon wani mafarki mara dadi da yayi da Nabila, ranar ma a daya daga dakunan Binta ya kwana, kuma da ya dawo sallar asuba wayarsa kawai ya zo ya dauka yana qoqarin ficewa ya hau sama.

Lokacin Binta na falo tana azkar, kasancewar babu haske sosai tun shigowarsa take bin sa da kallo, ta fara kallonsa ne da Allah wadarai, tare kuma da jinjina masa wannan rayuwar quncin da ya zaba wa kansa kuma da alama yana jin dadin abarsa, musamman yanzu da ya shigo da fuskar shanu, ya kalli wajen da take sau daya ya kawar da kai. Ya shige sabgarsa, da ya fito ma bai sake duban inda take ba ya wuce ita kuma ba ta iya dauke ido daga kansa ba har sai da ya fitan, sannan ta sauke kai cikin ajiyar zuciya, zuciyarta na karbar wani irin sauyi, ta ji a fili ta ce,

“Mts! Mutum sai kyau babu kyan hali”

Kamar da wasa ta jiyo sunan Nabila a bakinsa lokacin da yake hawa bene, ba ta jima tana shakka ba ta san cewa waya yayi mata da sanyin safiyar nan? Sai ta ji wani mugun ciwo irin wanda ba ta taba jin irinsa a qoqon rai ba, ba ta iya daurewa ba sai da ta tashi ta shiga leqensa daidai lokacin da yake shigewa dakinsa, ba ta yi qasa a gwiwa ba sai ta sami kanta da yin sanda ta bi shi, ta shiga yi masa labe.

Daga daga wayar Nabila ya san cewa lallai tana cikin damuwa, sai ya ji ransa babu dadi, Allah ya sani yana qaunar yarinyar tsakani da Allah, ba so na aure ba irin son da kowa ke wa jininsa, sam-sam ba ya son duk wani abu da zai taba ranta, ba ya son duk wani rashin sa’a ya ga qwallon kanta, don haka da qaddara ta jaza mata zama gidan mahaifinta wanda ya sha jin labarin cewa babu dadi, ya sha jimami da yi mata addu’ar Allah ya yanke mata, kuma saboda wannan dalilin ne ma bayan rasuwar innarta ya zama mai qarfafa mata gwiwar cewa ta auri honorable din da ta zaba kawai, ko ba komai yana matuqar sonta tamkar ya hadiye, wannan ya sa Mujahid ke dan jin qwarin gwiwa, kuma musamman da ya binciki halin Honorable ya tarar mutumin kirki ne, sai ya ji tabbas rayuwar Nabila ba zata wulaqanta yadda ba ya qi ba.

Suka gaisa cikin kulawarsa ta matsayin wa ita ma kuma cikin shanye so kamar yadda ta saba da kukan zuci, da ya kira ta duk damuwar da take ciki ta tafi, shi kawai take ji a zuciyarta da filin kunnenta.

A tausashe ya ce,

“Ki na lafiya kuwa Nabila?”

Ta na murmushin qarfin hali ta ce,

‘Lafiyata lau Yaya Mujahid, me ka gani?”.

Ya dan yi tsaki,

“Jikina ne kawai ya ba ni, ki fada min gaskiya”

Kuka ya qwace mata, lokacin da zuciyarta ta gama rauni, kuma ta gama jarumtar share kular wanda take tsananin so. tana da yaqinin Mujahid ba irin son dake buqata da shi yake mata ba, amma kulawarsa gareta ko wancan ya ishe ta.

Yayi shiru yana sauraron kukanta zuciyarsa a dame, don dama shi mutum ne da in dai zaka yi kuka to ba ya katse ka farko, sai ya bar ka ka rage nauyin qirji sannan ya tara da rarrashi, ya san muhimmancin kuka qwarai.

Sai da ya ji ta fara rage zafin kukan sannan a sanyaye ya ce mata,

“Dama na fada miki, tabbas kina da matsala. To me ya faru?”

Ta amsa cikin raunin murya,

‘Jirana ya koma baya, da ina da me tsaya min da na je makaranta Yaya mujahid”

Ta ba shi amsa a gutsire amma bai ji komai ba sai ya sake rarrashi,

“To me ya faru?”

“Kamar almara, wai honorble yanzu Anti Sadiya kanwar Momi yake so, jiyan nan ma ya kai mata kudin aure?”

Mujahid ya ji wani dum! A zuci, an sha ce masa Momin Nabila matar babanta kenan, tamkar tsatson Barbushe ce ita kan tsafe-tsafe, lokacin rasuwar Inna ya ji kannesa mata na zargin da kyar in ba ta yi naqasun raba Nabila da Honorable ba, ilai kuwa gashi zancensu ya tabbata.

Da qarfin hali ya ce mata,

“To shi ne me? Ba Honorable zaki rasa ki damu ba, addu’ar da nake miki ce ta sa ya janye, dama can bai dace da ke ba”

Hawaye kawai Nabila ta ke ta kasa tanka masa. Ba lallai ya gane, da ta rasa wanda yakamata ta damu idan ta rasa ma damuwarta ba ta dawo mata da shi ba.

Suka yi shiru na wani dogon lokaci, sannan ya nisa ya ce,

“Ki na ganin Mahaifinki zai bar ki kiyi karatun?”

Kai tsaye ta ce,

“Ai ba shi ne matsalar ba, matsalar Momi ce, na ji tana maganar ai tare za’a hada bikin da na Anti Sadiyan, ko wa zata aura min? oho!”

Sai ta qare maganarta da kuka.

Mujahid ya rasa abinda ke masa dadi, ya ji kamar ya zama ma wani mara amfani, yarinyar da ta taimaka masa iyakar qarfinta lokacin da yake fafutukar neman abinda yake so, amma shi ya kasa sanin hanya ko da babu gara babu dadi ce wadda zai hana hawayenta zuba?

Ya tuna ya sake amma ya kasa samun ko wacce irin hanya, kawai sai yayi mata abinda ya saba,

“Hakan ba zata faru ba in sha Allah, don Allah ki ba ni sati guda.”

Cikin saduda Nabila ta ce,

“Ba komai Yaya Mujahid, kar ka damu”.

Ya yi dariyar qarfin hali,

“Ke ma haka.”

Suka yi sallama ya sauke waya yana ambaton Innalillahi a hankali.

Binta ba ta fahimci komai a kan hirarsa ba sai zargin da ya cukuikuye ranta na zaton Mujahid na lallaba Nabila ta jira shi ne har ya gama alayinsa ya zo ya aure ta, shi ne yake ce mata ta koma makaranta.

Ta ja qafa cikin wani irin nauyin jiki da na zuciya ta sauka kasa, ta shige daki ta hau gado ta shiga sharar kuka.

Mujahid dan iska ne lamba daya, lokacin da ta dinga nana masa Nabila cewa yayi ba ya so, amma da yake shi ba’a hada lamari da shi bai jaza wa mutum hawan jini ba, sai yanzu zai kalle ta ya so?

Tana kuka tana tunanin hanyar da zata kubuta daga wannan zargagun din na wancan banzan mara mafanin mutumin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 37Rigar Siliki 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×