Skip to content
Part 47 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Yayi farin ciki da ganin Mujahid cikin walwala ya zo musu godiya, don da bai zaci hakan ba musamman da bai gan shi wajen daurin aure jiya ba, sannan ya kula kamar Alhaji Hassan hankalinsa a tashe yake da hakan shiyasa yayi zaton dole kawai yayi Mujahid shi kuma yake son bijirewa.

Shi ma haka yayi kwanan tashin hankali, don ya san in dai Nabila ba ta dace da mijin aure ba, to qila rayuwarta ta shiga garari kenan, in an sako ta zata zo gidan nan ta zauna fiye da baiwa.

Yayi farin ciki matuqa da wannan labarin baqin cikin ya zama tarihi.

Sai yau ya ji takaicin rashin ‘yan uwansa da zai kira su gaisa da mijin Nabila, don yawanci ba su ma halarci bikin ba, mazan ne ma suka daure suka halarci daurin aure jiya, shi ma daga wajen daurin auren suka samfe. Dole yanzu sai Momin dai uwarsa Ubansa ya kira suka gaisa da Mujahid, shinqimemeiyar mace me jar fuska, ta ci gwala-gwalai tamakar wata amaryar Indiya, komai nata na nuna isa da taqama, a haka suka gaisa, kuma ba ta tashi ba sai da ta yar musu magana inda ta ce,

“Amma dai kar a tsawaita tariyar nan, saboda babu dadi ‘yan kwanaki yarinya ta fara amaye-amaye a gidansu”

Cikinsu babu wanda ya tanka.

Alhaji ya fi kowa jin rashin dadin maganar tata, don ya kwana da sanin, nagartattun yara kawai Hassan yake da su masu bin Umarninsa ko ba sa so, amma ba don Mujahid na mararin auren ba ne.

Sai dai babu yadda ya iya har Momi ta gama ciye-ciyen fuskarta ta tafi, sannan ya dubi Mujahid a dan tsorace, sai ya ga babu ko wacce irin damuwa a fuskarsa, har yanzu murmushi mai tasowa tun daga qoqo zuciya. Sai ya ji hankalinsa ya kwanta.

Suna tare tsawon lokaci sannan Mujahid ya iya neman buqatar ganin Nabila, nan take Mahaifinta yayi mata waya, shi kuma ya tashi ya fita.

Yana fita Jamilu da yake yana da shegantaka sai cewa yayi,

“Kai ba dai wannan dangaramar ce uwarta ba.”

Mujahid yayi murmushi ba tare da ya dube shi ba ya ce,

“Matar babanta ce”

Jamilu yayi ajiyar zuciya ya ce,

“Haba ko da na ji, matar ba ta da lafazi”.

Shi dai Muajhid bai tanka ba, yanzu ya shiga fargabar ma da fuskar da zai karbi Nabila, gashi dai ya cika kowa da kurin ai yana sonta ciki har da ita kanta, amma da alama har yanzu dangantakar Yayancin nan na bin sa, kuma kamar yakamata ya ajiye shi gefe kadan don ya faranta mata.

Ta yi mintuna sha biyar kafin ta zo, cikin kasala da kunya, ta yi kwalliya da pink din shadda wadda aka yi wa aiki da shudin zare, babu dankwalin shaddar a kanta sai shudin mayafin da ta dora shi a ka, iyakar kwalliyar kenan ta sa kayan da suka dace da jikinta kuma sababbi, amma fuskarta a bushe ta ke ko kwalli babu bare wata hoda  ko foundation, amma duk da haka ta yi kyau sosai, don yanayin kyanta ba ya buqatar wata kwalliya, ko ba ta yi wanka ba aka dube ta sai an ji bugun zuciya. Mujahid bai taba jin haka ba sai yau, lokacin da ya dago da shirin yi mata kallon qanwa suka hada ido, ta yi qasa da kai da sauri yanayinta a raunane, ta bar shi da jin rauni a zuci, babu shiri shi ma yayi qasa da kan yana wayancewa da cewa jamilu,

“Ga ta, ta gama yauqin ta fito”.

Ganin Nabila ya sa Jamilu dena ganin beken Mujahid na rakito sabon so, ya ma yi jarumta da yake cigaba da mutunta wancan son.

Kan Nabila na qasa ta gaisa da su a ladabce, Jamilu ne yayi mata bangajiya da taro amma Mujahid bai tanka ba, yana can duniyar tuhumar kansa sauyin da yake ji game da Nabila a yanzu, bai taba jin haka a wata mace ba Binta ba, ita ma kafin ta fara daga masa hankali, lokacin da ta fara daga masa hankali nisanta fatansa yake daga kanta, har zuwa lokacin da zata yarda su zama daya.

Daga gaishe-gaishen da ba a rasa ba sai wajen yayi tsit, alamar babu abin fada, Jamilu da rashin sabo, su ma da nasu rashin sabon na sabuwar fuska da suka sami kansu yanzu, daga matsayin wa da kanwarsa zuwa miji da mata babu zato babu tsammani.

Ana cikin haka aka kira Jamilu a waya, kawai sai ya wayance ya tashi ya fita da zummar amsa wayar, alhali rashin sabon ya gano a fuskarsu ya zabgawa wani wansa flashing a saye.

Yana fita kuwa mujahid ya sami bakin magana, ya dubi Nabila cikin kulawa ya ce,

“Ya jikinki”

Kanta na qasa ta amsa a darare,

‘Na ji sauqi”.

Ya dan yi jim sannan ya sake tankawa,

“Kin tabbatar?”

Da sauri ta kada kai kanta a qasa.

Ya sami damar qura mata ido zuciyarsa na harbawa a guje, in haka ake ji idan an ga masoyin da yake so ake sonsa gaskiya Nabila ta fi shi jarumta da ta iya kama kanta, yadda har babu wata fuska da ke bayyana sonta, sannan ta iya riqe alhininta har yanzu tana jaddadawa Muryarsa a dan dashe ya ce mata,

“Amma dai yanayinki na nuna matsala Nabila, kin yarda?”

Nan da nan ta dago kai cikin hawaye ta dube shi,

“Anti Binta Yaya Mujahid, har yanzu ta qi daga wayata”.

Ya jima kafin ya tanka,

“To yanzu me kike so a yi?”.

Ta fara son ta yi shasshekar kuka ya dakatar da ita,

“In dai maganar ta in zauna na saurari kuka ne gara na tashi na tafi”

Nan da nan ta hadiye kukanta ta sake gyara zama kanta a qasa.

A tausashe ya ce mata,

“Kira ta yanzu na gani”

Ta rarumo wayarta da sauri ta shiga kiran Binta, abinda ya daure mata kai sai gashi Binta ta daga wayarta nan da nan.

Tuni ma ta manta akwai Mujahid a wajen ta shiga kuka kamar zata hadiyi zuciyarta tana ba Binta haquri, cewa ta ke,

“Don Allah Anti Binta ki gafarce ni, wallahi tallahi tallahi babu wanda yayi shawara da mu kafin ya yanke wannan danyen hukuncin, ba haka na zaba ba Anti Binta don Allah ki yarda da ni”

Binta ta tattare abinda ya cushe mata maqoshi ta bayar da ajiyarsa gefe, sannan ta amsa muryarta kamar babu komai,

“Haba Nabila kin hana ni Magana.”

Jin muryar Binta a tausashe ya sanya damuwar Nabila ta ragu, ta rage kuka ta ce mata,

“Ina jin ki Anti”

Binta ta sake cijewa ta ce,

“Ki na ji ko? Tun shekararn jiya aka nemi wayata a wajen aiki aka rasa, wayar ba ta hannuna, duk kiran da kike ba ta tare da ni Nabila, sai yanzun nan ta shigo hannuna”.

Nabila ta sauke ajiyar zuciya ta ce,

“Ayya Anti na zaci kin qi daga wayata ne saboda kina fushi da ni”.

Binta ta ce,

“Sam sam akan me zan yi fushi da ke Nabila? Ba Mujahid ne ya hada mu ba, ta yaya zai iya raba mu? Kin sani zan fi kowa farin cikin aurenku, tun kafin ya rakito banzan sonsa ya kawo min ma na sha maimaita miki yadda kuka dace da juna, kar ki damu Ubangiji haka ya qaddara, Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi.”

Nabila ta dinga maimaita cewa,

“Na gode da fahimtar da kika yi min Anti”

Tun da ta fara waya mujahid waje na musamman ya yi wa kansa ya na aikin qare mata kallo, yanayin kyau halinta da ke bayyana a maganganun da take a wayar ne yake matuqar burge shi, da alama shi yake haifar wasu miliyoyin abinda zai iya kira so ne na Nabila.

Da ya ji wannan godiyar ta qi qarewa shi da kansa ya matsa kusa da ita ya zare wayar yana cewa,

‘Haba bar ta haka mana.”

Kawai kuma sai ya kara wayar a kunnensa ya ce,

“To Malama mun gode da fahimta Allah ya saka da alkhairi”.

Kuma bai jira amsar Binta ba ya kashe wayar ya miqa wa Nabila kayarta yana ce mata,

“Ke yanzu fa na fi Binta matsayi da zaki dinga ba ta muhimmanci ni kina watsar da ni, tun da na zo kalmominki kadan na ji a kunnena amma kin sami Binta kina neman shaqewa da magana”

Nabila ba ta so abinda yayi ba, don ba ta da niyyar Binta ma ta san Mujahid na wajenta, ko da kuwa ya fada mata kafin ya zo, ita dai ba ta so a gabanta a nuna ya zo din.

Sai dai salin alin ta karbi wayarta tana juyawa a hannu ba tare da ta daga ido ta kalle shi ba.

Kansa tsaye ya sake wani qorafin,

“Na ji kuma kina fadin wai babu wanda yayi shawara da mu kafin ya yanke wannan danyen hukuncin, wanne hukuncin ne danye, auren?”

Qwallah na sauka a idonta tana girgiza kai, sai dai ba ta yi magana ba.

Ya ce,

“To ki dena fada wa kowa irin wannan kalmar, in ke ba a yi shawara da ke ba ni an yi da ni, ke matsalarki kina tunani akan kowa amma ba kya yi wa kanki, kina son kowa yayi farin ciki amma ba kya so ke kiyi, me yasa?”

Ta dago ta kalle shi a rude, tana son ta canko manufarsa amma tana fargaba, bakinta na rawa ta ce,

“Me yasa ka ce ni ba na so na yi farin ciki?”

Kai tsaye ya amsa,

“Na taba ce miki in na bawa Mutum muhimmanci har ji nake kamar ina iya karanta tunaninsa da muradinsa, na san muradanki da yawa, shin don me kike son lallai sai kin bar wa Binta abinda kike so ko kuma sai kin nuna mata ta fi dacewa da abinda kike so?”

Yanzu a tsorace Nabila take da Mujahid, don har ta miqe ta fara ja da baya, cikin zaro ido, ya san abinda take ji a ranta na game da sonsa, son irin wannan mutumin ta rakito ta kai zuciyarta?

Yana dubanta da murmushi ya daga mata hannu,

“Mu bawa wannan batun hutu har zuwa lokacin da ya dace, zo mu yi magana mai muhimmanci”

Qafarta na rawa ta yi saurin zama kujerar kusa da ita.

Ya gyara murya ya ce,

“Ba na son ki cigaba da dadewa a gida, zaki yi min haquri mu rarruma da abinda ya samu ki tare a gidanki?”

Kallonsa kawai take.

“In kin amince rana I ta yau zaki tare don kar mu yi abinda ake mana gargadi”.

Ta dube shi cikin rashin fahimta,

“Menene?”

Yayi fuska ya amsa,

“Momi ta ce ba ta so ki jima ba ki tare ba saboda kar ki fara yi mata amai a gida”.

Da sauri Nabila ta kife kai a cinya cikin tsananin kunya, tamkar qasa ta dare ta shige ciki haka take jin kanta. Ashe haka Mujahid din yake? Kodayake da tana taka matsayin qanwa ba lallai ta sani ba, sai yanzu da tayi tsallake ta wuce samartaka ta fada aure, shi ne zai bude mata ido gabadaya.

“Wai meye na kunyar?”

Ya tambaya cikin shanye dariya.

Ko motsi ba ta yi ba bare ta yi alamun zata tanka.

Ya miqe tsaye yana duban agogo yana cewa,

“To me kika ce? In kin ga kina son karya doka ki fara aman a gida babu laifi duk da ba haka na so ba”

Ta qoqarta dai ta tanka,

“Ko me ka yi daidai ne”.

“To ki zama cikin shiri kin ji?”.

Ta kada kai da sauri kanta a qasa.

“Ni zan koma”.

Sai lokacin ta dago ta kalle shi,

“Allah ya tsare;”

Har ya fara tafiya ya dakata ya juyo ya dube ta,

‘Babu ko wacce irin kyauta da zan tafi da ita?”.

Ta jahilce shi da ido, ko daya hankalinta bai canko inda ya dosa ba, fahimtar hakan ya sa yayi niyyar tafiya ya qyale ta, amma sai da yayi mata alamar da zai bar ta da ita, inda ya sumbaci hannunsa ya cilla mata.

Bai tsaya kallon yadda take son zama ruwa a wajen saboda kunya ba, kafin ta kama kanta ta wurga tunani.

Amma dai dama ta san,

“Da ganin Kura an san zata ci akuya.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 46Rigar Siliki 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×