Skip to content
Part 53 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Da safiyar Litinin sai farkawa suka yi ba su tarar da Binta ba, dama bai yi niyyar zuwa aiki ba, qiri-qiri yayi niyyar yanka qarya ya bijirewa zuwa aikin, ya dandani zumar zama da Nabila ya ji ba irin wadda za’a bi da ruwan haquri ba ce.

Nabilan ce ta fara zuwa da labarin Binta ba ta nan qarfe takwas bayan ta je gaishe ta, tana neman ta rakito damuwa ya ce mata,

“To menene na fara damuwar ke ba ki kira ta a waya kin ji inda ta je ba?”

Ya je ya dauko mata wayarta ya miqa mata,

“Ungo kira ta ki ji, kar ki fara yi min kuka yanzu tunda nine kika farka ba ki gani ba.”

Tana murmushi ta karbi wayar,

“Ba Kuka zan yi ba Yaya Mujahid”

Ya zauna a kujera ya yi tagumi hannu biyu yana kallonta cikin murmushi.

Sau daya wayar ta yi qara sai ga Binta ta daga, cikin walwalar murya ta ce,

“Yaya qanwata Nabila kin tashi lafiya?”

Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce,

“Lafiya qalau Anti, Na tashi ban gan ki ba.”

Binta ta yi dariya,

“Ai qarfe bakwai da rabi nake fita, Mujahid bai fada miki ba?”

Cikin jin dadi Nabila ta ce,

“Ban sani ba Anti, amma dai zan sha kewa, in dai zan dinga wuni babu ke.”

Binta ta yi dariya,

“Ki sha kuruminki, zan ajiye aiki in dawo gida mu zauna tare, yanzun nan na miqa takardar ajiye aiki…”

A razane Nabila ta ce,

“Amma Anti me yasa zaki yi haka? ba ki ko yi shawara da Yaya Mujahid ba Anti, yaushe zaki ajiye aiki saboda ni?”

Binta na dariyar yaqe ta ce,

“Mujahid shi ya fara kawo batun ajiye aikin saboda ke, kar ki damu ni da shi duk mun damu da ke, zamu yi komai don ki yi farin ciki”

Nabila zata yi magana Binta ta tare ta,

“Kar ki damu kanki, ke dai ko me kika ci ki rage min, zan dawo gida qarfe biyar. ina Mujahid, ba ni shi mu gaisa.”

Sai Nabila ta kasa musu, jikinta sanyaye ta miqawa Mujahid waya, yanayinta ya sa ya toshe Mic. ya tambaye ta,

“Me ya faru?”

Ta kalle shi da kyau,

“Ka daga, cewa ta yi na baka ku gaisa.”

Yana murmushin basarwa ya daga wayar da sallama.

Binta ta amsa a da qoqarin nuna komai ba komai ba ne, sannan ta zarce da cewa,

“Ka yi farin ciki? na yi kyan kai ban dau haqqin buga muku qofa don ka fito ka kai ni aiki ba.”

Ya tuno ranar da ya gasa mata wannan baqar maganar, don haka yayi dariya ya ce,

“Gaskiya kin kyauta, rashin jin dadi daya na yi da ba ki bari mun wayi gari na zo gabanki na durqusa na yi miki godiya ba.”

“Godiyar me?”

Ta tambaya cikin bugun zuciya don tana tsammanin shaqiyyancin nasa zai mata,

Ilai kuwa, yana nuna babu komai ya ce,

“Ok. Kyakkyawan tunaninki zan godewa wanda tun asali ya zabo min Nabila ya ba ni.”

Ta ji wasu tashin hankali na ruso mata a qahon zuci, gaskiya Mujahid dan rainin wayo ne, wato ya kwana da Nabila shi ne ita zai kinkimo cin fuska da safe ya kawo mata? tana jin qumajin qirqirar hawaye, amma daren jiya ta sha yi wa kanta fadan kai zuciya nesa da qaranta damuwa, don Mujahid dai yanzu hankalinsa yayi nisa ba ma ta tata yake ba ta matarsa mai digon gold a goshi yake.

Tuna hakan ya sa ta yi saurin cigaba da dariyar yaqe ta ce,

“In ka gode zan iya qara maka, sai na bar mata ma dukkan kwanana”.

Yayi saurin girgiza kai ba tare da tsawaita tunani ba,

“In kin yi hakan Nabila zata damu da neman ba’asi, abinda ba na so shi ne ta yi damuwa ko wacce iri ce.”

Ta sake hadiyewa,

“To shikenan bayan kwanaki bakwai ka zo dakina ka yi kwanan maneji, amma ina yi maka tayin duk abinda ka san zai faranta ran masoyiyarka ka yi min tayin taimako, zan yi maka.”

Dariya ce sosai ke neman shaqe shi yana yi mata birki,

“Na gode da karramawarki, Allah dai yayi miki sakamako da gidan aljanna”.

Ta cije ta fitar da, 

“Amin” 

Sannan ta sauke waya. 

Yana sauke wayar Nabila ta tambaye shi,

“Yaya Mujahid sai ka ce mata ta ajiye aiki saboda ni?”.

Ya girgiza kai,

“Wannan dalilin nata ne, ni nawa daban, qila ba zata iya fada miki nawa ba ne shiyasa duk ta hada mana dalilin ya zama daya”

Nabila ta kawar da kai tana duban gefe, Rigar Silikinta kenan Mujahid, wanda ba a gane ciki da wajensa. 

Nabila ta sami rayuwar farin ciki kamar yadda ta sha zato a Mujahid, yayin da Mujahid ya sha mamaki, domin shi ya sami fiye da abinda ya zata ko yayi fata, don kafin Nabila ta matso kusa da shi ya zaci zaman alfarma kawai zai yi da ita, sai da ta fara matsowa kusa da shi sannan ya fara fahimtar ashe mugun shiga rai ne da ita, ya sha tuna wata maganar Binta ta cewa, Ba irinsu Nabila ne matan da ake kalla a ce ba a so ba, ya yarda da wannan zai kuma iya bayar da shaida ko dan gaba, irin su Nabila in suka sami zuciya ba sa yi mata da wasa sai sun mallake ta tas yadda ba ta iya tuna komai sai nasu.

Aka sami gagarumin canji a tare da shi, a walwalarsa ta gida da ta waje, kuzarinsa da gabbansa yanzu duk sun taso suna nuna sun sami abinda ke sa su farin ciki, ta yadda a kwana bakwai babu yadda za a gan shi ba a ce yayi kyau kuma yayi qiba ba.

Binta na gefe tana kallon abin al’ajabi tana danne damuwa da kora ta da ruwan haquri, Tana ji tana gani Mujahid ya mayar da ita tamkar wata uwar miji ko wata yar gida, duk da dai ba ta wuni a gida, amma ba ta kasa gane yadda ake rayuwar tabara a gidan, da wahala ta ji motsin Mujahid kafin fitarta aiki, sannan idan ta dawo tana tarar da shi a gida, ta fara tunanin ko ma ajiye aikin yayi oho masa.

Abin takaici sai ta dawo Nabila ta taho wajenta sai ya debo tsawo ya biyo ta, su share waje su yi ta mata shirme tana kannewa, har sai dare zai raba su, su haye samansu su bar ta da kukan zuci da na fili.

Sai kuma wata yammacin, babu komai a tsakaninta da mujahid sai wannan karramawar, in babu Nabila sai ta kwana ta yini ma bai kawo qafarsa qofar dakinta ba.

Wannan ba qaramin damunta yake ba, amma dai tana iyakar qoqarinta na sharewa ta boye a fuska, yadda har shi Mujahid mai siyasar da qoqarin cankar abinda ta boye ya fara laluben manufarta a kansu. Yana dan jin damuwa jefi-jefi a rai, duk da Nabila na tafiyar da ita.

Ranar da ta karbi girki dukkansu cikin alhini suke shi da Nabila, ita zata shiga cikin kadaici, shi kuma zai tafi wajen Binta ya zama maraya yadda qila ma kalma daya ba zata shiga tsakaninsu ba a tsawon dare bare wani abu na sanya juna nishadi, yana son Binta amma yana kewar rashin kyautatawa daga gareta tabbas, sai yanzu ya fahimci hakan.

Har shadaya suna tare har Nabila a dakin Binta suna hira, sannan Nabila ta yi musu sallama shi kuma ya kore kunyar idon Binta ya raka ta har gadon baccinta yana bin ta da rarrashi ita kuma tana ta dariya tana nuna ba komai, sannan yayi mata sallama ya dawo wajen Binta.

Ya same ta har lokacin tana zaune a wajen da ya bar ta fuskarta babu yabo babu fallasa, amma yana qarasowa tsakiyar falon ta dago da murmushi ta ce masa,

“Na ce maka ka je da kwanakin ka qi, ka ga daga kai har ita ai yanzu da ba ku yi jan ido ba.”

Yayi murmushi kawai ya nemi guri ya zauna ya daki remote din Tb ya hau binciken tashoshi.

Tsawon lokaci babu wanda ya tankawa wani, shi bai iya labarin komai ba sai na so ita kuma ta ce kar ya sake ba ta labarin so, kar ma ya sake cewa yana sonta, gashi kuma son na bijiro masa, dan ma nata taurin kan na dakatar da shi.

Har lokacin da Binta ta miqe da alamun shiga barci, kuma cikin sakewa ta ce masa,

“To Ranka ya dade sai da safe.”

Ya bita da kallo har ta fara tafiya, da alama hankalinta kwance yake, sai ga shi cikin kuzari ya taka ya bi bayanta,

“Yauwa ji mana Anti”.

Ta tsaya ta juyo suna fuskantar juna, babu wani yanayi da zai iya fayyace yadda ta karbi kalmar Antinsa a fuskarta.

Shi ma ya maze,

“Bisa sharadin nan rannan yakamata na yi tambaya amma na sha’afa”.

Ya sake gyara tsaiwa,

“Yi tambayarka ina jin ka, amma dai ka sani duk tambayar da zaka yi sharadin ba zai jany ba.”

Ya amo kafadarta da hannu biyu yadda suka fuskanci juna,

“A’a ba cewa zan yi a janye ba, amma dai akwai buqatar qarin haske”.

Ta cigaba da kallonsa kawai zuciyarta na bugawa da dalilai biyu, dalilin kusancinsu hade da murza mata kafada da kuma na tuna yadda yake runtse ido da yayi sati guda ya zuba ta a kwandon shara, amma yanzu don kunya ba ta ishe shi ba ya zo zai raina mata hankali.

Ta daure ta ce,

“Ina jin ka”

Ya amsa,

“Ok, dama dai ba na ce miki My lobe, to Anti zan dinga kwaso miki ko kuma  Gwaggo? Na ga kin shiga wani acting na son duk mu dinga yi miki kallon wata yar gida, gaskiya kaina ya dan shiga duhu”

<< Rigar Siliki 52Rigar Siliki 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.