Skip to content
Part 57 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Duk da cikin kiciniyar biki ne Hajiya ba ta fasa lalubo Binta sun kebe ta tuhume ta rashin ganin Nabila ba,

“Allah sa dai Binta ba halin naki kike nuna wa yarinyar nan ba, me yasa na gan ki ke kadai?”

Binta ta ji daci da tuno yadda suka yi da Mujahid akan zuwan Nabila bikin Yaks, sai dai iyakarta kenan, ko zata iya bawa Hajiya labarin ba zata iya bayar da shi yadda za’a ga laifin Mujahid a yanzu ba, sannan ko da zata bayar da labarin ma ba lallai Hajiya ta yarda da ita ba tunda akuyarta ta riga ta yi kuka.

Tana dariya ta amsawa Hajiya,

“Babu yadda ban yi da shi ba Hajiya ya ce shi kishi ne da shi ba zai iya barin matarsa ta zo bikin Yaks ba, sannan ma ba ta da isasshiyar lafiyar da zai bar ta gararin biki, abinda ya ce min kenan, shi mai mata, don kawai ya sami dama ya fi ni iko da Nabilar”.

Hajiya ta yi tsam tana kallon Binta sai ta fahimci da zuciya daya take magana ba don ta munanawa kowa ba, Binta ta burge ta da ba ta saka kishin Nabila ya dami ranta ba, don haka ta ji haushin da take ji nata ya ragu da kaso mafi rinjaye, ta janyo waya tana cewa,

“Ai duk ke kika bi kika ruda Mujahid wallahi, qarfi da yaji kin canja masa dabiu”

Binta murmushi kawai take tana kallon Hajiyar ba tare da tankawa ba.

Mujahid da Nabila fitowarsu kenan daga asibiti sun sake komawa ganin likita saboda yawan amai da Nabilan take, ya dauki hanyar da zasu koma gida kenan kiran Hajiya ya shigo wayarsa, ya daga cikin ladabi suka gaisa, ta ce masa,

“Ban ga Nabila a gidan yinin nan ba, don me ka hana ta zuwa? daurin aure ne bare ka ce zata ga Yaks, ko kuwa kai ma kana nufin ba zaka je daurin auren ba gobe”.

Tamkar dama yana shirye, tana rufe baki ya amsa mata,

“Ayya ba haka ba ne Hajiya, mun je boto ne dubo Baba, kin san bai ji dadi ba, to ni na je, cikin Binta da Nabila kuma babu wanda ya sami zuwa duba shi, muna ta saka rana ana canjawa saboda sabgogi shi ne yau daga asibiti na ce mu zarce kawai”.

Yana magana da Hajiya cikin tuqinsa yayin da tuni yayi kwana ya dau hanya.

Ba wani ja Hajiya ta yarda da batunsa, kuma tana sauke waya ta labartawa Binta yadda aka yi.

Binta ta yi kamar ba ta ji komai ba ne, amma gaskiyar magana labarin ya taba ta da kyau, tabbas ta san cewa Babansa bai ji dadi ba, amma sam ba ta da labarin yana shirya su je su duba shi, yanzu ne dai yayi niyyar hakan don dalilin da shi kadai zai iya tabbatarwa, wala Allah don yana zaton in yace ta zo su je ta ce ba zata ba, ko kuma don yana jin haushin baqar maganar da ta fada masa game da Babansa a kwanakin baya, don haka yake da shirin nesantata da Baban nasa.

Ko ma meye amsar ita zata gyara ta yadda zata yi wa rayuwarta da kunnenta dadi, ba ta yi shawara da kowa ba ta sulale daga gidan bikin kai tsaye kuma ta yi shatar mota da zata kai ta boto qarfe uku daidai.

Ba qaramin kaduwa Mujahid da ke gaban Mahaifinsa suna hira daga shi sai mahaifin nasa a dakin, ya jiyo ana marhababin din zuwan Binta a tsakar gida, ya kwashi mamaki nesa ba kusa ba.

Mahaifinsa ya daga kai ya dube shi cikin tuhuma,

“Yaya haka? Da zata zo amma ka qi hado kansu ku taho tare? Sai kawai ka dauko amaryarka ita kuma ta taho ita kadai?”

Duk lauyar Mujahid ya rasa da basirar da zai kare kansa ko ya kare Binta a wannan bangaren, don haka ya dinga kame-kame alamun rashin gaskiya har zuwa lokacin da Binta ta yi sallama ta shigo dakin da zummar dubiya.

Ko duban inda take Mujahid bai yi ba, ita ma ba ta damu da duban nasa ba tana cike da ladabi ta gaishe da mahaifinsa wanda ya sa idon nazari kawai yana karantarsu, ta yi masa Jaje rashin lafiyarsa tare da bayana-bayanan dalilin da ya sanya ba su sami zuwa akan kari sun duba shi ba.

Mujahid dai ko motsi bai yi ba, saqe-saqe kawai yake a ransa yana tunanin ta inda zai kwance qullin Binta in har wani qaharun ta qullo kenan da wannan zuwan titsiyen nata ba tare da izininsa ba. Sai kuma ya ga har ta gama sunkuye sunkuyen kanta ba ta nuna wani alamu na cin zarafi ko fuska gare shi ba.

Sai da Babansa ya gama karantarsa sannan kai tsaye ya kutso da nasiharsa ga Mujahid,

“Na so ka dore daga sanin da na yi maka tun kana qaraminka kan adalci da riqon amana, ni ban taba sa maka ran akwai wani qyalli da zai saka ka juya baya ba”.

Daga Mujahid har Binta sun kai gano kan manufar Mahaifin Mujahid, zarginsa yake da fifita Nabila akan Binta.

Mujahid ba shi da cewa, dole yayi qasa da kai, yayin da hankalin mahaifinsa ke kansa, Binta kuma sai ta saki baki kawai tana kallon mahaifin nasa, shi ta sha yi wa kallon azzalumi, amma ga shi da alama shi yake son a mayar da ita ‘ya ba baiwar gidan miji ko wata aljihun baya ba. Komai fa ya zo mata a bazata.

Tana ta kallonsa yana surfe dansa da fada da nasiha, cikin jirwaye me kamar wanka duk na karrama ta, har da gwada masa idan ya wulaqanta Binta Mahaifinta ba zai ji dadi ba, kuma har ga Allah ma an saka masa alkhairi da mugunta.

Ko kadan Mujahid bai nuna musu ba, ya zauna sosai nasihar ta shige shi, daga qarshe kuma ya daukarwa mahaifinsa alqawarin duk zai yi abinda ya umarce shi, ya roqi alfarmar sanyawar albarkarsu sannan yayi sallama da shi ya riga Bintan ficewa, sai ta rasa da qwarin gwiwar da zata tashi.

Jigum-jigum suka dawo gida duk cikinsu babu mai sukuni, Nabila lafiya ba ta ishe ta ba, kishingida sosai ta yi cikin kulawarsu duk ta yi bacci, sai da ta yi baccin suka huta da yi mata sannu, sannan motar ta dauki shiru tamkar an shiga maqabarta.

Ba zato babu tsammani Binta ta ji Mujahid yayi mata magana cikin rashin walwala,

“Binta meyasa kika biyo mu ba tare da sanina ba?”

Bai jira ta amsa ba ya zarce da wata maganar cikin rauni,

“Kullum cikin girmama alaqa tsakanina da Iyayena nake, ko ba ni da kyan hali a wani wajen ina qoqarin na sabunta a wajensu, kuma na san ke ma dai in bisa adalci ne ba zaki dorar da munin halina ba Binta, me yasa kullum kike son sai ta hanyarki zan gwada rashin kirki?”

Duk ta daburce sai kallon qeyarsa kawai take tana kuma kallon Nabila a tsorace, ta madubi ya hangi fargabarta ta Nabila kar ta ji zancensu ne. muryarsa a sarqe kuma a dashe ya ce mata,

“Tana da nauyin bacci”

Binta ta yi ajiyar zuciya kawai ta kasa ce masa komai, matsalarsa yanzu ba ya duban qwayar idonta ma bare ya hango canjinta ko kuma jaririn sonsa da ta fara raina.

Ya gaji da shirun nata sai yayi ajiyar zuciyar shi ma ya ce,

“Amma ba komai, ni da zuciyata dama mun saba aiki daban daban, gabbaina su aikata daban zuciyata kuma wani daban take aikatawa…”

Ya dan dakata ya shaqi iska sosai sannan ya kada kai cikin dashewar murya ya ce,

“Dalilin abinda ya faru zan sake fada miki abu daya da zuciyata da bakina ke iya hada kai, wato sonki, ina sonki ba bisa ko wacce irin Alfarma ba sai ta Jalla da ya jarrabe ni da son, ba albarkacin kowa kike ci a qarqashin rayuwata ba, adalcin ubangiji ne a cikin riqon da nake miki, shi ya sa min sonki kuma ya hana ni cutar da ke idan ba ki zama tagari ba, don haka ya rage naki ki san ke kuma irin riqon da zaki min, ko ban ci albarkacin komai kin bar ni da halayya tagarin da kowa ya shaide ni da ita tun fil azal ba, kin bari na ci albarkacin don in kin je kabarinki ki same shi a share”.

Daga haka bai sake qoqarin ce mata komai ba, sai ya mayar da hankali kan Nabila wadda yake duba akai akai, ko kuma in ya ga ta lauya wuya ya gyara mata.

Binta ta sunne kai a mayafi ta dinga tirkar kukan da hadiye shi kawai shi ma abin sanya wani kukan ne, tana kukan murnar Mujahid ya dawo da jaddada mata so, sannan tana kukan kishin ya raba mata so da Nabila yadda har zai iya gama fada mata so a fatar baki sannan ya koma ya cigaba da bawa Nabila kulawa, ita biyu ya hada mata, labarin yana sonta a fatar baki sannan da nuna mata son a aikace.

Bai gama bata mamaki ba sai da ya tsayar da mota a qofar gidansu sannan ya juyo ya ce mata,

“Ki bude motar ki fita a hankali don Allah, zan jira ta ta farka, bai kamata a tashe ta ba, jiya ba ta sami baccin kirki ba”

Salin alin ta hadiye kukanta ta kwashe shi zuwa cikin gida. Shi kuma bai damu ba ya kwantar da kujera ya kishingida cikin tunani barkatai, gabadaya zuciyarsa a rude take, rigar silikinsa ta fi kowa iya Manuba, yana da tabbacin ba don Nabila ta shigo rayuwarsa ta kawo masa dauki da sonta da farin ciki ba, qila da yanzu ma ya zama kwarkwar.

Sai lokacin ya tuno da maganar Alhaji da ya ce masa nan gaba zai dawo ya gode musu bisa aura masa Nabila da suka yi, gashi nan kuwa tun  ba a je ko ina ba ya fara sanya musu albarka a zuci, ya ma kamata ya wanke qafa takanas ya je ya sake gode musu.

Bayan Binta ta yi kwanan damuwarta, ta sake sabunta zuciya da son canji, tare da mayar da rayuwar baya mafarki, ta qara haba-haba da Mujahid, sai dai shi da alama sam ba ta gabansa, cikin damuwa yake Nabila babu lafiya.

Da ta ga haka sai ta yi dabarar qara shiga hidimar Nabila, wannan ko dabarar ta ci ya fara ba ta hankalinsa, da wannan dabarar kuma ta dinga aika masa saqoonin da dole ya fara karba, sai dai shakku ya hana shi ko wanne irin katabus. Sai ya dinga watsa komai kwandon shara.

Rannan da yamma ya dawo gida da shirin kadaici, don ya kai Nabila gidansu, kuma sun yi sai dare zai je ya dauko ta. Da wannan jin haushin kadaicin ya dawo gida yana azamar yayi wanka ya je gaishe da Alhaji, kuma a yau ba sai gobe ba sai ya fito fili yayi masa godiyar da ya zata masa idan ya zauna da Nabila.

Sai da ya shirya ya fito sannan ya tarar da Binta a falo, ta ci kwalliya kuwa, ta sami arziqin yayi mata kallon sakan talatin a lokaci guda, hakan ne kuma ya sanya halittar sonta da ke qirjinsa ta motsa tana son nuna shan sharafi, kamar zai je gareta ya amayar mata son ko kadan ne, sai kuma ya tuna kamatar cigaba da kama kansa, in dai macace a fadin duniya babu irn wadda Nabila ba zata iya cike masa gurbinta ba.

A tausashe Binta ta ce masa,

“Ina za ka?”

Ya ji tambayar wata daban, amma dayake kansa ba a riqe yake sosai ba sai ya ji cikin raunin murya ya amsa mata,

“Gida zan je, kina da saqo ne?”

Ta girgiza kai da sauri,

“A’a, amma ina son na raka ka”

Yayi saurin kada kai,

“Ki zo mu je”

Da azamarta ta tashi ta je ta dauko mayafi suka fita tare.

Tafiyar mai dadin gaske a wajensu duka, duk da kuwa babu hirar kirki a tsakaninsu.

Sun kusa isa gidan Binta ta daure ta tambaye shi,

“Wai ma me zamu yo ne? gidan nan fa ya zama na hayaniya, in na je ba sa murna da ganina”.

Ya dan yi tunani kafin ya amsa cikin murmushi ba tare da dubanta ba,

“Kawai na yi sha’awar zuwa…”

“Haka kawai ni ban yarda ba, ba gaskiya ka fada min ba”

Ya sake jimawa cikin nazari yana murmushi, ya sauke numfashi ya ce,

“Eh to gaskiya kin canka, abinda zai kai ni wataqila in na fada ba zai miki dadi ba”.

Yayi tsammanin ganin gizago fuskarta, amma ga mamakinsa sai ya ga har yanzu tana da walwala,

“Kuma ni gaskiyar nake son ji ba, ka daure ka sanar da ni”.

Sai kuwa yayi fuska ya fara amsa mata,

“Da na dawo gida ban tarar da Nabila ba sai kawai na ji wani matsananci kadaici ya rufe min zuciya ya kuma baqanta ta, wannan ya sa ni tuna muhimmancin Nabila da wata kalma da Alhaji ya fada kafin nemo min aurenta, ya ce min in na aure ta sai na zo na gode masa saboda kyakkyawan zatonsa na yadda zata sanya rayuwata farin ciki…”.

Ya tsagaita da shakar numfashi, sai kallonsa take cikin bugawar zuciya da jin dardar, bai damu da cudewarta ba ya ci gaba,

“Don haka na wanke qafa zan je in jaddada masa alwashin da ya ci, Nabila ta taimaki rayuwata gaskiya, da na rasa ta da na rasa irin son da nake miki, da na rasa ta kuma da na rasa irin farin cikin da na sha yi wa aurena tanadi, da na rasa ta duk burina na haihuwa qila da ban fara danbar cika shi yanzu ba, Nabila ta zama bangon rayuwata ita ce rabina, duk wanda ya taimake ni na same ta har in mutu ba zan fasa yi masa godiya da addu’ar fatan alkhairi ba, cikinsu kuwa har da ke.”

Fuskarsa da zuciyarsa duk da gaske suke, Binta ta hango wannan a tare da shi, don haka kuka ya qwace mata duk da ta yi qoqarin ta riqe kanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 56Rigar Siliki 58 >>

1 thought on “Rigar Siliki 57”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×