Skip to content
Part 8 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Dukkan su ukun jinya suke har aka shude sati uku, tuni Nabila ta gama hutunta ta tattara kayanta ta koma gida, ta koma bakin darasi.

Da ma kamar ta fi su shan wuya a jinyar, domin ita tana jinyar abu uku ne, mayataccen son Mujahid wanda ya kamata a ce daga shi aka qago sunan maita ba wai shi kansa a danganta shi da maita ba. Sai abu na biyu, ciwo da takaicin yadda ta furta kalamin da ya tona asirin zuciyarta a kan Mujahid din ga Binta, don tana da yaqinin wannan nakasu ne a matantakar da ita aka sani da gadon kunya, kuma qila zai iya rage mata qima a idon Mujahid din, idan har Binta ta yi gigin yi masa irin tallan da ta yi mata.

Abu na qarshe na jinya a zuciyar tata shi ne, yadda Yaks ya bude wutar nacin nuna wa duniya yana sonta, yadda ta kai har Hajiya na son shiga maganar inda ta ce mata.

“Nabila qila fa in ki ka daure ki ka auri Yakubu ki yi jihadin raba shi da halayen wofi. Na fahinci son da ya ke miki ba kadan ba ne”.

Da za ta iya tanka wa Hajiyar ce mata za ta yi, Zan yi jihadi ta wata hanyar ba ta hanyar auren Yakubu ba”.

Amma da ya ke ba za ta iya hakan ba, da ido kawai ta bi Hajiyar, kuma a washegarin ranar ne ta balle lambar cewa, gidansu za ta koma, alal a qalla abin da ta zo domin shi wato Mujahid, wahalar samuwa gare shi.

Jinyar Mujahid daya ce, shi ne, ta ina zai bi ya samo kan Binta? Da alama kuma yana ganin yanzu zafi ya ragu, tunda Nabilar da ta ke ta kokawar aura masa bisa dole likin Yaks ne ke sonta ya balle a gabansa, idan dai ba idonta da bakinta sun cika rashin kunya ba ya san da wahala ta sake keta idonsa ta ce masa ya so Nabila.

Binta ce ta biyu a ciwo, domin nata ciwon biyu ne, na zargin Mujahid ita ya ke so, da kuma zargin yadda ta buntsulo da son da Nabila ke wa Mujahid fili, idan Mujahid ya furta ita ya ke so wanne duba Nabila za ta yi mata? Idan kuma wata daban can Mujahid ya ke so ta wacce hanya za ta wancakalar da gwamnatin waccan ta kafa na Nabila?

Kullum da neman amsar wadannan tambayoyin ta ke kwana ta ke tashi, kuma hakan ne ya jaza mata yawan kadaici da zaman daki yadda haduwa da Mujahid ta yi mata wuya, duk da cewa  shi ya ke nemanta ido rufe fiye da yadda ta ke nemansa, duk lokacin da za su hadu sai ya zama haduwa ce ta shaf-shaf kuma a idon mutane.

A haka har aka shiga sati na hudu.

Rannan Nabila ta kira ta da rana musamman, ta ce mata.

“Anti kiranki kawai na yi na gaishe ki”.

Wani dunqulelen abu ya tokare wa Binta a maqoshi ta ji tamkar za ta kece da kuka, a zatonta tunin Mujahid da Nabila ta ke mata.

A nan ta ji babu mafita sai na ta ketawa Nabila qarya.

“Kun  yi waya da Mujahid?”

Tambayar da ta yi wa Nabila ke nan cikn dakewa tamkar da gaske ta ke.

Nabila ta ji wasu abubuwa masu yaji sun ruso mata a qahon zuciya, tamkar ranar farko da Binta ta ce mata ta ga alamun Mujahid na sonta. Bakinta na rawa ta ce.

“A’a, ya ya aka yi?”

Wannan tambayar ta qara gaskata wa Binta cewa, don Mujahid Nabila ta kirata ta gaishe ta.

Dole ta tilasta kanta basar da damuwa a murya ta ci gaba da keta wa Nabila qarya.

“Satin da ya wuce kawai ya tare ni in ba shi lambarki, ban san abin da ya hana shi kiranki ba…”

Nabila ta danne dukkan son Mujahid da ke hanqoro a qirjinta don yin abin da ya dace.

“Ina fatan ba ke ki ka yi masa wata magana a kaina ba”.

Binta ta yi turus, amma dai ta daure ta wafto abin cewa.

“A’a ba ni na yi masa magana ba, to ma laifi ne idan na yi masa maganar?”

Cikin karaya Nabila ta ce.

“A’a Anti, kawai dai ba neman miji nagari na ke ido rufe ba, duk wanda zai zama mafi alkhairi gare ni ina so ba wai sai Yaya Mujahid ba… Ma’ana neman mijin qwarai da na ke bai azalzale ni yadda zan yasar da matantakata in ce ina son namiji ba…”

“Ni ma ba zan bi wannan turbar ba Nabila, don Allah ki yarda da ni”.

Da sauri Binta ta tare Nabila da fada mata haka, don ganin kamar tana gargadinta tabargazar da ta riga tuni ta yi mata.

“Ki yi haquri Anti, wallahi na yarda da ke Anti, kawai haka kawai ni zuciyata ta kasa nutsuwa ne… Na ga kamar na yi abin da ban kyauta ba…”

Nabila ta fada a sanyaye saboda ganin kamar ta nuna wa Antinta gazawa.

Cikin rashin abin cewa Binta ta daure ta ce.

“Da ki ka yi me?”

Nabila ta yi qaramar dariya.

“Kawai ya wuce, Anti a gaida min duk jama’ar gidan nan”.

Binta da sallamar Nabila ta fi yi wa dadi, saboda son zurfafa nazari ta yi saurin amsa mata.

“Za su ji da kyau, don Allah in kin ga baquwar lamba kar ki dagawa”.

Dariya kawai Nabila ta yi ta kashe wayar ba tare da ta tanka ba.

Haka ta wuni wasuwasi da lissafin ta yadda za ta daidaita wannan Rigar Silikin da ta yayimo wa kanta ta yafa.

Qarfe goma na dare ta raba kanta da lissafin saboda rashin samo amsa ta rakito wayarta ta fada yanar gizo, a whatsapp ta ci karo da lambar Mujahd kawai ta yi qunar baqin waken tura masa, “Salam”. Bayan ta lura yana online, ko sakan talatin ba a yi ba sai ga shi ya turo mata gwaigwai mai idon love hadi da amsar sallamarta.

Duk da ta yi muguwar kidimewa ba ta fasa jin su dore da hira don a yi ta ta qare a yau din nan, ta gaji da dakon fargabar da ta rakito wa kanta.

Bayan ta gama jimaminta ta tura masa nata gwaigwai din wanda ya zaro ido hade da alamar tambaya.

Nan ma bai bata lokaci ba ya turo mata yatsa mai alamar nuni.

Ta fahince shi tsab, amma sai ta ninke shi baibai ta hanyar tuna masa cewa.

“Na aika mata”.

Nan da nan sai ga raddinsa na tambaya.

“Wa?”

Ta amsa.

“Nabila, ba ka da lambarta me ya hana ka tambaye ni na ba ka yadda ba sai ka sha wahalar aiko min da saqon kana sonta na tura mata ba”.

Duk da ya ji haushin tana turbuda masa manufa a kwandon shara bai fasa aiko mata  alamar murmushi ba, bai jira ba ya sake turo mata.

“Kin manta dukkanmu musulmi ne?”

“Na yi wani abu mai kama da ridda ne?”

Ta tambaye shi.

Bai damu da amsar tambayarsa da ta ba shi mai kama da baqar magana ba ya turo mata da nufinsa.

“Manzon Allah (S.A.W)  ya haramta wa musulmi ciniki cikin ciniki, ko nema cikin nema”.

Ta san inda ya dosa, amma ta basar.

“Wani gida ka hango ka ke son siya ka tarar wani ya riga ka?”

Nan da nan ya aiko mata da amsa.

“Ni gidan da na hango na ke son siya babu kowa a hanyar, gidan da ki ke son tilasta ni siya ne na gano cewa akwai wani mai son, gidan da ki ke son tilasta ni siya ne na gano cewa akwai wani mai son gidan bilhaqqi”.

“Ka qaraci zaurancenka”.

Abin da ta iya rubuta masa ke nan.

Ya turo mata alamar dariya.

“Ni na tabo ka ne don mu yi zancen Nabila”.

Ta share dariyarsa, ta tura masa wannan maganar.

Ya aiko mata da cewa.

“Nabila da Yaks”.

Ita ma ta rubuta masa.

“Nabila da Mujahid dai”.

Ta kusa minti daya tana jiran cewarsa, sannan ya ce din.

“Wai kuwa kina da imani da tausayi?”

Ita ma ta yi jinkiri kafin ta amsa masa.

“Allah ne kadai zai iya shaidar ina da su ko babu, tunda ba lambobi ba ne balle ka ce ba ka gansu manne a goshina ba”.

“To kina da tabin qwaqwalwa”.

Ya aiko mata hade da gwagwai  din da ke nuna bacin rai.

Nan da nan ta tura masa.

“Duk biyun na hada kawai, rashin imani da hauka…”

“Gaskiya ya kamata a bincika”.

Ya sake aiko mata wannan baqar maganar hade da alamar nuna fushi.

Yanzu ranta ya soma baci, don haka nan da nan ta tura masa alamar sallama hadi da cewa.

“Da alama shirin kamawa da wuta ka ke saboda fushi, gara na yi ta kaina domin ni jona rayuwata na ke ba na yarda matsalar wani ta shafe ni. Mu kwana lafiya”.

Duk da ta yi hanzarn kashe data bayan ta tura masa saqon sai da amsarsa ta shigo.

“Ga shi ke kanki matsala ce ba, kin kyauta da ki ka yi min bankwana”.

Ta dinga jin wani matsanancin fushi tamkar ita ma shirin kamawa da wutar ta ke, zuciyarta ta dinga ingiza takunna data ta fesa masa rashin kirki ita ma, sai kuma wata zuciyar ta dinga haqurqurtar da ita tana tuna mata cewa, duk ma’abocin fushi ba ya cin riba. Wannan ya sa ta  yi lamo kan gado tamkar mai baccin  cikin runtse ido da jin qyashin zubar da hawaye. To a kan me ma za ta yi kuka? A kan Mujahid zai ce yana sonta, ko kuma a kan yana cewa qin Nabila ya ke? Duk dalilai biyun sun cancanci ta yi musu kuka, domin zafin son cimma buri ne da zafin qin Mujahid ya rikito so ya kawo mata.

Tana nan kwance har jikinta ya yi la’asar bacci ya fara surarta, saboda mutuwar jiki. Da qyar ta lallaba ta wanke baki ta dawo ta bi lafiyar gado, a fili tana mita.

“Haba Mujahid, ai ka yi kadan ka jaza min hawan jini, ba ka isa ka dami rayuwata ba wallahi.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 7Rigar Siliki 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.