Sanadin ke nan da ya sa daga wannan rana Binta ta zaga tutar boye wa idanuwan Mujahid, ga shi dai gidansu daya, amma duk hanyar da za su hadu sai da ta bi ta toshe, sannan yawan cushewar aikinsa ma ya sauqaqa mata boyen da ta ke masa, don ya kan fice daga gida tun takwas na dare, kuma ba ya dawowa sai bayan magriba, in an ganshi a gida qarshen mako ne, shima ba duka ba, don tana zuwa masa da ziyarce-ziyarce ko daurin aure, in ma babu ya kan yi zaman karatu.
A haka sati uku. . .