Skip to content
Part 9 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Sanadin ke nan da ya sa daga wannan rana Binta ta zaga tutar boye wa idanuwan Mujahid, ga shi dai gidansu daya, amma duk hanyar da za su hadu sai da ta bi ta toshe, sannan yawan cushewar aikinsa ma ya sauqaqa mata boyen  da ta ke masa, don ya kan fice daga gida tun takwas na dare, kuma ba ya dawowa sai bayan magriba, in an ganshi a gida qarshen mako ne, shima ba duka ba, don tana zuwa masa da ziyarce-ziyarce ko daurin aure, in ma babu ya kan yi zaman karatu.

A haka sati uku ya wuce, sai a na hudu Nabila da tuni ta gama fatali da jiran jin saqonnin so daga muryar Mujahid. Ta yi ta jaruman mata, ta kori ‘yar halittar sonsa da ta ke jin ta maqale mata, ba kora ta haqiqa ba, illa korar jin qarfin hali da kamfatar rayuwarta ko babu son, ta nemi asabar ta kawo ziyara.

Hajiya ta karbe ta da murna sannan ta zarce da yi mata wasa,

Yakubu ba ya kyautawa, qarfi da yaji yana son kore mana ke daga gidan nan

Nabila ta yi dariya ta ce,

Haba ba shi ba ne, kawai dai ban sami sukunin zuwa ba ne

Hajiya ta yi dariya,

Sai ki shiga ki sami Antin naki, tana nan ta canja kala, da alama wani Game din ta lalo

Ummi na gefe ta ce,

Hajiya ashe ma kin lura Anti Binta ta canja, da safe na dinga tambayarta ko bata da lafiya amma taqi bawa tambayar tawa muhimmanci

Hajiya ta kada kai cikin shanye takaici ta ce,

Ai ba zata iya fada miki ba, tunda ba zata iya fada miki gaskiya ba

Cikin rudu Nabila ta bar su ta doshi dakin Binta cike da wasiwasi, ita kuma Anti Binta meye matsalarta? Alhalin zuciyarta jaruma ce so ba ya iya yi mata komai.

Ta sami Binta cikin kasala tamkar wadda ta yi jinyar shekara, sai dai duk inda siyasa take ta yafito ta ta binne damuwarta da ita, ta dinga nuna wa Nabila fuskar ai babu komai. Sai Nabilan ma ta bi a haka, suka wuni suna hira babu wanda ya kawo maganar Mujahid ko ta Yaks.

Amma Binta a can qasan zuciyarta ta sanya ido a shige da ficen kowa a gidan, Mujahid kawai take son gani ta shirya  masa tuggun da ta haqiqance dole ma ya zurma.

Sai dai duk cikin masu shige da ficen babu Mujahid, hakan ya tabbatar mata bai wuni a gidan ba, abin da kuma ya hana ta sukuni ke nan, don yau ta shirya a yi bugun daga kai sai gola a maganar Nabila.

Qila cikin ‘yaammatan gidan an sami mai guntsawa Yaks cewa, Nabila ta kawo ziyara, qarfe biyar na yammacin ranar sai ga shi ya yi wa gidan tsinke, sai dai ya dogare daga can waje ya hau kiran aminiyarsa Binta, duk da ba ta yi masa rana a makauniyar soyayyar da zuciyarsa ta rakito masa.

Yana jingine da motarsa ta fito tana kwasa masa dariya.

“Ko ka sake wani wawan kamu ne a gidan nan da ya qara zama na surukanka?”

Ta fada bayan ta qarasa gare shi cikin tsananta dariya.

Duk yadda ya so ya zama cikin nishadi kamarta ya gaza, kololin yaqe iri-iri ke tashi daga kan fuskarsa da sunan fara’a da dariya.

“Idona ba ya iya ganin kowa sai Nabila, ita na sami labarin ta bayyana”.

Ya fada da rarraunar murya.

Binta ta amsa masa cikin ci gaba da dariyarta.

“Ai na san in don ita ce kai tsaye za ka shiga gida, ko don ka yi arba da ita a ba-zato hankalinka ya kwanta”.

Yaks ya lashi busasshen lebensa fuskarsa na nuna alamun dauriya.

“Ba in dinga arba da Nabila kawai ne burina ba Binta, kin sani aurenta na ke son yi, wannan damar ta hana ni don ita ta ke iyawa, ganinta ko ta qi ko ta so ai ina iyawa”.

Binta ta ci gaba da dariya da yi masa kallon zolaya.

“Yanzu nan tattago nin da ka yi auren naku zan daura?”

Dole Yaks ya yi dariya, ya miqa mata hannu wai su tafa, amma sai ta ba shi harara, bai damu ba ya ci gaba da cewa.

“Wayyo, da ma za ki iya hakan, lallai duk duniya sai na fi kowa alfahari da dangi”.

Yanzu Binta ta kasa hankalinta biyu ne, daya na tare da Yaks, daya kuma na tare da Mujahid wanda ba ta fahinci lokacin da ya shigo ba, amma dai ta hange shi can zaune cikin motarsa ransa a matuqar bace yana qare musu kallo.

Ta kawar da kai ta ja numfashi ita kuma zuciyarta ta ja ta lissafin dalilin kallonsu da bacin rai da Mujahid ya ke. Nan da nan ta canko kallon kishi ne mai qona zuciya, kamar wasa sai ta ji abin ya burge ta, don yana neman ba ta tata mafitar, kawai sai ta ware gudun fara’arta ta qara matsawa kusa da Yaks tana yi masa kallon kai tsaye ta tambaye shi.

“Tsakani da Allah bisa wanne dalili ka kira ni? Bisa harkar so ko qi kaina ma ba na iya amfanawa bare wani”.

Shi ma ya qura mata ido yana mata kallon rashin fahimta.

Babu dalili ta sake sakin fara’a tana girgiza kai, sai dai ba ta ce komai ba.

Mujahid ya ji numfashi na neman gagararsa shaqa, wani baqin shaidani ya fara shawaggi a saman zuciyarsa, yana rada masa babu dadi, duk qoqarinsa na ya fi qarfin zuciyarsa sai da ya yarda da radar cewa, Binta ke son Yaks ko da shi ya fi son Nabila, amma a matsayinsa na quda ba ka haram ya tabbatar in Binta ta ci gaba da tayawa, Yaks zai saya.

A fusace ya bankada mota ya fito cikin tsananin fushi tamkar kububuwa ya figa ya yi cikin gida ba tare da ya sake kallon wajensu ba, Yaks ya dinga zaga masa hannu har ya zarce da qwala masa kira, amma bai iya dakatar da Mujahid shigewa cikin gida a fusace ba.

Kan Yaks ya kulle matuqa, baki bude ya juya ya dubi Binta na ta bakin ya ke sake da murmushi, idonta na kallon qofar da Mujahid ya bace a ciki.

“Ke ma kin yi mamaki ko?”

Yaks ya tambaya a mamakance kuma jikinsa a sanyaye.

Ta juyo ba tare da wani abu ya taba fara’ar fuskarta ba.

“Mamakin me? Ta tambaya.

Ya nuna wajen da Mujahid ya vace.

“Yayanmu Mujahid mana, kamar wanda ya je kokawa ya sha kaye, a fusace ya ke fa”.

Nan da nan sai Binta ta ga gabar da ta ke nema, cikin karsashi ta ce.

“Ai duk daya, wai makafi sun yi dare”.

“Ban gane ba?”

Yaks ya fada yana yi mata duban rashin fahimta.

Binta ta jima cikin shiru tana kallon qofar gida kafin ta tanka fuskarta a dake.

“Ina tsammanin Mujahid ma ya fada irin tarkon da ka ke ciki…”

Yaks ya katse ta ta hanyar zabura da zaro ido a firgice.

“Wai Nabila ya ke so?”

Babu alamun shakku ko kadan Binta ta kaxa kai.

“Ai shi ya fi ka hadama ma, bayan hadama har da rainin wayo, wai ni da Nabilan ya ke so”.

Yaks ya dade yana qugi a salon nuna jimami gami da kama kai zuwa wani lokaci yana yarfa hannu, idanunsa tuni sun kada sun yi jawur, ya dubi Binta da su cikin qwalla-qwalla.

“Binta Yaya Mujahid ya dake ni a inda na ji zafi har da yi min rauni, ki taimake ni na rama ya fi ni jin zaf”.

Ran Binta tas saboda haqanta ya cimma ruwa, ta yi saurin amsa masa.

“Zan so hakan, don ni ma ya ci da gumina. Amma ka ba ni kwana biyu na yi tunani, ina son ka dauke qafarka daga gidan nan har sai na nemo ka, na yi maka alqawarin zan taya ka mu yi masa mahangurba a inda in an ce ya tashi shi da kansa ba zai tashin ba”.

Qala Yaks bai ce mata ba, kawai ya bude mota ya fada a fusace ya fige ta, saura kadan ma ya bangaje ta, amma haka ta bi shi da kallo cikin murmushin samun nasara, sannan ta kada kai ta nufi cikin gida.

Fuskarta a sake ta shiga falon Hajiya ta yafito Nabila,

Yar uwa rabin jiki zo mu yi wani sirri mana.

Duk aka yi dariya, Nabila ta taso cikin murmushi da nuna jin kunya wadanda suna daga dabiunta na gaba-gaba wajen qara mata nutsuwa.

Sai da Binta ta ja ta can quryar daki tana riqe da hannunta suka zauna bakin gado.

Ta dubi tsakiyar idon Nabila cikin walwala ta ce.

Mutuminki Yaya Mujahid ya nemi alfarmar in kira masa ke.

Tun daga tsakiyar kanta Nabila ta ji wani abu mai kama da murna ko fargaba sun tsarga ta gida biyu, sai suka janyo daukewar doka da odarta har tsawon wasu sakanni, da qyar ta girgije su ta lalubo kalmar tofawa daga fatar baki kawai.

Na zaci maganar ta wuce

Binta ta katse ta cikin tsare gira.

Me ya sa za ta wuce?

Nan ma da qyar Nabila ta lalubo abin tankawa bayan ta kawar da kai.

Ina shakkun in da gaske ya ke sona

Binta ba ta barta ta dire ba ta katse ta saboda tsarguwa.

Da qarya ya ke sonki ni kuma na shiga lamarin?

Nan da nan Nabila ta girgiza kai cikin yanayin nuna nadama.

Ba manufata ba ke nan Anti, ni dai na san in irin son da ki ke fada ne ba ya dannuwa a qirji

Yanzu ma Binta tare ta ta yi, sai dai ba cikin yanayn tsarguwa ba, na qoqarin canko wani abu.

Kin taba fadawa tarkon so ne?

Ta tambaye ta cikin qura mata ido.

Kai tsaye Nabila ta gyada mata kai, tsakaninta da Allah ta gaji da qarya.

A rude Binta ta ce.

“Waye Yaya Mujahid ne ko wani daban?”

Nabilaa ta yi mazantakar dakewa da qin ba wa Binta amsa, illa ta bige da murmushi tare da qoqarin hana kunya kawo mata farmaki.

Binta ta gama kai komonta a cikin tunani mai gasa zuciya cikin tsananin faduwar gaba tare da hadiye ta, ta nuna wa Nabila qofar fita.

Oya, maza ki je ki same shi, na gaji da zaurance.

Nabila ta jima cikin shiru da nata tuntunin kafin ta miqe jikinta a sanyaye ta tambaye ta.

Yana ina?

Cikin rawar murya Binta ta amsa.

Yana dakinsa.

Nan ma Nabila ta jima a tsaye kafin ta yi shahada ta kada kai ta tafi.

Fitowar Mujahid wanka ke nan yana sanye da jallabiyya ko mai bai shafa ba ya jajibo tea zai sha, don shi makwadaicin shayi ne tamkar goro da taba. Da qyar ma ya daure ya yi wankan, ko mai bai shafa ba ya hau aiki da qoqarin hadiye bacin rai da kuma tunanin hanyar da zai bi ya raba Binta da tantiri irin Yaks, yan uwantakar da bai taba tsanar wata irinta ba.

Duk da a cikin zaquwar ya sha shayin ya ke, wannan bai hana shi yi masa sha tamkar wanda ke kurbar mur ba. Yana da gaskiya, domin shi ne kawai ya ke jin tilasta wa kai walwala, uwar dakinsa wato zuciyarsa maqare ta ke da abubuwan da tuni ya gaza sama musu suna, domin in ya kira su baqin ciki ko kuma neman yardar so duk ya rage musu matsayi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 8Rigar Siliki 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×