Da sunan Allah Mai Rahma Mai jin Kai
Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammadu S.A.W
Rumfar Kara
Duk da tsananin duhun dare da kuma ruwa da iskar da ake yi, hakan bai sanya ta fasa gudu ba. Gudu take yi saboda tseratar da rayuwarta daga mutuwa!
Daji take ƙara kutsawa, ba ta san inda ta dosa ba, abu daya da ta sani, tana bukatar rayuwarta fiye da komai a yanzun. Tana bukatar tseratar da kanta da taimakon mahaliccinta. Ba ta yi aune ba ta ji, ta yi tuntuɓe da wani ice, ruf! Ta. . .