Skip to content
Part 1 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Da sunan Allah Mai Rahma Mai jin Kai

Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammadu S.A.W

Rumfar Kara

Duk da tsananin duhun dare da kuma ruwa da iskar da ake yi, hakan bai sanya ta fasa gudu ba. Gudu take yi saboda tseratar da rayuwarta daga mutuwa!

Daji take ƙara kutsawa, ba ta san inda ta dosa ba, abu daya da ta sani, tana bukatar rayuwarta fiye da komai a yanzun. Tana bukatar tseratar da kanta da taimakon mahaliccinta. Ba ta yi aune ba ta ji, ta yi tuntuɓe da wani ice, ruf! Ta faɗi, Allah Ya taimaketa ba saman cikinta ɗan watanni tara ba ne, wani radadi ta ji a hannunta sakamakon kwalba da ta ratsa tafin hannunta na dama, ta kokarta mikewa zaune.  Adaidai lokacin da aka yi walƙiya mai tsananin haske wanda ya taimaka wajen haska mata ƙartin mazan da ke tunkaro inda take.

Sunan Allah ta ambata, wanda hakan ya ƙara mata wani kuzari. Ta yi tsalle ta fada bayan  wata ƙatuwar bishiyar kuka ta laɓe sosai yanda ba za su ganta ba.

Ƙirjinta na bugu da karfi, ta runtse ido gam tana ci gaba da ambaton Allah, a daidai lokacin ta ji muryar wani a cikinsu na fadin.

“Kai! Ko za mu kwana a dajin nan ba zan hakura ba sai na ga yarinyar nan na yi gunduwa-gunduwa da namanta!”

Ta ji muryar wani shima na fadin.

“Gaskiyarka Gwaska! Ba zamu bari ta haifar wa Oganmu matsala ba a gaba! Dole mu neme ta  duk inda ta shiga, ya zama lallai mun raba ta da numfashinta!”

Jin wannan furuci nasu ya girgizata, tana jin lokacin da suka ƙara kutsawa cikin dajin suna waige-waige. Sai da ta tabbatar sun bar inda ta ke kafin ta yi saurin yunkurawa ta bar wurin. Nan Allah Ya taimaketa suka yi yamma ita kuwa ta miƙa gabas. Gudu ta ke ba’a hayyaci ba ga jini na ɗiga daga tafin hannunta, ga cikinta da gangar jikinta sun galabaita.   Tsayawa ta yi a gefen wata bishiya tana haki. A hankali ta dubi hannunta da ke fidda jini, ta yagi gefen ɗankwalinta ta kulle shi gam. Daga nan ta ci gaba da tafiya a hankali sakamakon galabaitar da ta riga ta yi. Hade hanya take yi, ganinta ya zama bibbiyu, daga nan ba ta kara sanin inda kanta ya ke ba, ta zube a kasa sumammiya!

*****

A hankali ta soma bude kwayar idanunta har sai da Allah Ya bata nasarar bude su gaba daya. Dakin ta kurawa idanu tana kare mi shi kallo. Gida ne na gargajiya wanda aka gina da jar ƙasa. Kanta da ke sarawa ta rike tana mai dan runtse idanu lokaci guda tana ambaton Allah.

Komai ya shiga dawo mata kamar a lokacin ya faru. Ta tuno sadda ta ke gudu a tsakar dajin da ba gida gaba kuma babu a baya. Ta kara tuna  lokacin da ta zube a ƙasa ba a hayyaci ba. Da sauri ta daga hannunta da zummar shafar cikinta, sai ganinsa ta yi daure da wani sabon kyalle, radadin ya ragu sosai ba kamar sadda ta ji a farko ba. Miƙewa ta yi zaune tana ambaton Allah tana kare wa dakin kallo.  Ya yi daidai da ɗaga asabarin dakin aka shigo da sallama. Wata dattijuwa ce hannunta rike da akushi. Ta karaso ciki tana wangale baki.

“Sannu, kin farka ashe?”

Da mamaki take duban matar.

“Ya akai na zo nan?”

Dattijuwar ta faɗaɗa fara’arta.

“Ashe kina jin Hausa? Kar ki damu, za ki ji komai, sai dai yanzu kina bukatar kimtsi da abinci ko don yaron cikinki.”

Ta gyaɗa kai tana bibiyar dattijuwarnan da kallo har ta ajiye akushin sannan ta ce.

“Zan kama ruwa.”

“To, mu je.”

Ta taimaka mata, ta mike, tana rike da ita har suka fito tsakar gidan. Yashi ne mai kyau a wurin sai kuma ɗakuna kamar dai irin wannan din da ta fito ciki. Fili ne sosai a gidan wanda har ya ba ta mamaki, kuma da alama wuri-wuri ne. Bayan dakin ta ga sun zagaya sannan ta nuna mata bayan gidan.

“Ga shi nan ki shiga, bari na miƙo miki ruwa.”

Maryam ta gyaɗa kanta sannan ta karasa tana dafe da bango, ba jimawa matar ta dawo dauke da ruwa a babban kwarya tana fadin.

“Idan za ki iya ki wanke jikinki gaba daya saboda kin kwana uku a kwance. Sai ki ji dadin jikin.”

Ta zaro idanu jin da ta yi wai kwanakinta uku a wannan yanayin. Ta dai daure ta amsa da to sannan matar ta fito.

Sai bayan ta kammala, ta fito, tana tsaye tana neman ruwan alwala sai ga wani yaro ya shigo gidan.

“Kai.”

Jin haka ya dube ta, tsai ya yi yana kallon ta, nan da nan ya gane marar lafiyar da Babansu ya kawo ce.

“Ina zan samu ruwa?”

Ya karasa ya ɗebo mata a kwarya ya dawo. Ta yi mi shi godiya sannan ta soma alwala. Tana cikin yi matar ta fito. Baki ta saki tana dubanta.

“Ruwan ne bai ishe ki ba ki ke karasa wankan a nan?”

Maryam ta dube ta da ɗan murmushi domin kuwa sosai ta ji dadin jikinta da ta yi wankan.

“A’a, alwala nake yi.”

Cikin rashin fahimta matar ta gyada kai kawai sannan ta juya. Bayan ta kammala ta koma dakin. Wasu kaya ta tarar saman gadon karfen. Ta soma tunanin mayar da kayan jikinta ne matar ta yi mata nuni da kayan.

“Yauwa ki sanya wannan, kin ga naki ya yi datti  kuma ma ya yayyage. Idan kin kammala ga abinci ki samu ki ci sosai ko don cikin jikinki.”

Ta amsa da to tana godiya. Tambayoyi ne fal a zuciyarta ga cikinta da ke murɗawa tsabar yunwa. A daddafe ta kammala saka rigar ta daura zanin. Tuwon gero ne sai miyar kuka, ai kuwa tas ta cinye, matar ta shigo.

“Ko dai na karo miki?”

Kunya ta sanya ta sunkuyar da kai ta kasa magana, murmushi matar ta yi ta dauki akushin ta fita. Can kuma ta dawo da tuwon. Nan ma Maryam ta ci sosai don kaɗan ta bari. Ta dauki ruwan ta kwankwaɗa da yawa kafin ta yi gyatsa da hamdala.

Sai a sannan ta ji yaron cikinta na bata naushi,  murmushi ta yi mai ciwo  yayin da kaunar abinda ke cikin ke ƙaruwa sosai a ranta.

Mikewa ta yi ta matsar da kayan abincin sannan ta dauki wankakken mayafin da ta gani  a saman kayan da aka ajiye mata ta yafa. Sai da ta tabbatar ya rufe jikinta sai kuma ta shiga neman gabas. Allah Ya taimake ta matar ta kara shigowa, wannan karon har sai da ta ba ta tsoro, don ganin ta ta yi kamar an hankado ta ba sallama.

Washe mata hakoranta ta yi wadanda suka tashi daga farare zuwa ruwan dorawa.

“Kin gan ki kyakkyawa da ke kuwa, kin fito tas!”

Maryam ta murmusa kadan.

“Za ki dan fito tsakar gidan ne ki sha iska ko…?”

“A’a, sallah zan yi. Ina ne gabas?” Ta katse ta.

Dan jim matar ta yi sai kuma ta yi ‘yar dariya.

“Au Gabas dai na gidan Nomau? Dama kin san wasu a kauyen nan?”

Da mamaki Maryam ta girgiza kai.

“Ko daya, ina nufin gabas dai inda kuke kallo idan za ku yi sallah.”

Ta kara yin shiru cikin nazari. Can ta tuna da irin sallar da ake yi a Rumfar Malam Haruna. Ta ji kuwa sunan da suke kiran abinda suke yi din kenan. Ta dan yamutse fuska tana bin Maryam da kallo irin na ta ga abin kyankyami.

“Wai ke musulma ce?”

Cike da wani dimbin mamakin ta gyada mata kai.

“Kwarai kuwa, ni musulmaa ce.”

Ta6e baki ta yi kawai.

“To gaskiya dai mu gidan nan ba ma sallah. Mu ba ma bautar abin da ba ma gani. Dodo muke bautawa, yanzu maganar da nake miki duka ‘yan gidan suna can wajen bauta, nima a dalilinki mijinmu Sarkin Dawa ya ce na zauna, zai nema min gafara wajen Dodo.”

“Wa’iyazu billah.” Maryam ta furta a fili tana mai dafe kanta wanda ta ke jin ya fara sarawa.

“Mene ne sunanki?” Tambayar matar ta katse tunaninta. Ta hadiyi yawu mai daci.

“Sunana Maryam.”

Yamutse fuska ta yi.

“Sunan Mamar Yesu gareki. Ƙauyen da ke maƙwabtaka da mu, su Yesu suke bautawa. Ba ma shiri da su.”

Ban da kalmar ‘Innalillahi’ ba abinda Maryam ke nanatawa a ƙasan ranta. Ita kam yau ta san ta shiga hannun 6atattu, hawaye masu zafi suka fara kwaranyo mata daidai sa’ad da matar ta fice daga dakin tana wani yare da ba ta san me take faɗi ba.  Ganin dai hakan ba mafita ce a gareta ba ya sanya ta fitowa waje, ta duba saitin rana don lokacin hantsi ne. Komawa ta yi, ta daidaita saitin wurin da ta tabbatar nan ne gabas sannan ta tada sallarta.

Jero salloli ta soma yi tana ramuwa, matar ta shigo kusan sau uku tana fita. Yanzun ma shigowarta ta huɗu sai kuma ta fice tsakar gidan tana jijjiga jiki ga wani tsoro matsananci da ya shige ta, ta farat ɗaya. Ta tabbatar Maryam ba alheri ce a garesu ba, domin muddin Dodo ya yi fushi to fa ƙarshensu ne kawai zai zo. Ba a isa a bautawa komai a ƙauyen ba face Dodo.

*****

Saman wani ƙaton dutse, mutanen Kauyen Cinnaku ne cike a kai, wasu a cikinsu rike da kayan kiɗa yayinda manyan dattawan Kauyen ke zaune a wuri na musamman tare da Maigari suna shan giya hankalinsu kwance fuskokinsu ke cike da annuri. Sauran mutanen garin kuwa na gefe a tsaye kowannensu ya maida hankali ga maza da matan dake tiƙar rawa suna waƙe Dodo.

Bayan sun kammala daya bayan daya suka nufi inda wani ƙaton mutum-mutumi yake  a cikin ƴar Bukka suna zubewa gami da damfara goshinsu a ƙasa. Haka suka yi ta yi daya bayan daya suna barin wurin. Bayan sun kammala ne Maigari ya mike da mutanensa suka nufi wurin Dodo, nan sukai kamar yanda wadancan sukai, a gefe Boka ne zaune, ya bubbuga ƙasa ya dago ya yi wani irin dariya.

“Kai da mutuwa har abada, Dodo ya biyamaka bukatunka! Za ka samu amfanin gona mai kyau fin wadda ka samu a Bara.”

Maigari ya shiga washe baki yana jin wani farin ciki ya kara zubewa ya gaida Dodo yana mai godiya. Haka masu muƙamin garin suka shiga gaida Dodo. Ana zuwa kan Sarkin Dawa, shima ya zube. Nan da nan Boka ya sauya fuska yana zaro idanu. Ya kara duban Sarkin Dawa kafin ya kara bubbuga ƙasa. Kowa sai ya yi turus yana jira ya ji abinda zai fito daga bakin Boka.

“Kai Sarkin Dawa! Dodo na matukar fushi da lamarinka. Babu abinda nake gani a gidanka sai wani haske wanda matukar bai fita ba toh kana cikin tashin hankali, bala’i da kuma asara! Ka gaggauta fitar da wannan hasken don kuwa Dodo ya tabbatar ba na alheri bane garemu baki daya ma.”

Jin wannan yasa wata yar tsohuwa da za ta yi kimanin shekaru tamanin a duniya ta matso sosai kusa da Boka. Fuskarta cike da tashin hankalin da ya fi na Sarkin Dawa take tambaya.

“Ya mai girma, ka fadamana menene wannan abu don mu gaggauta fitar da shi daga garinnan. Ina rantsuwa da Dodo koda ace ni Maikudi ce, zan fita daga yankinnan gudun abinda zai bata ran Dodo.”

Boka ya dubeta fuskarnan a daure tamau.

“Ya ke abar koyi ga sauran mata wajen bautar Dodo, ina muku rantsuwa cewa bansan wane irin haske ne wannan ba domin ban taba ganin irinsa ba sai a yau. Bana fatan na kara ganinsa kuma har abada gudun ɓacin ran Dodo. Ina mai sanar da ke da ɗanki Sarkin Dawa, ku gaggauta kawar da koma mene a gidanku! Idan ba haka ba ina rantsuwa cewa fushin Dodo zai sauka a kanmu gaba daya, za ka fuskanci tsinuwa fiye da na Haruna!”

Gaba daya mutanen wuri aka gigice, kururuwa suka hau yi suna fadin.

“Mun tuba Dodo, Mun tuba Dodo!”

Boka ya juya ya mika gaisuwa ga Dodo ya yi juye-juyensa da maganganu kafin ya dubi mutanen gari.

“Ina kara jaddada maku a fitar da hasken da ke gidan Sarkin Dawa muddin ana son zaman lafiya a garinnan!”

*****

Ta rasa dalilin da ya hana ta katsewa Maryam ibadarta, sau huɗun tana shiga da niyyar hana ta amman ba ta san me yake dakatar da yunƙurinta ba. Tana nan a tsaye, ta ji muryoyin jama’ar  gidan sun dawo. Kusan a guje wani saurayin ya sanyo kai. Yana ƙwala mata kira.

“Ta Goma! Ta Goma!”

Ta ƙarasa wajensa da saurinta.

“Ƙosau! Me ya faru?”

Yana maida numfashi ya ce.

“Ina baƙuwa? Tana ina?”

Kafin ta kai ga ba shi amsa sauran jama’ar gidan sun shigo yayinda mutanen Maigari ke tsaye a ƙafa suna jiran a miƙomusu koma mene don su miƙa ga Boka kafin ya yiwa garinsu lahani.

Sarkin Dawa ne kan gaba. Yana sanye da kayan da aka sassaƙa da fatar damisa. Fuskar nan kamar bai ta6a yin dariya ba. Ganin haka suka yi shiru. A bayansa kuwa sauran matansa har su goma cif, sai Ta Goma ta sha ɗayansu. Babbar Uwargidansa mai suna Fanteka tana gefensa tare da mahaifiyarsa; Maikudi. Kaf gidan tsoron Maikudi ake, ba ta ragawa kowa a cikin matan Sarkin Dawa wanda hakan ya samo asali ne daga masifaffen son da ta ke yi wa tilon ɗan nata, wato Sarkin Dawa. Fanteka ita kaɗai ta ke iya tunkarar Maikuɗi da magana kai tsaye ba tare da wata shakka ba. Wannan ne dalilin da ya sanya Maikuɗi jinjina mata har dai ta sakar mata suka haɗa kai suna zuba mulki son ransu.

Ta Goma da Ƙosau suka sunkuyar da kai a lokaci guda alamun ba da girma ga Sarkin Dawa.

“Ta Goma!” Yanda Maikuɗi ta kira sunan a kausashe ya ƙara tsoratar da Ta Goma. Ta amsa.

“Na’am.”

“Ina amanar da ɗana ya bari a hannunki?”

Hannu na rawa ta yi nuni da ɗaki.

“Tana ciki.”

Maikuɗi ba ta jira komai ba ta shiga tokare sandarta ta nufi ɗakin. Maryam tana jinsu don lokacin ta idar da sallah tana zaune tana addu’a. A haka ta ji an bankaɗa asabarin dake bakin ƙofar an shigo. Ba zato ta ji saukar sanda a kan yatsunta wanda ke sama tana addu’a. Don tsananin zafi da azaba ba ta san sa’ad da ta saki ƙara ba gami da ambaton Allah.

“Ya Allah!”

Fadin sunan Allahn da ta yi ne ya kara baƙantawa Maikudi rai, ta daga ƙafa za ta kai mata duka sai ta janye da ta hangi ƙaton cikinta. Wata razananniyar tsawa ta doka mata.

“Ke!! Mu nan ba ma bautar komai idan ba Dodo ba, don haka ki gaggawar barin dukkan abinda kike yi. A yau ba gobe ba za ki shiga taskun da ba ki ta6a tsammata ba!”

Jin wannan Maryam ba ta nuna alamun razana ba, da hawayen raɗaɗi da hannunta ke yi ta dubi Maikudi babu ko shakka.

“Ni kuma na zaɓi mutuwa da kowace kalar azaba muddin zan tsira da addinina. Ba zan ta6a barin bautar Ubangijina ba, Ubangijin dukkan halitta. Mai bayarwa da kuma Shiryarwa.”

Fadin haka Maikudi ta fisgo hannunta, Maryam ta mike tsaye da sauri, haka ta shiga janta har tsakar gidan. Mutanen gidan da sukai cirko-cirko suna dubansu suka mara wa Maikudi baya ganin ta nufi hanyar waje da Maryam. Babu turjiya ba komai ta ke binta a baya har suka isa kofar gidan inda mutanen Maigari da sauran jama’ar gari ke jiran ganin abinda zai fito daga gidan Sarkin Dawa. Gani sukai Maikudi ta fito tana jan hannun wata mace mai ciki, gaba daya mamaki ne ya kamasu. Kowanne da tambaya fal a bakinsa, yaushe wannan mata ta shigo Kauyen Cinnaku?

Cike da girmamawa Maikudi ta ɗan russunar  da kai ga Dakaci.

“Ga Bakuwar da ɗana ya tsinta a dokar daji, yau kwana uku kenan. Na tabbatar ita ce Annobar  garinmu don ba ta yi imani da Dodo ba.”

Sai hayaniya ya soma tashi daga ɓangaren jama’ar gari, kowa ya budi baki cewa ya ke a kasheta. Wani irin riƙon da jama’ar Dakaci sukai mata sai da yaron cikinta ya motsa. Ta ambaci sunan Allah da karfinta. Wannan ya kara fusatasu. Zasu kai mata duka Dakaci ya dakatar da su a tsawance.

“Ba huruminku bane! yanzu doka na hannun Boka. Ku kamata muje gaban Maigari.”

Kowa ya yi na’am da zancen Dakaci. Wani yaro da bai fi shekaru goma sha uku ba dake tsaye a gefe yana kallo har aka tafi da Maryam.  Ya ruga a guje ya nufi can wuraren wajen gari kusa da wani ƙaton dutse.

Malam Haruna, dattijo mai nagarta yana zaune saman buzunsa yana koyar da almajiransa daidai lokacin da wannan yaron ya ɓullo wurarensu. Ganin irin gudun da yaron ya ke yi ya dakatar da Malam Haruna, idanu suka ƙuramishi har ya ƙara so ya zube gaban Malam cike da girmamawa. Da mamaki Malam ya jefamishi tambaya.

“Ahmad, meke faruwa? Sun ƙara kama wani a cikin ɗalibaina ne?”

Girgiza kai Ahmad ya yi.

“A’a Malam, wata baiwar Allah ce kuma musulma, Sarkin Dawa ya tsinceta, yanzu ga ta can za’a kai ta gaban Maigari a yankemata hukunci.”

Jin haka gaba daya Malam ya mike tsaye yana ambaton Innalillahi. Ya dubi ɗalibansa.

“Aliyu, Umar. Ku taso muje. Kai kuma Ridwan ka saurari haddarsu. Ina zuwa.”

Cikin bin umarni suka amsa, Aliyu da Umar suka mara mishi baya kamar yanda ya umarta yayinda Ridwan ya ci gaba da sauraron haddar abokan karatunsa.

*****

A gaban Boka aka zubar da Maryam, ta dage cikinta wanda har lokacin zafi yake mata, gaba daya mararta ta riƙe, hawaye a saman fuskarta tana ci gaba da karanta dukkan addu’ar da ta zo bakinta saboda neman sauki daga Ubangijinta.

Boka ya yi mata ƙuri da idanu kafin ya hau zaro idanu yana duban Maigari da mutanensa hankalinsa a tashe.

“Shakka babu wannan ita ce hasken da Dodo ya haskamin a gidan Sarkin Dawa!”

Jin wannan sai Maigari ya dubi Sarkin Dawa wanda ke russune a gabansa cike da girmamawa.

“Sarkin Dawa, ina ka samo wannan matar?”

“Yau kwananta uku a gidana, na fita yawona na farauta safiyar Asabar daidai bakin Kogin da ya yi mana katanga da mutanen yankin Juju, na ganta kwance a bakin ruwa babu alamar rai. Sai da ta tabbatar akwai sauran ran a jikinta sannan ta taimaka mata adalilin tsohon cikin da na gani a jikinta.”

“Ka saɓa dokar garinnan Sarkin Dawa, ba ka sanar da mu komai game da Baƙuwa ba.” Maigari ya furta a fusace.

Sarkin Dawa a ladabce ya sunkuyar da kai.

“Ina neman gafararka, ina neman gafarar Dodo. Ba zan ƙara maimaita irin wannan ba.”

Jin haka Maigari ya ɗan sassauta. Ya maida dubansa ga Boka.

“Me ka ke ganin za’ayi ga wannan matar.”

Boka da tun dazu yake rarraba manyan idanunsa wadanda suka sha baƙin kwalli. Ya kara bubbuga ƙasa yana dube-dubensa. Ya dago da kai a matukar fusace.

“Kasheta za’ayi! Ba alheri bace a garinmu.”

Jin haka Maryam ta runtse idanunta tana ƙara ƙaimi wurin ambaton Allah. Tana ji Maigari ya yi umarni ga mutanensa su ɗagata a je a ƙulle kafin su ƙaraso.

Sun soma kiciniyar janta suka tsinci muryar da ba wanda ba ta yiwa kwarjini a cikinsu. Duk sadda suka ji sukan razana, har Bokansu.

“Kar ku sake ku ta6a ta!”

Gaba daya suka dubeshi, Malam Haruna ne sanye da kayansa farare ya sha rawani. Ya ƙaraso ya na duban Boka.

“Kai Matsafi! Ya mukai da kai? Ina alƙawarin da ku ka daukarmin na ba za ku ta6a almajiraina ba?!”

Boka da tuni ya soma zufa ya daure ya karfafa zuciyarsa ganin mabiyansa na kallonsu. Yasan Malam Haruna ya fi karfinsa sai dai kuma har abada ba zai saduda ya yarda da abinda Malam Haruna ke bautawa ba.

“Wannan ba ta kasance cikin almajiransa ba, asalima Sarkin Dawa ne ya tsinto ta a can bakin Kogi. Za ta sa Dodo ya hallakar da mu don haka ba zamu barta da rai ba!”

“Ba zan ta6a bar ku kashe ran da ya yarda ya kuma yi imanin babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Subhanahu wa ta’ala, ba zan bari ku cutar da ƴar uwata ba. Mun yi daku ba za ku ta6amin almajiraina ba, don haka ina gargadinku da ku kyale wannan baiwar Allah na tafi tare da ita.”

Shiru ya biyo baya, kowa ya zubawa Boka idanu yana jiran ji daga gareshi. Wani irin kwarjini na musamman Boka ya gani tattare da Malam Haruna wanda ya hanashi kataɓus. Can ya yi ta maza.

“Shikenan, zamu bar ka ka tafi da ita Rumfarka sai dai da sharadin kar ta sake zuwa yankinmu. Ta zauna can a wajenka! Koda wasa kar mu ganta cikin garinmu.”

Kai Malam Haruna ya gyaɗa.

“Na ji wannan kuma zan kiyaye. Ina muku fatan shiriya a koyaushe. Ina nan ina addu’a kan Allah Ya ganar da ku, ina jiran ranar da za ku yarda babu wani abin bautawa sai Allah. Za ku yarda da Annabi Muhammadu s..a.w ManzonSa ne.”

Maigari ya daka tsawa.

“Kai Haruna! Ba zamu ta6a yarda da wannan tatsuniyar taka ba. Kullum ga ka nan a tsiyace, talauci ya takura rayuwarka saboda gujewa gaskiya, ka bar Dodo, shi kuma ya saukar da fushinsa a kanka. Ba za ka ta6a arziki ba a duniya Haruna!”

Ya maida duba ga Dogaransa. 

“Maza-maza ku ba shi matar ya bar cikin garinmu tun bai sanya fushin Dodo ya sauka a kanmu ba.”

Ba musu suka saki Maryam ta nufi Malam Haruna a can ƙasan ranta tana jin wani sanyi da farin ciki. Hamdala kawai take yi ga Ubangijinta wanda Ya jefata hannu mai kyau. Ko ta mutu yanzu ba ta da fargabar hannun da abinda ke cikinta zai faɗa.

A daddafe take tafiya, cijewa kawai take yi saboda yanda take jin bayanta da mararta na riƙe mata. Malam Haruna tsaf ya fahimci ba ta cikin hayyacinta hakan yasa bai nemi jin komai ba daga gareta. Dakyar suka ƙarasa Rumfarsa, ya shiga ya hau kwalawa matarsa kira.

“Fatima! Fatima!!”

Da sauri ta fito daga madafa, tana mai amsawa.

“Na’am Malam.”

Nuni ya yi mata da Maryam wacce tuni ta zube a hanyar shigowa gidan tana salati. Itama da sauri ta karasa ta ɗagata tana ambaton Allah. Malam ya fita ya sa su Aliyu yiwa matansu magana, ba jimawa suka fito daga zagayensu suka faɗa gidan Malam domin taimakawa Maryam.

Ta sha wahala sosai, Malam ya wanke rubutu ya aikamusu aka bata ta sha, ba jimawa ta soma nishin haihuwa. Cikin ikon Allah ta haifi diyarta mace. Girman yarinyar ya ba su Fatima mamaki, lokaci guda yarinyar ta shiga ransu. Kukan da ta canyara ya sanya Maryam yin murmushi lokaci guda hawaye suka shiga zubomata tana duban diyar. Tausayinsu ne ya kamata lokaci guda, tunanin makomarsu kawai take yi.

A can waje su Malam sun ji kukan jaririyar, wani irin farin ciki da sanyi ya shiga ratsa zuƙatansu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Rumfar Kara 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×