Ya yi ta maza ya karasa ciki sai dai bai zauna ba. Anti Khalisat ta share ta maida abin matsayin tausayi ba komai ba.
Da irin maganar kurame suka gaisheta itama ta amsa musu. Shiru ya biyo baya don ba hanyar cewa wani abu ganin haka Anti Khalisat ta miƙe tsaye. Kallonta yake yana kara bambance aya da tsakuwa, miƙewar da Matarsa ta yi ya sanyashi ɗauke kwayar idanunsa.
Suka dubi juna.
"Muje toh." Ba musu ya juya ya fita ta bi bayansa. Ganin ya yi hanyar fita ta ce.
"Abeen Shuraim sai ina?"
Ya juya. . .