Skip to content
Part 15 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Ya yi ta maza ya karasa ciki sai dai bai zauna ba. Anti Khalisat ta share ta maida abin matsayin tausayi ba komai ba. 

Da irin maganar kurame suka gaisheta itama ta amsa musu. Shiru ya biyo baya don ba hanyar cewa wani abu ganin haka Anti Khalisat ta miƙe tsaye. Kallonta yake yana kara bambance aya da tsakuwa, miƙewar da Matarsa ta yi ya sanyashi ɗauke kwayar idanunsa. 

Suka dubi juna.

“Muje toh.” Ba musu ya juya ya fita ta bi bayansa. Ganin ya yi hanyar fita ta ce.

“Abeen Shuraim sai ina?”

Ya juya yana dubanta da murmushi.

“Sai wurin kawarki.”

Ta yi dariya shima ya tayata. 

“A gaisheta.” Ta faɗi don tasan wasa ne kawai. Ya kashemata ido.

“Ke wurin Babana zan je. Yanzu zan dawo in Sha Allah.” 

Ta amsa da toh sannan ya sa kai ya fice, hakan ne kaɗai zai ɗauke mishi tunanin da ya ɗarsu a ransa game da Maryam. Yana tsoron abinda zai je ya zo, yana gudun ɓacin ran rayuka, banda haka da ya fasa abinda ake gudu kawai ya faru. 

*****

“Kai Gwaggo.” Fadin Anti Khalisat da mamaki. 

Gwaggo Kubra ta jinjina kai.

“Ku kalleta dakyau, kamannin a fili suke sai dai kuma bansan me zance ba tunda bai zo nan da wata mata ba bayan Halisa kamar yanda naji labari.”

Yaha ta jinjina ki.

“Wannan hakane, sai dai kar ki kawo komai, dama akan yi kamanni har haka. Halittar Allah ce ba inda ba ta kasancewa.”

“Gaskiyarki Yaha, nima dai abinda na sanyawa zuciyata kenan. Mu bar ma maganar don Allah.” Fadin Anti Khalisat tana Kara tuno kamannin Maryam. 

Da wannan suka rufe tattaunawar, karshe Anti Khalisat ta mike zuwa sashin Engineer Bello don gaisuwa. 

*****

Daidaita Parking dinsa ya yi a harabar Hotel din sannan ya dauki tarkacensa ya fito. Kai tsaye ya nufi ciki. Yana shiga ya ajiye shirginsa ya kunna karatun Alkur’ani mai girma, Muryar Sheikh Sudais ta gauraye ɗakin sai dai ba sosai ya saki murya ba gudun shiga hakki. Sai da yayi wanka ya shirya cikin jallabiya maroon sannan ya ɗan kwanta saman kujera. Kira ya yi don a kawomishi abinci daga nan ya shagala da sauraron Alkur’ani yana bi. Ƙwanƙwasa kofar da akayi ya katseshi, ya miƙe duk a zatonsa abincin da ya bukata aka kawo. Sai ganin mutum ya yi tsaye yana murmushi mai bayyana haƙora. Ya haɗe fuska. Yau dai su yita ta ƙare don ya rasa nacin na mene. Hanya ya ba shi alamun ya shigo, ba musu Fu’ad ya shiga. Jin bai yi sallama ba ya ja hannunsa ya maida baya. Ya bishi da duban mamaki. 

“Ba ka tuna da sallama ba?” 

“Oh.” Ya fadi yana ɗan daga gira sannan ya ɗan bude haƙora kadan.

“Sorry.” 

Yanda ya furta sallamar ya tabbatarwa da Adam bai saba yinta ba. Fatan shiriya kawai ya mishi a ƙasan ransa, bai ga laifinsa ba sai na Hayat da Salma. A cewarsa. 

Wuri Fu’ad ya samu ya zauna. A hankali yake sauraron karatun, sai ya ji abin ya burgeshi. Ba kiɗa ba komai sai karatun Alkur’ani. 

“Ina sauraronka.” 

Faɗin Adam sa’ilin da yake ajiye mishi gorar ruwa, kafin ya zauna sai ga wani knocking din, waitress ce ta gaidashi a mutunce ya amsa kafin ta shiga , sai da ta ajiye komai sannan ta fito ta bar musu dakin. Rufe kofar ya je yi, yana juyowa ya ga Fu’ad ya ja plate din gabansa, suna haɗa ido ya shafi cikinsa gami da ɗan marairaicewa kamar wanda ke gaban wani yayansa ko Baba. 

“I am sorry, but I am hungry. Just three spoons.”

Daga nan ya dauki cokalin ya soma cin haɗaɗɗen fried rice din da akai da hadin salad a gefe sai kaza, a bowl guda kuma farfesun kayan ciki aka zuba. 

Adam ya fasa maganar da ya yi niyya kawai ya ƙara kiran waya a kawo irin plate din da aka haɗo yanzu. Daga nan  ya nemi wuri ya koma ya zauna gami da jan Laptop ya hau dannawa. Fu’ad kuwa jin ya mishi shiru ya ci gaba da kai loma duk a son ya tsokano shi don ya kulashi. Shi kuwa rabin hankalinsa na ga kallon Laptop rabin kuwa yana ga Fu’ad wanda ke cin abincin dagaske, bai san sadda ya yi murmushi ba. Da ace yana da ƙani babba ya tabbatar zai ga irin wannan wautar kala-kala. 

Ba jimawa aka kawo na Adam, kafin ya miƙe Fu’ad ya rigashi, bude kofar ya yi ya ba ta hanya ta ajiye ta fita. 

Adam ya dubeshi ganin ya kammala yana goge baki da tissue. 

“Uhm, ina jinka. Bibiyar da kake min ta mene? Nasan dai zuwa yanzu ka san waye Adam. So mene za ka takura kanka akan lallai sai mun yi zumunci da kai?”

Ganin babu wasa a fuskar Adam din ta sanya shima ajiye wasan a gefe. 

“Yes, na sanka na kuma san relationship dinmu yanzu, Mum ɗina na auren Dad ɗinka. Wannan ba shi zai hana mu kulla zumunci ba ko? Ina neman ka yafiyarka game da abubuwan da na aikata gareka a baya. Wallahi ban san ya akai nake kallonka kamar wani babban yayana ba yanzun, kamar we are from the same Dad.”

Dad din da yake furtawa ya fi komai baƙanta ran Adam sai dai ya danne ɓacin ran ya soma cin abinci da Bismillah. Shiru ya biyo baya har sai da Adam din ya kai loma ta hudu kafin ya ba shi amsa 

“Ba zamu iya zama inuwa daya ba saboda i hate your Mum. Don haka wataran zan iya faɗar baƙa a kanta.”

“Exactly the same way I hate your Dad. Amman hakan ba zai hana mu zama like friends oh sorry Brothers ba.”

Ya sauya zancen ganin banzan kallon da ya samu daga Adam. 

“Ba zan iya kulla zumunta da manemin mata ba.”

Kunya da bakin ciki suka kama Fu’ad,  duk yanda akai Adam ya ganshi ko kuma ya ji hirarsa da Hanan. Koda ba haka ba ya san dai halayyarsa. Sai dai ko mene ai bai cancanci ya mishi hakan ba.

“Kana iya tafiya.”

“Meaning?” Fu’ad ya tambaya zuwa lokacin ya soma jin ransa ba dadi da irin yanda Adam ke mishi. 

“Mun gama magana.”

Fu’ad ya mike a fusace.

“Wane irin mutum ne? Don kaga ina ta binka mu yi zumunci? Ko an fadamaka da wani ne yake min haka zan ci gaba da bibiyarsa har yanzu? Shikenan, ba za ka ƙara ganin ƙeyata ba from now on! Ba zan ƙara yi maka kallon ɗan uwana ba, zan yakice wannan bangaren na zuciyata da ke yawan fadamin kai ɗan uwana ne na ajiyeshi a gefe!” 

Daga haka ya fice ya bar ɗakin gami da rufowa da karfi. Sai kuma ya ji bai kyauta masa ba. Ya ji zuciyarsa ba ta yiwa Fu’ad din adalci ba saidai yana tuno da ko wace mahaifiyarsa ya share batun ya ci gaba da kai loma har sai da ya ji ya ƙoshi. Bayan tattare wurin ya koma ya zauna. Ganin lokacin sallar isha’i ya yi, ya sanyashi miƙewa ya ɗauro alwala. Duk yanda ya so ya yakice tunanin lamarin Fu’ad ya kasa, yana idarwa ya fice daga Hotel din. Asibiti ya nufa musamman don ganin Dr Ibrahim don yau ba ya cikin masu duty. 

Yana tafe yana gaisawa da sauran ma’aikata har ya ƙarasa ofishin Dr Ibrahim. Ciki ya sameshi yana duba patient, ya shiga da sallama ya nemi gefe ya zauna. Bayan sun kammala Dr ya dubeshi.

“Yau kuma kaine ba dutynka ba ba komai ba? Nasan dai akwai magana a bakinka.”

Adam ya ja guntun tsaki. Miƙewa ya yi ya dawo kujerar da patient din ya tashi ya zauna. Tiryan-tiryan ya ba shi labarin haɗinsa da Fu’ad da kuma yanda suka takarkare a yau. Ya ƙarashe da fadin.

“Bansan meyasa abin ya dameni ba, sai naji ban kyauta ba.”

“Saboda ba ka kyauta din ba Dr Adam. Dole ya dameka. Irin wadannan ai jansu ake a jiki, sai kaga ta silarka Allah Ya shiryar da shi ya bar duk wani abin banza da yake aikatawa. Wanda ke kaunarka ai ya fi makiyinka. Ka share batun iyayenku ko wani abu, tsakaninku da shi daban ne. Ka sa a ranka tamkar kana tare da ƙaninka da kuke ciki ɗaya ne. Ban ji dadin abinda ka yi mishi ba gaskiya.”

Adam ya jinjina kai.

“Hakane, zan duba yiwuwar zumuncin.”

“Ji, ba ka ji kunya ba, ashe zumunci sai an duba yiwuwarsa?” Fadin Dr Ibrahim yana ta6e baki.

Murmushi kawai Adam ya yi. Suka ɗan taɓa hirarsu ya raba dare anan sannan ya fice daga asibitin.

*****

Washegari da safe ya kwankwasawa Fu’ad kofa. Sai da aka jima kaɗan kafin a bude. Sigari yake zuƙa daga shi sai gajeran wando da singilet. Yana ganinsa ya yi azamar kashe sigarin saboda har ga Allah ba karamin kunya ya ji ba. Bai san yana da kunyar har haka ba, shi duk a zatonsa Haidar ne ma domin tun a jiya suka shirya ya ba shi hakuri kuma ya ce zai zo su fita. 

Adam kamar bai gani ba ya zarce da maganarsa.

“Ina mai ba ka hakurin abinda na maka jiya. Nasan za ka ji ba dadi.”

Ya yi shiru bai ƙara magana ba. Da sakin fuska da kuma wani irin mamaki ya ba shi hanya.

“Ka shigo ciki toh.”

Ya ɗan dubi yanayin ɗakin, kyankyami ba zai bari ya shiga ba. Kyankyamin ba wai na datti bane, a’a, na masu ɗakin ne. 

“No, ina ɗan sauri zan tafi wurin aiki.” Ya fadi da ɗan murmushi. Yanda Fu’ad din ke murnar saukowarsa har mamaki ya ba shi. Don kansa ya karɓi lambar Fu’ad don bai taɓa ajiye lambar ba a wayarsa. Wannan ya fi komai yiwa Fu’ad daɗi a zuciya. Ranar duk wanda ya ganshi ya san yana cikin farin ciki.

Bayan Sati Biyu

Da wani irin zumudi da murna ta shigo gami da sallama ta faɗa kan Mamarta. Maryam ta ɗan ture ta tana murmushi cike da kunya. 

Humaira na dariya ta zazzage ledar da ta shigo da shi.  Uniform ne sai Takalmi da Safa da kuma jakar makaranta. Maryam wani hawaye ya zubomata ma farin ciki ta sa hannu ta sharesu. Da saurinta ta dauki takarda hannu har rawa yake ta yiwa Mama rubutu kamar haka.

“Mama kin gani, Baba Hashim ne ya siyamin, an sanyani wai a firamare siri. (Pri 3) sun ce inada kokari zan iya. Ranar Litinin zan soma zuwa, yace Yaya Baharu ne zai dinga kaini.”

Maryam murmushi kawai ta yi ta maida mata amsa.

“Alhamdulillah, Allah Ya saka musu da alheri, Ya biyasu da aljannarSa. Sai ki dage da karatu banda wasa, wataran ki zama Likita ko? Fatan alheri.”

Humaira na karantawa ta yi dariya. Mamanta ta kware a rubutun Hausa ita kuwa ba ta da wannan kwarewar  wannan ta sanya ba ta yi mata sai rubutun Hausar ajami. 

Wannan farin cikin na Humaira kadai ya isa daɗaɗa zuciyar Maryam, ya kawar mata da dukkan damuwa. Burinta kenan sai  dai tilas ta ɓoyeshi, ta san dadin ilimi daga na arabin har boko, ganin Malam ba ya ra’ayi bata taɓa nunawa ba koda wasa. Ta yi mata alamar ta je ta nunawa su Gwaggo. 

“Toh.” Har za ta tafi Maryam ta buga kasan kafet. Humaira ta juyo, alama ta yi mata akan ta dawo. Ba musu ta zo, takarda ta dauka ta yi dogon rubutu mai sirki da English ta miƙamata. Gemu ta nuna da hula. 

“Wa zan ba? Malam?”

Ta girgiza kai alamar a’a. Can ta dan tsaya nazari kafin ta ce 

“Baba Hashim?”

Ta gyada kai tana murmushi, Humaira ta fice da sauri da ledar kayan. A tsakar gida ta yi kiciɓus da Hashim ya fito domin wucewa, shima yanzun ba zama don yana hada-hadar  soma shigo da kaya katafaren shagon da ya bude a Yobe. 

“Baba Hashim.”

Ya dubeta da murmushi.

“Ya akai ɗiyata?” 

Takardar ta miƙa masa.

“Gashinan in ji Mama.”

Da sauri kuwa ya karɓa ya yi godiya ta wuce sashin Gwaggo Kubra. 

Rubutu mai kyau da burgewa, sallama ce sa godiya ta biyo baya da fatan alheri da addu’a. Murmushi ya yi sai dai ya yi mamakin yanda ta iya rubuta turanci, tausayinta ya ƙara kamashi, bai ta6a zaton ma ta yi makaranta ba sai dai dama ba ta yi kama da jahila ba. 

Ganinta yake da muradi sai dai ba zai iya shiga ba saboda bata ji balle ta ji sallamar da zai yi ta kimtsa don haka ya hakura kawai ya fice bayan ya sanya takardar a aljihu. 

*****

Kamar da wasa, a hankali shaƙuwa ta soma shiga tsakanin Adam da Fu’ad, sukan mance ainahin dangantakarsu a zahiri, zasu yi wasa da dariya. A hankali Adam ya fahimci daga Fu’ad har Haidar masu wasa da ibada ne. Koda zasu yi ba su yinta kan lokaci hakanan akwai gyara a ibadunnasu. Alokacin ya kara yarda da zancen Dr Ibrahim cewar zai iya zama silar shiryar Fu’ad. 

Ya kuma fahimci suna da zuwa club hakanan don su shafi mace su sumbaceta da ma sauransu ba komai bane a wurinsu. 

Zuwa lokacin Fu’ad ya koma gida, sai dai duk sadda ya ganshi a Hotel ya san tare yake da Hanan. 

A bangaren Hanan ji take babu abinda zai iya rabata da Fu’ad. Ta lura mua’amalarsu ta ɗan ja baya tun shigowar Adam rayuwarsa. Domin sau da yawa idan ya ga sun shigo sai ya ja shi su fice daga Hotel din. A hanya zai ta yi mishi nasiha akan ya ji tsoron Allah da sauransu. Wataran ya kai su cin abinci wataran kuwa ya kai su shopping ko gidan Dr Ibrahim duk don ya ɗauke hankalinsa daga aikata masha’a. To haka ko sun dawo daga ya yi kokarin ta6a Hanan sai ya fasa. Duk yanda ta kai ga jan ra’ayinsa ba don yana so ba haka yake danne zuciyarsa ya hakura dakyar. Karshe ya raba shimfida da ita. Wannan ya sanya Hanan ta tsani tarayyarsu da Adam. Abin ya haɗemata ya zamar mata zafi biyu wanda ya zama tilas ta nemawa kanta mafita.

*****

Juya wayar yake lokaci guda yana juyi saman kujerarsa ta ofis. Ba jimawa ya ji shigowar saƙo. Abinda yake jira kenan, don haka ya duba. Daga Bank ne, an tabbatar masa transaction dinsa ya yi. Don haka ya kira Halima. Ba jimawa kuwa ta ɗaga.

“Yes, na yi receiving alert, mun kashe wannan saura ɗayan.” 

Hayat da ke jin kamar ya maƙureta a fusace ya amsa.

“Wanne kenan?”

“KA AURENI.”

Ya ji maganar tamkar saukar aradu a kunnuwansa, a gigice ya yi miƙewar da bai zata ba. 

“Ba ki da hankali!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 14Rumfar Kara 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×