Ta yaya? Yaushe kuka ɗinke har haka?"
Tiryan-tiryan Adam ya bata labarin komai tun daga farko. Umma banda murmushi ba abinda take zabgawa karshe ta yi hamdala ga Allah. Sosai ta yi mishi nasiha akan ya cire komai a ransa ya rungumi Fu'ad tamkar ciki daya suka fito.
"Ba ruwanka da alaƙarsu da mutane biyun nan (Hayat da Salma), Ka kaunaceshi domin Allah. Da zuciya daya, Allah Ya yi muku albarka."
"Ameen Umma."
*****
Gaisuwa irin ta kurame Maryam ke mishi, har sai da Yaha ta ce.
"Baba ana gaidaka." A sannan ne ya ɗan yi firgigit. . .
👍