"Ya farfaɗo, Alhamdulillah."
Fadin Dr Ashir yana duban dattijon marar lafiyar a lokaci guda kuma yana amsa wayar Adam da ya nemi ba'asi.
Dattijon ya yi mishi ƙuri yana dubansa, a hankali ya ji ya soma dawowa hayyacinsa. Ba da jimawa ba ya tuno da yanda motarsu ta yi dabo a titi ta faɗa can gefe. Bai manta salatin da kowannensu ke yi ba. Alokaci guda ya tuno da sadda mahaifinsa ya rike hannunsa gam yana kalmar shahada.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ku kaini wurin Babana, ku kai Ni na ganshi." Fadin Dattijon yana rike da. . .