"Sunanta Rumaisa. Ita ce matar da na soma aura a zamana a London."
Abinda ya furta ya sanya suka shiga kallon kallo a junansu sai dai ba wanda ya katse shi. Hakan ya sanya ya ci gaba.
"Idan ba ku manta ba na fadamaku a zamana a London nayi ɓarna kala-kala. Sai dai Alhamdulillah Allah Ya tsareni daga aikata zina. Babu wannan a cikin ɓarnar da ɗan uwanku ya aikata. Abokina daya a London, Suwaid. Shi ya koyamin shaye-shaye domin ba irin abinda ban taɓa sha ba a zamana a can. Ya kasance mu ne can wurin. . .