Kuka sosai yake yi yana ambaton Allah. Faɗi yake.
"Na yarda ɗannan, na yarda da kaddarata ce hakan. Bar nunamin madubi. Allah Yay maka Rahma Malam, Allah Ya ji kanki Nasiba. Allah Sarki Hassan da Al'amin."
Buhari ke wannan maganar yana kuka bayan gama ƙarewa kansa kallo a madubi wanda Dr Ashir ya nunamasa. A baya ya dauka tamujewar fatarsa sakamakon hatsarin da suka yi ne, sai dai furfurar da kuma girman da ya gani ƙururu a madubin ya sauya tunaninsa. Wannan bai girgizashi ba sai da ya ji shekarun da ya kwashe a wannan halin da kuma. . .