"Ita kuma wace ce?"
"Ɗiyata ce wacce Bariki ta bani."
"Kar ki mana shirme mana!" Salma ta dakatar da ita da faɗin haka.
"Ba shirme bane, ku dai ku nutsu saboda ni inada yaƙini akan Hanan za ta aikata ko menene idan muka sanyata. Amman fa barewa ba tai gudu ɗanta ya rarrafa ba, sai kun ba ta abinda za ku iya, tunda jihadi ne."
"Sai ka ce aikin Allah? Toh ko aikin Allahn ai a ɓagas ake yinsa don samun rabo a aljanna. Kee Halima, idan za ta yi, to ta yi. Idan kuwa a'a..."
"Salma. . .