Skip to content
Part 24 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Ita kuma wace ce?”

“Ɗiyata ce wacce Bariki ta bani.”

“Kar ki mana shirme mana!” Salma ta dakatar da ita da faɗin haka.

“Ba shirme bane, ku dai ku nutsu saboda ni inada yaƙini akan Hanan za ta aikata ko menene idan muka sanyata. Amman fa barewa ba tai gudu ɗanta ya rarrafa ba, sai kun ba ta abinda za ku iya, tunda jihadi ne.”

“Sai ka ce aikin Allah? Toh ko aikin Allahn ai a ɓagas ake yinsa don samun rabo a aljanna. Kee Halima, idan za ta yi, to ta yi. Idan kuwa a’a…”

“Salma wait please, haba mana, kar ki ɓata sha’anin. Cool down my heart.”

Hayat ke maganar cikin lallashi da kwantar da kai, kan Salma ya fasu, ji tayi inama tare suke a wuri guda ko don ta ga fuskar Halima. Sai dai dariya kawai ta ji Halimar ta yi gami da faɗin

“Sannu-sannu ba ta hana zuwa. Toh yanzu dai me ku ke tsayar?”

“Zamu yi shawara, duk abinda ake ciki, za ki ji mu.” Hayat ya furta daga nan suka cire Halima a conference din.

“My heart maganar ba ta waya ba ce, ki bari na zo tukunna sai mu san abin yi.”

“Ai shikenan, sai ka zo. Ina ƙara jaddada maka, ka kauracewa duk hanyoyin haɗuwarku da ita.”

“Wannan ba matsala bace.”

Daga nan suka yi sallama.

*****

Filo ya ji an maka mishi a fuska wanda ya sanya shi wartsakewa. Ya yi wurgi da filon kamar wani ƙaramin yaro ya ce

“Haba Dr, za ka yimin lahani a fuska.”

Dariya abin ya ba Adam da ke tsaye rike da brush da soso yana kokarin shigewa bandaki. Ya kalleshi kawai ya juya ya fada banɗaki. Har ya yi wanka ya fito Fu’ad bai tashi ba. Ganin haka ya dauki ruwan dake ajiye a cup saman bedside drawer ya watsa mishi a fuska. Shiru Fu’ad ya yi yana kallonsa a gigice, gaba daya ya tsorata. Me Adam zai yi ba dariya ba? Fu’ad kuwa shi har mamakin Adam din yake, daga jiya zuwa yau wata iriyar annashuwa yake ciki.

Ya mike da sauri ya zo ya tsaya gaban Adam gami da nunashi da yatsa

“Don Allah Dr meke faruwa?”

Cikin rashin fahimta Adam ya daga kafada.

“Kamar me?”

“Kamar kamar wanda ya faɗa soyayya.” Faɗin Fu’ad yana mai kashe masa ido ɗaya. Adam ya basar gami da karasawa gaban madubi yana goge kansa da tawul sai dai can kasan zuciyarsa murmushi yake da take neman suɓutowa a saman fuskarsa.

“Na canka kenan.” Fu’ad ya furta yana murmushi. Kallon kansa ya yi sosai a madubin, dagasken murmushin yake wanda yake ganin tamkar a baɗini yake yinsa. Ya juyo ya harareshi.

“Malam shiga ka yi wanka, Umma ta kira waya muje da wuri ayi breakfast da mu.”

Jin sunan Umma ya sanyashi tunawa da sahibarsa. Da saurinsa ya shige har ya ba Adam dariya da mamaki. Kafin ya fito Adam ya shirya tsaf cikin yadi baƙi mai kyau wanda ya dace da kalar fatarsa. Kansa babu hula.

Fu’ad shima ya shirya cikin shadda milk shima kan babu hula.

Har Adam ya fita ya dawo Fu’ad na tsaye yana karewa kansa kallo yana shafar suma.

“Kai, wai zance za ka je ne?”

Ya yi murmushi.

“Wa ya sani?”

“Ko? Wurin wa?”

Fu’ad har ya bude baki zai magana sai kuma ya yi wani tunani ya juya akalar zancen.

“Wurin Ummana zan je, kaga kuwa gwara ta ga ɗanta tas.”

Murmushi Adam ya yi.

“Hakane, sai ka ƙara da yin aski don wannan sumar taka ta yi yawa. Tsaf za ta kitsu.”

Suka yi dariya.

Fu’ad zuciyarsa gaba ɗaya tana ga Amira.  Burinsa ya yi tozali da ita. Ganin yanda yake taka motar ba da wasa ba ya sanya Adam yi mishi magana.

“My Lil, wannan gudun duk na don ganin Umma ne?” To ni wallahi ban shiryawa mutuwa ba, ban tara iyali ba.”

Ya ba shi dariya sosai har da sakin sitiyari.

“Mutuwar fa ɗaya ce jal.”

Harararsa Adam ya yi da wasa.

“Idan yanzu muka yi hatsari muka mutu ai ya zama har da gangancinmu. Mun wuce ƙa’idar tuƙin.”

A dole Fu’ad ya rage gudu yana murmushi.

*****

Amir da Amira suka soma riska a falon. Fada suke akan remote control, yana ya rigata ɗauka kuma wrestling yake son kallo, yayinda ita kuma ta tiƙe tana so ta kalli Zee World.

Sallamarsu bai sa sun bar jayayya ba.

“Meye hakan?”

Muryar Adam ta katse su. Fu’ad da tun shigowarsu idanunsa suka sauka kan Amira, banda murmushi ba abinda yake zabgawa. Ta yi mishi kyau cikin doguwar riga na material kalar ja.

“Yaya na fa rigashi zuwa falon, na ma rigashi daukar remote din amman wai shi sai ya saka wrestling ni kuma Secret Love nake son kallo.”

Maganar take kamar mai shirin fashewa da kuka. Adam ya dubi Amir.

“Ba haka bane.”

Ya fadi yana mai jan bakinsa ya yi tsit ganin Fu’ad a gefen Adam yana dariya. Amira ma ba ta kara magana ba suka gaisheshi. Har lokacin ita kam ta kasa sabo da shi, ta kasa daukar yanayin kallon da yake mata, wannan ta sa ta nemi wuri ta zauna ta bar Amir da ƙorafin a bari ya kalli Kokawa.

“Da ku ke wannan abin, inace kun soma test.”

“Sai Monday zamu soma.”

Fadin Amir, Amira Baki ya mutu sakamakon Fu’ad da ya yi zaune yana satar kallonta.

“Dakyau, to babu wanda zai kara kunna kallo. Zan faɗawa Umma kada a ƙara bari waninku ya yi zaman kallo.”

“Ni a bani labarin Secret Love.”

Fu’ad ya furta wanda hakan ya yi sanadin kallonsa da Adam ya yi gami da ƴar harara. Ya soma ɗagoshi daga yanayin kallon da yake kiran Amira da shi. Bai san meyasa ba, hakanan ya ji ba ya son shi da ita.

“Shiga ki cewa su Umma mun iso.”

Dama neman hanyar guduwa take don haka ta mike da sauri har tana tuntuɓe ta shige ciki.

Harara Fu’ad ya samu daga Adam, ya yi ƴar dariya gami da shafa ƙeya.

Anti Khalisat ta ɓullo daga kicin tana dubansa da murmushi.

“Ashe ku ne, ina ta jin tashin muryoyi.”

Suka gaisa kafin fitowar Umma.

Gaba daya suka hadu a tebur har Uncle Hashim. Umma ta shiga waige.

“Ban fa ga ɗana ba.”

Anti Khalisat ta taɓe baki.

“Uhum, rabu da wannan ɗan naki, yana can yana wani cika da batsewa na rasa dalilinsa.”

“Me ke nan?” Fadin Hashim da kulawa.

“Oho mishi.”

Umma ta dubi Amir.

“Maza je ka kiramin Yayanka.”

Har Amir ya tashi, suka ji motsinsa yana saukowa daga saman bene. Amira ta dubeshi kadan ta kauda kai. Tasan ita ce silar ko mene, a jiyan ya yi ta mata sababi akan wai tana wulakantashi.

Suna haɗa ido ya kauda nashi idanun ita kuwa ko a jikinta. Ya ƙaraso ya gaida iyayen kafin ya mikawa Adam da Fu’ad hannu suka gaisa.

“Meke damunka ne?”

Hashim ya buƙata.

Yamutse fuska Shuraim ya yi.

“Kaina ke ɗan ciwo.”

“Uhm.” Shi ne furucin da Anti Khalisat ta yi. Tasan take-taken ɗan nata, ita kuwa ba za ta taɓa yarjewa ba don ba son haɗin take ba.

“Yauwa, Salima wuraren karfe biyu za ta sauka. Idan ka sha magani zuwa anjima kai za kaje ka daukota.”

Jin an ambaci Salima ya sanya Amira satar kallonsa. Yanayinsa ba dadi sai dai su na hada ido ya maida duba ga Anti Khalisat yana murmushi.

“Allah Ya kaimu.”

Daga nan aka shiga ba ciki hakkinsa wuri ya yi tsit. Sai da aka kammala Hashim ya dubi Adam a nutse.

“Yaushe za ku koma Kanon?”

“Sai gobe da safe in sha Allah.”

“Allah Ya kaimu. Shima ɗan nawa ya biyemaka ya ƙi fidda matar aure ko?”

Ya ƙarashe da maida akalar zancen kan Fu’ad. Murmushi ya yi yana satar kallon Amira.

“A tayamu addu’a. Idan ta kama sai ayi mana na dole ma.”

Aka sanya dariya.

“Allah Ya kiyaye.”

Faɗin Umma.

Sun kwashe kusan awanni uku a gidan kafin su soma shirin tafiya asibiti wurin Engineer daga nan su yi babban gida. Adam ya san yau zasu je Kauyen Cinnaku domin kai Malam Buhari. Sai a bakinsa ma su Umman ke jin abinda ya kasance sun kuwa sha mamaki. Gami da taya Malam murna.

Bayan tafiyarsu Amira ke satar kallon Shuraim, haka kawai take jin ba daɗi yanda yake cin magani.

“Ki tashi ki goge muku kayan islamiyya.”

Muryar Umma ta katse ta, ta mike jiki lakwas ta fice. Sai a sannan ya bi bayanta da kallo kafin ya kauda kai. Amira na hargitsa tunaninsa, Yana kaunarta sai dai ta ƙi fahimta, a komai gani take wasa kawai yake. Guntun tsaki ya ja gami da miƙewa ya bar falon gaba ɗaya. Ita kuwa kasa hakuri ta yi ta samu takarda ta rubuta mishi gajeran saƙo sannan ta dunkule, sauri ta yi ta shiga falonsa ta ajiye inda ta tabbatar zai gani, a hanyar dawowa ta hangoshi, da wani irin gudu ta ɓoye a ƙasan bene. Bayan wucewarsa ta fito.

Koda ya gani murmushi ya yi, abin ya burgeshi ko ba komai ta san da zamansa ko yaya ne. Hakan ya sa shi sumbatar takardar gami da adanawa a cikin kaya. A cewarsa tarihi ne.

*****

Misalin karfe sha daya Yaha ta fadamusu sakon Malam akan su shirya Adam na hanya.

Kaya take sanyawa sai dai duk fuskar ta a dagule babu wata walwala, tana jin ciwon mara tana kuma tuna yanda suka yi da wata a islamiyyarsu. Sunan da ke jikin littafinta ta gani, wato Humaira Baffa Zubair. Ta ce sunan ya yi iri daya da na yayanta har ta ke tambayarta ko babanta ne. Ta ce a’a, baban Mamanta ne. Budurwar ta tambayi sunan mahaifinta da dalilinta na ƙin sanyawa, wannan ya jefata dogon nazari. Tun tasowarta take ganin Baffa Malam kamar babanta, a karshe ta gane baban Mahaifiyarta ce. Daga bisani kuwa ta ji labarin wai ba ta da asali a bakin Yalwa matar Yaron Malam. Yanzu ta san me kalmar da Yalwa ta fadi ke nufi, sai dai tana son tabbatarwa amman tana tsoron ƙarawa Mamarta damuwa.

Har ta kammala sanya kayan kasancewar tare zasu je Kauyen har su Malam Kabiru, ta karasa gareta, tana zaune tana jan casbaha, itama ta yi shirinta tsaf cikin doguwar riga da hijabinta har ƙasa.

Hannunta ta riƙo wanda ya sanya ta kallonta.

Ta yi mata alama da hannu akan damuwarta. Humaira ta yankwane fuska har da ƴar kwalla. Ta mike ta dauki takarda ta yi rubutu.

“Mama cikina ciwo yake min.” Ta zaɓi faɗar hakan kawai saboda ba ta son tona sauran sirrin zuciyarta.

“Sannu, je ki maza ki fadawa Gwaggo.”

Ganin amsar Maman ya sanya ta miƙewa tana tafiya kamar wacce ake yiwa allura a ɗuwawu. Idanunta ya rufe saboda azabar ciwo har tasa ba ta lura da takalman da ke a gaban dakin Gwaggon ba. Sallama ta yi ta shiga, idanunta ya soma sauka kan Gwaggo ta zauna tana riƙe da cikin tana runtse ido kadan.

“Ke Indo, lafiyarki kuwa?”

Humaira tana hawaye ta ce.

“Gwaggo cikina ke ciwo sosai, Mama ta ce na zo na fadamaki.”

“SubhanAllah, bari a jiƙa maki kanwa.”

“Allah Ya kiyaye! Haba dai Gwaggo, yanzu ai an wuce wannan lokacin.”

Fu’ad ya furta kansa tsaye, sai a sannan ta gane ashe da mutane, ta ɗago kai ta dubesu. Karaf suka haɗa idanu, ya yi shiru yana ƙaremata kallo cike da nazari. A gefe guda kuma sirrika ne daban-daban.

“Taso ki zo.” Ya fadi yana dubanta. Ta mike ta karasa wurinsu har lokacin tana riƙe da saitin mararta.

“Af, ga ma likitan abin a zaune. Mancewa nayi.”

Fadin Gwaggo, suka yi dariya banda shi da Humairar. Rigar ya kama zai ɗaga, ta sa hannu ta rike hannunsa da zummar hanashi, ya dubeta. Ba ta san sadda ta

saki ba, ya kai hannu ya taɓa wurin da ke ciwon. Ya ɗan daddanna wanda ba shiri ta sulale ta zauna kan ƙafarsa, ya janye da sauri.

“Kina al’ada?” Ta ji tambayar kamar daga sama, wata kunya da ba ta san tana da ita ba ta lulluɓeta.

“Tana yi mana.” Cewar Gwaggo iyakar gaskiyarta.

“Ta ya ya za ka kalli wannan yarinya ka ce ba ta soma al’ada ba, ai tana da jikin girma.” Ta ɗora da hakan.

“Answer me.” Ya furta da sanyin murya.

A hankali ta girgiza kai.

“Ke Indo bana son ƙarya, yanzu ba kya al’ada?”

Sunan ma kunya yake ba ta, ta san me yake nufi sarai saboda wata yar uwar Jamila ta taɓa somawa taron wani biki da suka je, kusan ita ce ma ta soma gani ta dauka ciwo ta ji har ya ɓata kayanta.

“Gwaggo please ki shiru mana.”

Adam ya katse ta. Gwaggo ta taɓe baki. Sallamar Baharu ya ja hankulansu. Fadamusu ya yi Malam ya ce su fito a wuce. Adam ya zari mukulli ya damkawa Fu’ad domin ya tada motar. Gwaggo kuwa ta wuce sallama da maigidanta. Ya rage daga Adam sai Humaira.

“Humaira.” Bai taɓa ambaton sunanta kai tsaye ba sai ai Gorgeous, yau da ya furta sai ta ji wani banbarakwai, ya ƙara sanyata jin wata irin kunya da nauyi.

“Uhm.” Ta amsa.

“Al’ada za ki soma, shi ne dalilin wannan ciwon naki. Yanzu zan rubuta magani na bada a siyomaki. Sai dai fa ba inda za ki bi mu. Ki yi zamanki a gida, I promise you zan kula da Mama kamar kuna tare.”

Kamar ta ce mishi a’a tana son zuwa ta kasa, kunyarsa take ji ba kaɗan ba. Wannan tasa har ya fice daga ɗakin ba ta ɗago kai ba. Tuni abinda ya ce ta miƙe, a lokacin ta ji zubar wani abu a wandonta. Wurin Mama ta je ta yi mata rubutu a takarda.

“Wai ku je, ni ance na zauna saboda bani da lafiya.”

Murmushi Maryam ta yi tana kokarin danne damuwarta tun sadda ta ɗago matsalar yarinyar. Babbar damuwarta wataran za’a ce Humaira za ta yi aure. Idan ta tuno hakan yakan taɓa ranta.

Gwaggon ce ta shigo da sallama ta ba Maryam umarnin fitowa. Humaira kasa motsawa ta yi domin ruwan da take ji yana zubomata. Bayan tafiyarsu ba jimawa Baharu ya shigo ya miƙomata leda. Ta karɓa, ganin always sai ta tsaya tana juyashi cikin rashin sanin taƙamaiman yanda za ta yi amfani da shi. Allah da ikonSa sai ya jefo Yaha gidan. Tun safe ta fita kai abinci wurin Engineer.

“Baaba!” Ta kwalawa Yaha kira da sunan da take kiranta. Ta amsa kafin ta shigo.

“A’a, Indo ba ki je ba?” Ta gyaɗa kai. Kamar ta yi kuka domin ta so zuwa. Nuni ta yi mata da always din gami da neman ƙarin bayani a kunyace. Nan da nan Yaha ta koyamata komai ta kuma sanyata zuwa ta sauya.

Bayan ta fito Yaha ta zaunar da ita ta yi mata doguwar nasiha sosai gami da nunamata ta girma banda biyewa ƴan ajinsu na boko a yi ta tsalle- tsalle domin yanzu ita ba yarinya ce ba a cikinsu. Ta yi mata dogon sharhi ta ɗora da wanda aka yi musu a Islamiyya game da mace baligaggiya. Humaira ta ji wani kunya da nauyi sun lulluɓeta, ta ji kamar wata sabuwar rayuwa ta shiga wanda dole sai ta yi takatsantsan kuma ta kiyaye lamuranta. Koda dai dama can ba sakarwa mazan fuska take ba. Jim kadan sai ga Baharu da ledar magani, ya miƙamata. Ta karɓa ta sha sannan ta koma ta kwanta. Hawaye ta shiga zubarwa gami da juya zancen Iklima ƴar ajinsu. Dagaske ne Baffa Malam sunan baban Mamarta ce, toh ita kuma ya sunan nata uban? Koda ya mutu tana da bukatar sanin sunansa. Da wannan tunane-tunanen bacci ya sureta.

*****

Inno ta yiwa Malam tambaya ya fi a kirga.

“Malam ka tabbatar dai lafiya ce za ta taso Malam Kabiru daga Yobe zuwa nan? Ya taɓa zuwa dama? Toh ko dai Maryam ce ta warke? Ko kuma wani laifin Humaira ta yi?”

Wannan shine kala-kalar tambayoyin da take mishi, gaba daya cikin fargaba take ta kasa samun sukuni da walwala. A karshe dai ya ce.

“Haba don Allah Fatima, nima ina zan sani? Sai dai mu kwantar da hankalinmu, kamar yanda yana tafe da baƙi. Mu tarbesu hannu bibbiyu, na fi tunanin ma yan uwan Maryama ne suka bayyana in Sha Allah. Ba ki ji nace baƙi ba?”

Inno ta gyaɗa kai tana murmushi da fatan ya kasance hakan. Ya dora da fadin.

“To kin gani, addu’ar zamu yi Allah Yasa hakan ya kasance. Yanzu dai akwai abinda ku ke buƙata na girkin ko kuwa shikenan?”

Ta kai duba ga zabbin da surukanta ke gyarawa na jan miya a gefe kuwa Jamila ke damun fura. Ta girgiza kai.

“Komai ya hadu.”

Ya yi hamdala sannan ya fita waje. Ta koma bakin aiki, Yalwa gaba daya bakin ciki ya cika zuciyarta. Ta dauki wannan matsayin rainin hankali. Suna gidansu a taso su aikin uwar miji acewarta. Banda ma wannan tana tunanin iyayen Maryam ne suka bayyana. Ta san ba wata tsiyar za’a yaga a jikinsu ba. A bangaren Jamila kuwa banda murna da son ganin Humaira ba abinda take, so take ta bata labarin yanda sosai take gane karatun boko take kuma daukarsa. So take su yi hirar yaushe gamo domin ba karamar kewarta ta yi ba.

Sai wuraren karfe biyu suka isa Yobe. Tsayuwar motocin guda biyu ya dauki hankalin Malam Kabiru da ke tsaye yana ba Haidar wanda ya zo hutu daga ABU Zaria umarnin siyo ruwan sha na roba. Ya dubi motocin har suka tsaya. Daya motar gidan Baba Engineer ne wanda direbansa ke ja, yayinda dayan na Adam ne. Malam Kabiru ne ya soma fitowa kafin Malam Buhari. Wannan ya sa Malam Zubair mutuwar tsaye. Ta ina zai iya mance fuskar da yake kwana da tashi da tunane-tunanensa? Ta yaya? Mutumin da ya yi silar kawo haske cikin rayuwarsa? Ya yi silar da ya fita daga duhun jahilci?  Da sassarfa Malam Buhari ya ƙaraso ya rike hannunsa.

“Zubairu? Kai nake gani ba mafarki nake ba?”

Malam Zubair da jikinsa har rawa yake ya kasa magana sai motsa baki. Hawayensa na zuba, abinda ya tada hankalin Haidar kenan, kusan zai iya cewa bai taɓa ganin hakan a fuskar mahaifinsa ba.

Suka rungume juna suna kukan murna da farin ciki, kukan da Allah kaɗai Yasan tarin  damuwa da farin cikin da suke ciki.

A cikin gida kuma Inno ta rasa sukuni, sai zirga-zirga take.

“Fatima! Fatima!!”

Malam Zubair ya dinga kwalawa matarsa kira. Inno ba ta san sadda  ta zabura ta fito daga ɗaki ba. Gaba daya wurin mijinta ta nufa ta rikeshi.

“Lafiya Malam?”

“Ƴar Baba?” Malam Buhari ya ambaceta da sunan da ya saba. Ji tayi kamar a mafarki da saurinta ta waiga gareshi. Ta yi jim tana karemishi kallo kafin ta sulale ta faɗa jikin Malam Zubair duk aka yo kanta.

<< Rumfar Kara 23Rumfar Kara 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×