Bayan Shekaru Goma Sha Uku
Kauyen Cinnaku
Ga duk wanda ya san Kauyen Cinnaku a shekarun baya, zai yi mamaki bisa sauye-sauyen da ya samu a wannan lokaci. Babban abin burgewa bai wuce yanda addinin musulunci ya ratsa ƙauyen da ma makwabtansa ba. Malamai da dama sun shiga sun yaɗa addinin musulunci wanda cikin taimako na Allah aka wayi gari yanzu duk wani mai bautar Dodo to sai dai ya yi abinshi a ɓoye. Zuwan haske sai ya kori duhun da suke ciki, kan da dama a cikinsu ya waye, sun karɓi shahada. . .