Skip to content
Part 3 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Bayan Shekaru Goma Sha Uku

Kauyen Cinnaku

Ga duk wanda ya san Kauyen Cinnaku a shekarun baya, zai yi mamaki bisa sauye-sauyen da ya samu a wannan lokaci. Babban abin burgewa bai wuce yanda addinin musulunci ya ratsa ƙauyen da ma makwabtansa ba. Malamai da dama sun shiga sun yaɗa addinin musulunci wanda cikin taimako na Allah aka wayi gari yanzu duk wani mai bautar Dodo to sai dai ya yi abinshi a ɓoye. Zuwan haske sai ya kori duhun da suke ciki, kan da dama a cikinsu ya waye, sun karɓi shahada sun kuma ci gaba da bautawa Allah kamar yanda Ya yi umarni.  Da yawa sun mutu ba tare da karɓar shahada ba, sai jikokinsu da ƴaƴansu ya rage. Cikin zuri’ar Sarkin Dawa, matansa da dama basu tare bisa zuwan Musulunci da kuma tsarinsa. Wannan ta sa ya rabu da wasu, ya kuma yi aure irin yanda ya zo a shari’ar Musulunci. Matansa hudu sai yaransa goma sha shida cif da sukai saura a duniya. Maikudi mahaifiyarsa na nan a raye, itama Allah Ya bata ikon kar6ar musulunci, ya zamana ba ta da abin yi sai istigfari da hailala da salatin Manzon Allah s.a.w.  Samuwar wannan sauyi ne ya sanya Malam Haruna dawowa cikin garin Cinnaku sosai, ya zama shi ne babban malamin da ke koyar da wannan mutanen karkaran. Manyan almajiransa na taimakawa sosai.

Gwamnatin Jahar Borno ta taimaka kwarai wajen inganta ƙauyukanta. Ta hanyar basu wadataccen ruwan sha da kuma wutar lantarki. A fannin makaranta, ta gina musu makarantu na boko da Arabia, cikin ikon Allah basu jahilci lamarin ba, sai dai Malam ba shi da ra’ayin yara mata su yi boko. Wannan tasa mazan ne kaɗai suke yi. Daidai gwargwado sun samu sauye-sauyen a kauyen wanda hakan ba karamin nasara ce garesu ba, kasuwancinsu na Noma da safarar nono da man shanu yana kara haɓaka, suna samun rufin asiri daidai gwargwado.

Babu wani DAN ADAM da ba shi da buri a rayuwa sai dai burin wani ya fi na wani. Haka ma a bangaren yarinya Aishatul Humaira, ta taso da burin son zama cikakkiyar yar boko. A duniyar Aishatul Humaira babu abinda ke burgeta take kuma bala’in so irin ta ga yau an wayi gari tana zuwa boko. Sai dai kuma hakan ya saɓa umarnin Baffa Malam, kamar yanda take kiran Malam Haruna.  Duk ranar da akwai makaranta, takan yi yanda ta san za ta yi ta fita daga gida don kawai ta je cikin makaranta ta dinga bi ta bayan aji don ganin dalibai da malamansu. Idan kuwa ta ji ana koya musu turanci nan za ta zauna har wani lumshe idanu za ta dinga yi kawai don yaren na bala’in burgeta.

Yau ma kamar kullum Inno ta aiketa karɓo zogale a Lambun Malam ta ɓige da zuwa makaranta. Maigadin makarantar, Iro, kasancewar sun yi mugun sabo wannan karon ma bai hanata shiga ba. Gaisawa kawai suka yi ta shige. Saɗaf-saɗaf take bin bayan windunan makarantar tana wangale baki ganin yanda ake koyar da su. Ba ta tsaya ko’ina ba sai bakin kyauren ajin su Bilal. Malamin sai rangaɗa turanci yake abinsa, ta yi lamo tana saurare. Bayani yake akan Aikatau (Verb), wata kalmar ta gane a dalilin yawan zuwa da take wata kuwa ba ta fahimta. Bilal kamar da wasa ya dago ya hangeta, zaro ido ya yi don kusan kullum sai ta zo shi kuwa tsoronsa ranar da Baffa Malam za gane. Cikin sa’a itama ta dubeshi da manyan idanunta wadanda dogon gashin idon ya kara musu kyau. Haƙora ta wangale mishi har wushiryarta na bayyana a gefe daya dimple dinta na fitowa. Alama ya yi mata da hannu da nufin ta bar wurin. Ƙarshe ma ta hau noƙe kafaɗa, ganin zai takura da yawa sai kawai ta zarce bakin tagar ajin ta biyu ta tsaya. Nan dai ta fahimci Aikatau da misalansa sakamakon malamin yakan haɗa da Hausa yanda zasu fahimta. Koda ta ji Malamin na neman misali, tana jin sadda yaran suka soma bayarwa, ba zato suka tsinci zazzaƙar muryarta daga waje na fadin.

“Za Boy Come.” Gaba daya suka dubi wajen, sai dai tuni ta sunkuya a karshe ta fice a guje. Da mamaki Malamin ke bin bayanta da kallo a sadda ya leƙa ta ƙofa, magana yake amman ko alamar ta juyo ba ta yi ba. Ya dawo ajin, duk da cewa akwai gyara a kalamanta, hakan bai hana ya jinjinawa kokarinta ba, kusan ta fi da yawa daga cikin daliban nasa. Ya dubesu ganin suna dariya.

“Ku bar dariya, yarinyarnan ta fi wasunku kokari. Wa ya san ajin da take?”

Da yawa suka ce sun san dai tana zuwa ta tsaya bakin tagar ajinsu. Abokin Bilal, Nuhu ya yi wuf ya ce ai Kanwar Bilal ce. Malam ya dubeshi yana murmushi, Bilal dai ya yi shiru gaba daya ya tsure, idan Humaira ta jawo aka fadawa Baffa Malam ai har shi dinma zai iya hanashi zuwa kuma babansa bai isa ya tofa ba. Yana jin yanda Malamin ke kuranta ta, har a ransa ya ji dadi amman tsoro ya hana ya nuna.

Iro na daga zaune karkashin bishiyar mangwaro yana shan iskar dake kaɗawa sai ganin mutuniyartasa ya yi ta arto a guje.

“Ke! Fillo!” Haka yake kiranta, amman ko juyowa ba ta yi ba, gudu kawai take. Sai da ta tabbatar ta yi nesa da makarantar sannan ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya gami da gyara zaman ɗamarar da ta yiwa ƙugunta. Hannunta daya ta ɗora saman goshinta ta sharce gumi.

“Humaira!” Ta ji an kwalamata kira, ta juya tana duban mai shi. Jamila ta gani kanwar Bilal wacce suke sa’anni. Ido waje take dubanta har ta ƙaraso hannunta dauke da leda wacce ke cike da zogale har yana fitowa. Tana zuwa ta yi kwafa.

“Wallahi yarinya keda Inno, ta aike ki shi ne kika wuce yawonki. Ta ce za ku hadu ne.”

Jin wannan ya sa hanjin cikinta suka kaɗa amma don karfin hali ta murguɗa karamin bakinta.

“To kika san abinda ya tsayar da ni?”

Jamila ta yi gaba tana fadin.

“Oho! Ke kika sani ma. Inno da Mama na jiranki a gida.”

Ta yi wuf ta warci ledar zogalen, kafin Jamila ta yi wani yunƙurin ta ruga a guje tana dariyar mugunta.

Maryam na dama fura yayinda Inno ke zaune tana mitar jimawar Humaira, suka ganta ta faɗo gidan. Kallon da Maryam ta watsamata ne ya yi sanadin komawarta baya gami da rangaɗa sallama, sai da suka amsa sannan ta sanyo kai.

“Ina kika tsaya?” Maryam ta jefamata tambaya.

Shiru ta yi ba tare da ta amsa ba, ta ajiye ledar kusa da Inno tana sauke numfashi sakamakon gudun da ta sha, ƙarasawa ta yi bakin randa ta ɗebi ruwa ta sha. Sannan ta karasa ga Mamanta, idanunta narai-narai, kafin ta yi magana Jamila wacce ta shigo da sallama ta riga ta.

“Wallahi yawonta ta tafi can hanyar makaranta, nan muka hadu ta warce ledar.”

Jin haka Maryam ta dubeta a harzuƙe. Humaira ta rasa abin yi don ita kam ba ta iya ƙarya ba.

“Ahaf, dama ai na sani, idan Humaira ce fin haka ma. Allah dai Ya shiryamana ke. Kar dai ki ce za ki ta6a ta, duka ba ya magani. Malam kadai idan ya ji tana zuwa makaranta ai ba ragamata zai yi ba. A juri zuwa rafi kinji ko Humaira?” Duk Inno ke wannan bayanin kafin a karshe ta ja ledar  zogale ta umarci Jamila ta miƙo tray su cire.

Maryam dake kallon Humaira wacce tuni ta soma hawaye, a duniyarta tana tsoron abinda zai ta6a lafiyarta. Mamarta kam tana da hakuri sai dai idan abu ya kai ta bango ba ta iya ɓacin rai ba.

Ganin Mamar ta jinjina kai kawai ta juya ta ci gaba da aikinta sai ta karasa ahankali kamar wacce ta yiwa Maigari sata ta zauna gefen Inno. Aikuwa tana zama Inno ta sakarmata rankwashi a ka, ƙara ta saki kafin ta ankara ta rike kunnen.

“Wayyo Baba Malam!” Inno ta hankaɗeta.

“Kin ci kaniyarki kinji ko? Ja’ira, ke kam Allah dai Ya shiryamana ke Indo. Shi kansa Malam din idan ya ji abinda ki kai sai ya sa6amaki. Ai shikenan, kin yiwa kanki, kafata kafar Jamila zamu je Yobe mu dawo, babu inda za ki je.”

Ai Humaira na jin haka sai kwalla musamman jin Maryam ta cafe maganar.

“Kin min daidai Inno, ai gwara ta zauna nan da mu a gidannan, yarinya ba ta ji, a can ma haka za ta yita ficewa yawonta. Allah dai Ya shirya.”

Dariyar dake cin Jamila ta fito fili, hararar da ta samu daga Humaira dole ta kama bakinta. Ko ba komai ba’a kawomata wargi, kaifin idanun su Mama kadai zai hana ta ta6a lafiyarta a yanzun. Humaira ta yi kwafa, ta maida dubanta ga Inno.

“Innota Indonki ce fa, In Sha Allah na daina ban karawa. Ki tafi da Ni kinji.”

Inno ko kallo ba ta ishe ta ba, da ta yi magiyar ta gaji ta yi shiru sai dai ta saka a ranta za ta je Yobe. Ta jima tana burin zuwa Yobe, duk zuwan da Inno ke yi ba ta ta6a zuwa da ita ba, wannan karon ne Allah Ya dorata kan Malam ya ba Inno iznin tafiya da ita. Idan ta yi sake ta ɓata rawarta da tsalle ta san babu inda za ta.

Umar ne ya shigo da sallama, suka amsa suna dubansa. Da gudu ta mike ta isa gareshi.

“Oyoyo Kawu.” Yana dariya ya sakarmata ledar dake hannunsa.

“Humaira ƴar gatan Inno da Malam, ƴar gaban goshi ba kya laifi. Ga yalo maza wanko mu ci” Ta hau wage baki cike da jin dadi, tana son wannan kirarin da Kawunta Umar ke mata. Wuri ya samu ya zauna yana gaida Maryam da Inno, suka amsa. Ganin yanayin fara’arsa ne ya sa Maryam jefamishi tambaya.

“Auta ya dai? Da labari ne, irin wannan fara’a kamar an maka kyautar kujerar Makkah?”

Suka dara gaba daya, daidai lokacin Humaira ta dawo dauke da robar Yalo.

“Ai wato Alhamdulillah, wani abin farin ciki ya samu. Ina jarrabawar da muka yi ta kwanaki na larabci a birni?”

Kusan lokaci guda Maryam da Inno ke fadin eh.

“Cikin ikon Allah sakamako ya yi kyau, har an daukemu mu goma sha tara. Gwamnati za ta biyamana domin karo karatu a Madina.”

Ai fa bakin su Maryam ya ƙi rufuwa. Inno har da hawayen dadi, ta dubi Maryam da ta kasa ko magana sai washe baki tsabar murna.

“Alhamdulillah, Maryam kin ji abu kamar a mafarki? Autana zai je garin ma’aiki s.a.w? Kai Allah mun godemaKa.”

Sai a sannan Maryam ta tofa. Hamdala ta soma kafin ta kara duban Umar.

“Mun godewa Allah, Allah Yasa wannan somin ta6i ne. Alhamdulillah. Yanzu zuwa yaushe ne tafiyar?”

Shima bakinsa ya ki rufuwa ya amsa.

“Tukunna, sun ce nan da sati zamu je a yi shirin yi mana passport da dai sauran shirye-shirye na tafiya. Kuma za’a bamu kudi domin muyi shiri na kanmu kama daga suturu da sauransu. Kai, wai ina Malam ne?”

Ya datse maganar cikin tsananin zumudi da farin ciki.

“Ya leka gona, amma nasan duk inda yake ma yanzu ya dauko hanyar gida saboda ya ce ba jimawa zai yi ba.”

Murna ta hana bayin Allahn nan sukuni, Humaira bini-bini za ta jefamasa tambaya. Yanzu Yaya jirgi za ka shiga? Yanzu za ka shiga sararin samaniya? Wurin larabawa za ka je garin Manzon Allah s.a.w?

Haka ya biyemata yana amsawa  da In Sha Allah ba tare da ya gajiya ba yana dariya, Maryam da Inno suma baki ya ki rufuwa. Sallamar Malam ce ta katse musu hanzari. Suka amsa lokaci guda, Malam din ne a gaba sai Yaron Malam wanda ke riƙe da leda. A guje Humaira ta karasa ta rike hannun Malam tana dariya. Shima ya maida mata martani kafin ya dubi sauran iyalan gidansa. Ganin fuskokinsu cike da fara’a sai ya shiga saƙe-saƙe. To shima Yaron Malam kallonsu yake yana ta mamaki har suka ƙarasa Inno na musu sannu da zuwa.

Bayan zamansu Malam ya watso tambaya.

“Wai nikam yau meke faruwa haka? Naga fuskokin mutan gidan nawa kamar wadanda akai musu albishir da zuwa Hajji.” Suka sa dariya gaba daya, kafin Umar ya ce uffan Humaira ta yi caraf ta soma magana.

“Malam wai fa Kawu Umar ne…”

Sauran maganar ya maƙale a fatar bakinta sakamakon kallon da Maryam ta watsomata. Wannan ne dalilinta na yin gum da baki. Dariya Malam ya yi.

“Maryama kin fa soma matsantawa jikata. Zan dauki mataki.”

Murmushi kawai Maryam ta yi kamar yanda ta saba a mafi yawan lokuta. Tiryan-tiryan Umar ya yiwa Malam bayani. Tunda ya soma Malam ke uhm, uhm, a karshe da ya ji inda maganar ta dosa ya hau hamdala ga UbangijinSa. Yaron Malam shima baki ya ƙi rufuwa.

“Alhamdulillah, Alhamdulillah, mun godewa Allah domin ba kokarinka ne ya kai ka ba, haka kuma ba wayonka ba. To dama dukkan abinda Allah Ya hukunta, ba makawa sai ya faru komai nisansa kuwa. Wannan abu ne mai kyau, muna fatan Allah Ya sanya albarka a ciki, Yasa kuma an soma kenan.”

“Ameen.” Suka amsa baki ɗaya. Ranar kam farin cikinsu ba kaɗan ba.

*****

Mota ƙirar Mercedes Benz ta shigo farfajiyar gidan, jim da tsayuwar motar ne, yaro mai kimanin shekaru goma sha uku a duniya ya fito daga gaban motar sanye da Kayan makaranta. Dogon wando ne maroon sai farar riga, wuyansa shaƙe da necktie, a saman kafadarsa kuwa top din rigar ce itama maroon colour. Kallo daya za ka yi mishi ka fahimci cewa ba karamin gajiya ya kwaso ba. Ya yi nisa ya tsinci muryar yar uwarsa na kwala mishi kira.

“Kai Amir!” Ta furta da zazzaƙar muryarta, ya juyo yana yamutse fuska.

Baƙa ce kuma siririya, hasken fata ce kawai Amir zai nunamata, kamanninsuu har ya ɓaci, don ma akwai bambancin jinsi. Itama tana sanye da dogon wando maroon sai farar riga iyakar gwuiwarta mai tsaga a gefe da gefe. Kanta lulluɓe da maroon hijab. Tana goye da jakarta ta makaranta, yayinda ta riƙe jakar ɗan uwanta nata da kuma lunch box dinsa. Wata harara take watsa mishi.

“Wa ka bar wa waɗannan?”

Ya mararaice fuska.

“Haba Sister, don Allah ki kawomin na gaji wallahi.”

Daga haka ya juya ya ci gaba da tafiya, kwafa ta yi kawai kafin ta bi bayansa tana ji direbansu na fadin.

“Hakuri za ki yi Uwarɗakina. A yi ta hakuri da halin Amir.”

Uffan ba ta ce ba har ta shige.

Falon nasu ba kowa sai kamshin girki da ke tashi daga kicin, wannan ne ya sa ta nufar kicin din. Can ta tarar da Ummansu tsaye tana aiki, Yaha kuwa na daga zaune can gefe tana yankan Alayyahu suna hira. Ganin yanayinta ya sanya Umman murmushi, sai da ta ajiye lunch box din Amir kafin ta karasa ta gaida Umman da Yaha. Cikin dariya Yaha ta amsa.

“Yauwa Biyu, kema sannunki. Duk Amir din ne ya ɓatamiki rai kike cika da batsewa?”

Ta yamutse fuska.

“To ba shi bane kullum sai ya bar min jaka da lunch box dinsa kawai don ya sa ni wahala, ai ba shi kadai ya gaji ba.”

“A’a, Allah Ya ba ki hakuri, bar ni da shi zan mai fada. Amman ki yi hakuri tunda gaba yake da ke.” Fadin Yaha.

Zaro idanu ta yi.

“Wa din? Tab! Ai Umma na rigashi zuwa duniya ko? Shi ne a baya…”

Daƙuwar da Umman ta yi mata ne ya sanyata yin shiru gami da ficewa da gudu tana dariya. Yaha ta kyalkyale da dariyar itama.

“Amira akwai ɓarota.”

Umma na dariyar ta amsa.

“Ni har mamaki nake, a farko na yi zaton Amir ne zai wannan shirmen saboda ya fi ta wayo da su na yara.”

“Hakane, shiru-shirunta ita kamar na Adam, amma yanzu ta watsar.”

Damuwa ta bayyana saman fuskar Umma jin sunan da Yaha ta ambata sai dai ba ta ce uffan ba. Itama Yaha ta gama karantar hakan, shiyasa ta bar wancan babin ta shiga wani.

“Wai nikam yaushe ne tafiya Yobe? Bikinnan na kara kusantowa.”

Umma ta dubeta.

“Wallahi yana raina tafiyar, Abbansu ne har yanzu bai min maganar ba. Amma zuwa anjima zan tuna mishi idan na ci sa’a ya dauki wayar.”

Cike da tausayi Yaha ta kalleta, tasan wannan ma wata damuwar ce, shekaru fiye da ashirin amman ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Ta kara kauda batun.

“Toh, amman har Babban Yaya za’a ko?”

Da murmushi Umma ta dubeta.

“Inada yaƙinin ba zai ƙi zuwa ba da yardar Allah. Adamu ne fa. Ban ta6a cewa eh ya cemin a’a ba. Ban taɓa kuka bai sanyani dariya ba.”

Jinjina kai Yaha ta yi tana murmushin itama.

“Adamu bawan Allah, yaro dan aljanna. Biyayya kam Alhamdulillah. Sai fatan Allah Ya kara mishi. Bar shi dai da rashin sabo da wuri.”

“Meyasa za’a bar ni?”

Suka tsinci tattausar muryarsa daga bakin ƙofar shigowa kicin. Dubansa suka yi lokaci guda. Dogon saurayi fari ƙal, kallo daya za ka yi mishi ka hango tsantsar kamanninsa da Umman. Yana sanye da baƙin wando three quarter sai rigarsa fara ƙal.

“Kaga likita bokon Turai, dan halak ka ƙi ambato.”

Yaha ke maganar tana washe baki. Ya shigo cikin kicin din sosai yana murmushi. Sai da ya soma gaishesu kafin ya maida duba ga Umman.

“Zuwa Yobe ya tashi ne?”

“In sha Allah.” Umma ta amsa.

“Ok, Allah Ya nunamana. Zan je naga ɗan tsohon da ya ƙi rami.”

Umma ta kai mishi bugu a kafaɗa ya kauce yana dariya irin wacce Mahaifiyarsa kadai yake wa.

“Gidanku nace, Baba shi da mutuwa ba yanzu ba In Sha Allahu.”

Yaha da Adam suka dara. Ya ɗan ta6e baki da murmushi saman fuskarsa.

“Allah Yasa. Ina yaran nan?”

“Sun dawo ba jimawa.” Cewar Umma sa’ilin da ta sa hannu ta dauki wayarta da ta yi ƙarar shigowar saƙo. Sunan wanda ta gani bai bata farin ciki ba.

“Gobe zan dawo.”

Shi ne abinda ya rubuta kawai a saƙon ba batun in Sha Allah. Ta numfasa gami da dubansu, hira suke amma hankalin Adam na kanta. Ta ƙaƙalo murmushi.

“Abbanku na hanya gobe.”

Ya basar kamar bai ji ba.

“Bari na shirya zan leka asibiti. Ina zuwa.”

Daga nan ya ficewarsa. Sun san dawan garin hakan yasa ba wanda ya tsaida shi har ya fice. Fatansu Allah Ya shiga lamarin.

Washegari da misalin karfe bakwai na safe, mutan gidan na saman tebur suna karin safe idan ka cire Umma dake zaune kawai tana hira da Adam. Yana shirye tsaf cikin kayan aikinsa na asibiti, Amira da Amir suma sun yi shirin makaranta. Ba jimawa yaran suka mike, Adam ya basu kudin makaranta, sukai musu sallama suka fice.

“An sanya ranar tafiya Yobe kuwa?” Ya katse hirar ta hanyar jefowa Umman tambaya. Ta girgiza kai.

“Tukunna dai, sai ya dawo yau.”

Ta6e baki ya ɗan yi ba tare da ya ce uffan ba, to idan ya dawo din ma ɓacin rai kawai zai basu.

“Ya maganarmu da kai?”

Ya ɗago ya dubeta, sai kuma ya sunkuyar da kai ya kur6i ruwan shayi.

“Ka yi shiru.”

Cike da rauni ya ce

“Umma, ki za6amin duk macen da kika ga ta dace da ni.”

Kai ta girgiza.

“A’a, ba za’ayi haka ba, na fi so ka yi zaɓi da kanka. Na fi kaunar ka samu macen da ta yi maka wacce keda kyakkyawar nasaba da kuma addini. Zan dai tayaka addu’a Adam, sai dai ka dinga tunawa auren shi ne cikar kowane ɗan adam.”

Murmushi ya yi cikin son basar da batun kalmarnan ta SO.

“Anya kuwa akwai mai aurena? Bayan naji kina yawan cewa mu RUMFAR KARA ne, ba abin a dogara da mu bane? Nima dai ina tunanin kowace ƴar budurwa kallon da take min kenan, Rumfar Kara.” 

Ya ƙarashe yana mai yamutse fuska, Umman ta kai mishi bugu tana dariya, shi dinma dariyar ya yi har kyakkyawan wushiryarsa na fitowa.

“Ba ka mantuwa ko?”

Ya jinjina kai yana wani irin murmushi na gefen kumatu. Lokaci guda ya lumshe manyan idanunsa ya bude.

“Eh bana mantuwa, da yawa sun faru da ba zan mance ba. Ba na jin zan mance har abada.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 2Rumfar Kara 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×