Gaba daya mutanen dakin wadanda jikinsu ya yi la'asar, ga tausayi ga kuma jimamin aikin dake gaban Maryam anan gaba ya hanasu magana. Engineer ne ya daure ya magantu.
"Alhamdulillah, dukkan yabo ya tabbata ga Sarkin Sarakuna, hakika Maryam ke jikata ce. Dukkan wasu shaidu sun nuna hakan, kama daga sunan iyayen Rumaisa da kika ambata da ma sauran jawabai da suka zo daidai da abinda ya shafi Rumaisa. Ina mai kara jin ciwon rashin ganin Rumaisa na kara neman gafararta. Amman na gode Allah da naji cewar ta yafemin kuma ba ta riƙeni da komai ba. Maryam. . .