Skip to content
Part 30 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Gaba daya mutanen dakin wadanda jikinsu ya yi la’asar, ga tausayi ga kuma jimamin aikin dake gaban Maryam anan gaba ya hanasu magana. Engineer ne ya daure ya magantu.

“Alhamdulillah, dukkan yabo ya tabbata ga Sarkin Sarakuna, hakika Maryam ke jikata ce. Dukkan wasu shaidu sun nuna hakan, kama daga sunan iyayen Rumaisa da kika ambata da ma sauran jawabai da suka zo daidai da abinda ya shafi Rumaisa. Ina mai kara jin ciwon rashin ganin Rumaisa na kara neman gafararta. Amman na gode Allah da naji cewar ta yafemin kuma ba ta riƙeni da komai ba. Maryam kinga rayuwa, muna fatan kuma wannan ya zama na karshe. Ina da tabbacin ko su waye keda hannu a kisan mijinki, ba zasu samu kwanciyar hankali ba har i yanzu tunda basu da masaniyar ko kin mutu ko kina raye. Suna cikin razani a koyaushe na cewar kowane lokaci za ki iya riskarsu ki tona asirinsu. To ki sani cewa Allah Yana tare da mai gaskiya shi ne dalilin da har i yanzu suka kasa cin galaba a kanki. Kuma muna tare da ke domin a yanzu wannan yaƙin ba naki ne ke kaɗai ba, har da mu a cikinsa gaba daya. Da iznin Allah sai asirinsu ya tonu nan kusa ba da jimawa ba.”

Kowa ya tofa albarkacin bakinsa. Inno ta mike da nufin ɗoramusu sanwa wannan ta sanya Maryam bin bayanta tare da Baraka.  Gwaggo Hadiza dake juya sunan Salma da Fu’ad a ƙasan ranta ta kasa hakuri har sai da ta furzar.

“Nikam kodai Salmar da muka sani ce wacce Maryam ke magana a kai, itama fa kar ku manta mijinta rasuwa ya yi, kuma sunan ɗanta ya zo ɗaya da wanda Maryam ta faɗi.”

“Hakane Yaya, nima nayi wannan tunanin wallahi sai dai fargabar abinda zan ji ya sanya na kama bakina nayi shiru.” Gwaggo Hannatu ta furta. 

“Bana tsammanin hakan, saboda Maryam sun taɓa haɗuwa da Fu’ad a asibiti sadda aka kwantar da Yaya Engineer, da ace ta sanshi ko a fuska ai za ta nuna.” Rakiya ta yi maganar cikin shakku.

Murmushi Malam Zakari da Malam Kabiru suka yi.

“Mata kenan.” Fadin Malam Buhari a hankali yana murmushi.

“Ku kwantar da hankalinku don Allah, mu guji zargi akan abinda ba mu da tabbacinsa. Kar ku manta fa ba su kadai bane masu irin sunan a duniya. Idan ma hakan ne to mu sanya ranmu a inuwa don ita karya fure take ba ta ƴaƴa. Wallahi duk jimawa sa asirinsu ya tonu.”

Malam Zakari ne me wannan nasihar, a karshe kowa ya yi na’am aka share maganar sai dai tunanin hakan na nan a zukatansu, amman tunda aka yi batun bar wa Allah ikonSa, dole kowa ya kama bakinsa. 

Acan kuwa, Inno suna aikin tana ƙara kallon Maryam wani dadi take ji. Maryam ta kalleta suka yi dariya. 

“Na kasa barin kallonki ɗiyata, baki san yanda nake jina ba. Ba abinda zan yi face na ci gaba da godewa Ubangijina da Ya nunamin ranarnan, yau ga Maryama da baki da kunne har ma da tunani gaba daya.”

Maryam ta dara, a haka su Yalwa aka shigo don tuni Jamila ta kai musu labarin warakar Maryam da ma dawowa hayyacinta. Suka gaisa ta kuwa ji murya raɗau.

“Ikon Allah, ashe dai dagaske ne kurma an yi baki. To Allah Ya kara lafiya.”

Murmushi Maryam ta yi don ta riga ta saba da halinta, a yanzu kuwa yanda take jin farin ciki ba ta jin wani hargagi ko habaicinta zai addabi zuciyarta. Hafsatu ma ta ji dadi sosai, labari har gidan Sarkin Dawa da ma makwafta. Nan fa aka shiga sintiri a gida Malam Zakari, maza a waje suke tayashi murnar samun saukin Maryam yayinda mata ke shigowa suna gaisawa da baƙi da kuma tayata murna. 

Basu bar Kauyen Cinnaku ba sai wuraren biyar na yamma, sun tafi da alkawarin nan da kwanaki uku za’a shirya tafiya Maiduguri wurin iyayenta. 

*****

Tun bayan tafiyarsu Kauyen Humaira ke cikin zullumi da zaƙuwa na son ganin dawowarsu, dakyar Gwaggo ta takuramata ta shirya ta wuce makaranta, Baharu ya miƙa ta. Koda ta dawo ta tarar basu dawo ba sai ta ji duk ba dadi. 

“Ai fa kya gama turo bakin ki zo ki ci mutuminnaki ɗan wake, yau shi Yahanasu ta girka.”

Jin abinda Gwaggo ta faɗi ya sanya ta sakin fuska ta sauya kaya da sauri ta gabatar da sallar azahar sannan ta karasa dakin Gwaggo. Tana ci suna maida zance, can kuwa Gwaggo ta zabura.

“Allah gatan bawa, ke Indo, ya muka yi da wannan baiwar Allahn da ta zo jiya nan ta ce ƴar uwarta na hannunmu?”

Shaf itama ta manta da maganar ma. Kanta ya daure.

“Wace ce Gwaggo?” Yaha ta nemi sani, nan Gwaggo ta labartamusu yanda suka yi da Hanan wacce ko sunanta basu sani ba. 

“Kai na tuna, to ko dai ƴar uwar Mama ce?”

Humaira ta yi furucin. 

“Nima na zargi hakan, sai dai mene amfanin guduwa ta bar gidan ba tare da ta tsaya ba? Anya akwai gaskiya a lamarinnan?” Gwaggo ta fadi tana dogon nazari. 

“Ba ma wannan ba, ya akai ta ji labarinta, ya kuma akai ta zo gidannan takanas dominta? Gaskiya dai akwai wata a ƙasa. Ko aljana ce?”

Faɗin haka da Yaha ta yi yasa Humaira zabura ta koma gefen Gwaggo ta zauna. Ta kai hannu ta ja kwanon ɗanwakenta ta ci gaba da kai wa baka tana rarraba idanu. Dariya ta basu, Gwaggo ta dunguremata kai.

“Ashe tsoron naki na ƙarya ne, ai da sai ki bar abincin kar ki ci.”

Ita kanta dariya ta yi. Sai da ta kai ga cinye lomar da ta sanya a baka kafin ta ce.

“Allah kuwa ban manta fuskarta ba, dama ta yi kama da aljanun don fuskarta ta sha bleaching  har fa wani ja take yi. Mantawa ma nayi ban kalli kafafun ba na gani ko akwai kofato.”

Suka sa dariya gami da neman tsari. 

Koda su Maryam suka dawo nan kuma sabuwar hira ta ɓarke, anan ne suke jin labarin rayuwar Maryam din a gajarce daga bakinta, Humaira sosai take kuka jin cewar kashemata mahaifi aka yi. Ta dubi Maryam tana mai jin wani zafi a kirji.

“Ba zan taɓa yafewa wadanda suke da hannu a kisan Mahaifina ba, har abada na tsanesu. Na kuma tsani duk wani da ya raɓesu.”

Maryam cike da tausayi take kallonta sai dai ba ta ce uffan ba, Gwaggo ce ta shiga rarrashinta gami da yi mata nasiha. Dakyar suka samu ta yi shiru. 

Koda suka je kwanciya, Maryam ta shiga labartamata labarin kuruciyarta da yanda Yayyunta ke sonta suke kuma kula da ita, wannan ne ya ɗebemata dukkan kunci a zuciya har ta ji damuwarta ta ragu akan mutanen da suka kashemata mahaifi kuma suke bibiyar rayuwar mahaifiyarta. 

*****

Shaƙar da ta yi mata ba ta wasa bace, dakyar Halima ta samu damar ɓanɓare Hanan daga hannun Salma gami da watsawa Salmar mari hagu da dama. Ta nunata da yatsa tana huci kamar bakin kumurci.

“Ke Salma! Idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri, ina ruwan maza da wankan biƙi? Laifin Hanan ne ko naku da za ki shaƙemin ƴa? Ko itama kasheta kike son ki yi kamar yanda kika kashe mijinki?”

Salma ta kunduma uban ashar gami da daka tsawa.

“Halima! Wallahi ƙaryarku daga ke har ita! Marin da kika yimin kema kinsan ba banza ki ka ci ba, wallahi daidai nake da nake. Ai ko giwa ta rame, ta fi kwando goma wallahi! Don kafar Giwa ta take ta raƙumi. Sai na nunamaki bambancin aya da tsakuwa daga ke har ƴar iskar ƴar taki haihuwar tasha! Me kuka sani a bariki? Aikin banza kenan! Don kinga ana lallaɓaki? To ki sani ko yau na so ganin bayanku babu wani ko wata da ya isa ya tsayar da ni. Wai ma, shege shege ne! Shi kadai kan mance halacci. Ki sani Halima, duk wani kudi da kika mallaka yanzu, kar ki mance cewa da bazata kike rawa!”

Halima ta yi wata shewa gami da tafa hannu.

“Ahayye! Mai akwai ai shi keda ikon gorantawa, me kike da shi? Burgar banza kawai! Mun ga san asalin balbela, da ace kowaccenmu za ta koma rayuwar gidansu, tawa rahma ce akan tsummar rayuwarki.”

Hanan dai banda roƙonsu akan su bari ba abinda take yi, tsoronta kada Salma ta fusata ta hana aurenta da Fu’ad anan gaba, zuwan Hayat ne ya sa abin ya yi sauki. Gaba daya kuma suka hakura suka zauna aka nutsu. Fada sosai ya yi musu gami da yi musu nuni cewar tashin hankalin da ke gabansa ya wuce wannan. 

“Yanzu na gama waya da direban can gida Yobe, ya tabbatarmin Maryam ta dawo hayyacinta asalima har wurin wadanda suka soma tsinceta aka je ta bada kaf labarin rayuwarta. Sanin kanku ne asirinmu ya gama tonuwa, ya rage namu kuma mu san matakin da zamu ɗauka.”

Hankalin kowannensu kuma sai ya tashi.

“Na shiga uku! Yanzu shikenan za’a abinda muka aikata?”

“Me ku ka aikata?”

Suka tsinci muryarsa daga sama, Hanan kallo ɗaya ta mishi ta yi azamar jan gyalenta ta rufe fuskarta jiki na rawa, sai dai ta makaro don kuwa sunanta ya soma ambata.

“Hanan? Har da ke? Me kike yi a gidanmu? Sannan me kuka aikata?”

Fu’ad na maganar yana kara shigowa cikin falon, fuskarsa kamar bai taɓa motsa bakinsa har a ga haƙoransa ba. A can ƙasan zuciyarsa babu abinda yake ji illa bugun zuciya da fargaba, haka kawai ya tsunduma da tunanin ko dukiyar da suka mallaka ce ta tsafi, yanzu kuma asirinsu ke tonuwa.

“Fu’ad, yaushe ka dawo?”

Ya watsawa Salma kallon tara saura, irin kallon da rabon da ya yi mata tun yana Fu’ad ɗinsa ɗan shagwaɓa Kuma sangartacce. 

“Tambaya nayi babu mai amsamin Mum.”

Ya share tambayar da ta yi, ta rasa ta cewa. Halima ta yi ƴar dariyarsu ta ƴan duniya.

“Wane laifi kuwa suka aikata banda na nemamaka auren ɗiyata Hanan ba tare da sun faɗamaka ba? Kodayake nasan wannan abin murna ne gareka, ko ba komai kuna kaunar junanku ai. An bar shi matsayin surprise, muna fatan ba za ka baɗamana ƙasa a ido ba?”

Sam amsar ba ta dace da furucin da Mahaifiyarsa ta yi ba. Ana da labarin abinda suka aikata, tabbas ya san akwai lauje cikin naɗi ya kuma ci alwashin ganoshi nan kusa. Ya biyemata gami da sakin murmushi wanda ke nuni da cewar ya gamsu a barikance. 

“Lallai fa, wannan ƴar taki ai sai dai a kai kasuwa. Sahun giwa ya take na raƙumi. Matar Fu’ad na gidan Malam a killace ko ince gidan Liman. Allah Ya kawomata daidai da ita.”

Daga nan ya kashewa Hanan idanunsa masu kara dulmiyar da ita cikin so da kaunarsa ya fice gaba ɗaya daga gidan. 

Hayat bai wani damu da abinda ya ce ba don jin dadin bai ja maganar da tsawo ba, sai dai Salma yana fita ta girgiza kai. 

“Kayya, ban yarda da Fu’ad ba saboda na mishi farin sani, yaronnan hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba har sai ya gano abinda muke ɓoyewa. Ni nasan waye shi, yana da kafiya wani lokacin.”

Halima wadanda kalaman Fu’ad ke mata ciwo musamman ganin yanda Hanan ta fusata har tana kuka. A fusace ta yi magana.

“Sai ya gano abinda zai gano don ubansa, yanzu kuna kallon yaronnan ya ci mutuncin ƴata amman saboda daɗi ɗa kuka kasa tsawatar masa? Kun kyautamin kenan?”

Hayat ya dakatar da ita cikin ban baki.

“Haba Halima, ke fa kika jawo wannan ruwa ai kinga dole ya dokeki, kiyi hakuri dai yanzu mun ji dadi da muka samu har yaron ya bar wurin. Batun auren Hanan da shi kuwa, ai dama wasa kike don bana jin Fu’ad na soyayya da ita.”

“Wallahi yana yi, kana ina muke zuwa Hotel mu kwana?” Fadin Hanan babu ko ɗarr, sai ma Hayat din ne ya ɗan ji kunyar. 

“Yanzu duk wannan a bar shi mu ajiyeshi gefe. Ke Hanan dan bamu wuri  muyi magana.”

Ta taɓe baki kafin ta mike ta nufi daya falon inda ta soma zama farkon zuwanta gidanta. 

“Salma, Halima, yanzu lokaci ya wuce da  sace tsaya ana wani faman cecekuce akan abinda bai taka kara ya karya ba, ya kamata mu zama tsintsiya madauri daya mu magance matsalarnan. Ke Halima, naki mai sauki ne saboda ko yau Maryam ta ganki sai dai ta ce kin mata zaman aiki amman banda wannan ba abinda za ta zargeki da shi. Mu ne masu hannu dumu-dumu a zahiri, ke naki kam bai fito ba anan. Saboda haka a ganina ya dace mu sanyo Gwaska da yaransa a karo na biyu cikin wannan lamari.”

Suka zuba mishi  idanu.

“Kana nufin mu ƙara yin yunƙurin da muka yi a baya?”

Hayat ya girgiza kai yana murmushin mugayen dattijai.

“Um um Salma, wannan karon sata zamu yi. Satar ɗiyar Maryam. A ganina wannan zai sa koda Maryam ta yi yunkurin daukar mataki a kanmu, to fa za ta fasa don kuwa ran ɗiyarta zai dawo a tafin hannunmu.”

Shiru ya biyo baya kowanne na dogon nazari. Sai kuma matan suka yi dariya gami da kai hannu da zummar cafkewa, sai dai suka tsaya gami da hararar junansu. Salma ta maida kai ga Hayat tana murmushi da farr da ido.

“Kai amman wannan tunanin ya yi, idan aka sace ta gidan wa zamu ajiyeta?”

Ya yi ƴar dariyar shaƙiyanci. 

“Inda ba za’a zargemu ba, asibitina zamu kai ta mu yi ta ɗuramata alluran da zasu kashemata jiki.”

“To Hayat, idan har zamu iya satar ƴarta, me zai hana muyi mai gaba ɗaya? Mu sace uwar.”

Fadin Halima, ya girgiza kai. 

“Haba Halima, ai mai ciwon ciki baya raina magani. Me kike ci na baka na zuba? Ki kwantar da hankalinki komai zai tafi yanda muke so. Idan muka sace ɗiyar, kamar uwar muka kashewa rayuwa ne.”

“To wani hanzari ba gudu ba, har yanzu fa bamu da tabbacin abinda Maryam ta sanar da iyayenka. Kada fa mu zo mu ɗaure kanmu da kanmu.”

Fadin Salma.

“Kuma fa kin yi magana, amman dai ku bar ni, zan bincika da kaina. Ai idan da kuɗi, to komai zai zo yanda muke da bukatarsa. Muna daga nan sai mu ji dukkan wasu bayanan da muka yi niyya.”

Suka yi dariyar samun nutsuwa ba yanda suka zata ba a farko. Daga nan kuma kowa ya kama gabansa. 

A hanya Hanan tana tuƙi banda kunduma ashar ba abinda take yi, wai Fu’ad ne ya gasamata magana. Ta dubi Halima wacce ta ke murmushi alamar ko a jikinta.

“Kambu…Kai, ya ina magana kina murmushi, wato don ba ke aka yiwa ba?”

Halima ranta ya ɗan sosu, ko ba komai ai ita ta haifeta sai dai ta yi sake don ko kaɗan Hanan ba ta daukarta a uwa.

“Yaro man kaza, ba wannan ne matsalata ba kuma ba shi ne damuwata ba a yanzu haka. Babban burina na ga bayan Salma, na tsaneta. Salma tana da gori, tana gorantamin akan komai da ta yimin a wannan rayuwa. Don haka idan gulbi bai ci ni ba, ƙorama ta bar ci na.”

“Me kike nufi?” Hanan ta nemi ba’asi.

“Ni zan tona asirin Salma, sai naga bayanta.”

Dariyar rainin wayo Hanan ta yi har tana buga sitiyari.

“Kai, abin haushi! Kin manta ba har da hannunki a komai ma da ku ka aikata ba? Ko kin manta da har kike tunanin za ki iya tunawa wata ramin mugunta ke kuma ki tsira?”

Jinjina kai Halima ta yi. 

“Eh, da ni aka yi komai amman ba duka ba, na fi tsoron tashin hankalin da zai fito na Fu’ad akan kisan Alhaji Haisam.”

Wani wawan birki Hanan ta taka domin kadan ya rage ta buge wani dattijo da zai tsallaka da kekensa. Ganin za’a yi mata ca, ta giftashi ta wuce sai dai jikinta a sanyaye.

“Menene akan Fu’ad? Ina jin kamar bani da masaniya, ki fadamin.”

Sai sannan ta san cewa ta yi kataɓora, sai dai yanda Hanan ta matsa dole ta sanya ta buɗar baki ta yi magana.

“Fu’ad ba ɗan wanda duniya ke zato bane! Fu’ad ba ɗan Alhaji Haisam bane, hakanan ba ɗa ne ga Salma da Hayat ba!”

Ai sai Hanan ta nemi wuri ta faka motarta tana duban uwar hankali a tashe. Cikin rawar murya ta ce.

“Ɗan..ɗan waye?”

Murmushi Halima ta yi gami da girgiza kai.

“Za ki ji komai idan lokacin ya yi. Yanzu dai ki bar ni na kai labarinnan inda ya dace.”

<< Rumfar Kara 29Rumfar Kara 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×