Skip to content
Part 31 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Ban fahimta ba.” Hanan ta faɗi har sannan hankalinta a tashe, ba ta san tana son Fu’ad har haka ba sai yanzu da ta ji labarin da ya shafeshi kuma take bukatar jin ƙarashensa.

Tsaki Halima ta ja.

“Kar ki cikan kunne, ki ja mu tafi mana. Kina da masaniyar dai yau Honorable zai zo wurina.”

Hanan jiki ba kwari ta ci gaba da tuƙi sai dai ta ci alwashin dole sai ta san asalin Fu’ad, wani so da tausayinsa suka mamaye zuciyarta. Har suka isa gidan ba ta bar tunanin ko shi ɗan waye ba? Ba ta bar tunanin ko shi shege bane kamarta?

*****

“Allah kuwa idan ka ƙara shigomin wuri a murtuke zan maka hukunci. Allura za ka sha.”

Adam ya yi maganar yana daga tsaye gaban karamin firij din dake ofishinsa da zummar ɗaukar ruwa. Fu’ad ya yi murmushi yana mai shafar suma.

“Sorry ɗan uwana, kawai dai idan ka ganni haka bana jin dadin yanayin ne. Amman ba komai.”

Taɓe baki kawai Adam ya yi, wayarsa ce ta yi ƙara wanda ta dauki hankalinsa. Fu’ad ya kwantar da kai saman kujerar ya dulmiya cikin tunanin mahaifiyarsa.

Har Adam ya kammala wayar bai sani ba sai muryarsa ya tsinta yana fadin.

“Toh wannan karon kuma ko wane abin alherin ne ya same mu?”

Jin haka ya ɗago kansa.

“A ina kenan?”

“Umma ta yi kirana akan na samu na shiga Yobe gobe idan Allah Ya kaimu, wani abin alheri ne ya samu.”

“Ko aure aka yi maka?” Fadin Fu’ad cike da zolaye. Harara ya samu a tare kuma suka ɗan dara.

“Wasa kake, babu macen da za ta aureni yanzu na mata tsufa ai.”

“Sai Humaira ko?”

Ya fadi yana mai kanne mishi ido daya. Murmushi Adam ya yi gami da girgiza kai.

“You are not serious, ƙanwartawa? Kai wai meke damunka ne kwanakin nan? Kasan kuwa ka ɗan rame ma.”

Ya share batun gami da watsomashi tambayar da ke cin ransa.

“Amira ce. Sonta nake ci kaunarta na zuba. A taimaka a bani kafin na mutu.”

Gaban Adam ya faɗi, ya ɗan haɗe fuska.

“Amman dai ba cewa nayi ka kawomin shirme ba ko? Na maka tambayar arziki kana neman sako wasa.”

Fu’ad ya yi murmushi, ya riga da ya san abu ne mai wahala Adam ya amince ya nemi auren Kanwarsa, sai dai yana da yaƙinin cewa idan har Allah Ya ƙaddara matarsa ce babu wani mahaluƙin da ya isa ya hana. Shirunsa ya kara ba Adam tabbacin cewar dagaske yake, a iyakar zaman da suka yi tare, ya shaƙu da shi hakanan ya san kaso mai yawa daga halayensa. Ya tabbatar koda ace bai zurfafa yanda ya fassara ba, to dagasken gaske akwai son Amira a kwayar idanunsa wadanda ya gani tun zuwansu na karshe.

“Sorry.” Shi ne abinda Fu’ad ya iya furtawa cikin dakiya, a karshe ya sanyo wata hirar yana mai danne damuwarsa tamkar bai ji zafin yanayin da Adam ya nuna adalilin ambaton Amira da ya yi ba. Daga bisani suka yi sallama suka rabu.

*****

Tunda Engineer ya kirashi ya ce akwai taro a Yobe, ya ji gaba daya ba shi da sukuni. Tunaninsa ya ba shi cewar Maryam ta fadi komai sai dai koda suka yi waya da Malam Kabiru sai bai ji wani abun ɗaga hankali ba sai dai ya shiga kokwanton manufar kalmar ƴar uwarku Maryam da Malam din ya furta. Maryam ƴar uwarsu ta wane ɓangaren?

Ya watsar da zancen gami da jan guntun tsaki. Ya kara bin ƙawataccen ofishinsa da kallo tamkar a ranar ya soma zama cikinsa. Hotonsa da matarsa Salma ya kafe da idanu yana kallo. Ba ya mance haduwarsa da Salma a karo na biyu bayan ta yi aure. A general hospital ne inda yake aiki matsayin ɗaya a cikin likitocin da ake ji da su waɗanda suka kware a ɓangaren mata, (Gyneacologists).

Murmushi Hayat ya yi gami da ƙara juyi saman kujerar da yake, sanyin Ac da kuma ƙamshin roomfreshner na ƙara sanya mishi nutsuwa gami da mantar da shi tashin hankalin da ke fuskantarsa.

Asalin saninsa da Salma tun a jami’ar Bayero ne. Duk kuwa da cewar sam basu haɗa komai a fannin ilimi ba, don shi ya karanci medicine, yayinda ita kuwa ta karanci Accounting. Soyayya da shaƙuwa ce kawai ta wanzu a tsakaninsu, kusan kaso tamanin ta soyayyarsa gareta ta ninka wanda ita ke mishi. Wannan ya sa ya zama tamkar bawa mai hidimta mana musamman da ya karanci babunta. Mahaifinta ba kowa bane face talaka, kusan zai iya cewa da taimakonsa da na sauran samarinta masu kashemata ta yi karatu ta kuma sanya sutura wanda ta so. Salma tana da kyau son kowa, wannan ta sanya yake ƙara susucewa a kanta a wancan lokacin. Ita ce wacce ya soma so a duniyarsa.

Yana dab da kammala karatunsa ya ziyarci Salma gami da  tabbatarmata yana karasa karatu zai aureta, ta nunamishi an yi mata miji sai dai ya yi hakuri. Duk iyakar nacinsa Salma ta gujeshi, karshe ma sai iv na bikinta ya tsinta daga hannun aminiyarta Murja. Hauka ne kawai bai yi ba, haka ya dinga sintiri gidan su Salma ta wulakantashi. Wataran ta fito wataran kuwa idan ba ta ga dama ba ko ƙeyarta ba zai ƙara gani ba. Ya sha zuwa yana cin karo da Haisam a wurinta, shima Haisam ya sha ganinsa sai dai kuma basu taɓa koda gaisawa ba. Koda ace Haisam ya yi niyyar su gaisa to fa zai doje, a duniya ba shi da maƙiyi sama da Haisam don a ganinsa shi ya kashe soyayyarsa a zuciyar Salma.

Bai hakura da Salma ba har sai da ya daina ji daga gareta, ta auri Haisam kuma ya rasa inda take da zama, shima ganin yana ɓata lokacin karatunsa ya sanyashi maida hankali sai dai gaba daya ya susuce, kokarinsa ya ja baya.

Bayan komawarsa gida ya iske batun  aurensa da Bilkisu. A haka aka yi auren.

*****

Hayat na kaiwa nan a tunaninsa ya yi murmushi.

“Adalilin Fu’ad, na ƙara haɗuwa da ke.” Ya yi furucin yana kallon hotonsa da Salma kamar wani taɓaɓɓe, sai da ya ji an ƙwanƙwasa ƙofa sannan ya nutsu gami da bada umarnin a shigo. Da tsananin mamaki ya mike tsaye gami da kallonsa.

“Fu’ad?”

Fu’ad wanda ya zura hannu cikin aljihun wando yana ƙarewa ofishin kallo da murmushin shaƙiyanci ha daure ya ƙaraso bayan ya tura ƙofar da ƙafa.

“Dr Hayat Bello, kana mamaki ko? Koda dai nima nayi mamakin zuwana nan.”

Hayat ya daure ya haɗiye fargabarsa gami da yin murmushin yaƙe.

“Ba abin mamaki bane, ɗa da ubansa? Ai abin naka ne. Bismillah, zauna.”

Wawan kallo Fu’ad ya watsamishi kafin ya dora kafa saman kujerar da aka mishi nuni yana dubansa cikin ido.

“Dr Hayat, ina mai gargadinku, ku sani, muddin na gano abinda ku ke ɓoyewa daga kai har Mum da wadannan karuwan, wallahi ina mai rantsuwa da Allah sai na tona muku asiri domin kuwa ban yarda da ku ba! Idan na cika jinin Alhaji Haisam Zakariyya, zan nunamaka kurenka! Saboda na tsaneka, na tsani duk wanda ya raɓeka! Ni bansan kaddarar da ta kai Mum da auren mutum irinka ba! Sai ka ce ba maza!  Mazan ma matsorata Ubangiji? Wadanda Ubangiji ke so da kaunarsu saboda tsarkakkiyar zuciya? Ina kara jaddada maka wallahi na tsaneka! Na kuma yi alkawarin duk sadda na gano abinda ku ke aikatawa to ko Mum itama ba zan yi sparing dinta ba!”

Yana kaiwa nan ya juya a fusace ya bar ofishin haɗi da buga kofar. Idan da Hayat ya yi dubu to ya ɓaci, a gefe guda kuwa tashin hankali ne da ba’a sa mishi rana,  Dr Alex ya turo kofar da zummar tambayar ko lafiya don duk hargagin Fu’ad yakan ji daga ofishinsa. Hannu ya daga gami da ba shi umarnin ya fice ya ƙyaleshi. Zaman asibitin gaba ɗaya sai ya fita a ransa, ya mike ya tattara komatsansa bayan ya danna intercom, kusan kamar wanda aka jefo, haka Saleh ya shigo don son ganin kwaf, dama kamar jira yake. Umarni ya ba shi da ya biyoshi da tarkacensa mota. Saleh ya dauko yana baza idanu ya ga ko an yi ta’adi da kaya don a yanda Fu’ad ya fito tamkar wanda ya yiwa wani duka haka yake huci.

*****

Gaba daya sun taru a falon Engineer, su Hashim, Nuhu, Zarah mazauniyar Gaidam da ma sauran yaran gidan da manyan jikoki. Hira suke ɗan taɓawa suna jiran isowar Maryam da Humaira. Har Lawwali zai sa a kirasu sai gasunan sun shigo da sallama.

Idanun Adam akan Humaira, kusan sakin baki ya yi yana kallonta ba tare da ya ankara ba. Ta kara girma a ƙanƙanin lokaci, aka yi sa’a tana zama idanunta ya kai kansa. Murmushinta wanda ya yi kewa ta sakarmishi, hannu ya ɗagamata kadan ta kauda kai ganin irin kallon da ya bita da shi.

A bangaren Maryam kuwa, kwalla ne suka cika idanunta ganin cewa duk wannan dangin mahaifiyarta ce, tasan ba karamin murna Anna za ta yi ba a duk sadda ta tsinci kanta a cikinsu.

“Shi Hayatu din ba zai zo ba kenan?”

Abinda ta tsinta kenan daga bakin Gwaggo Hadiza, sai da ta ji faduwar gaba duk kuwa da cewar ba ta san waye Hayat din ba.

“Ba zai samu zuwa ba saboda wasu ayyuka, ayi mishi uzuri.”

Cewar Kawu Lawwali, aka share zancen. Malam Kabiru ya buɗe taro da addu’a aka shafa kafin ya soma da sallama da godiya ga Sarki Allah.

“Babban abinda ya sa na tara ku anan ba komai bane face silar Maryama.”

Suka ɗan dubeta, kanta yana ƙasa tana doka murmushi. Malam ya basu tarihinta a taƙaice, iyakar abinda ya dace su sani da yanda aka yi ta zama zuri’arsu bai ɓoye ba. Masu kuka nayi masu mamaki na yi. Adam dai daskarewa ya yi a wurin yana jin tausayi, kauna ta ƴan uwantaka da kuma mamaki na zagaye a rai da gangar jikinsa duk a lokaci guda. A bangaren Umma kuwa, jin sunan mahaifin Humaira sai ta ji gabanta ya faɗi, tabbas zarginta ya tabbata. Shi ne wanda ta taɓa gani a gidanta a shekarun baya da suka wuce. Shi ya zo neman Hayat sai dai aka yi rashin sa’a ba ya gida. Duk da cewar ba ta san ko mene ba har a yau, amman ta tausayamasa hakanan ya tsaya a ranta. Ba ta san sadda hawaye suka kwaranyomata ba jin cewar ya rasu. Hashim ma ya kasa cewa komai, ashe kaunar Maryam da ya ji a ransa na yan uwantaka ne. Ba karamin dadi lamarin ya mishi ba.

Aka gama jimami sannan kuma aka yi batun tafiya Maiduguri, Malam Kabiru ya kwaɗaitamusu, ya nuna duk mai son zuwa kofa a bude take ya yi magana. Ƙalilan ne suka nuna zasu je sakamakon yanayin aiki da makarantar yara, ga Adam kuwa har aka tashi ba’a ji raayinsa ba, Humaira shi kaɗai take satar kallo ta ji abinda zai fito daga bakinsa sai dai bai furta kowa A bane.

Nan iyayen suka yi cirko+-cirko suna hira a tsakar gidan, Humaira ta yi hanyar waje da zummar zuwa wurin su Amira, ta yi kiciɓus da shi a zauren gidan Malam. Ta ɗan yi ƙasa da kanta za ta wuce, kafa ya sanya ya tokare bango wanda dolenta ta tsaya tana murza idanu kamar wacce abu ya faɗawa.

“Muna ƴar haka?”

Raunin da ta ji a muryarsa ya sanya ta ɗago kai ta dubeshi, idanunsa suka yi kyakkyawan shimfida a nata kwayar idanun, ta kauda kai tana mai lumshe idanu kaɗan.

“Ina wuni Yaya Adam.”

“A’a ba zan amsa ba tunda sai da na roƙa Humaira. Ashe akwai ranar da za ta zo ki kasa gaisheni? Shikenan.”

Jiki a sanyaye ya cire ƙafarsa ya juya ya bi ta gefenta da nufin barin wurin, cak ta rike gefen golden shaddarsa getzner.

Ya juya, daidai da karin hular Adam abin a kalla ne, cikar bazar girarsa da kuma sajen saman fuskar ta ƙara mishi kyau ba kaɗan ba. Ta shiga rawar murya don ta kasa magana, idanunta suka yi rau rau, a hankali ta saki rigar sai ta ga ya gyara tsayuwa ba shi da niyyar tafiya. Kallonsa ta yi, murmushi ya yi itama ganin haka ta murmusa har dimple dinta suka bayyana, sai da ya ji tashin tsinkar jiki.

“Ina tayaki murna, na kuma yi farin ciki matuƙa na zamtowarki ɗaya a cikin zuri’armu. Allah Ya jiƙan mahaifinki, Yasa can ta fiyemasa nan.”

A hankali bakin ya motsa.

“Amin, na gode Yayana.”

“Gobe za’a je Maiduguri ko?”

 Ta girgiza kai.

“Ba ka ji Baba Malam ya mayar da shi jibi ba? Saboda masu son zuwa wadanda basu shirya ba, su samu su shirya.”

Ya yi shiru yana kallonta kawai yana murmushi, duk wani mai hankali da hangen nesa idan ya ga irin kallon da yake jifanta da shi zai san ba ƙaramin so yake mata ba.

“Za ka je?”

Ta jefamishi tambaya wanda take fargabar yace a’a.  A karan kanta tasan abin ba zai mata dadi ba.

“Bani da tabbas Humaira. Amman zan so zuwa.”

Ta ji ba dadi har ya gane hakan a yayinda suka hada idanu.

“I’m sorry, ba fa na riga na yanke ba.”

Ta gyada kai da dan murmushi, jin muryar su Umma sun nufo gidan ya sanya ta saurin fadin.

“Bari naje wurin su Amira.” Ba ta jira amsarsa ba ta yi ciki. Sai ta sanyashi murmushi, yasan Humaira na sonshi don shi ba yaro bane. Yana da saurin ɗago mutum, sai dai kamar har yanzu ba ta saki jiki da shi ba. Ba ya son ya furtamata a yanzun, ya bar wa cikinsa zuwa sadda ya kamata ya sanar din.

*****

Hakuri take ba shi ta wayar bisa yanda ta yi mishi shishshigi har ta je gidansu ta nuna kanta matsayin tana son aurensa. Shiru ya yi yana sauraronta ta Bluetooth dake manne a kunnensa, hannunsa harɗe a kirji yana kallon tsuntsayen dake shawagi a harabar garden din nasu.

“Hanan, is ok, ina don ganinki.”

Dadi kamar ya kasheta.

“Fadamin inda kake zan zo na sameka. Dama ni taka ce a koyaushe.”

Ya ji kamar ta watsamishi dalma a zuciya, ya daure ya haɗiye ciwon.

“Hakane sweetheart, ki je Twillight Hotel, zan zo yanzu na sameki.”

Cikin sauri ta amsa gami da ba wayar sumba mai ƙara.

“I Love You!” Ya katse kiran da sauri yana mai jin takaici.

Ya zama dole ya nemi sani akan abinda ya hana zuciyarsa sukuni. Ya hanashi zaman lafiya da lumana. Ya rasa meyasa yake kasa bacci tun ganin da ya yiwa Mahaifiyarsa tana binne-binne. Yana ji a zuciyarsa ba dadi, akwai abinda ya kamata ace ya sani. Addu’a yake sosai don ko Haidar ya bar ganinsa sai kuwa Adam wanda shi ke zuwa wurinsa su gaisa. Anan yake samun ƴar nutsuwa don kuwa Adam akwai iya lafazi masu kwantar da hankalin bawan dake cikin damuwa.

Juyawa ya yi ya soma tafiya yana kokarin fidda mukullin mota a aljihunsa. Ya zama dole ya lallaɓa Hanan ko zai samu ya ji abinda bai sani ba. Yana ji a jikinsa bakinsu ɗaya daga yanayin kallon da duk suka mishi alamun razana da firgici a wancan ranar.

Da wannan ya tashi motar ya bar gidan gaba ɗaya.

*****

Hannunta dake cikin nasa take ƙarewa kallon mamaki. A gefe wani dadi take ji kamar ta shiɗe, yaushe rabon da ko hannun ya riƙe mata, yau gashinan da kansa ya riƙo yana ƙoƙarin shigar da ita inda zasu shana.

Shi kuwa Fu’ad ba karamin dauriya ya yi ba har suka shiga ya maida kofar ya rufe da mukulli gami da jefa mukullin a aljihun wandonsa. Gani ya yi ta rage kayan jikinta ya kasance daga ita sai doguwar rigar bacci wanda ta doramata abaya a kai, ya kara jin tsanarta da duk wata harka ta banza. Banda harkar banza da karuwanci, wace mace ce za ta yarda ta tallata surarta har haka saboda namijin da ba muharraminta ba ba komai ba. Ko a gaban muharraman ai ba kowa zai iya ganinka a yanda kake ba.

 Ji ya ji ta shafa kafaɗarsa, ya ɗan dawo hayyacinsa ya dubeta. Murmushi ya ƙaƙalo gami da janye hannun ya riƙe suka karasa bakin gado suka zauna. Jinta take a sama sakamakon magungunan da Halima ta haɗa ta bata ta sha kawai don ta mallakeshi a yau ya zama nata, kuma ai yanda tace ayi.  Gaba daya dauriyarta ta ƙare, kawai dannewa take amman iyakar ƙololuwar bukata ga kai gejinsa.

“Hanan, nasan kina sona.”

Ta gyaɗa kai idanunta na ƙara ƙanƙancewa.

“Nagode da wannan soyayya da kikemin sai dai nayi mamaki iyakar mamaki da har ta kasance har da ke za’a haɗa baki wurin cutar da rayuwata. Meyasa?”

Ya yi maganar yana cijewa tamkar a fusace, so yake ya zurmata ta faɗa kawai.

Ta yi saurin riƙoshi tana mai kara matsowa kusa da shi.

“Ka yi hakuri Fu’ad, ni bani da niyyar cutar da kai. Fu’ad kai ne mutumin da na fi so da kauna a rayuwata.  Idan na cutar da kai, kaina na cutar.”

Ya yi murmushi yana mai dan tureta.

“Cikani please, gashinan har ke kin kasa faɗamin abinda su Mum ke tattaunawa, kin yi shiru kina kallona ina tambaya kamar mahaukaci? Hanan ban taɓa tunanin za ki yimin haka ba, ni ina can ina tunanin yanda zan ɓullo da maganar aurenmu, nayi miki surprise ashe ke kina can kin haɗa kai..”

“Wallahi a’a, don Allah ka tsaya ka saurari duk abinda ya faru amma don Allah kar ka cewa kowa ni na faɗamaka. Wallahi iyayenka zasu iya kasheni!”

Gabansa ya yi mummunan faduwa, kisa?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 30Rumfar Kara 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×