"Ban fahimta ba." Hanan ta faɗi har sannan hankalinta a tashe, ba ta san tana son Fu'ad har haka ba sai yanzu da ta ji labarin da ya shafeshi kuma take bukatar jin ƙarashensa.
Tsaki Halima ta ja.
"Kar ki cikan kunne, ki ja mu tafi mana. Kina da masaniyar dai yau Honorable zai zo wurina."
Hanan jiki ba kwari ta ci gaba da tuƙi sai dai ta ci alwashin dole sai ta san asalin Fu'ad, wani so da tausayinsa suka mamaye zuciyarta. Har suka isa gidan ba ta bar tunanin ko shi ɗan waye ba. . .