"Ya zama dole ki shirya mu bar nan. Wallahi na miki rantsuwa ta Allah ba zan bar Halima da rai ba!"
"Hum, ture batun wannan Hayat, muji da zancen Fu'ad, bana fatan ya gano cewa BILKISU ce mahaifiyarsa ba ni ba! Ya zama dole mu nemi abinda zamu lulluɓeshi. Ya zama dole mu yiwa tufkar hanci."
Kan Fu'ad ya sara, da sauri ya damƙe yana mai ambaton Allah.
"Haba Salma, wannan gaskiya ce da ba za ta taɓa bayyanuwa ba. Ban ma ga ta inda hankali zai ɗauka ba. Ki sa ranki a inuwa, idan. . .