Skip to content
Part 33 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Ya zama dole ki shirya mu bar nan. Wallahi na miki rantsuwa ta Allah ba zan bar Halima da rai ba!”

“Hum, ture batun wannan Hayat, muji da zancen Fu’ad, bana fatan ya gano cewa BILKISU ce mahaifiyarsa ba ni ba! Ya zama dole mu nemi abinda zamu lulluɓeshi. Ya zama dole mu yiwa tufkar hanci.”

Kan Fu’ad ya sara, da sauri ya damƙe yana mai ambaton Allah.

“Haba Salma, wannan gaskiya ce da ba za ta taɓa bayyanuwa ba. Ban ma ga ta inda hankali zai ɗauka ba. Ki sa ranki a inuwa, idan ma yaron ya matsa ai sai mu ce iyayensa mutuwa suka yi kika daukeshi kika shayar da shi tamkar ɗan cikinki.”

Ya kasa jure sauran bayanan wannan ta sanyashi sakin ƙara kamar wani zaki ya nufi cikin falon a guje, wata irin hantsilawa Hayat ya yi sai a bayan kujera. Bai tsaya nan ba ya tunkari ɗaki, Salma za ta gudu ya yi nasarar cafketa gami da maƙure wuyanta.

“Karya kuke! Yau sai kun faɗamin asalina, ki yi magana ko na kasheki!”

Salma sai kakari take. A dakin kuwa Hayat bayan ya ƙulle ya dannawa Gwaska kira akan ya yi saurin zuwa gidan ya damƙe Fu’ad ya tafi da shi. Shi kuwa Fu’ad jijjiga Salma yake yana surutai marasa kan gado. A karshe ya wancakalar da ita gami da kifamata mari hagu da dama. Idanunsa kuwa tamkar an watsa barkono.

“Ki faɗamin wace ta haifeni! Ƙi buɗe baki ki yi magana!”

Baki na rawa sai dai ta kasa cewa uffan. Ya dage ya dunƙule hannunsa gami da kai mata naushi a baki sai jini! Tuni girman ya faɗi. Ba ya kallonta a komai.

Zai ƙara ta dakatar da shi cikin ɗaya murya.

“Ya isa Fu’ad! Kar ka manta ni na raineka tun kana karami! Na nunamaka so da kauna tamkar ɗan cikina! Kar ka manta wannan!”

Ya yi wata dariya na rashin hayyaci.

“Ko? To naji, kin ci wannan darajar. Amman yau ba zan bar ki ba har sai kin fadamin asalina.”

Ta waiga tana neman Hayat sai dai babu shi ba labarinsa, ta soma kuka. Dole ma a kashe Fu’ad, ba zai yiwu asirinta ya tonu adalilinsa ba. Dama ba ɗanta bane, wataran dole ta ga fiye da hakan.

“Bilkisu ce uwarka! Ita ta haifeka, kai ƙanin Adam ne! Hayat ne ubanka!”

Ya ji dum, taga-taga ya yi zai faɗi, Allah Ya taimakeshi ya tsaya. Tsayuwar ta gagareshi wannan ta sanya shi zuba gwuiwoyinsa a ƙasa yana kallonta kamar mai rangwamen hankali.

“Kika ce me? How??”

Ya tambaya wannan karon muryarsa dakyar take fita, hawaye kuwa tamkar an kunna famfo. Ta yi shiru ba magana. Shigowar su Gwaska ne ya yi daidai da fitowar Hayat don dama sun mishi waya.

“Ku kamashi!” Fu’ad bai ko kallesu ba, idanunsa na kan Hayat yana mamakin yanda ya zama ubansa. Yana ji aka damƙeshi, hawaye yake yana fatan komai ya zama mafarki.

“Ki cemin ƙarya kike Salma, domin wallahi bana murnar fitowa daga tsatson wannan mutumin! Ki ce karya kike ba mahaifina bane!”

Hayat ya yi wata dariya sheƙeƙe.

“Ni ne nan ubanka! Kuma ni na sauyaka tun a gadon asibiti! Ni na sanya  aka sanar da Bilkisu da mutuwarka tun haihuwarka. Nayi don na samarwa Alhaji Haisam magaji daga wurin Salma. Ina son Salma fiye da uwarka, ban ma taɓa son uwarka ba ballantana wani da ya raɓeta. Kaima da na soma so na bari! Ku fice da shi Gwaska ku ƙulle har zuwa sadda zan ba ku umarnin yanda za ku yimin da shi.”

Fu’ad ya girgiza kai, ya fisge daga riƙon da Gwaska ya mishi, cike da tsantsar tsana da wani nauyi da kirjinsa ke mishi ya soma magana yana nuna Hayat da yatsansa dake rawa.

“Idan kuwa har hakan ne kai ne ubana, bamu yi sa’ar uba nagari ba! Wallahi gwara na fito tsatson talaka liƙis da na kasance ɗa a wurinka!”

Wani duka Gwaska ya kaiwa ƙeyarsa da ya sumar da shi. Ya ba yaransa umarnin ficewa da shi. Daga haka ya bi bayansu. Hayat ya ƙaraso cikin falon ya zauna ya shiga sababi.

“Akan me za ki fasa mishi wannan ƙwan?! Me kika aikata? Yanzu da ace ban kira su Gwaska ba ya fita da wannan baƙin sirri? Bakya tuna makomarmu? Idan dangin Haisam suka ji bakya tsoron su sanya a garƙame mu?”

“Dallah yimin shiru! Na faɗa ɗin! Duka laifin wa? Yanzu da ace yanda na nema tun farko ka yi kama tunanin wannan rana za ta zo? Da ace Fu’ad bai haɗa jini da kowa naka ko nawa ba, da kana tunanin abin zai rincaɓemana har haka? Laifin naka ne kai da wanna banzar Halimar! Kuma wallahi sai ta bambance tsakin aya da tsakuwa. Za ta san ni ta yiwa illah!”

Daga wannan ta mike ta gyara zaman zaninta da ya kunce ta shiga ta dauko mayafi da mukullin mota. Duban Hayat ta yi, ko a jikinsa don ko kallon inda take bai yi ba. Ta ɗan sha jinin jikinta. Bata taɓa tsammanin a rayuwa akwai ranar da Hayat zai iya ganin fushinta ya watsar ba. Wato dai soyayyar ma ta soma ja baya. Ta yi kwafa ta fice fuu kamar za ta tashi sama. Gidan Hajiya Murja za ta je, ya zama dole ta nemi shawarar da za ta fissheta.

*****

Hanan ta shiga gidansu a gigice, ta yi mamakin ganin Halima ta ware kiɗa tana shan sigari hankalinta kwance tamkar ba wani abu. Ta karaso ciki, Halima na ganinta ta rage sauti tana dariya gami da ɗagomata hannu alamun jinjina.

“Kedai kin biyani! Yau nasan barewa ba ta yi gudu ɗanta ya rarrafa ba.”

Zama Hanan ta yi tana dubanta baki sake.

“Wai kina so ki cemin abinda na aikata daidai ne?”

Wata malalaciyar dariya Halima ta yi kafin ta zuƙi sigarinta ta furzar da hayaƙin.

“Naki wasa ne, an faɗamaki ban san take-taken Fu’ad ba? Yaron da ya gama kiranki Kilaki a gabanmu, shi ne zai zo miki da wani zancen soyayya da aure ya kasance gaskiya? To nasan duk buge ce! Da biyu na ba ki maganinnan saboda nasan ɗiyata kusan jarababbiya ce, a wannan yanayi kuwa ba abinda ba za ta iya furtawa ba. Sha kuruminki, komai na tafiya bisa shirina. Yanzu haka inada labari daga Gwaska cewa sun sanya an kama Fu’ad. Watakila kasheshi zasu yi.”

A hargitse Hanan ta miƙe tsaye.

“Me kike cewa? Kashe Fu’ad zasu yi?”

Halima ta dubeta.

“Idan na barsu kenan, sai dai abin ba zai tafi a haka ba. Na shirya komai Hanan. Da zarar na kammala na samu kuɗaɗen da nake da buƙatarsu zamu bar ƙasarnan gaba ɗaya saboda nima abin zai iya shafata. Yanzu abinda ya rage na kwashi rabona daga gurin Salma. Koda dai rabon ba nawa kaɗai bane har da Gwaska. Kar fa ki damu, Fu’ad nan za’a kawoshi, a gidannan zamu ɓoyeshi ko shi Hayat din ba shi da masaniyar tafiyarmu ɗaya da Gwaska. Don haka ba abinda zai samu Fu’ad, komai zai tafi yanda muka shirya.”

Ran Hanan ya yi sanyi, ta mike da sauri.

“Bari na gyaramishi ɗakina, anan zai sauka. Idan na kammala sai na yi mishi odar abinci.”

Ta dinga rawar ƙafa har abin ya ba Halima mamaki, ko wane irin so Hanan ke yiwa Fu’ad. Girgiza kai ta yi don yasan da kamar wuya ta samu Fu’ad.

*****

Mintuna kadan ya ji tsayuwar motarsu don tuni ya farka daga suman da suka sanyashi. Ji ya yi an kwance mishi daurin da aka yiwa idanun. Ya dubesu, aka hankaɗa ƙeyarsa zuwa ciki. Bayan sun shige Gwaska ya yiwa yaran umarnin tsayawa a farfajiyar gidan yayinda shi kuwa ya shige ciki da shi. A hanya ce mishi yake.

“Ka saki jikinka fa, ba wani abu da za’a yi maka. Killaceka kawai za’ayi.”

Fu’ad ya dubeshi. Kusan a haife, koda bai haifi kamar mai shekarunsa ba, to kuwa ya kai ya haifa. Siriri ne don gaba daya shaye-shaye ta kara lalata shi. Tafiyarsa ma ba a saiti yake yinta ba sai kuwa furfura da ta cika mishi sumar kai. Kauda idanu ya yi ba tare da ya ce uffan ba. Mamakin ganin Halima ya yi, bai santa ba amman ya taɓa ganinta sau ɗaya a gidansu kuma ya san itace uwar Hanan. Tana murmushi ta ba shi umarnin ƙarasowa ciki ya zauna. Kallonta yake, yasan duk tafiyarsu ɗaya da iyayen don haka bai ji wani farin cikin zuwa hannunta ba. Damuwar dake gabansa kaɗai ta ishe shi.

Zama ya yi yana mai nutsawa kogin tunani.

Tafiya ta soma gami da ba Gwaska umarnin ya biyota. Aka bar shi anan falon shi kaɗai. Tunaninsa ya tafi akan wacce aka ce itace mahaifiyarsa.

Matar da ya raina tun tasowarsa. Asalima a lokacin ya tsaneta, rashin kunya da baƙaƙen magana kuwa, babu irin wanda bai mata ba har da gorin tana cin arzikin ubansa.

Runtse idanu ya yi yana jin hawaye na sintiri bisa kuncinsa. Ya tuno da Amira, gabansa ya bada dam! Wato Allah ne Ya rufawa abin asiri da tuni da Kanwarsa zai yi soyayya? Koda dai yanzun ma ya yi nisa a sonta duk kuwa da cewar ba ta da masaniya.

Dage kirjinsa ya yi wanda ke ƙara zafi, a hankali ya soma ganin dishi-dishi, a karshe ya fadi ƙasan carpet yana juye-juye, hannunsa damƙe da kirjinsa wanda yake jin kamar zai fasa ya fito. Miƙewa ya yi sai dai wani jiri da ya kwasheshi sai gashi zube saman teburin gilashin da ke falon ji kake taratsatsa.

Acan kuwa Halima suna daga ƙuryar ɗaka, gargaɗi take ga Gwaska bayan ta ba shi maƙudan kudi.

“Ka rike alƙawari! Ni kuma zan cikamaka alƙawari daga ranar da na cimma burina akan Salma. Koda dai yanzun ma ina dab da cikawar.

Suka yi dariya, Gwaska ya ƙara rike ledar kuɗin.

“Kar ki damu ai ke tawa ce! Ina da tabbacin ba za ki bani ciwon kai ba!”

Suka ƙara darawa kafin Halima ta ɗan murtuke fuska.

“Sai na dauki fansa a hankali akan Salma. Wallahi sai na gwadamata karshenta! Har ni za ta kalla ta dinga tunanin ta yimin taimako a baya? Har ta goranta min? To don wanda ya haifeta sai na nunamata karshenta. Ka ƙyaleni da su, a hankali sai na nunamusu bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane.”

Gwaska ya daga hannu alamar jinjina gami da yi mata kirari. Kanta kuwa ya fasu, ta yi farr da idanu sannan suka fito Gwaska na shawartarta akan kada ta sake abokan harkarta su ga Fu’ad. Turus suka yi ganinshi kwance a cikin gilasai ga jini yana kwarara.

“Mun shiga uku! Kada dai kashe kansa ya yi?” Fadin Halima a kiɗime. Ya yi daidai da shigowar Hanan wacce ta dawo daga restaurant tana mai jin haushin yanda yaran Gwaska suka hanata shigowa gidan da farko. Ganin Fu’ad ta saki ledojin abincin gami da kiran sunansa da karfi. Kusan a tare suka je gareshi gaba daya, Gwaska ya ɗagoshi. Kwalbar champagne dake saman teburin ta fashe har ɗaya ta soke shi a gefen ciki.

“Sai fa mun kaishi asibiti!” Fadin Halima wacce ta ruɗe. Gwaska ya girgiza kai.

“So kike asirinmu ya tonu? Mu samu likitan da zai zo kawai.”

Suka shiga nazarin wane likita za’a kira, Hanan kuka take don gaba daya ta fita a hayyacinta ganin masoyinta guda a wurin.

“Ba zai yiwu ba dole a kai Fu’ad asibiti kada ya rasa rayuwarsa!” Fadin Hanan kusan a faɗa-faɗa. Halima ta rasa abin yi, karshe suka yarda da zuwa asibitin.

Basu je private ba gudun haɗuwa da idon sani sai suka zaɓi General. Sai da suka nemi ɗan sanda gudun abinda zai je ya zo, emergency suka nufa aka karɓi Fu’ad da gaggawa.

Bayan an shigar da shi ne suka yi cirko-cirko suna jiran sakamako. Hanan kuka ya ƙi yankewa sai faɗi take kasheshi suka yi niyyar yi, ganin za ta yi musu ɓaram-ɓarama ya sa Halima wanketa da mari kafin ta ankarar da ita inda suke.

Yana zaune a ofis suna hira da Dr Fati, Nurse Abida ta shigo bayan ta yi sallama.

“Dr Ibrahim, ka zo yanzu da sauri don Allah. Ana bukatarka. Wani marar lafiya ke kwance rai a hannun Allah.”

Ya yi salati ya mike babu wani jinkiri, mutum ne mai tausayi hakan yasa ba ya haɗa lokacin aiki da komai. Yanzun ma gama duba marar lafiyar kenan Dr Fati ta shigo.

Suna zuwa ya ga su Hanan tsaye. Bai ko dubesu ba ya shige cikin ɗakin. Ya iske ana ba shi taimakon da ya dace, fuskarsa duk jini ya ɓata, kallo ɗaya ya yi mishi ya girgiza kai.

“Operation za’a mishi.” 

Da sa hannun Halima aka yi amfani aka shigar da Fu’ad ɗakin tiyata.  Halima ga dubi Gwaska cikin raɗa-raɗa take faɗin.

“Mun shiga uku! Mun ɓallowa kanmu ruwa. Yanzu idan yaron nan ya mutu ya zamu yi? Ga shi da alama zaman asibiti ya kama mu.”

“Hakanan zamu yi hakurin ya warware. Kar ki damu babu wani abinda zai faru. Zamu yi iyakar kokarinmu. ” Gwaska ya fadi yana sharce gumi.

A ciki kuwa bayan nasarar yiwa Fu’ad aiki, aka gogemishi fuska inda jinin ya ɓata. Zaro idanu Dr Ibrahim ya yi.

“Fu’ad?” Ya ambata da tsananin mamaki, waɗanda suka san Fu’ad adalilin Dr Adam su kansu basu yi tsammanin shi bane. Tausayinsa ya ratsashi, sai dai yana mamakin abinda ya haɗashi da mutanen dake waje don kwata-kwata basu yi mishi kalar mutanen kirki ba.

Aka kai Fu’ad ɗakin hutu, ya basu umarnin kada su shiga sai nan da kamar awa biyu zuwa uku zai farfaɗo sakamakon alluran da ya mishi. Ya musu bayanin zuciyarsa na dab da taɓuwa, an kuma yi nasarar cire duk dafin kwalbar da ya shiga cikinsa. Sai dai su kula sosai a daina sanyashi damuwa.

Kamar ya nunamusu ya sanshi, sai dai hakanan ya ji basu kwanta a ranshi ba musamman Gwaska wanda duk wanda ya ganshi ya ga tsohon ɗan tasha. Ya tsinci kansa da jefamishi tambaya cikin sakin fuska.

“Hajiya ɗanki ne?”

Halima ta hau inda-inda can kuwa ta tuna ta nuna Hanan.

“Aa surukina ne, ƴata yake aure, Hanan.”

Dr Ibahim da murmushin yaƙe da al’ajabi ya jinjina kai yana duban wacce aka kira matar Fu’ad.

“Masha Allah, Allah Ya bashi lafiya toh.”

Daga nan ya musu sallama ya fice. Ya zama dole ya sanar da Dr Adam domin sam bai yarda da mutanen ba, inda ta ƙara kama kanta da ta ce Hanan matar Fu’ad ce alhalin ya san cewa Fu’ad ba shi da aure.

“Akwai lauje cikin naɗa.” Ya furta a fili sa’ilin da yake goge hannunsa da sanitizer.

*****

Sai da koke-koken ya lafa kafin hankalin Hajiya Rasheedat da Prof ya kai ga mutanen dake falon. Sai sannan aka gaisa,  Maryam ke gabatarmusu da su ɗaya bayan ɗaya a matsayin waɗanda suka taimaketa. Anan take shaida musu akwai maza a falon baƙi, Prof ya mike don zuwa shigo da su falon.

Maryam na hawaye ta kara riƙe hannun mahaifiyarta.

“Anna yau na kawomaki karshen kukanki in sha Allah. Yau ƴarki Maryam fa cika fatan da ta yi a baya. Allah Ya tabbatar ita ce silar share hawayenki.” Cikin rashin fahimtar inda kalaman ɗiyartata suka sa gaba ta yi shiru tana kallonta baki a sake. Humaira banda kuka da murmushi ba abinda take yi. Sauran matan ma hawaye suke don ba wanda abin bai taɓa ba. Mazan suka shigo da sallama, hakan yasa matan gyaramusu wuri su zauna. Adam yana al’ajabi yayin kallon Hajiya Rasheedat, ba shi kaɗai ba, har sauran iyayennasu. Kamanninta sak na Engineer ya fito ƙur da ƙur, babu inda ta kuskuro wurin ɗaukar kamanninsa. Har karamin baƙin tabon dake a gefen kuncinsa na dama, itama Hajiya Rasheedat tana da shi.

A bangaren Hajiya Rasheedat dubansu tayi gami da gaishesu. Tana mai jin wani sanyin jiki da kafafu. Hannunta Maryam ta ja ta kai ta je inda Engineer ke zaune yana kallonta yana hawaye, ta harɗe hannayensu wuri guda.

“Anna yau na cikamaki burinki. Na share hawayenki ta hanyar da ban zaci zan share ba. Ga mahaifinki Anna, shi ne wanda kika jima kina kuka dominsa, shi ne wanda kika ƙuri dukkan gori a dalilin rashinsa a kusa. Yau gaki ga Baba Bello.”

Ai sai Hajiya Rasheedat ta faɗa jikin Engineer ta shiga rera kuka mai tsuma zuciya. Kuka take ba kaɗan ba, shi kansa Engineer jikinsa har rawa yake yana fitar da hawaye gami da shafa kanta.

“Ki yafemin ƴata, ki yafemin.”

Ta ɗago kai ta rike hannunsa gam, girgiza mishi kai ta yi.

“Shekara da shekaru ina neman na sanyaka a idanuna. Ina addu’ar koda a ranar zan mutu Allah Ya nunamin kai na ganka, don me zan yi fushi da yin Allah? Ba zan yi ba, ban riƙe ka da komai ba Babana. Ina kaunarka. Burina koyaushe na ganni nima da Babana, na kira sunansa ya amsa, na yi mishi laifi ya tsawatar hakanan na yi mishi aikin da zai ce Allah Ya min albarka. Akan me zan yi fushi da kai alhalin kaddararmu ce haka? Allah Ya ƙaddara adalilin Maryam zan sanka?”

Kuka sosai ta sanya mutanen falon, har Mujahid da ya shigo ya daskare a bakin ƙofa don ko sallamar ma ya kasa. Kallon Maryam yake da kuma Wada aka kira mahaifin Anna da tsantsar mamaki. Ya tsufa sai dai Allah Ya ba shi lafiya da kuzarin jiki.

Humaira wacce kalaman Anna ya tunasar da ita da nata mahaifin da aka kashemata aka hanata jin dadinsa  sai ta fashe da kuka ta kwantar da kai jikin Inno.

Engineer ya bata labarin abinda ya faru bayan rabuwarsa da Rumaisa da irin neman da ya zo ya yi mata daga baya bai risketa ba. Ya dora da fadin.

“Ina kaunarta da abinda ke cikinta, Allah bai yi zamu zauna a inuwa ɗaya ba. Ki yi hakuri ki yafemin ɗiyata. Allah Ya miki albarka, dama ke mai albarkar ce.”

Ta yi murmushi tana ji kamar a mafarki, ta dubi Maryam

“Na gode Maryam, Allah Ya biyaki da aljannarSa.”

Sai a sannan Mujahid ya shigo, da sassarfa ya karasa ga Maryam suka rike hannun juna sai kuka.

Ranar an sha kukan murna da farin ciki. Abba na Abuja domin ya samu transfer ɗaga Jigawa zuwa Abuja. Ca yake zaune da iyalinsa, labari na zuwan mishi kan dawowar Maryam ya ji ba zai iya kara kwanaki bai ganta ba. Suna saka ran zuwansa a washegari.

Kusan raba dare akai hira, Maryam ta keɓe da iyayenta da ɗan uwanta ta basu labarin duk abinda ya sameta wanda har aka rasa ta.

“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Kalli mutum kawai Maryam. Amman mu labarinmu ya sha bamban da wanda kika bamu. Don ce mana aka yi kin fice daga gidan aurenki ba’a hayyaci ba har Maigadi na tambayar inda za ki je ba ki sanar ba. Karshe kuma aka kawo wata ƙonanniyar gawa da kayanki a jikinta aka ce kin mutu. Kin ƙone a mota.”

Murmushi Maryam ke yi tana girgiza kai ba tare da ta ce uffan ba.

“Ya zama dole a ɗauki ƙwaƙƙwarar mataki akan wannan case din.”

Fadin Mujahid ransa a ɓace.

“Aifa, ko ba ka faɗa ba nasan akwai sauran magana a bakin Maryam. Na tabbatar akwai abinda ta ɓoyemana a kalamanta.” Fadin Anna.

Maryam ta yi ƴar dariyar yaƙe.

“Kar ki damu Anna, jira nake a kammala, daga nan Kano zan nufa.”

Gaba ɗaya suka dubeta. Ta yi shiru tana kallonsu yayinda kwalla suka cikamata idanu. *****

Missedcalls ya tarar har tara duk daga Dr Ibrahim. Wanka ya shiga bayan an kaisu masauki sai da ya shirya ya jawo wayar. Daga Huzaifa har Shuraim ba wanda ya ji kiran sakamakon wayar a silent take.

Bai yi wata-wata ba ya bi bayan kiran bayan sun gaisa ya ce.

“Sorry Dr, na bar wayar a silent bana kusa kuma.”

“Ba komai Dr, nima wani muhimmin abu zan faɗamaka.”

Jin ya ce muhimmi ya sanyashi sanya takalmi ya fice daga ɗakin ya nufi farfajiyar gidan.

“Ina jinka Dr, tell me.”

Tiryan-tiryan ya labartamasa abinda ke faruwa. Kan Dr Adam ya ɗaure. Jin sunan Hanan ya ji hankalinsa ya tashi.

“No Dr, basu da gaskiya. Karya suke. Hanan ba matarsa nace! Budurwarsa ce a baya ni da kaina na rabasu. Kar ka bari su cutarmin da shi don Allah. Ina nan zuwa gobe In Sha Allah. Kar ka sallameshi. Ka barshi a asibitin har na zo.”

“Shikenan Dr, dama shiyasa nace bari na sanarmaka don gaskiya i don’t trust them.”

“Na gode Dr, na gode. Ya jikinsa?”

“Da sauki, amman to be sincere yana cikin ciwo ba kaɗan ba. Ina tsoron kamuwarsa da ciwon zuciya. Akwai damuwa mai yawa a zuciyar Fu’ad.”

Nan da nan Adam ya ji inama yana Kanon, ya yi mishi godiya gami da ƙara roƙonsa akan kula da shi. Daga nan suka yi sallama.

Sai sannan ya dinga tunano yanayin da Fu’ad ke zuwar mishi a ofis, ya tuna da wayar Haidar da ya amsa a ɗazun inda yake tambayarsa ko yana tare da Fu’ad, ya kasa samunsa a waya.

“Biri ya yi kama da mutum.” Fadin Dr Adam kafin ya shiga ciki zuciyarsa duk ba dadi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 32Rumfar Kara 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×