Washegari da misalin karfe goma na safe, Abba da iyalinsa suka iso. Nan kuma gidan ya kara kacamewa da murna.
"Kinsan wani abu Maryam? Wallahi jikina bai taɓa bani cewar mutuwa ki ka yi ba."
Abba ya furta idanunsa a kan Maryam wacce tun zamansu take murmushi sosai.
"Yau ga Allah Ya bayyanamaku ni."
"Hakane, sai dai kin ƙi bayyanamana mutanen da suka yi miki wannan aika-aikar. Ko meyasa?" Fadin Abba.
"Gwara dai ka yi mata magana Babana ban san rufa-rufar ta menene ba abinda bakin alƙalami ya riga ya bushe." Hajiya Rasheedat ta furta.
Har. . .