Skip to content
Part 34 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Washegari da misalin karfe goma na safe, Abba da iyalinsa suka iso. Nan kuma gidan ya kara kacamewa da murna.

“Kinsan wani abu Maryam? Wallahi jikina bai taɓa bani cewar mutuwa ki ka yi ba.”

Abba ya furta idanunsa a kan Maryam wacce tun zamansu take murmushi sosai.

“Yau ga Allah Ya bayyanamaku ni.”

“Hakane, sai dai kin ƙi bayyanamana mutanen da suka yi miki wannan aika-aikar. Ko meyasa?” Fadin Abba.

“Gwara dai ka yi mata magana Babana ban san rufa-rufar ta menene ba abinda bakin alƙalami ya riga ya bushe.” Hajiya Rasheedat ta furta.

Har lokacin murmushi bai gushe a saman fuskarta ba ta amsa.

“Ku yi hakuri, ku bani lokaci har muje Kanon.”

Sallamar Humaira ce ta katse zancen, suka amsa suna dubanta. Saƙo ta samu daga ɗiyar Abba wacce ba ta wuce sa’arta ba, Laila. Akan ana kiranta. Ta karaso, Abba hannu ya miƙa mata.  Da murmushi saman fuskarta a ɗan kunyace ta karasa ta miƙa hannun kafin ta durkusa tana gaisheshi. Yana murmushin ya amsa.

“Allah Hakeem, kamanninta da mahaifinta tamkar an tsaga kara an karya. Duk wanda ya san Haisam, ba sai an mishi bayanin cewa ɗiyarsa bace.”

“Ai ko anan magana ta ƙare.” Cewar Mujahid. Aka yi ƴar dariya. Tambayoyi ya shiga yi mata game da karatu kafin daga bisani ta koma gurin ƴan uwanta.

Umma ta yiwa Adam ƙuri da idanu sadda ya shigo gaishesu.

“Wannan yaron anya kuwa ka yi bacci? Kaga idanunka kuwa?”

Gwaggo Hannatu ta riga tambaya. Ya yi murmushin yaƙe gami da shafa kansa.

“Ban fa san sa ido, ko don kin ji nace aure zan ƙara?”

Ta mishi daƙuwa.

Haka ya wayance kafin daga bisani ya ce musu zai koma bakin aiki. Sai da Umma ta nace da tambaya kafin ya faɗi abinda ke faruwa da Fu’ad.

Salati suka sanya.

“Kai, yaro mai hankali da biyayya ba kamar uwarsa ba. Wallahi kamar ba tsatsonta ba. Allah Ya ba shi lafiya.” Fadin Baba Yaha cike da jimami. Duk suka amsa da Amin.

“Allah Ya ba shi lafiya, idan ka je ka gaisheshi don Allah. Ai ina tunanin zamu shiga Kanon gobe. Zan je na dubashi.”

Ran Adam ya yi mishi dadi da maganar Umma. Nan ya mike kowa na mishi fatan alheri.

“Af, ya kamata dai ka shiga ku yi sallama da mutan gidan.”

Bai yi musu ba ya amsa kafin ya fito ya tsaya neman hanyar ɗakin da suke. Humaira ya hango ta fito, sanye cikin riga da siket na leshi mai taushi purple. Suka haɗa idanu, murmushi ya sakarmata, abinka da wacce ba ta iya riƙo ba itama sai ta mayar da martani. Ta karaso.

“Yaya Adam ina kwana.”

“Lafiya kalau Kanwata. Ya kwananki?”

Ta amsa. Rakiyarta ya nema zuwa wurin su Maryam, a ƙofa ya tsaya ta sanarmusu tukunna.

“Haba Adamu, waye baƙonka anan? Kaima ɗan gida ne ai.” Faɗin Prof kenan bayan Adam ya shigo. Ya gaishesu kafin ya yi musu sallamar tafiya Kano bakin aikinsa.

“Sai mun shigo kenan?”

Fadin Maryam tana dubansa fuska a sake.

“Eh Mama, Allah Ya bada ikon zuwa.”

Aka amsa da amin sannan ya fice.

Har ya kai ƙofar fita farfajiyar gidan ya ji muryarta.

“Yaya Adam.” Juyowa ya yi, idanunsu suka tsarke da na juna.

“Allah Ya kaika lafiya.”

Ji yayi kamar wanda aka daskarar da jinin jikinsa. Sai ya ji kamar kada ya tafi ya bar abar sonsa. Tafiyar ta zama dole ko ba don Fu’ad ba, ballantana kuma yana jinsa a rai tamkar ɗan uwansa ciki ɗaya.

“Ameen na gode. Ki hakuri.”

Daga nan ya fice don tuni ya yi sallama da su Engineer, ta shiga maimaita kalmar hakurin da ya furta, kada dai ga gane cewar bata ji daɗin tafiyarsa ba? Ta sauke ajiyar zuciya ta koma ciki.

*****

Tsaki take tana kara gwada kiran Gwaska sai dai duka amsar ɗaya ce, wayar a kashe.

“Kin sameshi?” Faɗin Hayat dake shigowa falon.

Cilli ta yi da wayar saman kujera gami da jan tsaki.

“Ina fa? Wayoyinsa har yanzu a kashe. Ta ya ya zai ɗau yaro kuma bai kira mun ji ya sukai ba?”

Kafin Hayat ya samu abin cewa wayarta ta yi ƙara, cikin azama ta ɗauka. Ganin lambar Halima ya sanya ta ƙara fusata, kamar ba zata ɗauka ba, sai dai ta ɗauka.

“Menene?” Shi ne abinda ta soma cewa. Wata muguwar dariya Halima ta yi.

“Kodayake ban tsammaci sallama daga gareki ba Salma. Kira nayi na sanar dake Fu’ad na karkashin ikona.”

“What?! Me kike kokarin cemin? Bakar munafuka me kika yiwa Gwaska?”

Hayat ya bata umarnin saka wayar a handfree, ba musu ta saka.

Dariya sosai Halima ta sanya kafin ta ɗora.

“Wannan ba abu ne da ya shafeki ba. Wallahi ina mai sanarmaki nan da awa ashirin da huɗu muddin ba ki ban rabin abinda kika mallaka ba na daga dukiyar da kike iƙrarin ta Fu’ad ce. Ni da kaina zan dauki Fu’ad muje gidan su Alhaji Haisam a fasa kwai kowa ya huta.”

Gaban Salma ya faɗi, tasan halin Halima tsaf za ta aikata fin hakan ma. Gumi ya shiga fesomata daga ita har Hayat din. Tuni ya soma rage shaƙar da ya yiwa wuyansa da necktie. Ya fidda coat din saman.

“Me kuke nufi? Kar ki manta duk wani abu da za ki yi kema ba tsira za ki yi ba Halima. Kar ki manta ke da kanki kika shiga wurin Bilki matsayin nos kika sanarmata da mutuwar ɗanta.”

“Sai me?! Don anyi haka da ni nace sai me? Ke ni bana tsoron abinda zai je ya zo. Ai tunda kika shiga shirgina ni kuwa zan nunamaki gaba da gabanta. Ƙaryar banza kawai! Kuna wani taƙama da kuɗin da ba ku da haɗi da shi. Ni ce makashinku muddin ba zaku yi yanda na bukata ba! Kar ki manta awanni ashirin da hudu kacal na ba ki. Ki nemi mijinki ku yanke abinda zai fissheku domin ba zan saɓa abinda nayi niyya ba.”

Ƙit! Ta kashe wayar. Salma ta yi wurgi da wayar tana kunduma uban ashar ta lailaya ga Halima.

“Ubanta zan ci! Za ta kasheni da raina! Tsiyar talaka kenan bai san ka yi mishi rana ba! Ta gama kurarin auren miji yanzu ta dawo tana haɗamar dukiyata! Ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa.”

Daga yanda take zirga-zirga a falon tana bugun cinya har zani na neman faduwa, ya tabbatar ba’a hayyacinta take ba. Zage-zage kawai take tana cin alwashin ɗaukar fansa akan Halima. Hayat ne ya dakamata tsawa.

“Ya isa haka! Ya isa! Ban taɓa ganin wasu matan mahaukata bane sai yau! Ba ku iya bada shawarar da za ta amfanemu ba! Daga ke har ita gashinan kun jefamu a matsala! Ni na rasa dalilin rashin yin amini namiji! Toh wallahi ki tattaro duk abinda ta buƙata mu bayar! Kina sane dai ke ce silar komai. Soyayyarki ce ta jefani wannan halin! Ba zai yiwu na jawowa kaina mutuwa da sanina ba. Sai ki soma tattara abinda za’a bata da gaggawa.”

Yana kaiwa nan ya fice zuwa dakinsa sakamakon uban gumin da ya haɗa ba don babu na’urar sanyaya ɗaki ba. Kiran sunansa take amman ko waige. Salma ta yi zaman ƴan bori tana share gumi.

“Hayat? Yau Hayat ne ke dana sanin wani abu a kaina? Allah Ya tsinewa Halima!”

Ta ƙarashe da karfi. Wayarta ta dauka ta dannawa Hajiya Murja kira.

“Murja abubuwa sun ƙwaɓe, bana jin akwai bokan da zai mana magani.”

“Kece tun farko bakya shawara Salma sai abu ya taɓarɓare, da ki ka zo min da batun kisa me nace maki? Ban hanaki ba? Amman ki ka biyewa  namiji ku ka aikata ba daidai ba.”

“Na sani Murja, ke kadai ce Aminiyata ta gari mai ɓoye aibuna. Da na bi shawararki gwara a mishi asirin ya haukace. Yanzu gashinan abinda ya faru shekaru da dama yana taɓa zuciyata. Ya hanamu sukuni. Kinsan ma me Halima ta ce?”

“Sai kin faɗa.” Ta labarta mata yanda suka yi da Halima a waya.

“Amman wannan ba karamar ƴar tasha bace. Sai dai bakya ganin da sa hannun Gwaska?”

“Nima na yi wannan tunanin. Idan kuwa har haka ne, Halima ta fi mu karfi.”

“Ki mata abinda take so, kinga idan asiri ya tonu wallahi kasheki za’ayi.”

Hanjin cikin Salma suka kaɗa, tayi zuru-zuru.

“Shikenan Murja zan duba na gani.”

Daga nan suka yi sallama.

*****

Murja na sauke wayar ta kyakyace da dariya. Kafin ta dauki waya ta danna kira.

“Yau dai ruwa ya ƙarewa ɗan kada. Na kara yi mata famfo, ina ba ki tabbacin haƙanmu zai cimma ruwa. Sai dai kar ki kuskura ki saɓan alƙawari. Maƙon Salma ya sanya nake son nunamata karshenta. Har abada kuma ba za ta gane bakinmu ɗaya ba.”

Dariya Halima ta sanya ta cikin wayar.

“Na gode Hajiya, yanzu abinda ya rage mu jira saƙo. Don zancen da nake maki ɗan iskan likitan nan ya hana mu shiga wurin yaron nan. Gwara na yi wannan yaƙin na samu abinda na samu na arce daga ƙasar. Ina mai tabbatarmaki akwai kasonki a ciki. Dama na riga na san halinta da maƙo. Matar da uwarta ma dakyar take yagarmata wani abu sai ka ce arzikin ubanta.”

Haka suka ci gaba da zagin Salma son rai kafin daga bisani su yi sallama ran kowannensu fari ƙal.

*****

A hankali ya soma buɗe idanun yana ƙarewa ɗakin kallo. Komai na dakin fari ne ƙal har ya soma tunanin ko an mishi sutura ya koma ga mahaliccinSa. Daki-daki ya shiga tuna abubuwan da suka faru. Hawaye ya sulmiyo daga kwarmin idanunsa zuwa gefen fuskar har yana ratsa kunnuwansa. Ba wadanda yake son gani a yanzu face mahaifiyarsa da ƴan uwansa. Yana jin wata iriyar kewarsu da kauna tsantsa na ratsashi. Da zarar ya tuna ya so Amira ko kuwa ya gasawa Umma magana a baya, sai ransa ya yi baƙiƙirin ya ji duniyar ta mishi zafi.

kin wannan hali Dr Ibrahim ya shigo da sallama. Fu’ad ya dubeshi sosai, bai san sadda ya murmusa ba. Wato sai Allah Yasa suka kawoshi hannun idon sani. Yana da tabbacin basu san Dr Ibrahim ba da ba abinda zai sa su barshi a asibitin. Shi kansa Dr Ibrahim ya ji dadin ganinsa haka don a jiya da ya farfaɗo kusan sambatu ya yi tayi ba a hayyaci ba dole ya kara zarƙama mishi alluran da ya sanyashi nannauyan bacci.

“Sannu Fu’ad, ya jikin?”

Fu’ad ya gyaɗa kai gami da motsa leɓɓansa, haka kawai ya ji bakin ya mishi nauyi. Ya shafi cikinsa dake ɗaure da bandage. Dr Ibrahim ya gama aune-aunensa kafin ya taimaka mishi ya tashi zaune. Da kansa ya fita ya sanya aka siyo mishi brush da Maclean. Ya yi kiran matarsa a waya akan ta bada a kawo abinci. Shi ya taimaka ya gogemishi jikin, dama tuni ya tahomishi da kaya cikin nasa. Da taimakonsa Fu’ad ya sanya.

“Na gode Dr.” Ya furta a hankali bayan ya zaunar da shi saman kujera.

“Ji, ba ka daukeni ɗaya da Adam ba ko? Kar ka ƙara yimin godiyarnan bana so. Kaima ai ƙanina ne kuma aboki.” Fu’ad ya yi murmushi cike da damuwa.

Umarni ya ba Nurse da ta shigo akan a sauya shimfiɗar gadon, ta kuwa chanza aka yi shara da guga.

Ba jimawa sai ga saƙon abinci daga gidan Dr Ibrahim. . Abincin marar nauyi ne kamar yanda Dr ya bukata. Kadan ya ci sannan ya maida duba ga Dr Ibrahim.

“Za ka iya bani aron wayarka please?”

“Sure.” Ya miƙa masa. Lambar Adam wacce tuni ya haddace ya shiga dialing. Sai dai a kashe. Har ya ja guntun tsaki.

“Ya ya dai?” Dr Ibrahim ya nemi sani.

“Yaya Adam nake nema ba ya shiga.”

“Ka yi hakuri yana hanyar zuwa watakila ba service. Na sanar mishi komai.”

Ya yi murmushin da tun soma hirar su bai yi irinta ba.

“Fu’ad, su waye waɗannan bayin Allahn da suka kawoka?”

Gabansa ya fadi, shi ko maganarsu ake sai ya ji hankalinsa ya tashi. Ganin ya yi shiru Dr Ibrahim ya ƙara faɗin.

“Ita babbar ta cemin kai surukinta ne, kana auren ɗiyarta. A iyakar sanina da kai ba ka yi aure ba. Wannan ta sanya ko da suka dawo jiyan, na nunamusu ba buƙatar su zauna tunda na ƙara maka allurar da za ta sanya da ikon Allah idan ka farka ka dawo hayyacinka. Suma kamar basu da ra’ayin kwanan sai ita budurwar, dakyar uwar ta janyeta suka tafi da zummar zasu dawo. Toh kuma ɗazun da safe sun zo na tabbatar musu ba yanzu za ka farka ba, koda suka so yimin musu, sai na bude kofa suka ganka kana bacci a dole suka tafi. Haka kawai ban yarda da lamarinsu ba wannan ne dalilin da ya sanya na yi kiran Adam na mishi bayani shi ne ya taso. Ai ina da tabbacin ma ya kusa shigowa garinnan.”

Ya ƙarashe zancen yana mai duban agogon dake ɗaure tsintsiyar hannunsa.

Kafin Fu’ad ya ƙara magana aka shigo kiran Dr Ibrahim. A dole ya yiwa Fu’ad sallama ya fita daga ɗakin da zummar yana zuwa. Da wayar Dr Ibrahim  ya yi amfani ya kira Haidar. Jin muryarsa Haidar ya kunduma ashar.

“Kai haka ake yi? Ina ka shiga ka tashi hankalina ina ta cigiyarka? Naje gidanku an ce duk bakwanan, kuma nasan ko barin ƙasar zaku yi, wallahi sai ka nemeni.”

Murmushi Fu’ad ya yi.

“Sorry Buddy, ban kyauta ba. Ban ji dadi bane ina ma asibiti amman ka yi hakuri.”

“Ya Salam, meke samunka?”

“Ba komai, kawai minor injury ne.”

“Wane asibitin kake?”

Shiru Fu’ad ya yi, ba ya son su yi maganar da zasu yi da Adam a gaban Haidar. Dole dai ya dage da ba shi hakuri akan ba wani ciwo bane idan ya samu sauki zai shigo. Daga haka suka yi sallama.

*****

Wuraren karfe biyar na yammacin ranar, Adam ya faka motarsa. Ya yi daidai da zuwan Hanan a nata motar. Hankalinta ne ya gaza kwanciya ta shigo duba Fu’ad.

Cak ta yi ta kasa sauka daga motar ganin Adam ya fito daga nashi motar, ransa a jagule. Fuskar kamar bai taɓa dariya ba, tsoro da fargaba suka cikata, ta haɗiyi miyan wahala. Ta tabbatar idan ya samu labarin ƙaryar da Halima tayi kan cewa ita matar Fu’ad ce ba zai barta ba sai ya ji dalilinsu. Yanda take kallon Adam a marar imani, zai iya sanyawa a kaita cell a rufe. Kauda kai ta yi ganin ya zo saitinta, sai da ya wuce kafin ta yi ribas ta fice daga asibitin gaba ɗaya. Ya zama lallai ta shaidawa Halima abinda ake ciki. Muddin idan ya zamana Adam anan yake aiki, to shakka babu yana da labarin Fu’ad asibitin, hakan na nufin komai zai iya faruwa.

*****

Kai tsaye ofishin Dr Ibrahim ya nufa, ya iske shi yana duba marar lafiya, yana ganinsa ya mike suka yi musabaha. Ganin da marar lafiya ya sanya kai tsaye ya tambaya.

“Fu’ad fa?”

“Amenity  3.”

“Thank You.” Cewar Adam sannan ya fita ya nufi ɗakin.

Da sallama ya shiga, yana saman kujera ya dubi gabas yana sallah a zaune. Kallonsa kawai Adam ya shiga yi cike da tausayi, gaba daya ya rame ya ɗan yi duhu. Kamar ba Fu’ad dinnan ba mai ɗan ƙiba.

Tsayuwa ya yi jikin kofar yana mai kara duban agogon hannunsa. Mamakin yanda akai sai yanzu yake Sallah ya yi. Sai tunaninsa ya ba shi cewar bacci ya sha. Fu’ad yana idarwa  ya dubeshi. Cak ya kasa kauda kwayar idanunsa, wannan jininsa ne dagasken gaske. Ashe ba banza ba yake jinsa tamkar ɗan uwan. Shekara da shekaru an rabashi da su, an kai shi can wata ƙasar (London) ya ci kuruciyarsa. A daddafe ya kama hannun kujerar zai miƙe, Adam da sauri ya karasa ya taimaka mishi.

“Sannu.”

Ji ya yi Fu’ad ya rungumeshi ya fashe da kuka sosai, kukan dakyar yake fita sakamakon duk wani kwakkwaran motsi idan ya yi to ji yake tamkar yankan dake cikinsa zai ƙara faɗi. Idanun Adam suka kaɗa, yau ya zama dole yasan damuwar Fu’ad. Ya rasa dalilin wannan damuwa mai tarin yawa a zuciyar dan uwannasa. Ɗagoshi ya yi ya taimaka ya zaunar gefen gado gami da jingina mishi filo a baya ya ɗan kwantar da bayan sannan ya zauna gefensa.

“Fu’ad wai meke damunka? Meke faruwa har haka? Haka za ka yi shiru ba za ka sanar da ni ba? Mene haɗinka da su Hanan a karo na biyu da har iyayenta ke iƙrarin kai surukinsu ne? Ashe nan duniya idan kana da damuwa ban cancanci na ji ba? Dama ba ka daukeni ɗan uwan ba?”

Fu’ad ya girgiza kai da sauri ya ɗan share hawayen kuncinsa.

“I am sorry bro, kai kuwa ne shaƙiƙin da ya dace ya ji dukkan wata damuwata.”

Tiryan-tiryan ya shiga ba shi labari, bai ɓoyemishi komai daga abinda ya ji kuma aka faɗa masa ba. Adam tun yana ji hankalinsa na iya ɗauka, har ganinsa ya dawo dishi-dishi ya kasance kawai sauraron yake amman kansa a juye. Jijiyoyin kansa sun fito raɗau.

“Ya isa Fu’ad! Rantsemin! Rantsemin da Allah cewa abinda ka faɗi babu karya ciki!”

Fu’ad ya mishi uzurin rantsuwar da ya sanyashi adalilin cewar ba’a hayyacinsa yake ba. Ya rantse mishi da abin bautar da babu na biyunSa. Adam bai ƙara saurarar komai ba ya fice daga ɗakin a gaggauce. Fu’ad na kiransa amman ina!

Ya yi daidai da shigowar Dr Ibrahim hankali tashe.

“Lafiya?”

“Dr tsayar da Yaya! Kar ya kashe kansa! Kar ya yi tuƙi a wannan yanayin!”

A guje Dr Ibrahim ya bi bayansa sai dai ina! Yana zuwa Adam na ba motarsa wuta ya yi ribas ya fice daga asibitin a miliyan.

*****

Gidan Hayat ya dira kansa tsaye, Maigadin ya dubeshi gami da gaisheshi.

“Hayat fa?”

Maigadin ya ji abin banbarakwai sanin da ya yi mahaifinsa ne.

“Ai ya tashi daga gidannan, amma ko jiya ya zo, yau dai basu kwana nan ba.”

Ya bugi gate din da hannu, har abin ya soma jefa Maigadin a yanayin tsoro. Ya ɗan ja baya.

“Bani kwatancen gidannasa!”

Girgiza kai ya yi a tsorace.

“Wallahi bansani ba Maigida. Ban taɓa zuwa ba.”

Ya juya, har zai shiga mota ya ji an kira sunansa.

“Adamu?” Baban Hanifah ne tsohon makwafcinsu. Yana ganin mutuncinsa ko don irin zaman da aka yi a baya na aminci. Ji ya yi ya ɗan samu nutsuwa. Ya gaidashi. Ya amsa yana mai lura da yanayinsa.

“Lafiya kake kuwa? Ya wajen su Bilkisu?”

Adam ya yi murmushin yaƙe.

“Lafiya kalau Baba, suna nan kalau.”

“To masha Allah. Adamu ko mene damuwarka ka nutsu domin Allah, yanayinka ya nuna ba karamin abu ke tafe da kai ba. Ka yi koyi da mahaifiyarka wurin hakuri da kawaici. Ka ji tsoron Allah, duk lalacewar uba, uba ne.” Ya ci gaba da mishi nasiha wanda har Allah Ya sassauta zuciyar sai dai ba ya kallon Hayat matsayin uba domin bai cika hakkokin da suka rataya a kansa, nasu ba. A wurinsa, Hayat ba ubansa bane.

“Na gode Baba. Allah Ya bar zumunci.”

Ya amsa da amin da murmushi kafin su rabu bayan ya ba shi lambarsa. Sai da ya yi tafiya mai nisa sannan ya faka motar ya jingina kansa jikin kujera.

“Ashe mahaifiyarmu ɗaya? Tun ina jariri ya sanarwa Umma da mutuwata ya damƙawa Salma ni?”

Ya ji abin ya mishi nauyi, wane irin uba ne wannan? Wane mahaukacin so ya yiwa Salma? Kuma wace irin kiyayya yake yi ga Umma har zai rabata da ɗanta tsawon shekaru sama da ashirin?

Ji ya yi ruwa a kuncinsa ya shafa, ashe hawaye yake? Akan Hayat? Tausayin Fu’ad da na Umma?

“Ba zan kyaleka ba Hayat! Ba zan iyaba.”

Ba wanda ya faɗomishi a rai sai Uncle Hashim. Shi kaɗai ne zai taimaka mishi a duk hukuncin da zai yanke. Wannan ta sanya ya kira wayarsa.

<< Rumfar Kara 33Rumfar Kara 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×