Skip to content
Part 37 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

 Wani farin gida ne mai kyau da tsari, daidai nan suka faka. Hashim ya dubeta.

“Nan ne gidan bisa kwatance da kuma lambar gida da ya ba ki.”. Maryam ta gyada kai.

“Nan ne.”

Suka fito a tare, an rubuta Barrister Munir’s residence a jikin wani ɗan katako. Waya ta yi mishi, ba jimawa sai Maigadi ya budemusu gidan. Suka shiga da motarsu, bayan Hashim ya faka, dama Maryam na tsaye a harabar tana jiransa.

Ya fito ya tako har inda take tsaye, fa kauda kai.

“Mu shiga?”

Ya tambaya idanunsa a kanta. Ta amsa da toh. Suka shiga bisa jagorancin Maigadin. A falon saukar baƙi suka iske Barrister Munir zaune. Dattijo mai tarin ilimin boko da arabi, kansa duk furfura ya sanya tabarau a idanunsa. Kar yake kallonsu. Tun shigowar Maryam din yake ƙaremata kallo yana jinjina hukuncin Ubangiji.

“Allah Hakeem! Mrs Haisam Zakariyya, kece dai nake gani din ba karya ba.”

Maryam da Hashim suka yi dariya.

“Ni ce Barrister. Fatan na sameku lafiya.”

“Lafiya kalau Maryam, to ya akai aka haihu a ragaya?”

Sai kuma ta ji idanunta sun yi rauni.

“Kukan ya isa fa, haba.” Ta tsinci muryar Hashim ta ɗan dubeshi sai ta yi murmushi.

Barrister Munir da Hashim wanda sai yanzun yake jin wasu abubuwan, ba karamin tashin hankali suka shiga ba. Hashim ya yi mugun kaɗuwa da ya fahimci Hayat na da sa hannu dumu-dumu cikin kisan Alhaji Haisam. Ciwo yake ji a kirjinsa ba kaɗan ba yana Allah wadai da kasancewarsa cikin zuri’arsu.

“Biri fa ya yi kama da mutum, bana mancewa ana gobe Alhaji zai rasu. Ya bukaci ganina da gaggawa, sai dai kuma dayake Allah bai ƙaddara saduwarmu ba. Alokacin ina Abuja na kuma bashi tabbacin da zarar na dawo zan zo. Kafin na kai ga dawowa naji labarin rasuwarsa. Wallahi ba karamin girgiza nayi ba, ba ki ji ba? Shiyasa nake tambayar ko akwai wata wasiyya da Alhaji ya bari, ku ka ce a’a. Zuciyata sai ta ɗan samu nutsuwa.”

“Hakane, a sannan bani da masaniyar abinda ke cikin Diary dinsa. Koda na fito bayan na karanta, bansan karambanin da ya sa na nufi Salma ba kai tsaye a maimakon na zo gareka. Sai dai hakanan Allah Ya ƙaddara.”

Suka jinjina kai. Shakka babu hakan ne.

“Abinda ya rage yanzu shi ne shigar da magana hannun hukuma a soma shari’a. Zuwa yanzu inada tabbacin suna da labarin abinda ke faruwa, koda ba duka ba. Domin irin wadannan mutanen shu’umai ne. Duk wani mataki da za’a dauka sai mu yi shi da gaggawa, ba zasu taɓa tseremana ba da yardar Allah. Kuma mu yi ta addu’a har Allah Ya bamu nasara a kansu. Kar ki damu Maryam, Allah Yana tare da mai gaskiya.”

Barrister ya kammala jawabi, ya kira iyalinsa suka gaisa kasancewar sun san juna. Suka ɗan ci suka sha, Maryam na lura da Hashim yanda gaba daya mood ɗinsa ya sauya. Ta yi murmushi mai ciwo sanin dawan garin, tasan duka bai wuce adalilin sabon labarin da ya ji game da ɗan uwansu ba. Babu yanda za’a yi, daman sai dai ka haifa ba dai ka haifar da halayyar ba.

Tuƙi yake ya yi jugum, ta dubeshi.

“Ya akayi Abban Shuraim?”

Sai sannan ya ɗan dubeta da murmushi sannan ya kauda kai.

“Mamaki nake yi Maryam, duniyar ke ƙara bani tsoro wallahi.”

“Ba duniyar bace Abban Shuraim, mutanen cikinta ne masu ban mamaki. Abinda ma mutum bai taɓa hasasowa ba, sai ya tsinci ya faru. Koda ba ga naka ba, to ga waninka.”

Ya jinjina kai.

“Koda dai ba mamaki, idan mutum musulmi zai iya daukar hakkin uwa ya rabata da ɗanta tun yana ɗanyen jariri, bai bata damar shayar da shi ba, kula da kuma tarbiyyarsa ba, mene ne abin mamaki don ya kashe rai? Kusan da wancan aikin da wannan duk abu daya ne domin a zaton mahaifiyarnan ɗanta ba ya duniya.”

Tausayin Umma ya dira a zuƙatansu. Maryam gyada kai kawai ta yi. Tare da fatan Allah Ya ganar da shi. Hashim ya kara fahimtar dalilin Hayat na son sace Humaira, wato tunda ya gwada sa’a kan uwar abin ya ƙi yiwuwa, to bari ya ɓullo ta bayan gida.

*****

Gaba daya dakin suka zubamishi idanu cike da tsananin tausayi. Fu’ad ne kwance da robar oxygen makale a hancinsa. Kallonsu yake ta ƙasan ido ɗaya bayan ɗaya, ya kara sankara hannun Ummansa dake zaune gefensa tana kuka.

A hankali wasu hawaye masu zafi suka zubo daga kwarmin idanunsa. Ya kai hannu ya cire robar da aka sanyamishi, ganin haka Dr Garba wanda shi ne a duty ya yo wurinsa. Adam ya kasa zuwa ma sai tsayuwa da ya yi kallonsu.

Zai gyaramasa ya riƙe hannunsa yana fidda numfashin dakyar gami da girgiza kai.

“Ka bar ni nayi magana da ƴan uwana, bansani ba ko shi ne na karshe.”

Jin haka kowa ya yo kansa, Humaira fuskarnan ta koma ja tsabar kukan da ta ke yi.

Murmushi ya yi yana dubansu.

“Me kake fada ne? Ka yi shiru ka dinga salati.”

Adam ya furta yana duban Fu’ad ba tare da ya matso ba.

“Just joking.”

Cewar Fu’ad din da murmushi mai dauke da sakonni da dama a saman fuskarsa.  Basu wani jima sosai ba kasancewar Dr Garba ya ce yana bukatar hutu. A dole suka tafi aka bar shi da Umma wacce ta ce tana tare da shi.

*****

Karfe goma da wasu mintuna, Hayat da Salma na harabar hotel din Noor.  Salma na zaune tana jiran Hayat domin ya kammala yi musu booking ɗaki.

Ya taho yana amsa wayar ɗiyarsa SALIMA, yana kokarin ganin ta ba Antinta Khalisat wayar su gaisa ya hangota. Fidda gilashin ya yi daga idanunsa yana son tantance gaskiyar magana. Ita din ce. Ya karasa gareta haɗi da mata sallama. Salma ta ɗago ta dubeshi. Gabanta ya faɗi.

“Salma? Dama kina nan?”

Ya furta da mamaki. Ta daure ta shanye nata mamakin, Alhaji Idris Zakariyya kenan, yayan Haisam wanda suke uba ɗaya. Da ɗan murmushin yaƙe ta amsa.

“Ina nan Alhaji, kwana biyu? Yaushe ka dawo daga Egypt din?”

Ya murmusa.

“Kwannan nan, ban wani jima ba. Nan Abuja nake zaune da iyalina. Ina Fu’ad? Salma ba ki da kirki.”

Ta daure fuska da nufin waskewa.

“Wane rashin kirki kuma?”

Ta ƙarashe zancen gami da yiwa Hayat wanda ya taho ido alamun ya tsaya. Ba musu ya juyamusu baya gami da yin gaba kaɗan.

“Na samu labari daga Sadik cewar kin hana yaronnan zuwa wurin Hajiya, ita kuma ta ki hakura sai faman sintiri take a gidanki. Meyasa ba za ki duba zaman tare da kuma cewar suna da hakki a kansa ki barshi ya je ba? Kar ki manta ita ta haifar maki Haisam din.”

Ta ɗago gami da watsa mishi kallon banza.

“Wannan kuma ba matsalata bace, ka tambayi yaron ni na hanashi zuwa ko shi ya hana kansa? Idris ka fita a idona! Ba ruwanka da shirgina! Ka rabu da ni!”

Yanda ta yi maganar murya a sama ya sanya jama’ar dake wurin duk suka kallo su. Ganin za ta yi mishi abinda ba shi ba ya gyada kai rai a ɓace.

“Shikenan, watarana ko ance ki yi ba za ki yi ba.” Daga nan ya yi gaba cikin ɓacin rai, ya yi danasanin kulata yanda ta iya dubansa ta ambaci sunansa kanta tsaye. Kwafa kawai ya yi sadda ya shiga motarsa ya fice a harabar.

*****

“Shi wannan din waye?” Hayat ya nemi sani bayan shigarsu ƙawataccen masaukinsu.

Salma ta ja tsaki.

“Yayan Haisam ne, ƴan uba suke. Kar ka so ka ji yanda ya ɓatan rai. Kowa ya tashi Fu’ad! Fu’ad! Da ace zasu san asalinsa da ba haka ba!”

Ran Hayat ya ɗan sosu kadan sai dai ya danne don a yanzu ji yake zai iya komai akan a rabashi da kudi da kuma mutuncinsa. Hakan yasa bai sanya abin Fu’ad a ransa ba duk kuwa da cewar yana jin kaunar yaron a ransa.

“Ki share batunsa, yanzu dai mu ci abinci sai mu san abin yi. Akwai yaron da na sa ya kularmin da takun Halima, inada yaƙinin ba za ta kufcemana ba. Duk inda za ta shiga, zamu kama ta.”

Salma ta yi murmushi, ko ba komai ta ji dadin hakan. Itama akwai shirin da  take yi, a yanzun ji take Murja ce idonta a Kano. Duk wasu bayanai na abinda ke faruwa a gidan su Haisam za ta sanarmata.

*****

Cikin daka tsawa ta kara ba Maigadin umarni a karo na biyu don ya budemata ƙofa ta shigo. Abinda ya gigitashi kenan ya matso yana mai bata hakuri. Hanan ta ja dogon tsaki ta koma motarta ta rufe da karfi. Ya bude ta faɗa ciki, nan ma ba ta hakura ba sai da ta fito ta yi mishi kaca-kaca cewa gidan uwarta ne tana da hakkin shiga sadda ta so. Maigadin ya russunar da kai cikin ban hakuri ya ce.

“A yimin afuwa ba laifi na bane, Hajiyar ce ta yi umarnin kada na bar kowa ya shigo. Yan sanda ne suka tafi da ita.”

Duk da ba wani ƙimarta Hanan ke gani sosai ba amman sai da ta ji hanjin cikinta sun kaɗa. Ba abinda ta soma tunawa sai Fu’ad, kodai mutuwa ya yi ake binciken abinda ya kashe shi?

A rude ta kalli Maigadin.

“Za’ayi mintuna nawa da hakan?”

“Ai ya fi awa biyu ma ranki ya daɗe. Har ta fito ta sanya kaya cikin mota za ta tafi, sai gasunan.”

Jin haka Hanan ta nufi motar da sauri, ƙatuwar jakar hannun Halima ta fiddo, na tarar da takardun kadarar da Salma ta damƙamata sai kuma kudi da zasu kai kusan dubu dari uku. Ta maida duba ga akwatinta, tana da tabbacin gwala-gwalanta suna ciki, fiddo jakunkunan ta yi ta maida ciki gami da yi musu kyakkyawan ɓuya a ɗakinta kafin ta fito ta shiga mota ta fice daga gidan.

Kai tsaye asibitin ta nufa, wannan karon ta rantse sai ta san lafiyar Fu’ad, hakan tasa bata damu ba koda ace za ta yi kiciɓus da Adam.

Allah Ya taimaketa har ta isa dakin da tasan nan ne inda Fu’ad yake kwance, ba ta hadu da idon sani ba. Sai dai tana budewa ta ci karo da baƙin fuska don mace ce mai jinya a dakin ba shi ba. Ranta ya jagule, ta rasa meke mata dadi. Ta rufe kofar ta tsaya raba idanu, Allah Ya taimaketa ta hangi Nos. Ƙarasawa ta yi gami da yi mata kwatancen Fu’ad matsayin kanin Dr Adam. Nan da nan Nos ta fahimta. Da hannu ta yi mata kwatancen ɗakin da yake kwance. Wannan kadai ma ya yiwa Hanan dadi a rai, wato Fu’ad yana raye bai mutu ba. Ta karasa sai dai tsoro ya hanata shiga dakin, ta window ta tsaya tana kallon yanda ya sauya tamkar ba shi ba. Hawaye ta ji na ɗiga daga idanunta, ta sa hannu gami da shafawa. Mamaki take ashe har akwai sadda za ta zubar da hawaye saboda tausayin wani bawa a doron ƙasa?

“Me kike anan?” Muryar Adam tamkar daga sama ta ratsa dodon kunnenta. Ta waiga da sauri ta dubeshi. Babu fuskar kawo raini, ta shiga inda-inda.

“Tambayarki nake, me kike anan? Kin zo ki karasa aikin da uwarki ba ta cika ba?”

“Ba wannan ne ya kawoni ba, Fu’ad na zo dubawa. Kana gani ai gudun zargin ko shiga ban yi ciki ba.”

Daga yanayin da ta yi maganar za ka fahimci tsoro da fargaba kwance a muryarta. Ya yi wani malalacin murmushi.

“Ko? Dakyau.”

“Kar ki sake na kara ganin keyarki a wurin dan uwana idan ba haka ba, kamun da aka yiwa Uwarki, kema zan sa a yi miki shi. Ba zan rabu da Halima ba har sai ta fayyace dukkan wani abu da ta sani game da kullin da suka shirya. Ki je ki faɗawa sauran mutanen naku cewa ni Adam daidai nake da ku. Zan tsaya tsayin daka sai na ga karshenku. Ina kara gargadinki a karon karshe, kar ki ƙara takowa asibitin nan da sunan kin zo duba Fu’ad, idan kuwa ki ka ƙi ji…”

Ya yi kwafa ya gifta ta ya shiga dakin, labulen kawai ya saki. Hanan ta ji hawayenta sun gaza yankewa. Meyasa Adam ba zai gane da zuciya daya take Son Fu’ad bane? Meyasa ya ƙi fahimta?  Sam batun kamen da yasa aka yiwa Halima bai mata ciwo kamar yanda yake kokarin watse igiyar soyayyar da ke tsakaninta da Fu’ad ba.

Jin alamun za’a bude kofar ya sa ta saurin ɗaga ƙafa ta bar wurin sai dai har ta fice ba ta bar zubar hawaye ba.

Ba ita ta tashi komawa gidan ba sai bayan Isha’i. Duk irin hon da take bai sa Maigadin budewa ba. A matukar fusace ta yunkura za ta fito bayan ta yi wurgi da karan sigarin ta tagar motar. Sai ta ji an ja gate ya bude. Ta taka motar ta shige da zummar yau sai ta zagi uwar Bala.

Sai dai tana sa kafarta gami da yunkurin fitowa ta ji bindiga a saman kwanyarta. Dagowar da za ta yi sai da numfashinta ya yi daukewar wucin gadi ganin Gwaska da fuskar marasa imani.

*****

“Wayyo! Wayyo Allahna!”

Halima ke kurma uban ihu sakamakon tafkar da ƴar sandar ta kai mata a gadon baya. Ta kuwa gantsare gami da riƙe bayan, abinka da wacce ta ci bleaching, har jiki da fuskar sun koɗe sun yi ja da baƙi-baƙi.

Hannu inspector ya ɗagamata alamar ya isa, ya maida duba ga Halima.

“Madam, kinga bamu yi niyyar taɓa lafiyar jikinki ba, ke din ce kike mana taurin kai.”

Cikin muryar kuka Halima ke fadin.

“Wai me nayi ranka ya daɗe? Me na aikata ga yaron? Duk abinda Hayat da Salma suka yi su meyasa ba’a yi musu kalar wannan izayar ba sai ni? A wace shari’ar aka ba ku damar duka…”

Ba ta kai ƙarshe ba ta ji matarnan ta ƙara tafkarta. Wani wawan ashar ne ya taho maƙogwaronta ba shiri ta haɗiyeshi gami da yin kwafa.

‘Allah Ya isa, tsinanniya kafirar banza kawai.’ Ta yi furucin a ƙasan ranta.

“Ki hutar da kanki ki fadamana gaskiyar abinda kika sani game da rayuwar Fu’ad. Idan kika kuskura ki ka yi mana karya zamu kaiki kotu ne ta yanda komai zai iya faruwa.”

Jin wannan barazanar ta Inspector, hankalinta ya tashi. Ta dubeshi ido waje sai kuma ta fashe da kuka. Mene ribarta ma na ɓoyewa? Alhalin wadanda suka aikata suna can cikin walwala da jin dadi.

“Wallahi babu hannuna ciki yallaɓai, duk abinda kaga ya faru laifin Salma da Hayat ne. Su ne baƙaƙen munafukai. Su suka kashe Alhaji Haisam Zakariyya. Hayat ya dauki ɗansa ya ba Salma da zummar nata ne tun ma Alhaji Haisam yana raye. Suka yi kokarin hallaka matarsa Maryam wacce keda tsohon ciki gudun kada ta haihu ace za’a raba gadon har abinda ta haifa. Toh shine ta gudu basu ganta ba, yanzu dai suna cin arzikin wasu, Fu’ad kuma ya san wani bangare na labarin amman ba shi da labarin komai. Wannan ne dalilin da suka yi yunkurin ganin bayansa ni kuma na taimakeshi na ƙwaceshi a hannunsu. Ban yi niyyar yin kisan kai ba Yallaɓai ka yarda da ni.”

“Tirƙashi!” Cewar inspector Kabir gama jin labari mai kama da almara. Ya katse recording din da ya yi yasa aka maidata cell tana ihun a kyaleta ta tafi tunda ta faɗi gaskiya.

Shi kuwa inspector kai tsaye waya ya ciro ya yi kiran Adam.

*****

Alokacin Adam na tare da su  yan uwansa ana cin abinci. Rabin hankalinsa yana ga Humaira wacce ta ƙi sakewa ta ci ganin yanda suke fuskantar juna saman teburin. Tana cikin damuwar nisan da za ta yi da shi don Mama ta rantse a washegari za ta tura ta dangin mahaifinta ta yi musu sati don a santa. Ba zuwan ne ba ta da muradi ba, ganin Adam din ne bai isheta ba kwata-kwata musamman yanda ba zama yake ba.

Ƙarar wayarsa ta katse dukkan hanzarinsa, ya fiddo gami da dannawa.

“Yes inspector.”

Furucinsa ya sa duk suka dubeshi.

“Adam case dinnan ba karami bane yanda muke kallonshi, akwai laifin kisan kai.”

Ya ɗan runtse idanu kafin ya bude.

“Uhum, ina jinka.”

Ya karanto mishi komai da Halima ta ce, idanu Adam ya kafawa Humaira sai dai hankalinsa ya kasu gida biyu. A tashi daya ya gane wanda aka kashe, mahaifin Humaira kenan. Ya kuma girgiza jin wadanda suka kashe din. Ya girgiza da lamarin mahaifinsa matuƙa.

“Na gode inspector, don Allah a tsananta bincike, duk wasu masu hannu a lamarinnan kada ka yi musu da sauki. A kama su. Ya zama dole a yanke musu hukunci.”

Da wannan ɓacin ran suka yi sallama da Inspector, ya mike ransa a ɓace da lamarin mahaifinsa zai bar wurin. Hannunsa ya ji an damƙe. Ganin Uncle Hashim ya sanyashi dakatawar da bai shirya ba.

“Ya Rabb, wai meke faruwa ne Adamu? Wa ka sanya aka kama?”

Fadin Prof kenan cikin tashin hankali. Ganin yanda aka yi mishi ca da tambayoyi ya sanyashi komawa ya zauna a dole. Har ya bude baki zai magana ya kasa bayan ya kai duba ga Humaira. Sai ta ji me? Mahaifinsa na da hannu a kisan mahaifinsa? A’a, ba zai iya furtawa ba. Umarni ya ji daga sama Maryam na ba yan matan kan su dauki kwanon abincinsu su bar wurin. Jiki a sanyaye suka shige ɗaki. Kansa a ƙasa don a ganinsa abin kunya ce babba. Ya zayyane dukkan abinda ke faruwa. Wadanda basu sani bane suka dauki salati.

“Anya kuwa? Kar ka yi saurin zargin wannan mummunan aikin ga mahaifinka Adam tunda zai iya kasancewa ƙaryar Halima ce.”

Cewar Alhaji Mujahid kenan cike da tausasawa.

Maryam da tausayin Adam ya rufe ta ta kasa magana, ita kanta Umma mutuwar zaune ta yi tana jin ba dadi da Hayat ya kasance uban ƴaƴanta.

“Zai aikata abinda ya fi kisa.” Umma ta furta ranta a jagule.

“Lokaci ya yi da zan sanar daku abinda ba ku da labarinsa.”

Maryam ta furta. Adam ya kalleta sai kuma ya maida kansa ƙasa.

“Ban taɓa faɗamaku yanda aka kashe Haisam ba. Yau za ku ji komai.”

“Mu koma falo.” Prof ya nemi hakan. Ba musu duk suka mike zuwa falon gidan aka zauna.

“Sadda na fiddo kundin sirrin da Haisam ya damƙamin. Ya rubuta cewa wataranar Laraba yana falonsa zaune bayan kammala jin tafsir na azumi. Intercellular dake ajiye saman tebur ta dauki ƙara. Ya sanya hannu ya dauka, har zai yi magana ya ji muryar Salma a dole ya dakata.

“Meyasa haka Hayat? Ban fadamaka ba koyaushe za ka kira ta wannan layin ba? Idan wani ya ji fa?”

Hayat ya yi dariya.

“Salma kenan, wallahi kewarki nake na kasa jurewa. Ke din ce idan ma kin ce za ki kira mantawa kike. Salma Ina miki son da bansan adadinsa ba. Kar ki yunƙurin yaudarata, kar ki ce ba za ki cika alƙawari ba. Shekaru fa sun soma ja.”

Jin wannan ya sa Haisam ƙara maƙala wayar a kunne.  Ya tsinci muryar Salma.

“Haba My Hayat, me kake ci na baka na zuba? Mutumin da ya dauki kyautar ɗa ya bani halak malak mene ba zan iya aikatawa don ganin mun kasance abu ɗaya ba? Kar ka damu, lokacin Haisam a kididdige yake, da zarar mun kautar da shi a doron ƙasa, zan kasance taka har abada. Zuwa yanzu ya shaƙu da yaronnan, ya daukeshi matsayin ɗansa na cikinsa. Ka bari zamu yi maganar idan mun hadu gobe. Kar ka kara kira ta wannan layin.”

Hayat ya yi dariya.

Fadamin kalma mai dadi mana.

“I love you.”

Tana faɗa ta katse kiran, Haisam wanda ya yi mutuwar zaune, ya rasa meke mishi dadi. Ya ajiye kan wayar ya mike gami da shiga daki. Ya rasa meke damunsa a wannan ranar. Kasancewar girkin Salmar ne, koda ta shigo bangarensa tare da Fu’ad din kallonta kawai yake kafin ya maida hankali ga Fu’ad yana ƙaremishi kallo. Sai a sannan yake ƙara lura da bambance-bambancen dake tsakanin halittarsu (daga shi har Salmar) da shi yaron. Ya tuno irin don da suka nunawa juna da Salma, bai taɓa tsammanin hakan ba. Daurewa ya yi ya sakarmata fuska a ranar.

Cikin dare ya kasa bacci sai juyi yake, karshe ya mike ya faɗa wa Ubangiji cikin sallarsa. Bai zaci idon Salma biyu ba, ta dubeshi tana mutsistsika ido.

“Wai Abban Fu’ad  meke damunka? Kamar ba ka yi baccin kirki ba.”

Kalmar Abban Fu’ad ya ƙara tunzura zuciyarsa, ya ji ba zai iya dannewa ba sai ya mata magana tsabar bakin ciki da kuma tsantsar tsanarta da ya gama mamaye zuciyarsa. Ganinta ma ba ya kaunar yi.

“Tashi ki zo, inada magana da ke.”

Jin haka ta mike sai dai jikinta ya yi sanyi. Zama ta yi a kusa da shi ya ɗan ja baya.

“Salma.” Ta dubeshi.

“Na’am.”

“Mene sakamakon mutumin da ka yarda da shi ya ci amanarka?”

Gaban Salma ya faɗi, ta haɗiyi miyau.

“Ai idan har cin amanarka ya yi bai ma kamata ka zauna da shi ba. Ku raba hanya kowa ya yi nasa wurin. Cin amana ba shi da dadi.”

Jin abinda ta ce ya sanya shi murmushin takaici.

“Hakane Salma, toh ki je ni Haisam na sakeki. Har abada ba na kaunar ganinki ballantana ɗan da kike iƙrarin nawa ne. Yanda kika ci amanata keda saurayinki ki je akwai Allah, ba Ya bacci. Yana kallonku, komai daren daɗewa zai min maganinku.”

Gabanta ya faɗi. Shakka babu Haisam ya ji duk abinda suka tattauna da Hayat. Ta ji haushin kanta don ba ta ga dalilin da za ta yi sakewar da har ta fadi sirrinta ba ta hanyar wayar tebur. Ta manta cewa komai zai iya afkuwa.

“Me kake nufi da cewar har Fu’ad? Me yaron ya yi maka? Ba ɗanka bane? Yau ni ka saka Haisam? Ni Salma?”

Haisam ya dubeta da jajayen idanunsa wadanda ɓacin rai suka kaɗa.

“Ke din dai Salma, ni Hayat na sakeki. Wallahi bana kaunar ganinki. Ki bar kiransa da ɗana domin naji wayar da kika yi kuma..”

“Dakata!” Ta furta ranta a matukar ɓace. Sai kuma ta saki wata banzar dariya gami da tafa hannu.

“Ka yi kaɗan Haisam, wallahi ko ka ƙi ko ka so, Fu’ad ɗa ne a wurinka.  Ni Salma ban fito ba sai da na shirya. Yanda kake taƙamar gida nake ne, nan bada jimawa ba zai koma karkashin ikona saboda na haifar maka magaji. Daidai nake da duk wanda zai yi fito na fito da ni.”

Daga haka ta fice fuu daga dakin nashi, ya dafe kai ransa na zafi. Bai taɓa zaton samun Salma da cin amana har haka ba. Ya yi dana sanin kasancewarta matarsa.

Ranar ta kama Alhamis, ya kasance sam ba shi da walwala, tambayar duniya ya samu daga Maryam amman ya nuna babu komai. Sai daga baya labarin sakin Salman ya risketa daga bakin Halima.

Tambayar duniya Hajiya ta yi bai fadi dalilin sakin ba ya bar shi a cewar sai ya dawo daga Lagos. Haisam ba Lagos ya tafi ba, killace kansa ya yi a Hanif Guest Palace ya kama daki, ba wai domin jin dadi ba sai don samun nutsuwa da jinyar zuciya.

Haka yake zama ya yi kuka, ya faɗa wa Allah damuwarsa.

A kwana na uku ne ya kasa hakuri sai da ya ziyarci gidan Hayat wanda ya sa aka bincika mishi. Ya san Hayat da jimawa tun zamanin da ya nemi auren Salma sai dai magana ta fatar baki ba ta taɓa haɗasu ba. Ya rantse sai ya yi shari’a da su don ba karamin kwararsa suka yi ba.

Tsayuwa ya yi yana ƙarewa gidan kallo kafin ya matsa. Bai iske Maigadi ba hakan ya sa ya shiga buga kofar.  Jin takun ana tahowa ya sa shi barin bugun. Ta bude sanye da hijabi. Suka gaisa kafin ta bada hanya ya ɗan shigo farfajiyar.

“Maigidan yana nan?” Haisam ya tambayi Bilkisu. Ta girgiza kai.

“A’a ya fita.”

“Kiyi hakuri, amman Ina son ganin matarsa.”

Bilkisu ta ɗan yi murmushi kadan.

“Ai ni ce.”

Ya ɗan yi dum kafin ya yi magana a sanyaye.

“Idan Mijinki ya dawo ki ce masa Haisam Zakariyya ya zo. Ki fadamasa ya ji tsoron Allah! Ya kuma sani cewar zan yi ƙararsa.”

Bilkisu ta ji abin ya yi mata nauyi a kai.

“In Sha Allah zan isar da saƙonka, ka yi hakuri kar ka ce na maka katsalandan. Me Hayat ya yi maka?”

Haisam ya dubeta da idanunsa wadanda ɓacin rai ya rina.

“Kar ki damu, watarana abin ɓoye zai fito fili. Wuyarta na shigar da zancensa kotu.”

Daga nan bai ƙara sauraronta ba ya fice daga gidan.

Washegari ya tattara ya wuce Lagos. Sai da ya yi kusan sati da kwanaki kafin ya dawo.

Ba jimawa da dawowarsa ya samu kyakkyawan labari game da cikin da ke jikin Maryam. Ya yi murna ba kaɗan ba.

Ana gobe zai rasu, yana ofis zaunar ya ji an ƙwanƙwasa. Umarni ya bada na a shigo. Kallonsu yake sosai, Salma ce sanya da nikaf sai Hayat. Ta daga nikaf din suna dubansa da murmushi. Salma ta zauna tana fuskantarsa yayinda Hayat ya dora ƙafarsa daya saman kujerar.

“Me ya kawoku wurina?”

Fadin Haisam ransa a ɓace.

“Nemana ka je yi har wurin matata, har kana iƙrarin kai ƙara kotu ko? Shiyasa muka ga ya dace mu zo don neman gafararka. Kada a kashe mu.”

Ya ƙarashe da shaƙiyanci  suka kece da dariya shi da Salma. Haisam ya miƙe tsaye ransa a ɓace.

“Ku fitarmin a ofis! Ku sani wallahi ko nawa ne zan kashe don naga karshenku. Azzalumai! Wadanda basu tsoron Allah.”

Wata dariyar suka yi har da cafkewa kamar mata da miji.

“Haisam kenan! Wallahi wasa kake da rayuwarka domin ba mu ƙi mu ga bayanka ba saboda wannan case din. Idan za ka yi yanda muke so to ka sani zamu fita daga rayuwarka muyi nesa da kai da iyalinka. Amma matukar ba za ka bamu abinda muke so ba na daga dukiyarka, toh ba mu ƙi mu kasheka a banza ba!”

Salma ta furta babu shakkar komai. Ya yi ƴar dariya.

“Bari kiji wani abu, ke kanki kinsan Haisam ba shi da tsoro. Daga ke har karen naki, baku isa ku aikata komai gareni ba. Sannan wallahi sisina ba zai shiga hannunku ba. Ni Haisam na dogara da Ubangijina, inada yaƙinin Yana ji Yana kuma gani.  Tunda ba ku ji kunyar aikata laifi gareShi ba, ba zai bar ku ku zalunceni ko wani a zuri’ata ba. Idan kuna da karfin ja da ikon Allah musamman cikin wannan wata na Ramadan, ku je ku ja son ranku. Amman ku sani ko bayan raina, Allah ba zai barku ba.”

Salma da Hayat suka dubi juna suka kara tuntsirewa da dariya. Kafin Hayat ya dubeshi cikin fuskar rashin imani.

“Haka ka zaɓa ko? To mu zuba mu gani! Tsakaninmu da kai shege ka fasa!”

Daga haka suka juya suka fice, ya kwalawa sakatarensa kira. Nan ya budemishi wuta kan dalilin barin kowane kare shigowa ofishinsa. Abinda sakataren bai taɓa gani ba daga shugabannasa. Sosai ya ba shi hakuri gami da daukar alkawarin ba zai ƙara ba.

Tun a ofis ya nemi lauyansa Munir akan yana son ganinsa. Sai dai ba ya garin ya je Abuja. Ya rokeshi akan idan ya dawo ya neme shi akwai muhimmiyar maganar da zasu yi.

A daren bayan dawowarsa gida ya yi zaman rubuta dukkan wani abinda ya faru gareshi a cikin kundin sirrinsa. Bai ɓoye komai ba har zuwansa gidan Hayat. Da zuwansu ofishinsa.

Washegari bayan fitarsa ya yi kalamai masu kama da wasiyya ga Maryam, karshe ya damƙamata kundin sirrin.

Labarin mutuwarsa ya riskemu a wannan lokacin.

******

Maryam ta dubi mutanen falon wanda tausayi ya sanya wasunsu zubar hawaye. Adam kam tunda ya sauke kai bai ɗago ba har sai da ta kai karshen labarin. Ta tabbata Hayat na da hannu a kisan Alhaji Haisam.

Ya mike da zummar barin wurin ko ransa ya yi sanyi, cak ya tsaya hangota da ya yi jikin bango ta na sheshsheƙa, ga dukkan alamu duk labarin da Maryam ta bayar a kan kunnenta. Itama ta fito ne da zummar daukar ruwa da maida farantin da ta ci abinci. Jin inda labarin ya nufa ya sanyata yin laɓen da ba ta yi niyya ba.

Ta dubeshi duban tsana da kyama kafin ta yi saurin shigewa dakin. Ya kasa tantance irin kallon da kuma silarsa. Ya daure ya karfafa zuciyarsa ya kara daga kafa. Sai dai kiran da Hashim ya kwalamasa ne ya sa a doke ya dawo.

Zama ya yi, Malam Kabiru ne ya soma da yin nasiha akan tsoron Allah da kuma yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinsa kafin daga bisani ya bada shawara kan lallai a kamo Hayat duk inda yake don ya cancanta a hukuntashi. A karshe bayan tafiyar kowa, Prof da Malam suna sanya Adam a tsakiya suka ci gaba da yi mishi nasiha mai ratsa zuciya don sun san abu ne da zuciya ba zata iya dauka ba ace mahaifi shi ne shugaban dukkan wani makirci da mugun ta’adda ci da aka yiwa wasu.

Ji ya yi ransa ya ɗan sanyaya, ya yi musu godiya sannan ya wuce masaukinsa. Tun soma wannan case din idan aka ce ya samu baccin kirki to karya ne, wannan ya haifar masa da zazzaɓi mai zafi da tsananin ciwon kai a gefe guda tunanin kannensa da su, a gefe kuwa ya kasa fahimtar ma’anar kallon da Humaira ta watsamishi. Kada dai ace tana jin haushinsa matsayin wanda babansa ya kashemata uba?

Girgiza kai ya yi gami da ɗan runtse idanu. Ya tabbatar abu ne mai wuya, wannan ba halayyarta ba ce. Idan kuwa ya tabbata hakan ne, bai san kan zai kai tulin so da kaunar da yake mata ba. Ko me zai je ya zo, zai shawo kanta har ya ji matsalar.

*****

Mari ya kifamata a karo na biyar. Hanan duk ta rude ga kuncinta ya tashi ya yi luhu-luhu. Wannan karon kukan ma ta kasa don ta yi har ta gaji idanun sun kumbura.

Ya kara nuna kanta da bindigar.

“Ke ƙaramar kilaki! Ki tambayi uwarki ni ba karamin shege bane don na soma sana’ata tun kafin uwarki ta soma kirgar dangi. Kar ki maidani dan iska don na wuce wannan sunan a yanzu! Ki fito ki fadamin inda uwarki take tun ban lallasaki ba nayi gunduwa-gunduwa da namanki ba.”

A wahalar ta girgiza kai.

“Wallahi gaskiya na fadamaka, tana hannun ƴan sanda, Adam ya sanya an kamata.”

Gwaska ya zuƙi wiwi kafin ya ɗago yana lumshe idanu.

“Toh naji, ina ta kai kudi?”

 Za ta girgiza kai gyara zaman bindigarsa. Gwara ta ba shi ta huta da wannan baƙar izayar.

“Shikenan zan ɗauko maka wallahi.”

Ya yi wata bahaguwar dariya.

“Yauwa ƴar gari, muje. Shi dama yaro bai san wuta ba sai ya taka. Karamar karuwa maza shige mu tafi tun muna shaidar juna.”

 Jiki na rawa ta hantsila kafin ta mike ta yi daki ya bi bayanta. A gabansa ta fiddo takardun

Wayar Gwaska ta dauki

ƙara. Ganin Hajiya Murja ya daga.

“Ke shegiya! Halima tana daure a ofishin ƴan sanda don haka kiyi ta kanki! Nima na yi ta kaina yanzu haka!”

Wannan magana ba karamin tsorata Murja  ta yi ba, babu ko sallama ta katse kiran ya yi wata dariya ta mugayen arna. Hanan ta zuba mishi idanu da mamakin wannan makirci kamar mace. Ya karɓi takardun kasancewar ba ilimin boko balle Arabi, ya rasa gaba da bayansu. Ganin yanda ya juya takardar a jirkice yana dubawa ya sa Hanan kallonsa tana tsoron abinda zai biyo baya.

“Ke! Takardun me za ki bani? Me zan yi da su? Kudi nake so! Kudi!!”

Ta gigice.

“Wallahi su ne takardun da Salma ta damƙamata kudaden, dole sai da sa hannun Halima za ka samu ko me kake buƙata.”

Ya yi shiru yana kallon takardun wadanda yake ji kamr ya yagasu. Can kuma ya dubeta.

“Ki gaggauta nemo inda aka kai uwarki tun kafin na kashe ki!”

Ta amsa da sauri sannan ya watsamata takardun ya yi gaba yana kunduma ashar.

*****

“Wai nikam ina Adam ne? Humaira maza je ki kirashi ya fito ya karya. Har karfe goma mutum bai sa komai a cikinsa ba. Ki ce ya fito ya karya muje wurin Fu’ad. Daga nan ke kuma a sauke ki gidanku.”

Maryam ke maganar tana duban Humaira wacce ta daure fuska tamkar an ce ta shiga wuta. Sharewa ta yi kamar ba ta ga yanayinta ba, a jiya ta tabbatar Humairar ta ji komai ita kuwa ba za ta dauremata gindi yanda laifin Hayat zai shafi yaransa a wurinta ba.

“Ba da ke nake ba?” Fadin Maryam wannan karon ranta a matukar ɓace.

Dole ta mike ta nufi dakin Adam sadda ta ji wani kwalla ya tahomata. Bata son ganin wanda duk ya haɗa jini da Hayat, ji take gwara ma ta koma hannun dangin mahaifinta yanda za ta kaurace musu gaba daya.

Wayar Inspector ya amsa inda yake ba shi tabbacin za’a shigar da ƙara kotu, abinda ya rage nemo Salma da Hayat.

“Ba zai yi wuya ba in Sha Allah.” Adam ya furta cikin rawar murya don dakyar ya iya miƙewa ya yi sallar Asuba. Tambayar Sa Inspector ya yi ko ba shi da lafiya, ya nuna komai lafiya. A karshe godiya ya yi mishi  kafin su yi sallama.

Kara kudundunewa ya yi cikin bargo yana rawar sanyi. Da haka ta yi sallama, jin muryarta ya daure ya amsa ta shigo dakin. Ganin yanayinsa ya ɗan daki zuciyarta. Sai kuma ta yi kamar bata lura ba.

“Ka zo inji Mama.” Tana fadin haka ta juya za ta fita.

“Gorgeous.”

Ta manta rabon da ya kirata da wannan sunan hakan yasa ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba. Yana jin jiri haka ya daure ya mike ya ƙaraso inda take gami da riƙe hannunta. Wani irin zafi ta ji a hannunsa. A lokaci guda wani irin shock ya hau har saman kanta. Ta dubeshi. Daga shi sai wando na kamfanin Adidas sai vest.

“Me nayi miki?” Ya fadi dakyar yana dafe kai jin da ya yi jiri na neman kwasarsa.

“Wane laifi nayi gareki?”

Nan da nan ta tuna da Hayat, ta ji wani bakin ciki. Bata san sadda ta fincike hannunsa daga nata ba ai kuwa ya zube a ƙasa. Sai kuma ta kasa jurewa ta durkusa da sauri tana tallafo kansa.

Bai damu ba sai dai ya yi mamakinta.  Girgiza mata kai ya shiga yi idanunsa sun kaɗa.

“Kar muyi haka, kar kimin haka. Ba kimin adalci ba.”

Ta kasa dubansa, ta yi azamar sakinsa ta mike da sauri ta fice. Tsayuwa tayi bakin kofar ta yi kuka mai isarta sannan ta share hawayen ta koma falon.  Tun shigarta mahaifiyarta ta zubamata idanu tana kallo.

“Yana ina?”  Wannan karon Umma ce ta tambaya cike da kulawa.

Humaira ta kauda kai daga hararar da Mama ke watsomata.

“Ba shi da lafiya, jikinsa zafi.” Jin haka hankalin Umma da Mama ya tashi, suka mike don zuwa dubashi. Ita kuwa daki ta shige tana maimaita abinda Adam ya furtamata a ƙwaƙwalwa.

‘Ta yaya ba zan maka haka ba? Bayan mahaifinka shi ya kashemin uba?’

Ta fadi a ranta kafin a zuciya ta jawo akwatinta ta soma kokarin hade sauran tarkacenta ciki.

“Humaira, wai meke faruwa? Me ya sameki tun jiya kin wani sauya?”

Amira ke maganar a sanyaye. Kallon da ta watsamata ya bata mamaki. Ta kasa hakuri gami da karasawa wurinta ta Dafa kafaɗarta.

“Don Allah meke damunki? Me akai maki har yake fusataki haka? Ki faɗamin ko..”

“Nace ki rabu da ni!  A’a! Dole sai kin ji damuwata? Ina ruwanki?!”

Yanda ta yi maganar ya ba Amira tsoro, ta soma tunanin Humaira nada iska. Ta matsa ta janye daga gareta don tsira da lafiyarta. Ta yi alkawarin ba za ta sake tambayarta damuwarta ba, a zauna a hakan.

Makalewa ta yi a dakin ta ƙi fita don tasan yanzu haka suna can suna nan nan da Adam kamar shi kadai ne namiji a gidan. Tsaki ta ja sai kuma ta shiga zubda hawaye. Tsinewa Hayat take a kasan ranta, duk shi ne ya ja ta daina ganin girman Adam da yan uwansa. Yanzun da take tare da su, ji take kamar ana mintsininta. Allah-Allah take yi su fice daga gidan a kaita gidan Kakarta.

*****

Isowarsa garin Kano kenan daga Abuja. Yakan zo duk karshen sati ya gaida uwar da ta riƙeshi tamkar ɗan cikinta ba tare da nuna bambanci ba.

Yanzun ma yana zaune a gabanta suna hira ta sakomishi maganar da ta sanyashi farin ciki.

“Hajiya nasan duk abinda zai fito daga bakinki gaskiya ne, yanzun ina ita Maryam din mu gaisa? Allah Mai iko.”

Cewar Alhaji Idris cikin wani irin farin ciki marar misaltuwa. Dariya Hajiya ta yi.

“Maryam tana nan, ko dazu mun yi waya ta tabbatarmin za ta shigo kawomana Humaira. Kai dai babu yanda Allah ba Ya ikonSa. Kar ka so ka ga kamannin yarinyar da Haisam, wallahi bambancin kawai shi namiji ne ita kuwa mace ce. Kamr an tsaga kara an yar. Don ko Fu’ad ba ya kama da Haisam irin yanda Humaira ke yi.”

Murmushin farin ciki Alhaji Idris ya yi.

“Alhamdulillah. Shi Fu’ad din ya zo kuwa? Dama yau na zo da niyyar shiga wurinsa, idan ita uwar bata da hankali ai shi ɗan yana da shi ko don kasancewarsa tsatsonmu.”

Jinjina kai Hajiya ta yi.

“Tabbas wannan gaskiya ne, nima na gaji da bibiyarta. Ya isa hakanan, zan nunamata ba tsoronta ake ba.”

“Ai Hajiya kar ma ki wahalar da bakinki, shima Fu’ad din yana da laifi. Zan dai sameshi mu yi magana. Ita Salmar ai mun hadu a Abuja, na ganta ganin idona a Hotel sadda nake ganin wani abokin aikina.”

Hajiya ta gyara zama.

“To, tare da mijinnata suke kenan?”

Alhaji Idris ya taɓe baki game da ɗaga kafaɗa.

“Wannan ne bani da tabbas a kai gaskiya. Sai dai na ganta a can kuma ta yimin halinnata. Ta nunamin ita ƴar kananan mutane ce.”

Nan ya ba Hajiyar labarin yanda sukai.

“Allah Ya kyauta, Ya shiryeta idan mai shiryuwar ce.”

Fadin Hajiya, Alhaji Idris ya amsa.

*****

“Meyasa kika ɓoyewa mahaifiyar Haisam cewar Fu’ad ba ɗan Haisam bane? Mene hikimar?”

Hashim ya watsawa Maryam tambaya sa’ilin da suke kokarin shiga asibiti duba Fu’ad. Ta ɗan numfasa.

“Zan fadamata, ina tausayin yaron ne, amman zan fadamata a yau idan na shiga kai Humaira.”

Jinjina kai Hashim ya yi.

“Akwai tausayi, amman hakan shi ne daidai. Gwara su ji daga bakinki. Radadin zai ragu akan su ji a waje idan an soma shari’a. Idan hakan ta faru ba’a kyautamusu ba.”

Maryam ta yi shiru tana tunanin ta inda za ta soma fasa wannan kwai mai mugun wari.

<< Rumfar Kara 36Rumfar Kara 38 >>

1 thought on “Rumfar Kara 37”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.