"Sannu Fu'ad, Allah Ya baka lafiya."
Ya dubi Mama gami da murmushi.
"Amin Mama, na gode." Maryam ta mayar mishi martanin murmushin tana kokarin ɓoye ciwon zuciyarta sanadin ganinsa a wannan yanayi.
"Adam da Umma fa?" Ya watsa tambayar ga Uncle Hashim. Ajiyar zuciya ya sauke.
"Zasu taho anjima kadan, Baba Malam suke jira. Zai yi baƙi daga Kauyen Cinnaku."
Maryam ta dubi Hashim, tasan hakan ne ta kuma san dalilinsa na ɓoyewa Fu'ad rashin lafiyar Adam gudun kada ya damu.
"Uncle na gaji da asibitin nan, ku tayani addua Allah Ya bani lafiya ko. . .