Skip to content
Part 38 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Sannu Fu’ad, Allah Ya baka lafiya.”

Ya dubi Mama gami da murmushi.

“Amin Mama, na gode.” Maryam ta mayar mishi martanin  murmushin tana kokarin ɓoye ciwon zuciyarta sanadin ganinsa a wannan yanayi.

“Adam da Umma fa?”  Ya watsa tambayar ga Uncle Hashim. Ajiyar zuciya ya sauke.

“Zasu taho anjima kadan, Baba Malam suke jira. Zai yi baƙi daga Kauyen Cinnaku.”

Maryam ta dubi Hashim, tasan hakan ne ta kuma san dalilinsa na ɓoyewa Fu’ad rashin lafiyar Adam gudun kada ya damu.

“Uncle na gaji da asibitin nan, ku tayani addua Allah Ya bani lafiya ko kuma za ku huta.”

Yanda ya yi maganar sai ya ƙaryar da zuƙatansu. Uncle Hashim ya karasa gami da dafe kafaɗarsa.

“Wa ya ce maka mun gaji da jinyarta Fu’ad? Kaima ɗanmu ne. Ba ka da laifin komai. In sha Allah za ka warke. Dr yace ka dinga motsa jiki ta hanyar yin tafiya ko yaya ne, zan tambayeshi idan ya shigo ko yau ma ana iya farawa. Idan ya ce eh sai mu soma ka ga harabar asibitin kadan ka shaƙi iska. Muna nan muna addu’a, In Sha Allah za ka warke tamkar ba’a yi ba.”

Murmushi Fu’ad ya yi mai bayyana haƙora. Ya lumshe idanu gami da gyaɗa kai.

*****

Ta dubi agogo, awan su Mama kusan uku kenan da barin gidan, ba karamin takaici ta ji ba ganin tare zasu wuce da Adam asibiti. Ta zauna kawai a falon bayan sun dawo daga rakiyar Inno da su Malam Zakari wadanda zasu kama hanyar Dambatta wurin yan uwansu. Sun rabu da Jamila zuciyoyin ba dadi sai dai ba yanda suka iya. Amira ko kallonta ba ta yi ba ta shige ɗaki. Humaira ta ji ranta ya ƙara zafi, gidan ya fice a ranta tamkar ta yi tsuntsuwa. Shigowar Umma falon ne yasa ta ɗan dubeta kadan gami da rage daurin da ta yiwa fuskarta.

“Yauwa Humaira shirya yanzu zamu wuce kinji ko? Ya tashi daga baccin kuma Alhamdulillah jikin da ɗan kwari.”

Ciki-ciki ta amsa da toh kafin ta shige ciki don dama abinda take jira kenan. Ita yanzu bata damu da wani Adam ba balle samun saukinsa. Tana shiga dakin, Amira kamar wacce aka mintsila, ta mike ta fita. Abin ya taɓa zuciyarta sai dai koda ta tuna abinda ke faruwa kawai ta ji ranta ya ƙara ɓaci, ta ja tsaki ta yafa mayafinta gami da jan akwatinta.

A hanyar barandar gidan suka ci karo da shi, ya shirya cikin baƙar t-shirt da jeans blue. Kallonta ya tsaya yi dakyau yana wasa da mukullin mota, ganin haka ta dire akwatin ta juya zuwa dakin su Prof.

Ta riskeshi tare da Hajiya Rasheedat suna ɗan taɓa hira, ta gaishesu gami da yi musu bankwana.

“Toh, tafiyar ta tashi? Sai yaushe za mu ƙara ganinki kenan?” Fadin Prof yana dubanta.

“Ai zan dawo ba da jimawa ba. Tare zamu wuce Maiduguri ma.”

Ta fadi ba don tana da tabbacin hakan ba. Suka yi mata fatan alheri da mika sakon gaisuwa zuwa ga Hajiya Karime sannan ta mike ta fito. Nan ma wurin Baba Malam ta shiga, ta yi bakin cikin tarar da shi a ciki kamar ta juya sai dai ba dama don har sunanta Baba Malam ya kira ƙarewar ganinta. Ta shigo ta gaidashi.

“Lafiya kalau Indo, har zaa wuce? Toh ki zama mai hakuri a kauda kai a komai na duniyarnan don Allah. Kada ki zama mai riƙo da sanya abu a ranki kinji ko?”

Ba ta fahimci dalilinsa na yin nasiha game da hakan ba, ta dai amsa ya ce ta gaida su Hajiya. Kusan tare suka fito da Adam. Ji ta yi an riƙe mayafinta

“Meke damunki A’isha, me nayi miki?”

A’ishar da ya ambata ya kashemata jiki, ta ji kwalla sun cika idanunta.

“Ba komai, ka sakarmin mayafi su Umma na jira.”

Adam ya dawo ta gabanta ya tsaya suna kallon kwayar idanun juna. Ta yi kasa da kanta saboda kaifin da nashi idanun suka yi ga nata.

“Kin ji abinda ke faruwa kenan? Kin tsane ni saboda na kasance ɗa ga Hayat? Nima na tsaneshi Humaira. Mahaifina ne amman na tsaneshi.”

Ta kalleshi kadan, sai ta ji kamar yana neman raina wayonta ne.

“Ni ban ce haka ba, bai shafeni ba, babu abinda naji. Ka ƙyaleni don Allah.”

Tana kaiwa nan ta fincike mayafin da gudu-gudu ta bar wurin. Jan akwatinta ta yi zuwa gaban motar.

“Wai ina ya tsaya ne? Idan jikin ba zai barshi ya kaimu ba, ya zauna mu samu mai kaimu.”

Ita kam Humaira ba ta amsa ba, Amira kuwa fuskarta a daure don jikinta ya yi sanyi da lamarin Humaira. Umma na shirin kara magana sai gashinan. Hakuri ya bayar kafin ya budemusu su shiga. Umma ce a gaba su kuwa a baya. Yana lura da yanda suke hararar junansu asalima kowacce kusa da window ta zauna kamar wasu baƙin juna. Bai ji dadin yanda Humaira ta kalli abin ba, ta kasa yarda da kaddarar abinda ya afku ga mahaifinta adalilin nasu mahaifin wanda ko haƙƙokinsu bai san ya cika ba ballantana na wasu.

Har suka iso shi da Umma kawai ke taɓa hira.

Tunda suka soma tafiya a dogon barandar asibitin suka saki baki suna kallon Fu’ad da mamaki. Hannunsa alan kafaɗar Uncle Hashim suna tafiya a hankali. Shi da Maryam sun saka shi tsakiya, sai Haidar dake gefe yana basu labari wanda ya sanyasu dariya sosai. Umma don farin ciki bata san sadda hawaye suka zubomata ba. Shi kansa Adam sai ya mance dukkan wani ɓacin ran da Humaira ta haddasa mishi toh ballantana Amira da Humairar wadanda ke kwana da tashi da tausayin Fu’ad din.

“Yaya Fu’ad.” Amira ta furta murya a sama kadan. Sai a sannan suka lura da su, Fu’ad ya ɗagomusu hannu. Suka karasa, Adam baki sake ya riƙe hannun da Fu’ad ke miƙa mishi.

“Ya haka?” Ya tambaya ba da zato ba.

“Jiki fa Alhamdulillah, mun fito da shi bisa umarnin likita. Ya ce idan har aka ci gaba da ba shi kulawar da ta dace suna kyautata zaton sallamarsa nan da kwanaki ƙalilan.” Uncle Hashim ya fadi cike da tsananin ɗoki.

“Alhamdulillah, ba abinda zamu ce ga Allah sai godiya. Allah Ya karamaka lafiya.”

“Ameen Umma. Ni kaina na matsu ya warke don bikina ba zai yi dadi ba babu shi. Adalilinsa na sanya aka ɗaga fa.” Haidar ya furta yana duban Umma don zuwa lokacin ya ji labarin komai daga Fu’ad ya kuma nuna jin dadinsa da wannan sauyi na uwa da Fu’ad ya samu sai dai ya tayashi jimamin ɓoyon da akai masa.

Dariya Haidar ya basu.

“Ai shima auren zamu yi mishi da zarar ya farfaɗo ya maida ƙashin wuya in Sha Allah.”

Fadin Mama cike da zolaya. Fu’ad ya narke fuska yana duban Adam.

“Bros kana jin su ko?”

“Yo me zai iya fadi? Ai da kai da shi duk tafiyar guda ce. Gwara kai yanzu kake naka tashen samartakar, yanzu shi sai dai ya bi sahun tuzurai.”

Maganar Umma ta sanya kowa dariya banda Humaira. Adam dai bai ce komai ba, shi kansa hankalinsa na ga Humaira ya ga ko za ta murmusa, ya kara tsorata da yanayin daurewarta.

Suka dunguma zuwa ciki, Hashim da Maryam suka yi musu sallama tare da Humaira suka fice.

Bayan tafiyarsu, Haidar ya wuce, ya rage daga su sai su.Fu’ad ya dubi Adam.

“Yayana.” Kusan duk suka dubeshi banda Amira da ta maƙala earpiece a wayar Umma tana kallon Film.

“Lokaci ya yi da zasu girbi abinda suka shuka. Ban ji wani a cikinku ya ce an dauki wani mataki ba. Ina kyautata zaton ba iyakar abinda suka shuka ba kenan. Akwai sauran rina a kaba.”

Daga Umman har Adam sun fuskanci manufar maganarsa, yana magana kan Salma da Hayat.

“Hakane, kar ka damu. Yanzu abinda ya rage a kaisu gaban kotu a yanke musu hukunci.” Adam ya furta.

“Kana nufin an gano laifin da suka aikata? Me suka aikata bayan wannan?”

Fu’ad ya nemi sani cike da ɗoki.

Umma ta dubi Adam gami da girgiza mishi kai alamar kada ya ce uffan. Fu’ad ya dubeta gami da riƙemata haɓa.

“Na fa ganki Umma, kina so ki hanashi fadamin ko? Kina tsoron kada jikina ya rikice? To wallahi na warke Umma. Alhamdulillah.”

Yanayin maganar ta basu dariya suka murmusa, Umma ta rike hannunsa.

“Zuwa yanzu da na gane kaima ɗana ne, bana fatan abinda zai ƙara sanyaka bakin ciki a rayuwa. Ina kaffa-kaffa da dukkan abinda zai taɓa lafiyarka. Ina fatan kulawar da ban baka kana karami ba, na ba ka ko kalilan ne daga cikinta a yanzu. Ka yi hakuri, muna nan da kai za ka ji komai ɗayansa abubuwa suka wakana. Yanzu mun fi kaunar samun saukinka.”

Shiru ya yi yana kallonta yayinda idanunsa suka kaɗa. Ya damƙe hannunta sosai.

“Umma kin sha wahala a rayuwa, ina fatan karshensa kenan. Idan na kalleki na kara tabbatarwa kece kika haifeni, sai naji wani sanyi da dadi sun ziyarci zuciyata. Umma kina da hakuri, kin jure dukkan wani wulakanci daga wancan mutumin..”

“Mahaifinku ne Fu’ad, hakanan zaku yi hakuri.” Fadin Umma tana share hawaye gami da nunamishi ya girmama shi ko don kasancewarsa mahaifinsu.

“Don Allah abar maganar.” Adam ya nemi hakan ganin ransa ya soma zafi. Fu’ad ya dubeshi yana murmushi. Shi kadai yasan me yake ji a ransa, ganin kallon zai yi yawa Adam ya ɗan yi tafi a gefen idanunsa. Wanda ya sanya Fu’ad dauke kai ya maida ga Umma. Karshe ya kwantar da kan nashi saman kafaɗarta yana mai bata hakuri.

*****

Mama ta dubi Uncle Hashim bayan kammala waya da Barrister Munir.

“Ya tabbatarmin zai zo gidan yanzu. Inaga gwara shi ya yi musu bayanin sai na ɗora da nawa don su fi fahimta.”

Hashim ya jinjina kai da murmushi.

“Hakane kin yi gaskiya.”

Har suka iso gidan suna hira Humaira ba ta sanya musu baki ba don ita yanda suke wa juna murmushin mamaki ya koma ba ta, duk da karancin shekarunta ta shinshino wani abin tsakaninsu.

Tarba da hannu bibbiyu suka samu daga Hajiya Karime, zamansu ba jimawa sai ga Alhaji Idris ya dawo gidan. Sakin baki ya yi yana kallon Maryam har ya ƙaraso ya zauna.

“Allah Mai Iko, Maryam ce dai dagaske.”

Ta gaishe shi a ladabce ya amsa da mamaki. Nan kuma aka shiga hira yana karewa Humaira kallo da tsantsar mamakin kamanninta da Haisam.

Maryam ta dubeshi dakyau.

“Na godewa Allah da samunka da nayi Alhaji. Ina son a yi komai a gaban kowa dama. Idan don samu ne a kiramin sauran yan uwan marigayi Haisam don Allah.”

Ta ƙarashe da duban Hajiya Karime. Ba musu Hajiya ta umarci Alhaji Idris kan ya kira duka yaranta don dama shi kadai ne wanda suke yan uba.

Ya kira kowa, zuwan Barrister Munir ya basu mamaki don rabonsa da gidan an kwana biyu.

Jim kaɗan yan uwan suka zo. Maryam ta umarci Humaira akan ta basu wuri. Ta mike don itama ba ta son ki ta riga ta san abinda za’a maimaita fadi tunda ta ji a gidan Prof.

Kaf yaran Hajiya Karime maza ne, idan ka ganta da ƴa mace, to riƙonta take.

Haisam ne babban ɗanta sai dai bata ba shi wannan matsayin saboda alkunya da kuma kara irin ta mutanen da. Idris take kira matsayin babban ɗan ta, ta fi yin shawara da shi hakanan ta shaƙu da shi sosai, tafiyarsa Misra ne ya janyo suka yi baya-baya har sabo mai karfi ya shiga tsakaninta da Haisam. Daga Haisam sai Sadik sannan Nura. Yaranta uku cif a duniya.

Barrister Munir ya soma da Bismillah kafin ya karanto musu abinda ke faruwa har da kiran da Haisam ya mishi akan yana son ganinsa da kuma abinda kundin sirrin Haisam ya ƙunsa dangane da kisan da aka yi mishi. Maryam ta ɗora da abinda basu sani ba dangane da Fu’ad da kuma rashin lafiyarsa a yanzun.

Hajiya Karime kuka take har da majina tana tsinewa Salma.

“Haba, ashe kashemin ɗana aka yi? Ba yanda ban yi akan ya fadamin dalilinsa na rabuwa da Salma ba amman Allah Bai ba shi ikon ya fadamin ba. Ashe sai bayan ransa nake da rabon jin komai. Amman daga Salma har shi Hayatun tsinannu ne. Don Allah lauya kar ka barsu su sha iskar duniya. A yi musu kalar kisan da suka yiwa ɗana.”

“Kenan hatsarin ba hakanan ya afku ba, adalilin su ne? Kai Allah Ya isa! Allah Ya sakawa wannan bawannaSa.”

Sadik ya furta a zafafe cikin matukar bakin ciki da ɓacin rai. Aka amsa da amin.

“Amman fa kada ayi kuskuren ƙara wasu kwanakin ba’a cafkesu ba domin kuwa da idona na ga Salma a Noor Hotel dake Abuja. Ina tsoron ace ƙasar suke yunƙurin bari.” Alhaji Idris ya furta yana dubansu.

Maganar ta tashi hankalinsu, ya zama dole a gaggauta daukar mataki tun kafin su tsere hakan yasa Hashim fita waje ya yi kiran Adam. Inda Salma take ya fadamishi don a gaggauta daukar mataki.

*****

Shi kuwa Adam kai tsaye ya yi kiran Inspector Kabir ya labarta mishi, ya ba shi tabbacin za’a yi duk abinda ya dace don su zo hannu. Daga bisani ya mishi godiya suka yi sallama.

Fu’ad ya dubeshi.

“What happened?”

“Ba komai, Umma ɗanki fa yana so ya koyi gulma. Shikenan bani da damar waya sai ya nemi ba’asi? Bari na wuce ofis.”

Dariya kadan Fu’ad ya yi yana taunar  tsokar naman da Umma ta sanyamishi a baki. Hararar wasa Umma ta jefawa Adam.

“Ɗana bai iya gulma ba. Kawai dai so yake ya ji ko ka samar mana suruka ne.”

“Yes Mom, I love you!”  Fadin Fu’ad yana ɗagamata hannu alamar ta burgeshi, Amira na dariya. Ganin kallon da Adam ya watsamata yasa ta kama bakin ba shiri.

Bude kofar ya yi kawai ya fita bayan ya yiwa Fu’ad alamar zai kamashi. Umma na son tambayar jikinnasa sai dai tana gudun Fu’ad ya tashi hankalinsa don Adam ya roƙi da a ɓoye rashin lafiyarsa a gabansa.

“Wai shi Amir ba zai zo na ganshi ba?”

Murmushi Umma ta yi.

“Zai zo, tare zasu taho da Khalisat karshen satinnan.”

Ya jinjina kai.

“Har karshen sati?”

Yanda ya furta a sanyaye sai ya kashemata jiki.

“Yaushe kake son zuwansu?”

Ya girgiza kai kawai ya miƙa mata baki alamar ta sanya mishi lomar abinci. Itama ta share maganar.

*****

Tayi parking a ofishin ƴan sandan bayan kiran da ta amsa daga Halima gami da kwatancen ainahin inda aka kaita.

Fitowa ta yi tana mai jin rayuwarta cikin matsi sakamakon Gwaska da ya hanata sakewa da sauke kyakkyawan numfashi.

“Wa kike nema Hajiya?” Ta karewa mai tambayar kallo, siriri da shi tamkar a hure, guntun tsaki ta ja a ranta. Ba don bakin hali irin na Halima ba, ba ta taɓa tunanin tako ofishin ƴan sanda ba a rayuwarta.

“Na zo ganin Halima Badar.”

Ya ƙaremata kallo yana kara ganin shaidar cewar yar uwarta ce saboda kamannin da suke yi da juna. Record ya budemata ta rubuta sunanta gami da yin signing kafin ya karɓi wayoyinta ya mata jagora zuwa inda take. Halima na ganin Hanan ta miƙe tana mai ji kamar an mata bushara da gidan aljanna.

“Hanan?” Hanan ta watsamata harara tana jin kamar ta shaƙo wuyanta. Aka basu damar ganawa.

“Halima kin cuce ni! Kin hana kanki rayuwa mai dadi nima kin tauyemin nawa. Mene fa’idar abinda kika ɓoyewa wadancan banzayen ku ka aikata? Yanzu ina kika ƙare? Kalleki fa!”

Halima ta haɗiyi miyau na bakin cikin da ya taso mata.

“Ai kuma wannan ta wuce. Hanan Kinga dukiyoyina? Kin adanamin?”

Tayi maganar kamar mai raɗa.

“Na gani, sai dai ya zamemin tashin hankali da barazana domin yanzu haka maganar da nake miki takardun suna hannun Gwaska. Ya kuma cemin lallai nasan yanda za’ayi a shirya takardu ki saka hannu komai ya dawo karkashin ikonsa. Na rasa yanda zan yi da rayuwata. Gaba daya ya bi ya takuramin.”

A matukar gigice Halima ke girgiza kai.

“Kar ki fara Hanan! Kar ki soma wannan gangancin! Ki tattara ki koma gidan ƙawayenki da zama kafin na fito. Insfeta ya tabbatarmin da zarar an cafke Salma da Hayat zai sakeni. Gwaska zai iya kasheki, na sanshi fiye da tunaninki.”

Shiru Hanan ta yi tana ƙare mata kallo.

“Halima waya Ubana?”

Harara ta watsamata.

“Hanan Ina a wannan hali ba ki damu da komai nawa ba dai ta ubanki kike? Toh wallahi kinji na rantse rashin jin waye ubanki ya fiyemaki alheri akan ki sani. Shashasha kawai!”

Ranta ya ɓaci, haka kawai take hangowa uwarta mutuwa wannan yasa take son sanin ubanta saboda watarana.

“Ki je ki killace kanki, kada ki yarda ki sake Gwaska ya damƙe ki don ina mai rantsemaki ba zai miki ta daɗi ba. Na sanshi farin sani.”

Jin haka Hanan ta sauke ajiyar zuciya.

“Shikenan.” Daga haka ta juya babu ko fatan alheri ga uwar ta tafi, Halima ta bita da kallo tana jin inama akwai damar fita ta bi bayanta. Ai da Hanan ko ta ƙi sai ta bita sun bar garin sun ke sun ci rayuwa mai dadi a ko ina ne ma.

Bayan Kwanaki Uku.

Shigar da case din kisan Alhaji Haisam kotu ya janyo hankulan ƴan jarida da gidajen rediyo. Tuni aka yi nasarar damƙe Hayat da Salma a Noor Hotel tare da kawosu garin Kano domin yin Shari’a. A kwanakin duk inda ka shiga zancen da ke tashi kenan a Kano, batun kisan Alhaji Haisam. Kasancewarsa mutum mai taimako da kuma yi don Allah, yasa da yawa an sanshi ya yi suna a unguwar da yake har ma da wasu wuraren.

 Nan kuma kallo ya koma sama, babu wanda ya taɓa kawo cewa kashe shi aka yi face ana kyautata zaton wa’adinsa ne ya cika Allah Ya dauke abinsa.

Ana gobe za’a shiga kotu, Adam tare da Uncle Hashim da Malam Kabiru suka kai ziyara ofishin ƴan sanda don ganin Hayat. Koda suka isa Adam tsayuwa ya yi cak a waje ya ce ba zai ƙarasa ba suna iya shiga su ganshi. Hashim zai matsa Malam Kabiru ya hanashi ya ja hannunsa suka fice.

Hayat zaune a bayan cell sai muzurai yake gami da kwafa yayinda Salma ta hada kai da gwuiwa tana rizgar kuka.

“Hayatu.”

Ya ɗago ya dubi Malam Kabiru, bai taɓa zaton akwai wata kalma makamanciyar kunya da za ta riskeshi ba ballantana ita kanta kunyar. A yau ji ya yi ba zai iya kallon kwayar idanun tsohon suruki kuma ɗan uwa gareshi ba. Wannan ne dalilin da ya sanya shi sauke kai ya ƙaraso ya durkusa yana mai gaidashi.

“Malam Barka da dare.”

Hashim dubansa yake kamar ya shaƙo wuyansa haka yake ji, sai dai kaifin idon Malam da irin kashemin da ya jaddada gareshi ya sa a dole ya ja bakinsa ya yi shiru. Salma kuwa jin muryoyi ya sa ta ɗago kai a firgice tana dubansu kafin ta rarrafo tana kuma ta riƙe karfe idanunta kan Malam.

“Na tuba Baba! Don Allah kuyi hakuri ku sanya yan uwan Haisam su yafemin a sakeni. Wallahi ba zan ƙara kashe ko kiyashi ba balle mutum.”

Hayat ya yi mata duban yanda ta zama mai son kanta. Ya yi turr da kalar soyayyar da ya yi mata wanda a sanadinsa ya tozarta yake kuma kan tozarta fiye da na yanzun muddin aka shigar da shi kotu a gobe.

“Hayatu ka cuci zuri’armu. Ka ɓata sunanka saboda ka biyewa ruɗin duniya. Mace da dukiya fitina ce agaremu! Yanzu Hayatu wa gari ya waya? Ka biyewa don zuciya ka raba uwa da ɗanta na fin shekaru ashirin. Ka biyewa son zuciya ka kashe rai. Me ya yi zafi? Hakkin Bilkisu kadai da ka dauka a zamantakewarku ashe bai isheka ba? Kaiconka Hayatu, ka gaggauta tuba. Mahaifinka na can a kwance ba lafiya tun sadda labari ya riskeshi akan abubuwan da ka aikata da kuma kamun da akai maka. Me ya fi wannan zafi da raɗaɗi ace ɗa ke jazawa uba rashin lafiya da cutuka? Ba abinda zan ce maka, sai dai ka sani, yana dakyau ka nemi gafarar Bilkisu da kuma yaranka wadanda ka ɓatawa suna ka ɗauki haƙƙinsu. Ka tauye rayukansu duk saboda ka tsani zaɓin da mahaifinka ya yi maka. Haihuwa kadai da ku ka yi da Bilkisu wannan ya ci ace ka saduda a lokacin ka gane cewar  ita din ce dai uwar yaranka ka rungumi ƙaddara kun zauna lafiya. Sai dai kuma ka bar gini tun ran zane. Ka yi babban kuskure, ka dage da tuba don Allah Mai ji ne kuma Mai gani ne. Ba Ya kyale zalunci duk daɗewar da zai yi. Yanzu ka duba ka ga, wa gari ya waya? Ina Fu’ad? Yaron da bai ji ba bai gani ba, ka dauki hakkinsa ka raba shi da mahaifiyarsa tun yana cikin jinin haihuwa. Adalilin irin tarbiyya da rainon da ku ka yi mishi da kuma bakin cikin da ku ka haddasa mishi,  yana can kwance a asibiti rai a hannun Allah.”

Malam Kabiru na kaiwa nan ya kasa kwakkwarar magana a dole ya fice sakamakon kukan da ya tahomishi. Hashim ya dubi Hayat wanda ke kuka har da sheshsheƙa kansa a ƙasa sai dai Malam ma cewa Fu’ad  rai a hannun Allah ya ɗago.

“Dagaske Fu’ad ba shi da lafiya? Meya sameshi?” Hayat ke tambayar Hashim a ruɗe. Don bakin ciki Hashim kasa magana ya yi ya juya ya bi sahun Malam. Yana ji Hayat na kwala masa kira kamar makogwaron zai cire amman ko juyowa bai yi ba. A motar suka iske Adam ya haɗa kai da sitiyari ya yi shiru, Malam ne ya shiga yi mishi nasiha mai ratsa zuciya akan hakuri da yarda da ƙaddara. Haka ya daure ya kai zuciya nesa suka fice. Har a lokacin yana dana sanin kasancewar Hayat mahaifi gareshi.

*****

Karfe uku da mintuna na dare, ya ƙurawa mahaifiyarsa idanu kasancewar ranar ita ta tayashi kwana a asibitin sai kuwa Adam dake nashi ofishin yana aiki. Yakan leƙosu ya koma. Aikin ma yana yinsa ne sai dai zuciyar ba dadi domin maganar mahaifinsu babu inda ba ta zagaya ba a asibitin. Wasu sun sa cewa mahaifinsa ne yayinda wasu basu da labari.

Runtse idanu ya yi yana mai jin sautin kukanta a cikin sujjada. Ya mirgina ya juyamata baya, kwanciyar ma ya daina jin dadinta wannan ta sanyashi miƙewa ya zura takalmi. Har ya sa ƙafa ya fita daga dakin bata da masaniya a kai. Kai tsaye ofishin Adam ya nufa, asibitin shiru sai tsilli-tsilli kake ganin jama’a. Ya iskeshi shima kwance saman three sitter  yana sauraron karatun Alkur’ani a wayarsa idanun a rufe. Ƙarasawa ya yi ya zauna kusa da ƙafarsa wanda ya ɗan firgita Adam, ya dubeshi sannan ya mike bayan ya dauke wayar daga saman kirjinsa ya kashe karatun.

“Fu’ad lafiya? Ina Umma?”

Fu’ad ya kwantar da kai saman cinyar Adam sai kuka, kuka sosai yake kamar yaron goye ya kasa cewa uffan.

Adam duk dauriyarsa sai da ya ji hawaye na gangarawa saman kuncinsa. Ya kunna karatun ya ci gaba da saurara ba tare da ya ce mishi uffan ba, bai kuma hanashi ba. Tunawa ya yi da  Amira wadanda suma dakyar ya rarrasheta har sai da Malam ya haɗa da nasiha kafin a shawo kanta ta nutsu. Suna da labarin komai a yanzun dangane da mahaifin da tun haihuwarsu ya tsanesu don kawai sun mishi zuwan bazata duniyar tamkar shi ya Haliccesu.  Amir kam ko a jikinsa don dama shi bai daukeshi a matsayin Uba ba tun tashinsa. Ya fi girmama Adam ma a kansa. Ya tabbatar da Adam abin ya shafa zai yi abinda ake kira kusan hauka.

<< Rumfar Kara 37Rumfar Kara 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×