"Haidar kira Dr." Fu'ad ya furta a hankali yana dafe da saitin zuciyarsa ganin Haidar ya yi tsaye tsoro ya sanya ya rasa abin yi sai kiran sunan Fu'ad din. Maganar Fu'ad ta farkar da shi daga suman tsayen da ya yi. Da sauri ya fice yana kwalawa Dr Ibrahim kira kasancewar shi ne on duty.
Jim kadan suka dawo tare sai dai ina! Har kwayoyin idanun Fu'ad sun yi sama. Dr Ibrahim ya yi iyakar yinsa ya fahimci aikin ba nashi ne shi ɗaya ba don haka ya nemi taimakon sauran likitocin. Nan da nan. . .