Skip to content
Part 40 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Haidar kira Dr.” Fu’ad ya furta a hankali yana dafe da saitin zuciyarsa ganin Haidar ya yi tsaye tsoro ya sanya ya rasa abin yi sai kiran sunan Fu’ad din. Maganar Fu’ad ta farkar da shi daga suman tsayen da ya yi. Da sauri ya fice yana kwalawa Dr Ibrahim kira kasancewar shi ne on duty.

Jim kadan suka dawo tare sai dai ina! Har kwayoyin idanun Fu’ad sun yi sama. Dr Ibrahim ya yi iyakar yinsa ya fahimci aikin ba nashi ne shi ɗaya ba don haka ya nemi taimakon sauran likitocin. Nan da nan aka rufu akan Fu’ad, Haidar kuwa na waje tsaye yana hawaye. Amininsa tun yarinta, yau shi ne a wannan yanayi babu halin da zai iya taimakonsa. Ya ji zuciyarsa ta karye. Waya ya ciro da zummar kiran Adam sai kuma ya fasa. Jin wayarsa na ƙara ya dauka, mommynsa ce. Nan ya fashemata da kuka yana bata labarin abinda ke faruwa da Fu’ad. Mintoci kadan ta iso asibitin tare da mahaifinsa, Alhaji Hussain Dikko. Ga duk wanda ke garin Kano, fuskar ba ɓoyayya bace gareshi a dalilin riƙe muƙamin mataimakin gwamna da ya yi shekarun baya. Hakan ta sa mutane da dama suke tsayawa gaisheshi. Haidar ya faɗa jikinsa.

“Please Daddy, bana son na rasa Fu’ad.”

Cike da lallami yake dukan bayan ɗan nasa.

“Da yardar Allah ba zai mutu ba, addu’a ya fi buƙata yanzun.”

Suna nan tsaye Dr Ibrahim ya fito. Bai ko lura da mutanen ba ya yi ofishinsa da gaggawa. Haidar na magana bai ko juyo ba wannan ta sa Alhaji Dikko bin bayansa.

“Dr ya jikin Fu’ad din?”

Dr Ibrahim wanda ke kokarin kiran Uncle Hashim a waya, ya ɗago yana dubansa. Kamannin Haidar ya hango da kuma kamanninsa da tsohon mataimakin gwamnan garin.

“Sunana Alhaji Hussain Dikko, mahaifi ga Haidar aminin Fu’ad.”

Hannu Dr Ibrahim ya miƙa suka gaisa.

“Ciwon Fu’ad ina tsoron ya kasance ba na tashi ba. Yana cikin wani hali mai ban tsoro ga karancin kayan aiki da muke fama da shi a asibitin nan,  idan son samu ne, ya kamata a fitar da shi ga kwararrun likitoci su ceci rayuwarsa.”

Girgiza kai Alhaji Dikko ya yi.

“Idan da dama, ina son ganin dan uwannasa.”

“Yanzu haka sun je wata sharia, amman na tabbatar yana..”

Kofar da aka banko ya dauki hankalinsu baki daya. Adam ne a hargitse.

“Ibrahim meke faruwa? Ina Fu’ad din?”

Hannu Alhaji Dikko ya ɗora saman kafaɗarsa.

“Ka nutsu ɗana, In sha Allah ba abinda zai faru da Fu’ad.”

Yasan ko waye, mahaifin Haidar ne.  Dakyar ya samu ya zauna, Dr Ibrahim ya yi mishi bayanin akan lallai sai dai a sauyawa Fu’ad asibiti duba da karancin kayan aiki sannan ana bukatar yi mishi aiki a zuciya da gaggawa. Anan Alhaji Dikko ya yanke shawarar sauya mishi asibiti.  Adam bai wani ja ba, fatansa da uwannasa ya samu lafiya. Ba jimawa su Hashim duk suka iso har da Umma wacce ke kuka. Jin shawarar da aka yanke na fitar da Fu’ad waje, ya kara hada hankalinsu, dakyar suka samu ganinsa, gaba daya ya sauka fuskar ta ƙara fari fat. Rai ba a bakin komai yake ba.

*****

A kwanaki biyar Fu’ad ya samu sauyin asibiti. Likitoci ne fararen fata wadanda suka ƙware a fannoni da dama.

*****

Tana zaune ta kudundune cikin kujera ta zurfafa cikin tunanin rayuwa ta ji sallamar mahaifiyarta. Ta ɗago da sauri tana mai amsawa kafin ta karasa a guje ta rungumeta. Maryam ta tureta ta wuce ciki fuska a daure. Wannan ya ƙara kashemata jiki. Ɗakin Hajiya Karime ta shige suka gaisa, ta jima sannan ta fito.

“Mama ina wuni.”

Harara Maryam ta watsamata lokacin da ta ke zama.

“Ba zan amsa ba. Ai kin isa, kin kai. Kin nunamin cewa dangina ba komai bane a wurinki. Kin isa ki sauya kaddarar Ubangiji? Ki faɗamin, daga kan Adam  har Amir a kasan ransu dadin yanda mahaifinsu ya kasance suke ji? Ke ga ki isassa wacce ba ta amfani da iliminta. Ba ki aiki da shi ba. Har kin san ki ja da ikon Allah? Da don ta su ne, an faɗamaki zasu so kasancewa da mahaifi irin Hayat ne? Wata nawa ki ka yi tare da su, kin taɓa ganin wani mummunan ɗabi’a a halayyarsu? To wallahi muddin ba za ki sauya tunani ba, da ni Maryam kike gaba ba da yan uwana ba. Kar ki sake ki tako gidanmu muddin ba ki chanza wannan banzan tunanin naki ba. Allah Ya ƙaddara ta wannan hanyar mahaifinki zai rasu. Ki godewa Allah kina da mahaifin ma, wadanda aka haifesu aka watsar a bola basu san asalinsu ba, su kuwa su ce me? Sai su tsani duk wani mai uba? Dakyau Humaira, ga Fu’ad can rai a hannun Allah har ana tunanin fitar da shi wata ƙasar, shi da aka rabashi da mahaifiyarsa shekara da shekaru? Shi kuma sai ya ce me? Mu zuba ni da ke tunda ba ki da kirki.”

Daga haka Maryam ta dauki jakarta ta yi hanyar waje, tana dab da fita ta ji Humaira ta rukunkume kafafunta tana kuka da fadin ta tuba ba zata ƙara ba.

Zuciya irin ta uwa, sai jikinta ya mutu. Ta juyo ta dubeta a sanyaye bayan ta ɗagota.

“Ba haka ake rayuwa ba, da haka ake daukarta mutane da dama tuni da sun mutu. Bilkisu jaruma ce wacce ba kowa ne zai iya jurar abinda ta shaƙa ba a rayuwarta. Hakuri babu wanda ba ta yi ba, har ta mutu tabon abinda Hayat ya yi mata da yaranta ba zai gogu a ƙasan ranta ba. Ba zan dauki wannan sakarcin naki ba Humaira, ban riƙi Bilkisu da yaranta akan komai ba, kada na kara ji ko ganin kin musu wani kallo da ba daidai ba.”

Gyaɗa kai Humaira yi tana sharar hawaye. Tausayin Fu’ad ke ratsa dukkan sassan jikinta.

“Mama ya jikin Yaya Fu’ad?”

“Yana bukatar addu’a, shi kadai ne soyayyar da zamu nunamasa a yanzu.”

Daga nan Maryam ta fita, Humaira har wurin mota inda direba ke jiranta ta yi mata rakiya sannan ta dawo ciki. Ta jima da nadamar abinda ta yi sai dai kunya take ji. Ta tausayawa Adam da su Amira ganin suna ji suna gani za’a yankewa mahaifinsu hukunci kisa. Allah kaɗai Yasan yanda suke ji a ƙasan ransu.

Da wannan ta koma dakin Hajiya Karime. Zama ta soma kokarin yi saman cinyarta, Hajiya ta bata kyakkyawan mintsili a gadon baya wanda sai da ta gantsare gami da sakin ƴar ƙara. Da kukan shagwaɓa ta dubeta.

“Kai Hajiya, don mugunta? Da na sani ma na bi uwata mun bar gidan.”

“Aikin ɓur, yo anan din me kike yi tun zuwanki banda aikin kumburi da shan ƙamshi? Na ga karshen fulawa ma da ta sha yeast, har ta fashe hakanan muka soye muka cinye.”

Murmushi Humaira ta yi gami da kwantar da kai saman cinyarta.

“Ai fa, sai ki ƙarasa ni tun ban ga tattaɓa kunnen nawa ba.”

Turo baki kawai tayi.

“Af, tashi maza ki ce Dije yau ta yi danwake, ai na manta inada baƙuwa. Babbar jikata za ta iso.”

Da alamun rashin fahimta take kallon Hajiyar.

“Wa kenan? Na dauka dai ni ce babbar jikarki duk fadin family dinnan?”

Daƙuwa Hajiya ta mata.

“Ƙaniyarki, ai ba Babanki ne ɗana na farko ba. Ko kin mance ina da Idrisu? To ɗiyarsa Salimatu ce za ta zo. Maza je ki ce Dije ta girkamata. Tana sonsa.”

Taɓe baki kawai Humaira ta yi ta fice zuwa kicin din ta isar da saƙo. Dakin da aka bata matsayin mallakinta nan ta shige gami da faɗawa saman gado. Kogin tunanin Adam ta faɗa, duk yanda ta so ta kaucewa zuciyarta, ta kasa. Shakka babu ko ba’a fassaramata abinda take ji game da shi, ita ta fassara da Kanta. Soyayyar Adam ce ke nukurkusarta. Ta lumshe idanu tana tuna kyawawan siffofinsa a kwayar idanunta. Ta tuna ire-iren abubuwan da ta aikata gareshi dab da tahowarta nan, ji ta yi ranta ba dadi. Wasu hawaye masu ɗumi suka zubo ta goge a haka har bacci ya yi awon gaba da ita. Ba ita ce ta farka ba sai wuraren hudu da mintoci. Sallah ta soma yi sannan ta fito falon ba tare da ta cire hijabi ba. Sakin baki tayi tana duban Anti Khalisat tare da wata budurwa da bata san ko wacece ba. Nan da nan ta sa a rai ita ce Salima kuma ta fahimci ita ce Amira ta taɓa bata labari matsayin wacce ke soyayya da Shuraim.

“Anti Khalisat?” Jin muryarta suka dubeta, da fara’a sosai Salima take dubanta. Suka gaisa da Anti Khalisat ba yabo ba fallasa, tana mai jan Jidda da wasa.

“Yar uwata.” Ta tsinci muryar Salima, wannan ta sa ta juya suka gaisa a mutunce.

“Kinga Mama ba ta jima da tafiya ba kuwa, nasan da tasan nan  za ku zo tare zaku taho.”

Anti Khalisat ta yi fuska kamar ba ta ji ba, Humaira ta yi zuciya da irin yanda take wani yankwane fuska kamar ba ta santa ba.

“Ai kuwa zan so ganin Mama, tun zuwana ban sanyata a idanu ba. Na santa sadda tana matar Late Uncle Haisam. Ban taɓa haɗuwa da ita ba a Yobe.”

Salima ke maganar da zuciya daya, sai ta burge Humaira. Nan suka hau hira ita kuwa Anti Khalisat, Hajiya na fitowa suna gaisawa  ta mike ta ce tafiya zasu yi ta bar Shuraim yana jira. Hajiya ta yi fadan dalilin da yasa bai shigo an gaisa ba, a karshe dole Hajiya ta sanya ya shigo. Humaira ta dubeshi. Murmushi ya sakarmata. Gaidashi ta yi ya amsa a sake. A karshe da zasu wuce har saƙon gaisuwa ta ba shi ya miƙa ga Amira. Ya amsa da hannu bibbiyu sannan ya bi bayan Anti Khalisat wacce tuni ta yi gaba. Abin ya ba Humaira mamaki sai dai koda ta tuna irin kusancin da ke tsakanin mijinta da Mama sai abin ma ya so bata dariya. Kishi ne irin nasu na manya dai. 

A wuni ƙalilan Humaira da Salima suka yi wani mugun sabo don Salima ba ruwanta. Yarinya mai raha da daukar komai ba komai ba. Humaira ta sha mamakin jin cewar tasan Shuraim ba ita yake so, kawai dai ta bar wa zuciyarta.

“Anti Khalisat nake kunya, amman na jima da cireshi a raina Humaira. Zumuncin Allah dai, shima ya sani kuma tuni nasan wacce yake so. Kawai dai na ba shi shawarar a bi komai a sannu kafin zuwa sadda hankula zasu nutsu.”

Ba karamin dadi lamarin ya yiwa Humaira ba, ji take inama Amira na kusa ta yi mata wannan albishir sai dai kuma tasan ko kallo ba ta isheta ba duba da cin kashin da ta yi mata.

*****

Jugum ta yi tana duban Halima cikin zubar hawaye. Halimar ma kallonta take tana kuka wiwi.

“Ban taɓa sanin cewa akwai ranar da lamura zasu kwaɓe har ni ciki ba sai yanzu, na yi zaton asirinnasu idan ya tashi tonuwa, to nawa zai rufu. Ashe ba karamin kuskure nayi ba. Ki yafemin Hanan. Ki tuba ki koma ga Allah ko albarkacin hakan da za ki yi, Allah zai min rahma.”

Hanan ta tsaida dubanta gareta, ita kanta yanzu ta cire rai da abubuwa da dama. Kwanakin nan ta samu tabbacin tana dauke da juna biyu kuma lissafinta ya bata cewar na Sidi Oscar ne. Ta sameshi da batun ya nuna ba sa hannunsa, ta je tasan yanda za ta yi. Kuma tasan ko giyar wake ta sha, Fu’ad ba zai taɓa aurenta ba. Rashin lafiyarsa a yanzu ya fi komai taɓa zuciyarta.

“Naji Halima, naji kin tuba. Sai dai ki sani, idan kika bar ni a haka toh ba abinda zai hana ni ci gaba da harkar baɗala. Halima mene asalinki? Waye mahaifina? Ki fadamin wurin wanda zan je na tsira da mutuncina.”

Girgiza kai Halima ta yi tana sharce majina da gefen riga.

“Bani da dangi Hanan, na tashi a matsayin shegiyar da Lanto mai siyar da tuwon dawa ta tsinta a wurin sana’arta ko yanken cibi ba a yi ba. Lanto ita ta yimin komai ta tsaftace ni. Ita ta riƙeni har zuwa girmana, a hankali na koyi sana’ar abinci, tare muke fita da ita. Kusan duk abinda ya shafi bariki ita ta koyar da ni. Ita ke yimin kwalliya don a cewarta ya fi jawomata kwastomas na abinci. Ta koyar da ni kissa da kisisina. Bayan tashi daga gidan abinci za mu tattara mu koma gidan da take haya wanda kafataninsu karuwai ne. Shan sigari, burkutu, wiwi babu wanda ba’a yi. Zama da breziya da ɗan fantai ba komai bane a rayuwar gidan. Da haka na tashi na zama kwararriyar yar bariki. An sha zubarmin da ciki a karshe bayan na hadu da mahaifinki GWASKA. Ya daukarmin kusan dukkan nauyina. Shi ya kara buɗemin idanu a harkar bariki domin shi bai tsaya a bariki da ni kawai ba, sai ya kasance yana haɗani da alhazai ina samo mana abinda ya samu. A lokacin Lanto ba lafiya, ni ke jinyarta da ɗan abinda na samo a yawon bariki. Ba jimawa Lanto ta rasu, nayi kuka kamar zan zare saboda ita kadai nake yiwa kallon uwa a gareni. Ba jimawa da rasuwarta aka ƙona gidan da muke ciki. Anan ne na hadu da Salma ta taimakeni ta daukeni zuwa gidanta a matsayin yar aiki. Duk wata ƙullalliya tare muka shirya alokacin har da Gwaska. Ba jimawa da haihuwar Fu’ad, na samu cikinki wanda bayan lissafi da gwaje-gwaje suka tabbata na Gwaska ne. Ya rantse akan sai dai a zubar ni kuma likita ya ce muddin aka kara zubarmin da ciki to fa ina cikin hatsari don zan iya rasa rayuwata. Wannan tasa a dole na rantse ba zan zubar ba. Gwaska kuwa ya ci alwashin duk radda na danganta cikina da shi sai ya kasheni a ranar. Wannan ce tasa ko sau daya ban taɓa gwada cewa cikinsa ne a jikina ba, fahimtar da Salma ta yi ciki gareni ta ce na tattara na kama wani gidan ta dinga biyamin haya har sai na haihu. Hakan kuwa aka yi, ta kamamin gida, Gwaska bai bar lallaɓowa muna aikata alfasha ba. Cikina nada wata tara na haifeki. Sai da kina shekara na yayeki na nemi mai tayani rainonki ina biyanta domin kuwa lokacin karuwanci ƙara buɗemin ya yi.

Bayan kisan Alhaji Haisam, Salma da Hayat suka yi kokarin kashe ni ta hanyar sanya Gwaska ya bankawa gidana wuta gudun tonuwar asirinsu a gaba, sun manta ni na kawo Gwaska wurinsu, shi ya ce na gaggauta fita a gidan na kuma dau dukkan abinda suke da muhimmanci wurina. Ta hanyarsa na samu tafiya Saudiya neman kudi da sunan na jima da mutuwa a wurin Salma da Hayat.  Kudina kuwa na aikin da nayi musu babu na labari wannan ne ya fusatani da su. A Saudiya muka ci gaba da rayuwa da ke har sai bayan dawowarmu Nijeriya na kara waiwayonsu da zummar daukar fansa wanda a nan kika sansu.

Amman ni Halima bani da wasu yan uwa na kaina, bansan asalina ba. Tsintacciyar mage ce. Ki yafemin Hanan.”

Halima ta ƙarashe tana kuka, ita kuwa Hanan ashar ta shiga lailayamata tana jijjiga karfe. Kira take.

“Halima kin cuceni! Meyasa Gwaska ya zama ubana? Kin cuceni Halima! Allah Ya isa ban yafe ba! Wayyo ni na shiga uku!”

Kuka take kamar zautacciya har sai da dan sanda ya dakamata tsawa gami da cewa ta fice kar ta ƙara zuwa. A gigice ta kwashi tarkacen wayoyi da mukullin motarta ta fice. A motar ta jima tana kuka da tunanin mafita, Halima ta dasamata bakin fentin da har ta mutu ba za ta iya kankareshi ba. Mutumin da hallakata ma sai ya yi, shi ake kira mahaifinta. Ba ta mance ranar da ya taɓa kokarin kai hannu jikinta da ya zo gidan a buge, Halima ce ta dakamasa tsawa gami da daukeshi da mari wanda ya wartsakar da shi. Ashe shiyasa take ba ta kariya daga sharrinsa? Ranar ji ta yi ta tsani karuwanci da duk wani mai aikatashi. Me ake da zina. Ta shafi cikinta, ji take inama mutuwa ta yi ta huta da wannan masifa. Haka itama za ta haifi ɗa ko ƴa ta dasamusu bakin ciki a rayuwa. Nadama da dana sani suka mamaye zuciyarta. Garin za ta bari gaba daya ta huta da bakin ciki. Wannan shi ne shawarar da ta yanke a karshe, can kuma ta girgiza kai ta share hawaye.

“Aure zan yi! Wallahi Sidi Oscar sai ka aureni! Ba zan ci gaba da rayuwa irin ta dabbobi ba.”

Tana fadin haka ta tashi motarta ta bar wurin.

*****

Ana gobe za’a shiga kotu aka samu Fu’ad ya dawo hayyacinsa. Banda godiya ga Allah ba abinda iyaye da kannensa ke yi. Dama abin ya zamemusu gobe da ashirin don kuwa a can Yobe, Engineer jiki ya rikice yana can rai a hannun Allah don sun samu labarin ya kamu da shanyewar ɓarin jiki.

Tun farfaɗowarsa yake kallonsu yana korafin don me aka bar Ummansa ba t cin abinci duk ta rame.

“Ai tunda ka tashi sai ka dinga bata a baki. Nan da kwana uku mu ganta ba ƙashin wuya.”

Mama ke maganar da zolaya, ta basu dariya har Adam wanda ya manta rabonsa da irinta.

Fu’ad ya gyara zama don hatta cikinsa da kan daure ji yake ya warware ba kaɗan ba.

“Lah Mama, nifa ba da ke nake ba.”

Maryam ta harareshi tana murmushi.

“Ka ji da shi. Yar uwa yanzu dai da alamu ke zamu yi jinya tunda ɗanki ya soma korafin muna barinki da yunwa.”

Murmushi Umma ta yi tana duban Fu’ad. Ya ɗagamata gira yana dariya kadan, ta harareshi. Ji ya yi dadi na ratsashi, uwa daban take.

“Please ka ce su sallameni. Nifa ras nake jina.”

Ya furta kamar mai raɗa yana lallamin Adam.

“Sai ka ƙara sati.”

Ya marairaice.

“Haba Bros, Haba Uncle Hashim! Ki duba kuga yanda  duk aka fasamin hannuwa. Jijiyoyina duk sun kumbura, please ku sa baki ayi discharging dina. Na gaji da gadonnan, jina nake kamar acikin makara wallahi.”

Ya basu dariya da tausayi gaba daya.

“Don ma ba ka ga yanda ka koɗe ka rame ba. Na rantse maka ko Helen ta ganka ba za ta aureka ba. Cewa za ta yi akai kasuwa.”

Sakin baki Fu’ad ya yi yana kallon Haidar yana yar dariya don ma ya rasa me zai ce, cuta dai, Haidar ya gama cutarsa tunda ya haɗashi da Helen, tsohuwar mayyarsa don kuwa ita ta mishi son mutuwa a zamansu a London. Yarinya ƙashi da rai.

“Allah Ya isa.” Shine kawai abin ya iya furtawa yana kallon Haidar. Haidar me zai yi ba dariya ba, wani nishaɗi yake ji na farfaɗowar amininnasa.

Sallamar Alhaji Dikko da amininsa Alhaji AbdulKarim shi ya dauki hankalinsu. Dan dakata suka yi su Umma suka gyara lulluɓi sannan suka shigo. Gaishesu suka yi, yayinda Malam da su Kawu suka miƙawa Alhaji Dikko hannu sannan amininsa.

“Kai Alhamdulillah, jiki dai ya samu. Sannu ɗana.”

Murmushi Fu’ad ya shiga yi yana shafar sumarsa wacce ta yi masifar yawa, ya gaishesu. Suka amsa.

“Wannan aminina ne, shima ya zo check up ne muka hadu shi ne ya ce bari ya ƙaraso a gaisa.”

Aka kara gaisawa. Hankalin Alhaji AbdulKarim na ga Umma wacce duk ta bi ta tsargu, ya dai daure ya barwa cikinsa don tsoro da fargabar ko matar aure ce ya fi ruɗashi. Ya yi musu fatan alheri sannan ya ɗebo kudin da baisan yawansu ba ya ajiye gaban gadon Fu’ad. Ana a’a, amman ina! Ya sa kai ya fice. Suka bi shi da kallo, da gani mutumin ba shi da hayaniya, kallo daya za ka mishi ka san cewar bafulatanin usuli ne ko daga yanayin lankwasawar harshensa wurin magana. 

Bayan fitarsa a daidai inda motocinsu suke Alhaji AbdulKarim ya dubi Alhaji Dikko.

“Ni kuwa Alhaji, wannan matar dake gefen marar lafiyar, ita wace ce?”

Cike da tausayi Alhaji Dikko ya ba shi labarin su Fu’ad a gajarce. Ya dora da fadin.

“Yanzu haka zancen da nake maka, zaman kotu ake akan case din mahaifinsu. Abin dai akwai tausayi da ban mamaki. Bilkisu da kake gani a yanda naji labari, ba karamin hakuri ta yi da halayyar tsohon mijinta ba da matarsa.”

Tausayi, so da kauna suka mamaye zuciyar Alhaji AbdulKarim lokaci guda. Bai ce komai ba sai addu’a mai kyau akan Allah Ya musu sauyi sannan suka rabu ya nufi motarsa. A ƙasan ran Alhaji Dikko, fata yake abinda ya shinshino ya zama gaskiya.  Ya san waye Alhaji AbdulKarim, namiji har namiji mai dakakkiyar zuciya. Sai dai tun rasuwar matarsa, ya yi aure sai biyu yana hakura da auren adalilin ɗansa tilo mai shekaru goma sha uku kacal a duniya. Duk matar da ya aura sai ya ga burinta ta hallaka dansa saboda abin duniya wannan ta sanya ya hakura da auren ya jingine zuwa lokacin da ɗansa zai ƙara hankali. Mutum mai gudun zuciya da duniyar gaba daya, yana da hakuri ba ya son hayaniyar mata ko kaɗan.

“Shakka babu Bilkisu za ki dace da miji.” Alhaji Dikko ya furta a fili yana murmushi. Shi dai direbansa bai ce komai ba ya ci gaba da jan mota.

RUMFAR KARA..BA ABIN DOGARO BA.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 39Rumfar Kara 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×