Kwai Ya Fashe
Sauraronsa suke yana kora jawabi, daga masu kuka sai masu salati. Umma na gefe kanta a kasa, itama banda kukan ba abinda take yi. Adam kuwa tunda ya sunkuyar da kansa bai ƙara ɗagowa ba, wani sanyi yake ji a kasan ransa, yau yana ji a ransa Allah ne Ya kar6i adduarsa. Ko ba komai ya kuɓuta daga saɓawa mahaifiyarsa ta hanyar fallasa rayuwar gidan aurenta ga kowa, sai gashinan Allah gwanin hikima don kanta ta furtawa Hashim.
"Ya isa haka, ya isa." Muryar Malam Kabiru ta katsewa Hashim hanzari ganin yanda yake. . .