Skip to content
Part 8 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Kwai Ya Fashe

Sauraronsa suke yana kora jawabi, daga masu kuka sai masu salati. Umma na gefe kanta a kasa, itama banda kukan ba abinda take yi. Adam kuwa tunda ya sunkuyar da kansa bai ƙara ɗagowa ba, wani sanyi yake ji a kasan ransa, yau yana ji a ransa Allah ne Ya kar6i adduarsa. Ko ba komai ya kuɓuta daga saɓawa mahaifiyarsa ta hanyar fallasa rayuwar gidan aurenta ga kowa, sai gashinan Allah gwanin hikima don kanta ta furtawa Hashim.

“Ya isa haka, ya isa.” Muryar Malam Kabiru ta katsewa Hashim hanzari ganin yanda yake kausasa magana ga dukkan alamu cikin fushi yake. Ya dubi sauran jama’ar falon.

“Ku bamu wuri zamu yi magana da Bilkisu.” Dukkansu suka miƙe, Malam ya dakatar da Hashim.  Bayan fitarsu, Malam ya dubi Bilkisu fuskarsa na nuni da tsantsar damuwa.

“Mai gado, yayanki bai ta6a yimin karya ba, bana fatan ace ya yimin wataran. Sai dai Mai gado bansan dalilin da a yau nake jin na kasa gaskata zantukan da ya yi game da rayuwarki da Hayatu ba. Ka yi hakuri Hashimu, sai dai ina son ji daga gareta kafin yanke hukunci.”

Hashim ya gyada kai kawai domin radadin da yake ji a kirjinsa ba zai bar shi ya tofa uffan ba. Tiryan-tiryan ta koro jawabi har ma da wanda Hashim bai san da shi ba ta manta ta faɗi a baya.

Malam Kabiru ya maimaita salati sau uku, sannan ya dubi Hashim.

“Dauki waya ka yimin kiran Hayatu, ban ce ka yi magana ba, ni za ka miƙowa wayar.”

Ba musu ya dauki wayar Malam  ya kira 

Alokacin Hayat na zaune a ofishinsa na asibiti yana duba marar lafiya. Yana kai su Salma gida ya zo.

Ganin sunan “Uban Billy” ya fito a saman screen din wayarsa ya sanyashi jan guntun tsaki, yasan bai wuce don a gaisa ba. Har a ransa bai kawo Bilkisu za ta tona mishi asiri ba, yana da wannan tabbacin. Da ace za ta yi, da tun a shekarun da suka gabata da tuni ta aiwatar. To yanzun me zai sa ta yi?

Bai mantawa tun fitarsa daga gidan Bilkisu bai ƙara komawa ba, gidan Salma ya yi kwanciyarsa, da sassafe ya fice asibiti. Karfe biyu na yi ya wuce Airport tare da direba ya dauki Salma zuwa gida.

Yana kallon wayar na ƙara bai ko motsa ba har sai da ya sallami dattijon da yake dubawa. Kamar kada ya kira sai kuma ya tuna yanda Malam Kabiru ke mutuntashi.

Har Hashim ya ƙara daukar zafi, bai kai ga magana ba kiran Hayat ya shigo. Hannu Malam ya miƙa.

“Ban ce ka dauka ba, latsa ka bani nan na mishi magana.”

Hashim bai so hakan ba, sai dai dole ya hakura ya miƙa wayar. Gaisuwar mutunci suka yi kamar yanda aka saba. Ya kara da faɗin.

“Ya wajen su Mai gado da yara?”

Da ƴar dariya ya amsa.

“Suna nan lafiya ƙalau, na baro su a gida ma.”

Malam Kabiru ya ji wani ɓacin rai, ya daure ya ce.

“To madallah, a gaishesu.”

Daga nan ya katse kiran, ya dubi Bilkisu.

“Kar ki ta6a dana sanin rayuwarki ta baya. Ki sa a ranki wannan kaddararki ce. Ki kuma godewa Allah da Ya azurtaki da yara masu albarka wanda su ke gudun zuciyarki da abinda zai ɓata ranki. Hakika kin yi ibada Bilkisu, shi hakuri kamar taki ne a gona, don haka kada ki damu. Hayatu ya zalunci kansa, ya kuma ci amanar zumunci. Muna mishi fatan shiriya, zan je da kaina na samu ɗan uwan nawa mu yi magana ta fahimta. Kafin ya ji a wurin wani, gwara ya ji a wurina. Allah Ya yi miki albarka, Ya yi miki sauyi nagari.”

Umma ta share hawayenta.

“Ameen Baba, na gode.”  Ya ɗan yi shiru yana nazari, yau da ace Malaminsa kuma abokinsa na nan, da babu wani wuri da zai je neman shawara sai a wurinsa. Zuciyarsa har lokacin ba dadi, dakyar ya iya miƙewa ya ɗauro alwala ya fice masallaci ganin la’asar na nufowa.

*****

Tsalle suka dinga yi a ɗakin har sai da Maryam ta dakatar da su.

“To sarakan shiririta, ai ba tsallen za ku tsaya yi ba, ku je ku yiwa Hajiyar godiya.”

Da dariya Humaira ta amsa.

“To Mama mu gwada?”

“Um um, a je a dawo tukunna.”

Suka dunguma zuwa falon Hajiyar. Yanzun ma tare suke da Inno su na maida zance, muddin Inno ta zo to fa ba sa rabuwa. Ganin yaran ya dauki hankalinta ta maida kansu fuska a sake.

“Kai, yan matannan nawa da kyau su ke tubarakAllah, wannan idan kun saka kayan ya za’a ganku?” Suka sunkuyar da kai alamun kunya su na dariya ƙasa-ƙasa. Sai da suka isa dab da ita sannan suka  russuna su na godiya. Ta murmusa.

“Ba komai, Allah Ya yi muku albarka.”

Inno ta amsa da Amin sannan suka koma ciki. Hajiya Hafsatu ta dubi Inno.

“Ni kuwa Fatima, haka za ku ci gaba da zama ba tare da kun taimakawa Maryam neman ƴan uwanta ba?”

Inno cike da jimami ta amsa.

“Ya zamu yi toh? Ta ina zamu soma nema Hafsatu? Matar da ta kasa tuna komai game da rayuwarta? Ki fadamin ta yaya za’a taimakamata? Ina jin ciwo wallahi duk sadda na ga yanda shekaru suke ja Maryam na zaune ita ba aure ba ita kuma ba dangi. Kowane bawa dai da kaddararsa.” Sai muryar Inno ta soma rawa adalilin tuno nata yan uwan da ta yi. Tausayinta ya kama Hajiya Hafsatu.

“Hakane, sai hakuri da kuma addu’a. Da ace ko sunan garinsu ta tuna, da komai zai zo da sauki. Allah Ya yayemata wannan duhun, Ya kawo mafita da gaggawa.”

Inno ta amsa da ameen.

“Kuna leƙawa Dambatta? Ko za’a samu wani labarin?”

Inno ta yamutse fuska kadan cike da  damuwa.

“Zumuncin yanzu ne ya lalace Hafsatu, ba irin na baya ba. Da ace ta mutanen za ka duba, da ba za ka yi shi ba sai dai kana duba ga Allah wanda Ya umarci a yi din. Nakan leƙa don ko sallar da ta wuce a can na yi. Labarin su Malam babu, ni ban san ma me zan kira wannan lamari ba. Abin dai akwai ɗaure kai. Ɓatan mutane ba wuya, rai kuma har kusan biyar?”

“Ba abin mamaki a ikon Allah tunda bamu san me ya faru ba, sai dai a duk inda su ke muna musu fatan kasancewa a hannu nagari. Allah Ya bayyanamana su da gaggawa.”

“Ameen ameen.”

Daga nan su ka ci gaba da lissafe-lissafensu na biki.

*****

“Look Haidar, ya kamata ka hakura yanda na dawo kaima ka dawo. Ka sani, ba zan ji dadin zaman wannan garin ba idan babu kai.”

Daga wayar Haidar ke kallonsa yana dariya, kasancewar videocall suke. Ya kai baki ya sumbaci farar baturiyar da ke a gefensa sannan ya bada amsa.

“Kar ka damu, ina nan zuwa. Ai dole a zo a dan bada wuta. Zan samo mana fine babies da za’a  shana da su kamar irin su Sexy Angela” Ya ƙarashe yana kara rungumo budurwar jikinsa ita kuwa kusan ma rabin hankalinta yana kan Fu’ad tana yar dariya.

Fu’ad ya ja tsaki ya katse kiran gami da yin wurgi da shi. Miƙewa ya yi daga saman gadon ya soma rage kayan jikinsa, idan bai ɓata a lissafi ba wanka na biyar kenan zai yi daga zuwansu garin har zuwa wannan lokacin da agogo ya nuna karfe takwas na dare. Bayan ya fito ya ɓata lokaci wurin shafe-shafen turarukansa, ya jima yana abu ɗaya kamar mace sannan ya fiddo rigarsa body hug fara ƙal ya sanya da dogon wanda baƙi. Fitowa ya yi bayan ya dauki wayoyinsa. Kai tsaye sashin mahaifiyarsa ya nufa. Babu ko sallama ya bankaɗa labule ya shiga, ta dubeshi a dan tsorace sannan ta sauke ajiyar zuciya.

“Kai my son, babu ko sallama?”

Ya ji abin banbarakwai, ya dan yi turus kafin ya yi yar dariyar shaƙiyanci.

“Sallama kuma? Ba ki koyamin ba ai.” Ya ƙarashe yana mai yamutse fuska.

“Look, ba wannan ne ya kawo ni ba, mukullin mota za ki ban da kudin ƙasarku. Zan dan fita.”

Har lokacin ba ta bar murmushi ba. Tana masifar son ɗan nata wannan yasa duk abinda ya yi maimakon ma ya bata haushi burgeta ya ke.

“Kaga Daddy dinka ya fita da ɗaya.”

“Damn it! Kar ki kara haɗani da wancan mijinnaki! Na roke ki akan ki bari bana so! He is not my Father, so please.” Ya harɗe hannunsa alamar roƙo.

Ya kara da fadin.

“Besides, ina son zuwa wurin paternal grandies dina.”

Miƙewa tayi irin wanda ba ta shirya ba. Mutumin da ko gaisawa da danginta ba ya son to a waya balle ya kaunaci ganinsu shi ke iƙrarin zuwa gun maƙiyanta.

“Ba ka isa ba Fu’ad! Ba za ka je ba! Mutanen da ba su damu da kai ba! Ba za ka je ba!”

“Kuma kina tunanin za ki iya tsayar da ni?”

Ya yi wata dariya irin ta raina mishi hankali, ya ƙarasa ya kama hannunta suka zauna. Gira ya ɗan ɗaga.

“Mum, kar ki da a ranki akwai wanda ya isa ya juyamaki ɗanki ko ya raba ki da shi. Karya ne! Ba wanda ya isa, don haka ki kwantar da hankalinka. Ba’a isa a juyani ba, ba ma mace ba, hatta da namiji bai isa juya Fu’ad ba. Namiji daya ne ya isa ya lankwasa ni, and he’s no more. Daddyna, so kar ki damu, just give me the address zan je mu gaisa ne, ba cinyeni zasu yi ba ko? After all nasan Daddyna zai ji dadi ko baya raye.”

Ta yi shiru, kirjinta banda bugu ba abinda yake, ba ta kaunar abinda zai kara haɗata da dangin tsohon mijinta sai dai kuma ta tabbatar a yanda Fu’ad ya furta zai je to ba zai fasa ba don haka ta 6ullo da dabara.

“Amma kar ka manta su ma yan 9ja ne, ka tsani duk wani ɗan 9ja.”

“Ban ce miki har da dangin ubana ba. Da dai dangin mijinki ne zan iya ce miki EH da karfina ma. Na tsani mijinki da ma duk wanda ya ra6eshi. Da ma duk wani baƙon fuska musamman waƴannan villagers naku.”

Miƙewa tsaye ya yi.

“Kina ɓatan lokaci, bani abinda na buƙata zan je na duba naga me zan samu.”

Ta mike jiki a sanyaye, har lokacin ba ta dawo daidai ba, nan da nan ta kudurce yiwa abin tufka ta hanyar kaiwa ga Bokanta. Nan da nan ta saki fuska ta sauke ajiyar zuciya, ranta ya yi haske. Ko ba komai ta tuna boka ta samu salama. (Waiyazubillah).

Ta mikamishi bandir din dubu daya har biyu sai mukullin sabuwar motar da Hayat ya siyamata. Babu ko na gode ya fice daga gidan.

Haidar ya kira a waya kasancewar ya fi shi sanin kan gari, yana da friends ƴan Kano hakanan yana hira sosai da yan uwansa na Kano. Shi ya fadamasa sunan wurin da ya bukata, ya yi amfani da location din wayarsa ya yi tracking area, a hankali ya dinga bi yana jan tsaki saboda irin lalacewar titunan garin har ya isa.

“Alexandra Club.” Shi ne abinda ya gani ɓaro-ɓaro a jikin signboard dinsu.

“Ba laifi.” Ya furta da ɗan murmushi, ba komai ya sanyashi ba sai ganin ƴanmata kusan ma tsira hakanan da alamun wayewar kai. Bai yi zaton akwai su haka ba. Tun kafin ya kai ga bude motar idanun ƴanmatan ke rawa a kan motar. Sai juye-juye suke su na jira su ga mace ko namiji ne zasu fito. Koma waye cikinsu, akwai kalarsu. (Allah Ya shirya).

Ganin haka ya zaro dubunnan kudi, yana fitowa suka yi wurin, bai ko kallesu ba balle ya tankawa masu Hi, har ya rufe motar ya yi gaba ya tsaya ba tare da ya shiga ciki ba. Sai a sannan ya watsa kudin sama, nan da nan suka hau rawar kafa suna cafka. Hankalinsa ya kai ga wata da ke gefe, sanye take da matsassun riga da wando. Rigar iyakarta cibi, ta jingina da mota tana zuƙar karan sigari, kallonshi kawai take ba ta ko damu da kudin da ke watse ana kwasa ba. Fara ce ƙal babu ko ɗigo, buzuwa ce. Gashinta tufke ya zuba a gadon bayanta. Dirinta da komai ya yi mishi, bai san sadda ya karasa gareta ba, kafin ya kai ga magana ta yar da karan sigarin ta sanya hannu saman kafadarsa. Daidai saitin kunnensa ta furta.

“Hanan.” Ya fahimci sunanta ta faɗamishi, ba wannan yake muradi ba, don haka ya bata sumba a wuya ya dubeta.

“Hope ba ta kowa ba ce?”

Ta yi murmushi gami da ɗan goga hancinta saman  nashi, nan ya kara sumewa ya tabbatar da ya zo hannu. Shakka babu kalar wacce yake nema ce. Da gira ta ba shi amsa gami da kashe ido. Murmushi ya yi gami da sakinta ya nufi motarsa. Sai da ya zauna ya sannan ya zuge gilas yana dubanta. Ta dubi kawarta da ke gefe tana jin takaici da kishin ba ita ce da wannan handsome din ba.

“Sai mun hade.” Daga haka ta soma tafiya cikin takun da take hargitsa zuƙatan maza masu sha’awar irin rayuwarta.

Tana shiga ya dubeta.

“Kin iya driving?” Da dan mamaki ta amsa da eh. Ya fito ya zagaya ya dawo bangarenta.

“Matsa can.”  Ta matsa mazaunin da ya bari shi kuwa ya shige nata ya rufe.

“Hotel mafi kyau a garin za ki kaimu.” Ta yi murmushi ta tashi motar suka fice suka bar ƴanmatan wurin da bin ƙurar motar da ido, masu  hassada da kushe nayi yayinda masu santin dubunnan da suka tsinta su ma su na nasu.

Bristol Hotel, nan ta nufa da su. Sai da suka shiga ta yi parking, sannan ta shafi gefen fuskarsa. Ya ci gaba da bin ta da kallo tun daga sama har ƙasa da idanunsa wadanda tuni suka rage girma.

Ranar Hanan ba irin wasan da bai yi da ita ba, sai da ya sanya ƴar roba (condom) sannan ya shigeta. Ranar ta san ta haɗu da namiji har namiji kalar wanda take so wanda baya gajiya kamarta. Sun jima cikin saɓon Allah a karshe suka hakura suka yi bacci. Wayoyinsa gaba ɗaya kashesu ya yi domin ba ya bukatar takura sanin halin Mummynsa yanzu sai ta tada hankalinsa akan ya dawo.

*****

Hannunsa har rawa yake saboda ɓacin rai. Ya kar6i wayar. Saukar muryar ɗan nasa a dodon kunnuwansa ya haifar mishi da wani raɗaɗi a kirji. Yau ɗaya ya kasa amsa sallama. Ya zarce ga batunsa.

“Duk yanda za’ayi. Ka zo gobe ina nemanka.”

Bai saurari amsarsa ba ya kashe wayar gaba ɗaya gami da share gumin2 da ya zubo mishi adaidai lokacin da hawaye ya taho, ya fidda gilashin idonsa ya share gami da duban ɗan uwansa.

“Mai yiwuwa bakin cikin da na jefa iyayenmu ciki a baya nake gani yanzu akan ɗana.”

Malam Kabiru ya dubi ɗan uwannasa da tausayawa ya girgiza kai.

“A’a Alhaji, ka daina faɗin haka. Ka yarda cewa dama rubutacce ne daga Allah. Hakan sai ya kasance.”

Alhaji Ibrahim ya share fuska.

“Mai yiwuwa fitinar da nayi a waje ke shafar ɗa..”

“Haba Alhaji, ka daina furta irin wadannan kalaman marasa dadin ji. Ashe ba ka yarda komai ya yi zafi maganinsa Allah ba?”

Alhaji Ibrahim ya yi shiru, sosai Malam Kabiru ya yi mishi nasiha mai ratsa jiki wanda a karshe ya hakura ya rungumi ƙaddara. Sai dai idonsa idon ɗansa Hayat, sai ya dau mataki mummuna a kansa.

*****

Hayat ya shiga juya waya yana tunanin irin wannan kira na gaggawa da mahaifinsa ke mishi. Wani abu ya fado ranshi, da sauri ya dau waya ya yi kiran Maigadi. Bayan ya dauka ya jefamasa tambaya

“Ina Bilkisu?”

Tambayar ba ta wani ba Maigadin mamaki ba, shekarunsa sama da ashirin a gidan, ba abinda bai sani ba. Shi tafiyar Bilkisun ma dadi ta mishi. Ya jima yana tausayamata.

“Ai Yallaɓai yau kwanakin Madam uku bata gidannan. Tun zuwan wani dan uwanta daga Misra suka wuce Yobe.”

A firgice ya mike tsaye gami da dakawa Maigadin tsawa.

“Kai Danliti! Mene amfanin zamanka a gidana har haka ta faru ba ka fadamin ba?”

Danliti ya ji rainin hankali, miji ke tambayar Maigadi matarsa. Ya hau ban hakuri, Hayat ya yi jifa da wayar gami da dafe kirjinsa da ke bugu da sauri-sauri. Ya tabbatar yau karyarsa ce ta ƙare! Bilkisu ta shayar da shi mamakin da bai zata ba.

“Za ki dana sanin abinda ki kai gareni Bilki!” Ya furta a kausashe sannan ya dau wayarsa ya fice daga ofishin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 7Rumfar Kara 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×