Abba yana gama fadin haka shi da Anti suka tashi suka hau sama. Ya zama daga ni sai Ya Omar don Maryam Jamila ma ta sauka daga jiki na ta bi bayan Anti, daga ni har shi kan mu na sunkuye don ji nayi kamar Abba ya dora min dutsen Uhudu a kai na, ya daddaure ni da kalaman sa.
Umar kuwa tunanin sa daban ne da nawa wanda daga shi sai Ubangijin sa suka sani. Ba yau ya fara jin na ce ina son wani daban ba shi ba, karewa ma ya riga kowa ji tun ina fifteen years. . .