Ummati na kishingide a falonta tayi shimfidar siririyar katifar da take hutawa a kai, a gefe kwarya ce cike da kindirmo mai sanyi da radio a kunne tana saurare. Ko sallamar dana yi mata bata ji ba kasancewar murya ta ta dakushe iyakar dakushewa sabida yunwa da jigata. Sai gani na tayi a gabanta wurjanjan da ni.
Tunda na zube a gabanta na shide na wasu mintoci sabida galabaita da yunwa, salati da sallallamin da Ummati ke yi hade da hamdala shi ya saka ni kara lumshe ido na.
Ina ji tana shafa min ruwa a fuska kafin ta dago. . .