Skip to content
Part 16 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Ummati na kishingide a falonta tayi shimfidar siririyar katifar da take hutawa a kai, a gefe kwarya ce cike da kindirmo mai sanyi da radio a kunne tana saurare. Ko sallamar dana yi mata bata ji ba kasancewar murya ta ta dakushe iyakar dakushewa sabida yunwa da jigata. Sai gani na tayi a gabanta wurjanjan da ni.

Tunda na zube a gabanta na shide na wasu mintoci sabida galabaita da yunwa, salati da sallallamin da Ummati ke yi hade da hamdala shi ya saka ni kara lumshe ido na.

Ina ji tana shafa min ruwa a fuska kafin ta dago ni ta rike a jikin ta ta kafa min kofin danyar madara a baki. Kulawa iri – iri Ummati ta shiga yimin saida ta tabbatar na dawo hayyaci na. Ba jimawa kuma sai barci a gadon Ummati. Barcin da ba ni na farka ba sai safiyar washegari.

A daren Ummati tayi waya da Abba ta gaya masa gani na zo mata hajaran majaran ko lafiya,  budar bakin Abba sai cewa yayi “Ummati sallameta ta kara gaba, tunda ta yi sanadin salwantar min da Umar bata da sauran amfani a gabana itama”. Ummati na iya jin irin numfarfashin da Abba ke yi domin a lokacin yana ta neman Umar sama da kasa cikin garin Abuja da wajen ta, ya kuma yi wa Wasila iyaka da magana ta yayi mata togaciya da igiyar auren ta don haka Wasila ta rasa abinda ya kamata ta yi tun bayan fita ta.

Daga baya ne Baba dattijo ya kira ta a waya ya shaida mata cewa ya kai ni ya sakani a motar Numan ta yi min addu’ar sauka lafiya. A lokacin ne ta dan samu nutsuwa har ta so bugawa Ummati waya, amma data tuna gargadin Abba dole ta bari, ta koma addu’ar Allah ya kai ni lafiya.

Ummati ta ce “ban gane ta zama silar salwantar da Faruku ba” Abba ya ce Ummati doguwar magana ce da bazata yiwu ta waya ba”. Tace “to lallai-lallai gobe kuzo kai da Wasila ina neman ku”.

Sai dare na fara murmurewa, tambayar duniya Ummati ta yi min kan me ya hada ni da Abba ban ce komai ba. Ta tambayeni Ya Faruk da yadda aka yi suka barni na taho nikadai haka nan ma ban tsinka mata ba sai goge hawaye da nake yi lokaci-lokaci don nasan duk wannan kulawar data ke bani itama in taji abinda na aikata kuma na bijirema auren Omar sannan ya bar gida sabida ni, zallar kiyayya zata koma watakila har sai ta fi ta Abba.

A haka muka kwana nida Ummati cikin dare ina kallon ta tana ta sallah tana addu’a kan Allah ya kare mata zuri’a ya albarkace su ya cire rabon shaidan daga zukatan mu, don ta fahimci al’amarin duk da ya rabo ni da Abba ba mai dadin ji bane, tunda yau har Abba ke fadin itama ta kore ni kamar yadda ya kore ni.

Abba da Anti basu samu isowa Mambila ba sai bayan kwanaki biyu, lokacin har na ware damuwa ta yi min sauki. Na yarda kwanciyar hankali na shine in manta da shi, kamar yadda Omar ya fadawa Abba cikin wasikar sa,

“Ba kowanne mafarki ne ya ke zama reality ba.”

(Dreams are conceived, but not all dreams are born alive).

                                                      -Zainab Alkali.

Abba da Anti Wasila shigowar dare suka yiwa Mambilla, tun da rana na gyara sashen nasu na share tsaf na saka turaren wuta don mukullin wajen Ummati yake ajiye.

Ummati bata samu zama da su ba sai a safiyar washegari don sun gaji. Na tashi zan fita in basu wuri amma sai tace “in zauna ayi komai tare da ni kada in juya mata magana daga baya.”

Abba ya kwashe komai ya gaya wa Ummati. Da ya zo wajen shan fiya-fiya Ummati ta dora hannayen ta biyu a kan ta tana salati da sallallami. Ta dube ni tace “amma kuwa da kin mutu kafira…..”. Sai ta saka kuka wiwi tana fadin wannan zamani ina zaka damu Boddo akan ki auri dan uwan ki da baki da ya shi a duniya kika zabi wannan hanyar, hakika kin yi kuskure, ina jiye miki yin sakacin da bazaki iya gyarawa ba a can gaba. Yanzu ina Omar din?”

Abba ya ce “ban sani ba Ummati, koda ya zo nan kiyi gaggawar gaya masa ya dawo gare ni na janye aura masa Boddo, ko ‘yar wa yake so sai inda karfina ya kare wajen aura masa. Nima na yi masa sakon hakan ta layin wayar sa na san duk ranar da ya bude zai gani.”

Anti Wasila bata iya magana saboda daga ni har Abban tausayi muke bata, kana iya ganin soyayyata a idanun sa wadda karfi da yaji so yake ya dakushe ta.

A daren Ummati tsinemin ne kawai bata yi ba, na rasa inda zan saka kaina, washegari kuwa tunda assubah Abba da Wasila suka koma suka barni dakin Ummati don Abba ya ce ba zan kara taka masa gida ba.

Na so tun a daren in je in bashi hakuri duk da ban san matakin dana daukarwa rayuwa ta ba, amma na san har yanzu ba wai ya huce bane, gara in dan kara bashi sarari zuwa ya huce. Tun kafin na tashi barci kuma suka dauki hanya sukayi tafiyar su.

Zama na a gidan Ummati wannan karon sam babu armashi a cikin sa kamar da. Ummati ta fita hanya ta bata shiga sha’ani na kuma bata saka ni aikin komai illa idan ta gama abinci ta zuba min a wulakance, bata hirar komai dani, tayi kamar bata san ina existing a cikin gidanta ba. In ta tuna wai Boddo akan kada ta auri Umar ta sha fiya – fiya duk sai ta ji na fita a ranta. In ta tuna Umar ya bar gida akan Boddo basu san halin da yake ciki ba itama sai ta ji ta tsane ni kamar yadda Abba ya tsane ni, banbancin Ummati da Abba ita mace ce akwai zuciyar Uwa a tare da ita.

Don haka bata hanani ci bata hanani sha, amma fa bata saka ni aiki sam kuma bata kula ni, harkokin ta kawai take yi cikin gidan ta, a mafi awancin lokuta kuma in ji ta tana yiwa Umar addu’a a fili, tana fadin duk inda yake Allah ya yi riko da hannayen sa. Allah ya saka shi a hannu na gari. Yasa fitarsa ta zamo masa silar daukaka a duniya.

Haka muka cigaba da zama ni da kakata Ummatin Mambila cikin gidan kowa bai kula kowa ko kuwa in ce zaman kowa tasa ta fishsheshi. Tace tunda abinda na zaba kenan to in yi ta zama in karata amma fa kada in sake in shiga harkar ta idan ba jikan ta ne ya dawo lafiyar Allah ba daga inda nayi masa kurciya na tura mata shi don kar na aure shi.

A haka na debi sati biyar a Mambila amma mu’amalar ta ki dadi tsakanin mu, ta ki komawa mai dadi kamar da, tsakani na da Ummati na yanzu sai kyara da hantara da tsana a fili.

Hakan yasa na fara ramewa daga tsaye. Kullum ina tambayar kaina ta ina zan ga Mr Radio ko na samu sanyi daga gare shi? In gaya masa halin da soyayyar sa ta jefa ni a ciki tsakani na da kowa nawa, ya raba ni da Abba ya raba  ni da Ummati ya raba ni da rabin jiki na Ya Faruq, yet shi din bai bayyana kansa ba har yanzu ya bar ni cikin tsammanin warabbuka.

Above all ya raba ni da farin ciki da walwalata ta Siyaman Abba ya shiga tsakanina da iyaye na, ya jefa ni a sabuwar rayuwa mara focus, don kuwa bansan ina rayuwata ke dosa ba a yanzu, tunda a dalilin sa har karatu na ya lalace daga karshen kammala shi.

“Dream Husband” dina isn’t this enough? You are not fair to me at all. Ka kyale ni haka ka sakar min zuciya ta sarara, tayi rayuwa cikin walwala irin ta kowa, I think is high time da zaka tausaya min ka bayyana hakanan. Rayuwa ta juya min baya, Ya Omar ya guje ni, kowa ya yanke alaqa da ni, iyaye na duka sun ki ni a kan ka!”

Nayi kuka mai yawa a wannan daren harna ba uku lada. A karshe na koma yin azumin tadawwi’i don bana iya cin abinci sam. Watarana na dauko Radio na wadda nayo guzurin ta daga gida na kunna don ta debe min kewa sai naji ana fadin sakamakon jarrabawar WAEC na wannan shekarar ya fito. Ummati na da talbijin amma sam bata kunnawa bansan me yasa ba, tafi sauraren radion jahar Taraba.

Muna zaune a falo na juya na ga gyangyadi take, daga baya kuma ta bingire a shimfidar donlop dinta tana barci, sai na lallaba na dauki wayar ta na fice can bayan dakin Anti Wasila na gidan.

Numbar Ya Umar na shiga gwadawa hawaye fal idanu na, a kwanakin nan kewar sa nake ba ‘yar kadan ba, rayuwar duka ta gundure ni ta zame mini boring, amma cikin rashin sa’a kwamfuta ke gayamin an ma daina amfani da layin.

Anya ban yi wa rayuwa SAKACIN da bazan iya gyarawa ba?

Na gwada kiran Anti Wasila ba jimawa wayar ta shiga ta kuma dauka. Jin muryar Anti kadai nayi duk raunin duniya ya ruftomin, na shiga kuka ba sassautawa.

Duk matsalar dana fada na tabbata ni na jawa kaina ba wani ba, ina cikin rayuwata mai dadi ta gata da soyayyar iyaye da dan uwa na kinkimowa kaina rigimar da bazata bulle da ni ba; Son gaibu, ko in ce “son wanda bai san ma ina yi ba.”

Duka wadannan abubuwan marasa dadi dana ke gamuwa dasu kuma bai rage ko kankani daga soyayyar da zuciyata ke masa ba.

Anti tace “komai ke kika jawowa kanki Siyama, mahaifin ki baya hada kaunarki data komai a duniya amma single biyayya kin kasa yi masa, shin menene laifin Omar a duniya da bazaki aure shi ba ki hutar da ranki daga takunkumin wahalar da kika jefa shi, ki hutar da mahaifin ki da dan uwanki walagigin da kika jefa su?”

Da sauri nace cikin kuka “Anti wallahi na tuba na bi Allah na bi Abba na, ki gaya masa na yi nadamar abinda nayi masa, zan kuma nemo masa Omar. Abinda ya same ni ki dauka cewa jarrabawa ta ce ki tayani rokon Allah ya kawomin karshen ta da sakamakon da zan iya dauka. Na kasa manta shi, na kasa daina son sa!”

Anti Wasila tace “duk ranar da kika daina zancen son mutumin nan na mafarkin ki, ranar ne Abba zai huce ya saurare ki, ranar da kika yarda zaki auri Omar akan radin kan ki, mahaifin ki yace zai manta da komai ki dawo gida ya nemo Omar duk inda yake yayi muku aure”

Ko yaushe ce wannan ranar? Ko yaushe zata zo? Ranar da zan manta da Mr. Radio? Me yasa bazasu gane cewa ba ni na sakawa kaina ba, ba ni na dorawa kaina iftila’in da na ke ciki a kan sa ba? Balle in cirewa kaina a sanda suke so?

Kanin Uba Makwafin Uba

Yammacin yau muka wayi gari da bakin Lagos, Young Abba (Baffa Adamu) da matar sa Anti Nasara. Sun kusa shekara basu zo Mambila ba sai wannan lokacin da suka zo yi wa Ummati sallama. Young Abba ya samu sauyin wajen aiki daga Lagos.

Sai yau ne Ummati ta dan kula ni, albarkacin autan ta Young Abba, a daki ta same ni ina barci ta zabga min duka a cinya. “Ki tashi ki dafawa auta da matar sa abinda zasu ci, ni tuwo nayi kuma sunce duk basa so.”

“Ummati Young Abba ne ya zo? Da Anti Nasara don Allah?” Ban jira amsar ta ba nayi waje da gudu kasancewar ina shiri da Young Abba sosai, sannan ya auri wayayya “Nasara Alkali” wadda ta maida dangin sa tamkar nata, sosai Anti Nasara ke ji da ni ta kan ce wai sabida ina kama da Young Abba din ta.

A falon Ummati na cimmasu, suna cikin shiga ta alfarma, ta karshen gayu, kai kace basu cikin damuwar da suke ciki ta rashin haihuwa har yanzu shekaru biyar da aure, fuskokin su banda annuri ba abinda suke fitarwa. Aunty Nasara ta bude min hannuwa na shige ta rungume ni, bansan ya akayi ba kawai naji na saka kuka kamar itace Wasila.

Young Abba ya zare bakin gilashin Prada a idanun sa ya dubeni sosai yace “Siyama bata da lafiya ne Ummati? Wannan rama haka?”

Ummati ta kyabe baki tace,

“Gata nan dai, itada Ubanta ne”

“Me ya faru?” Young Abba ya tambaya idanun sa na karakaina a kaina. “Idan ka ji abinda ta yi kaima sai ka daina jin tausayin ta, Azumi ta bata wayonta, ta kuma batawa kanta don da ta  mutu a irin mutuwar da ta so wa kanta da yanzu ta jima a wutar jahannama.”

“Ya Subhanallah” inji Young Abba da Nasara a tare,

“Me yayi zafi haka Ummati?”

“Fiya-fiya ta sha don ta mutu kada ta auri Umar. Da kyar aka ceto ran ta. Sakamakon haka yanzu zancen dana ke maka Faruku ya bar mu, ya bar gida ba mu san inda ya fada ba, a cewar sa don kada Baban ta yayi mata auren dole dashi ya zabi ya bar gida, mu kuwa me zamu yi wa Boddo mu huce banda mu sallamata ta yi rayuwar ta yadda take son ta?”

Young Abba sai jera “subhanallah” yake yi ba kakkautawa, yace “Boddo why? Kin san hukuncin suicide kuwa a wajen Ubangiji? Me yayi zafi a kan dan uwan ki?” Cikin kuka nace “Young Abba ba haka bane inada wanda nake so ne, sun kasa fahimta ta””ko kina da wanda kike so you shouldn’t attempt this, sabida da kin mutu me zaki ce wa Ubangiji?

Nima bana bayan a yi miki auren da bakya so, kuma bazan bari ba, amma maza-maza kiyi istigfari ga wannnan dingimmemen laifin da kika aikata.”

Nasara ta rungumo ni a jikin ta ganin yadda Young Abba ya bude min wuta sosai, ita sai take Magana cikin lallashi tana cewa “ina miki kallon mai hankali Boddon Omar, na san soyayya, i can relate with you amma ni kam kin ganni ko sigari bazan sha don na illata kaina akan namiji ba, ba zan kuma taba zabar sa akan rayuwa ta mai daraja ba balle iyayen da bani da kamar su.

Maza kiyi istigfari”.

A fili na soma jero “ASTAGHFIRULLAH” suna taya ni. Kalmar da tunda na sha fiya fiya ban ambata ba. Young Abba ya miko min hannun sa na kama a hankali ya mikar da ni ya ja ni gefen sa ya zaunar dani a kwibin sa, yace,

“Boddo do you want to stay with us? We don’t have a child yet, and you know ina son ki tun kina karama ko?”

An yi min relocation na wurin aiki na daga US Diplomatic Mission na garin Lagos zuwa babban reshen mu na birnin Washington D.C.

Boddo zaki bi mu? Kin ga sai ki shiga makaranta ki zauna da Antin ki Nasara ki manta da wata soyayya kin ji Boddo? You are still a baby, baki kai ga cimma komai a rayuwa ba, tunda baki cika shekaru ashirin ba har yanzu, wannan rayuwar da kika jefa kan ki ta kuncin soyayya ba taki bace, ba kuma inda zata kai ki, kuma ko wanene ya sace min zuciyar diya ranar da Allah ya nuna min shi zan saka kafar wando daya da shi tunda ya hanata karatu sai soyayya.”

Kunya sosai naji na rufe fuska da tafuka na yace “Ummati dama sallama muka zo miki nida Nasara, to ga karin ‘ya mun samu. Ku kwantar da hankalin ku Omar ba yaro bane ba zai kai kansa mahallaka ba. Ina tabbatar muku da cewa zai kula da kan sa a duk inda ya tafi. Kuma hukuncin da yayi ya burge ni, ya zabi farin cikin ‘yar uwar sa akan nasa, wannan ya nuna shi mai kaunar ta ne kuma insha Allahu a hankali Boddo zata so Omar zata aure shi don radin kanta.

Yanzu ki amince mana Ummati mu tafi tare da ita?”

Ummati ta kyabe baki ta ce “ni ina ruwana abinda ba’a kaina take zaune ba, ku dai je can Abujar ku fara gaya musu in mahaifinta ya barta ni meye nawa a ciki?

Na riga na sallama Boddo”

“Kiyi hakuri Ummati ki daina fadin haka a kanta.”

Inji Young Abba.

Ummati tace “zan yafe mata kadai ranar dana ga Faruku a gabana ya dawo gida yayi aure tunda ba ita ce autar mata ba.”

Haka kawai naji hankali na ya nutsu da bin Young Abba da maidakin sa Nasara zuwa US. Ina fatan hakan ya zamo min hanyar samun kwanciyar hankali na har abada. Yasa ya zamo silar da zan manta da “Dream Man” dina nima in hutawa rai na. Ya sa kafin in dawo gida Ya Omar ya riga ni dawowa. Ya kuma sa tafiyata ta zama hanyar manta komai da ya faru dani a baya.

(Bansan cewa wata kaddarar kana gudun ta tana bin ka bane. Ban san cewa mun riga mun saka kafar wando guda ni da kaddara ta ba. Kuma ita din tamkar Zanen Dutse take dan adam bai isa ya kankare ta ko ya tsallake ta ba).

<< Sakacin Waye? 15Sakacin Waye? 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.