Skip to content
Part 15 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Hakika akwai kwararru ba na wasa ba a Nizamiye, watakila kwarewar su ce ko kuma ince Astagfirullah Allah bai yi kwanaki na sun kare ba kawai shi ya cece ni. Amma an kashe kudi ba na wasa ba. Sannan daga farfadowa ta Abba ya bi ni da wadannan muggan maganganun. Wanda suka nuna ko kadan suicidal attack dina bai sauko da shi daga kan dokin kudirin sa ba.

Anti da Ya Omar suka dukufa roko, rokon Abba suke akan ya janye ya kyale ni in yaso duniya ta koya min hankali don wanda nake so din ma fa babu shi babu dalilin sa cikin duniya, imagination ne kawai nake yi.

“Ai kuwa zata mutu cikin hasashe” inji Abba. Sannan ya juya ga Omar da ke durkushe a gaban sa, ya ce “Omar ba ka son Boddo?”

A firgice Omar ya daga kai ya dubi Abba, Abba ya ce “amsa nake so eh ko a’ah ba wani dogon turanci ba”. Omar ya rasa inda zai kansa, ya ce “it does not matter Abba son da nake yi wa Boddo tun tana zanin goyo, tunda ita bata so na na yafe soyayyar dana ke mata, na sadaukar da tawa soyayyar don farin cikin ta da kasancewar ta cikin kwanciyar hankali.”

Abba yace “magana ta kare Omar bana son jin karin komai. Ka tashi mu tafi, gobe zamu wuce Mambila ko sun sallameta ko basu sallameta ba a daura muku aure.”

Omar zai sake magiya Abba ya daka masa tsawar data gigita shi. Ya kuma sa kai ya fice  a dakin asibitin. Dole Umar ya bi bayan sa don mukullin motar Abban na hannun sa. Yana fita yana waiwaye na. Gani yake kamar bazai dawo ya tadda ni a raye ba. A lokacin na lumshe idanuna bansan ya akayi ya akayi ba, kawai naji kwallar tausayin Umar sun wanke min fuska.

Ni da Anty muka kwana duk wani motsi da zan yi a kan idanun ta nake yin sa, don tsoron ta na ko zan sake wani attempt din na salwantar da rayuwa ta. Akwai maganganu fal a bakin Anti amma ta adana su zuwa in samu lafiya. Bakin cikin abinda na aikata ya hana duk wani masoyi na sukuni a zuciyar sa kuma babu wanda na baiwa tausayi banda Ya Umar. Ita Anti da zata samu dama so take ta dan yi min shegen duka ko zata huce tashin hankalin dana jefa ta.

Kwance kawai nake da ledar karin ruwa a jikin hannu na nida ita mun zama tamkar kurame ba mai ce da dan uwan sa uffan. Sai likitoci da ke ta shige da fice a kaina don tabbatar da aikin su na tafiya daidai.

A daren Umar Faruq ya kasa barci, ya tabbata in har ya wayi gari jibi a gidan mu Abba ba zai fasa abinda zai zo yana nadama ba, idan a da yana ganin abin na Boddo wasa ne yanzu ya tabbata Boddo da gaske bata son sa, koda za’a dora mata wuka a makoshi bazata zauna da shi ba, tunda har Boddo zata iya kashe kanta a kansa shi kuwa meye ribar sa a cikin auren ta?

Wane farin ciki ko alheri zai tsinta a cikin auren matar da ke kin sa har haka? Matar data zabi shan guba fiye da hada shimfida da shi. Tausayin Abban mu kadai ya ishe shi amma ya yanke hukuncin da yake ganin yafi masa alkhairi. Ya kuma fi zama maslaha ga Abba sannan ya fi zama kyautatawa a gare ni.

Washegari tunda safe likita ya sallame ni, Anty ta dauko ni muka taho gida jikina duka babu karfi. A falo muka cimma Abba yana saukowa daga matattakalar bene cikin shirin sa tsaf, da gani yayi shirin wucewa Mambila ne daurin aure na a gobe, don sun yi waya da Anti kafin mu taho ta gaya masa an sallame mu yace to yana jiran mu zamu wuce Gembu yanzu.

Don haka muna shigowa Anti ta wuce dakin ta don dauko kayanta, nima na wuce nawa dakin kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ina hawaye, ganin irin kallon tsanar da Abba ya jefa min yau.

Anti ta fito jaye da akwatin ta ta nufo daki na don ta hada min nawa kayan don ta san ba hadawa zan yi ba. Ita ta daukarmin komai ta hada cikin akwati sannan ta kama hannu na muka tadda Abba a falo, yana ta faman gwada layin Ya Omar ya ki shiga don shi zai ja mu a motar.

Bayan tun daren jiya sun gama magana ya kuma gaya masa karfe goma na safe zamu kama hanya ko an sallame ni ko ba’a sallame ni ba, in ya so in karasa mutuwa a hanya. Amma gashi yanzu ana gaya masa layin Omar a rufe yake bakidaya.

“Ban san ina Omar ya yi ba, ki duba min dakin sa ko bayan gida ya shiga” Abba yace da Anti. Anti Wasila tabi bayan Omar amma haka ta dawowa Abba tace bata gan shi ba, kuma bata ji motsi sa a bayan gida ba.

Abba da kan sa ya tafi BQ neman Umar Anti ta rufa masa baya. Babu inda basu duba ba a dakin ba Umar babu mai kama da shi. Sai a lokacin ne ma suka lura babu kayan sa na sanyawa a dakin sai daidaiku. Akan chest-drawer Anti ta hango wata takarda da rubutun Umar ya dora biro a kai alamar bai jima da ajiye ta ba. Kawai sai ta dauka, ganin sunan Abba a jiki baro-baro yasa ta mika masa cikin kidimewa.

-ABBAN MU

Samun mutum irin wanda zumunci ne silar shigar su aljannah tamkar namu Abban na tabbata zai yi wuya a wannan zamanin da muke ciki. Hakika baka nufin komai a kan mu ni da Boddo sai zumuncin da kake so ya dore a zuri’ar Ummati har ‘ya’ya da jikoki.

Amma Abba ba kowanne mafarki da buri ne da muke da shi yake iya zama reality ba. Wasu mafarkan a mafarkai suke tabbata musamman idan Ubangiji ya san cewa ba alkhairi bane a gare mu.

Hakika Abba ka yi duk iya kokarin ka na kulla wannan alkhairin a tare da mu, amma kaddara ta riga fata Boddo ta kamu da son wani na wanda take ganin zai hana ta yimin biyayyar aure, maimakon a nemi lahira da auren sai ya zame mata mujazar fadawa halaka. Na fahimci Boddo anan. Ba zan jagoranci ragamar wargajewar rayuwar ta ba sabida nawa farin cikin.

Ni dan ka Omar ina bayan kanwata Boddo, and i will always stand by her, zan taya ta neman wanda take so cikin duniya kuma bazan aure ta bisa tirsasawa ba.

A karshe ina baka hakuri Abban mu hakuri kan hakuri, na san na bata maka nima, akan hukuncin dana yanke. Bani da zabi ne Abba sai hakan don ka ki ka fahimce mu.

Na bar gida Abba zuwa duk inda kaddara zata kai ni sai idan ka janye maganar aure tsakanina da Boddo ne zan dawo bayan shekaru uku masu zuwa in Allah ya kai mu. Idan har lokacin baka janye ba Abba zan ci gaba da zama a duk inda kaddara zata kai ni. Ni na san tunda inada kai to ni ba maraya bane Abba, amma idan na auri Boddo zan koma maraya idan na rasa soyayyar ta.

Ina baka hakuri Abba, Abba Allah ya huci zuciyar ku. Ka yafewa Boddo ka kuma sa mata albarka ba don ni ba don Allah Abba.

Daga Yayan Boddo Umar Gidado.

Gumi, zufa, iri-iri suka ketowa Abba Dr. Mamman Gembu. Omar ya gudu! A dalilin Boddo bata son sa. Kuma yana ikirarin idan har Abba bai janye ba ko bayan shekara ukun da ya ambata ne ba zai dawo ba.

Jikin Abba yayi mugun sanyi, ya saki takardar a kasa kawai sai ya juyo, da ni muka yi ido biyu idanuna a bubbude domin na fuskanci abinda ke faruwa Ya Omar ya zabi ya bar gidan mu akan dai Abba ya tursasa ni ga auren sa, kafin na ankara Abba ya yo kaina, ya soma duka na ta ko’ina da hannaye da kafafun sa iri dukan na huce bacin rai. Anti ta sa kuka ta rufu a kaina ta ce “gara kayi mana dukan tare.

Yadda Omar ya ke Da a gare ka itama ‘yar ka ce mai ‘yanci. In shi maraya ne itama marainiya ce. Tana da damar ta auri wanda take so, tsaurin ka ne ya janyo komai, ka san Umar son da yakewa Boddo ba zai bari ya zabi nasa farin cikin akan nata ba.

Abba yace “to kuwa bazata zauna min a gida ba, yadda Omar ya bar gidannan itama sai ta bar shi, bazan haifi dan da ban isa in tankwara ba”.

Kuka nake ina baiwa Abba hakuri na kuma ce zan nemo masa Ya Omar, zan kuma aure shi koda bana son sa…

Wannan kalma ita ta kara tunzura ran Abba, yace “kada Allah yasa ki so shi, ki sani daga yau nima na janye maganar aure a tsakanin ku, kije ki auri duk wanda kikeso Boddo, amma ki tabbata kafin na dawo gidannan kin bar min gida na.”

“Kada ka yi wa ‘yar ka baki Mamman!”

Anti ta tunasar da Abba cikin yanayi na rauni, Abba ya ce “ban yi mata baki ba ai, amma na janye nawa kudurin, na janye nawa burin don in samu Da na ya dawo gare ni. Ya fiye min ita sau dubu, kuma lallai -lallai yanzunnan ta bar min gida na”.

Anti zata kara magana Abba ya rufe idanun sa ruf, ya ce da ita. “Idan kika kara kare Boddo a ido na, ko kika kara nema mata alfarma ko afuwa daga gare ni a bakin auren ki.”

Wannan magana ba Anti kadai ta firgita ba har da ni. Ina jin sanda fitsari ya kwace min daga tsayen dana ke. Abba ya nuna min kofa da dan alin sa yace “kama hanya ki bar min gida na”.

A yanayin dana ga idanun Abba sai naji tsoron sake furta wata kalma, na tabbata in yi masa abinda ya bukata daga gare ni shine kawai mafita ta a wannan lokacin. In yaso daga baya idan ya huce na dawo na bashi hakuri.

Ni kuka Anti kuka Jamila da Nadiya kuka haka na dau jakar kayan da Anti ta hada min na fito, babu ko sisi a jikina kuma bansan ina na nufa ba.

A bakin gate maigadin mu ya biyo ni ganin ina tafe da jaka ina kuka wiwi, ya ce “uwardaki na kada kije ko’ina bada yardar iyayen ki ba, babu wata albarka a cikin sabawa iyaye kuma babu kwanciyar hankali cikin bijirewa umarnin su”.

“Abba shi yace in tafi Baba Dattijo, biyayya na yi masa zan tafi”.

“To kada kije da nisa, nemi wani waje mara nisa cikin gidajen yan uwa ki fake zuwa gobe idan zuciyar sa tayi sanyi ki dawo ki bashi hakuri ki kuma bi duk umarin da yayi miki.”

Na yarda da maganar Baba Dattijo amma ina zani? In ba gidan su Anti ba sai ko gidan su Ko’oje, wannan kuwa matsala ce ta cikin gida da bata bukatar third party, gara kawai in wuce Gembu gun Ummati ko kashe ni zata yi itama tayi, ita kadai ce zata iya shawo min kan Abba. Duk da yakinin dana ke da shi na cewa bazata taba bin bayana ba itama.

“Ka taimaka min da kudin mota in tafi Mambila gun Ummati”,

Baba Dattijo ya sanya hannu a aljihun sa yana lalubawa yana cewa ” anyi sa’a jiya Abban ya bani albashi na, gashi duka ‘ya ta ki je kafin ya huce, ki kula da kan ki, nasan baki taba zuwa Gembu a motar haya ba, don haka muje in saka ki motar Numan.”

Shi ya daukar min akwatin ya tare mana drop wadda zata kai mu Jabi park, Baba Dattijo ya saka ni a motar Numan ya kuma gayawa direban ya saka ni a motar Jalingo in an je Numan. Sannan ya ce “daga Jalingo zaki hau motar Gembu amma ki nemi ko gidan mai unguwa ne ki kwana a Jalingo in yaso kiyi asubancin shiga motar Gembu.”

Nayi wa Baba Dattijo godiya kamar halshe na zai tsinke, kamar yawun baki na zai kafe. Sai yace “yar nan babu komai Ubanki mutumin kwarai ne babu abinda baya yi min nida iyali na tun da ya dauke ni aiki yake faranta min. Allah ya kai ku lafiya, Allah kuma ya huci zuciyar sa.”

Ya sayo kosai mai zafi da soyayyen dankalin hausa aka kumshe masa a leda da takarda ya miko min ta taga. Baba Dattijo bai bar wajen ba sai da ya ga tashin motar mu. Muna dagawa juna hannu hawaye sun ki tsayawa a idanu na.

“Yau ga abinda ka janyo min Dream Husband, yau ga inda soyayyar gaibun ka tayi da ni; kora daga Abba.”

Ji nayi na tsani kaina iyakar tsana, na tsani soyayyar da nake masa amma shi din, nayi nayi in tsane shi na kasa. Na dauki alhakin komai na daurawa kaina. Tunda shi bai san ina yi ba. Ba kuma shi yace in ki zabin Abba na ba.

Tafiya ta mika mana sosai muka naushi Arewa maso gabashin Najeriya.

Sai dare muka isa Numan, na rasa yadda zan yi ga gajiya ga yunwa, karo na farko dana shiga motar haya zuwa Gembu don ma dai direban da Baba Dattijo ya baiwa amanata yayi ta kulada ni har muka iso Numan. Kuma da muka sauka daga motar sa saida ya tabbata na samu wajen da zan kai zuwa wayewar gari wato gidan sarkin Tasha, na kwana a dakin matar gidan, washegari Asubah na yi nayi sallah na yi harama tasa aka rakani na koma tasha aka sanya ni motar Mambila.

Hankali na bai kwanta ba saida na fara jin sanyin yankinmu na Mambila a cikin jiki na, na hango tsaunin Mayo-Selbe, na tuna kuruciyata mai dadi a Mambila. Sai na ji rabin damuwata ya yaye ko ba komai watakila yadda na baro Abuja haka na baro duk wani memories dinsa a can.

Sai kuma na tuna ai al’amari na da shi ya fara ne tun a Mambila ba a Abujar na samo ba. Wanda ke nufin watakila da soyayyar sa aka haife ni.

Babbar damuwata Abba na yayi fushi dani ban san ranar da zai huce ba. Yaya Umar bani da haufi akan sa na san shi din namiji ne, wanda a ko’ina zai iya kula da kan sa kuma ba zai taba kai kan sa ga halaka ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 14Sakacin Waye? 16 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×