Skip to content
Part 14 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Nasara da Wasila ba inda basu shiga sun fita ba a kasuwannin garin Lagos suka hada lefe mai tsari, sannan kayan sakawa a gidan amarya. Kwanan Anti uku suka dawo. Ashe har da Ya Omar suka dawo gidan.

Bai nemeni ba sai ana daurin aure saura kwana biyar muka hadu a kitchen yana shan ruwa daga firji, ni nasan na rame sosai amma dana dubi Ya Omar sai naga ya fi ni ramewa, ga kasumba ya bari a fuskarsa wadda a baya bashi da ita. Ya kara zama cikakken namji.

A zuwan sa Lagos ma Young Abba ya yi masa tayin aiki da ofishin su, yace shi a’a a ofishin su Abba zai yi aiki sabida Abba ya kusa retire.

Kaina a kasa na shiga kitchen din nayi kamar ban gan shi ba, har zai fita sai ya dakata yace.        

“Boddo ko gaisuwa babu?”

Muryar sa kamar ta wanda ke fama da mura, na kasa kallon cikin idon sa don alkawarin da yayi min bai cika shi ba, ya ce zai lallashi Abba kada a yimin auren dole amma yayi hakan? Shirin angwancewa yake yi.

Da ya ga ba zan gaishe shin ba kamar yadda na saba sai yace “kada ki damu fa Boddo ni ba bakon zafi bane, it’s a promise bayan auren mu ba zan zo inda kike ba, I mean… I mean ba zamu hada shimfida ba don na fahimci damuwar ki kenan.

Zan yi hakuri zan jure har sai ranar da kika karbe ni as a husband don radin kan ki. Ranar ne zaki banbance da banbancin da ke tsakanin Aya da tsakuwa; soyyayyar Yaya da ta wani bare da kike underestimating dina a kan sa.

Zaki tabbatar soyayyar gaskiya ba a mafarki take gudana ba, a zahiri take; from theory to practice.

Na tabbata Dream Man din naki, bai fi ni komai ba, haka bai fi sauran maza mazantaka ba, watakila ma…..watakila ma…..ya kyabe baki kafin yayi kasa da murya kada wani ya ji abinda zaya ce, kamar cikin rada ya ce,

“watakila Boddo ko kwakkwarar sumba wannan (kissing) bai iya ba sai shegen tsayi kamar falwaya da bakar kalar sa dana fahimci sune abubuwan sa da ke rudar ki!”

Hannaye na biyu na saka na toshe kunnuwa na na fita daga madafin ina mamakin sa. A baya in wani yace min Ya Umar zai iya irin wannan maganar ba zan taba yarda ba. Sabida kallon wani kasurgumin shaihin malami nake masa.

A raina nayi murmushin tausayin sa, sabida ya gama amanna da ya same ni ya gama. Shi yasa bazai damu da abinda nake gudun auren sa a kan shi ba, tunda ya san ko ba dade ko bajima zai zama nasa ne.

“Ya Omar da muguwar rawa gwanda kin tashi. Zamu ga wa za’a kai gidan ka balle har ayi batun hada shimfida ko akasin ta. Bana yin magana don yaudarar kowa amma tunda an zo wannan gejin zan yanke hukuncin da zuciyata ta fi amincewa da shi.

Lokaci ya kure min da zan nemo ka Dream Husband, kamar komai ya kurace min muddin na bari aka daura min auren nan, suna maganar daurin aure nan da kwanaki uku. Omar ba zai taba saki na ba muddin igiyoyi na suka shiga hannun sa. Damuwa ta daya ce a ina zan nemo ka?”

Anti ta gama shiryawa tsaf, shirin tafiya Mambila a washegari, inda za’a fara gudanar da bikin mu yadda Al’adar garin Gembu ta tsara.

Na tabbatar muddin na saka kafa a Gembu, dakin Ummati aka shafa min lalle; aure na da Ya Omar ya gama tabbata, mai iya raba Omar Gidado Gembu da igiyar aure na kuwa sai dai mutuwa balle in yi fatan zan shiga ne in fito a sanda nake so, ko in Dream Husband ya bayyana kan sa, in bar Omar in koma masa, a halin yanzu kuwa bana bukatar auren kowa na fi so in bar duniyar bakidaya in huta da azabar soyayyar dana ke dandana, tunda bani da nasara a kan ta, da zai bayyana da ya bayyana haka kafin lokaci ya kure mana.

Da in ganni a gidan Ya Omar matsayin matar auren sa gara in bi bayan mahaifiya ta, ko na samu cikar buri na a aljannah, ko mayi aure da wanda nake so a wata duniyar ba wannann tamun wadda muke ciki ba, tunda ya ki bayyana a duniya har gashi za’a yimin auren dole a dalilin (SAKACI) NEGLIGENCE irin nasa.

“FIYA-FIYA TANA TSINKA HANJI IDAN TA SHIGA JIKIN DAN ADAM. DON HAKA UMMATI KADA KI KARA AJIYE FIYA FIYA A DAKI SABIDA YARAN MAKWABTA DA NAKI JIKOKIN KANANA DAKE SHIGOWA SUNA DABDALA A TSAKAR DAKIN KI.”

Na tuno wata magana data taba gudana tsakanin Anti da Ummati a zuwan da muka yi mata yawon Arba’in din Nadiya, Maryam Jamila ta dauko wata kwalba akan talbijin tana tambayar Ummati ko turaren Dan Duala ne a ciki? Ummatin ta ce “a’ah fiya – fiya ce maganin sauro guba ce, maza ajiye ki je ki wanke hannun ki.”

Abbana ya ce wai ko gawata ce a kai gidan Umar, kafin a wuce da ita makabarta, to watakila ya fada da bakin mala’iku ne. Domin furucin iyaye karbabbe ne shi yasa ake so a kowanne lokaci su dinga tauna kalaman su a kan ‘ya’yan su. Na zabi in sha fiya-fiya a kan dai na je zaman aure gidan wanda bana yiwa so na soyayya! 

(A wasu lokutan idan baka barwa Allah lamarin ka ba, idan ka zabi ya barka da dabarar ka sai ya barka din. Babban kuskure na ni Siyama, tunda na fara mafarkan nan da shi ban taba neman zabin Allah a kai ba, ban taba cewa idan soyayyar da nake yiwa wannan bawan Allah daidai ce da addini na, tarbiyya ta da lahira ta, kuma alkhairi ce a gare ni da addinin Allah, Allah ya sada ni da shi cikin hikima, buwaya, mulki da iyawar sa da tsarkin mulkin sa.

Ni na san tun farko da ace wannan addu’ar na dukufa ina yi tsahon shekarun nan dana fara mafarkansa, na tabbata da tuni na rabauta cikin zabin Allah. Amma a yanzu lamari na yana hannu na ne kacokam! Kuma shedan ya yi min kyakkyawar jagora yana gaya min rayuwa ba tare da shi da na kallafawa rai ba aikin banza ce, don ba zan taba jin dadin ta ba.

Na daga kwalbar fiya-fiya na rufe ido sannan na yi kalmar shahada, ban sani ba ko Allah zai karbi shahadar nan tawa? Tunda ni nayi nufin yin ta da hannu na bata Allah da Annabi bace? Ko kuma shan fiya fiya don gujewa auren dole daidai yake da kashe kai??? Gara in taimakawa Abba ya cika burin sa ya kai gawa ta dakin Ya Umar, sannan a zarce da ita makabarta.

Shi kuwa Dream Husband dina bazan taba yafe masa ba, duk ranar da ya gama yangar sa ya ga damar bayyana kan sa gare ni, ya samu labarin na gaji da jiran sa na kashe kaina a kan sa he will then take it for granted…. I  would love to see his reaction a lokacin da ya samu wannan labarin. Reaction din sa na samun labarin mutuwa ta a dalilin sa, shi zai nuna girman matsayi na a zuciyar sa….. shi zai bayyanawa mai karanta labari na cewa shima yana so na ko ni kadai nake koshin wahala a kan sa? Duk da 90% na zuciya ta na tabbatar min our hearts are jointly connected  internally by the creator….. Ba ni kadai nake wannan suffering din ba.

Na hango kaina Abba na binne ni yana kuka yana cewa da na sani na taimaka miki kin nemo shi Boddo, ba wanda ba zan iya nemowa a duniya ba idan na saka kaina, da na sani ban yi gaggawa ba wajen yanke hukuncin yi miki auren dole, da na sani ban ki bin shawarar likita ba da ya ce a tsahirta, da na sani Omar ya zabo duk macen da yake so da kan sa, in ya so na aura masa ko wacece koda zan rasa banten daurawa….Da na sani din da Abba zai yi a kan hukuncin da yayi wa rayuwata tana da yawa….

Amma me? Wani bangare mafi rinjaye na zuciya ta ya ki amincewa da hakan, cewa yake dani cikin amsa-kuwwa….

“Abba ba zai taba yin dana sani ba, don hukuncin sa bai sabawa Allah ba, ke ce zaki yi da kin sani, kece zaki dawwama cikin sa, kuma ki tabbata cikinsa daga nan har karshen rayuwar ki muddin kika aikata abinda zuciyar ki ke umartar ki a yanzu.”

Amma hakan bai sa ko kadan na fasa abinda nayi niyya ba, a ganina hanyar tsira daga auren dolen da Abbana zai min kawai kenan wanda zai zamo shinge/katanga ga tabbatuwar mafarkaina da wanda nake so. Da in rasa wadannan mafarkan nawa gara na rasa rayuwar dungurungum bakidayan ta. Love is real, kuma nawa baya karbar uzurin kowa face na samun wannan soyayyar gaibun dana ke so.

Na soma tittila ruwan fiya-fiya a baki na ina hango DREAM HUSBAND dina, yau kam tar-tar nake ganin sa cikin idanu na ba kamar kullum da a fizge kawai nake iya ganin sa ba; those beautiful eyelashes sun kwanta sosai a saman lumsassun idanun sa, that cool man’s pride da ke dimauta ni, wanda ya tafi ya zagaye habar sa ya kwanta lambam a kan kyakkyawar bakar fuskar sa sai sheki da salki gami da walkiya yake yi. Hakika Ubangijin halitta ya kyautata surar sa a cikin bakaken mutanen Africa, ya qawata min shi a zuciya da ruhi fiye da duk wani da namiji mai numfashi a duniya.

Gani nake kamar ya bude min hannuwa yana min murmushin da ya lotsa gefen kumatunsa guda daya yana jiran isowa ta. Na amince Allah ne ya hada mu ba don komai ba sai don mu rayu tare, rayuwa ta har abada amma a wata duniyar daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba!

Mai Rabon Ganin Badi

Acewar Hausawa ko ana ga uzuru ana ga Shaho sai ya gani. Allah ne ya kawo Wasila a daidai wannan lokacin, wanda yayi dai-dai da zuke kwalbar fiya-fiya da nayi, idan Allah ya ce kwanan dan adam bai kare ba to babu abinda zai kashe shi sai kudura da iradar Ubangiji.

Na yarda da hakan a yau a kaina domin tabbas na san na sha kwalbar fiya-fiya, daga nan sai shigowar Wasila da ihunta da na ji a kaina, bayan wannan ban kara tantance meke faruwa da ni a duniya ba.

Na bude ido ne na ganni akan gadon asibitin Nizamiye, inda anan file din duka ‘yan gidan mu yake, sauran abinda ya biyo baya mai ban tausayi ne domin kuwa Abba ba ta jinya ta da Wasila ke yi ya ke ba shi, bata tabbacin da likita ya bashi na nasha guba an samo ni da kyar da taimakon Ubangiji yake ba a’ah, ta shirin daurin aure na yake yi ko in mutu ko in yi rai.

Koda na farfado na yi ido hudu da Abba ban iya kara yi masa kallo na biyu ba, sabida yadda fuskar sa ta koma ta tsantsar bacin rai ban taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan halin ba. A gefe Wasila na share hawaye, Umar na gefenta ya kura min ido harde da hannayen sa a kirji, gabadaya yayi wani zuru-zuru kamar wanda ya mutu ya dawo. Ina jin bai taba gamuwa da tashin hankali da bacin rai a rayuwarvsa irin na wannnan lokacin ba.

Da Abba ya tabbatar na dawo cikin hayyaci na sai ya ja kujerar zaman ‘yan dubiya gaba na ya zauna. Ya kura min ido yace “Siyama! Anya Siyamar dana sani na kuma haifa tareda Asshe ce wannan ko kuma dai Nos din data karbi haifuwar ki ta musanya min tawa Siyamar da wani jinin daban? Ina mamaki!

Domin dai nawa sanin. Jinin malam Dalhatu Abdullahi Gembu ba zai taba aikata kisan kai ga kowa ba balle ga karan kan sa a bisa sani kuma, ba zai so ya zo duniya a banza ya koma a hofi ba. Haka ba zai so ya mutu kafiri ba. Akan wata kankanuwar bukata tasa ta duniya.

A matsayi na na uba bazan ce ban so kika kubuta ba, amma na so ki cika burin ki kije lahira ki dandana azabar wuta kona wuni daya ne sannan ki dawo, watakila zaki fi sanin cewa iyaye ba abin wasa bane. Kuma duk wanda ya zabi son zuciya yayi SAKACI dasu yana tareda dawwamammiyar nadama.

A karshe ina sanar dake cewa har yanzu ina nan akan baka na na cewa Omar na zaba miki, kuma jibin dana saka don daura muku aure ba zan fasa ba. Wannan karon sai ki sa wuka ki farke cikin ki don kifi mutuwa da sauri, a mika gawar ki gidan Omar kafin a wuce da ita makwanci…”

Abba ya fada cikin wani mashahurin bacin rai da ban taba gani a tare da shi ba. Daga bayan sa Ya Omar yayi gyaran murya cikin karaya ya soma rokon Abba “Abba don Allah…. na roke ka ka janye kudirin ka, ka bar Siyama ta nemo wanda take so ka aura mata.

Abba rayuwar Siyama cikin farin ciki ta fiye min auren ta. Abba tunda har Siyama zata iya iya yunkurin kashe kanta a kaina Abba na hakura da Siyama na haramtawa kaina ita. Ina rokon ka kaima kayi hakurin musulunci kada ka yi fushi da ita, ka bata dama ta auri zabinta, don Allah Abba”

Omar ya fada cikin despair da kuma karaya da al’amarina bakidaya.

Anti tace Abba tunda har Umar ya hakura kaima kayi hakuri. Rayuwar Siyama gaba take da komai don Allah Abban Siyama…” Anti ta fada cikin hawaye, don hakika ta shiga tashin hankali irin wanda bata taba shiga a rayuwar ta ba, da tazo ta same ni ina shan fiya-fiya kuma babu jimawa na bi kwalbar muka zube a kasa, kumfa na fita daga baki na.

Allah ne ya so Omar na falo a lokacin, da gudu ta fita tace “Siyama ta kashe kanta Omar, ta sha poison, ban san a ina ta samu ba.”

Irin zaburar da Omar yayi kamar ta fitar kibiya ya kuma daukoni a kafadar sa yasa a mota Anti ta shiga gaba basu zame ko’ina ba sai Nizamiye. An karbe ni a emergency likitoci suka rufu akaina don ceto raina. A lokacin ne Anti ta samu sukunin iya kiran Abba wanda bata san ina yayi ba a ranar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 13Sakacin Waye? 15 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×