Skip to content
Part 13 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

A hankali Anti ke jan motar kamar bata so mu isa gida, sai ta dauke kan motar ta yi wata hanyar daban, inda muka isa wani katafaren asibiti, ta dau jakarta tace in biyo ta, na gane asibiti ne na kwakwalwa daga karanta sunan. Wani bakin ciki ya tokare ni na ki fita, daga baya kawai sai na daura hannaye aka na saka mata kuka ina cewa “kema haukan zaki lankaya min?” Anti ta kidime, mutanen da ke wajen kuwa sun saba ganin iri na sai basu wani maida hankali a kan mu ba.

Waya naga Anti ta dauko tana yi daga can gefe sai ga wani likita mai kamala ya fito tare da ma’aikatan jinya biyu karfafa da su. Ma’aikatan suka ce salin alin ki bimu mu shiga ofishin likita, in kika yi gardama mu saka ki a ‘guard room’ mu kulle”. Ai jin haka na hadiye kuka na bakidayan sa ina kuma sakawa a raina gara fa in nutsu, idan gwajin su ya nuna lafiya ta kalau kowa zai shafa min lafiya.

Likita ya bude firjin sa ya dauko ‘fresh milk’ mai sanyi ya bude ya tsiyaya min a tambulan ya miko min da murmushi, bayan ya bani kujerar da ke fuskantar sa na zauna, Anti na tsaye can gefe. Sai na kasa tankwabe wannan kulawar tasa, ko babu komai shi babu kallon mahaukaciya tattare dani cikin idanun sa.

Dama a yunwace nake, na karba na shanye ya kara min na kuma shanyewa. Na lumshe ido nutsuwa ta ziyarce ni. Ya bani kujerar kusa da shi na zauna ina satar kallon Anti. Ya bude file yace

“Yaya sunan kanwar tawa?”

“Sunana Boddo” Na amsa a matukar gajarce. Fuska a gimtse. “Siyama dai ko? Meaning… Ramadan ko? Kyakkyawar yarinya dake haka ki ce sunan ki Boddo?” Sai ya bani dariyar data sa ni murmusawa, Anti ma ta murmusa cikin damuwa, tace masa Boddo yana nufin kyakkyawa, ni kuma nace “Aisha-Siyama sunana”. Likita yace “koda na ji.

Siyama Maman ki ta kawo ki a bisa zargin kin samu delusions, haka ne?””To ai ko na ce maka lafiya ta kalau ba lallai ka yarda ba, tunda an ce majority carries the vote”. Dr. Amir yayi murmushi yace “wani lokacin majority din suna taruwa su duka su zabi wrong action da zaki ga ya zo ya dame su bakidayan su, wadanda suka zabi kalilan sai kiga sune on the right path.

Don haka Aisha-Siyama saki jikin ki, i’m not among that majority na mutanen da ke miki kallon tabuwa, ina kan katanga ne ina kallon yadda rikicin zaben yake gudana, in an gama a matsayi na na likitan kwakwalwa, sai nayi alkalanci na gaskiya a tsakanin ki da su.”

Wani murmushi ya subuce min. Na ji kamar in gamsu da abunda ya ce mun. Wata zuciyar na cewa wayo ne kawai da hikima irin na likitoci in suna son sanin gaskiyar abu. Dr. Amir yace.

“Aisha-Siyama menene damuwar ki har kike zana Radio akan NECO answersheet? Answersheet din ma ta mathematics?”

“Duk abinda kayyi tunani a kaina, daidai ne”

Na baiwa Dr. Amir amsa a gajarce. Don na daina kare kaina a kan haukan da suka riga suka lankaya min, saidai in karbi kowanne magani da za’a bani, amma ba zan sha ya yi min illa ba. Zubarwa zan yi.

Duk dabarar likita naki cewa komai, a karshe ma sai na fashe masa da kuka nace “Dr. Na yarda da duk abinda suke ikirari na cewa na haukace, amma idan aka yi min auren dole zan kashe kaina”.

“An zo wurin!”

In ji Anti. Wato irin har na iso critical stage na depression mai sanya wa mara lafiya suicidalthought. A tunanin Anti fa.

Dr. Amir Yasa biro a gefen kunnen sa yana kallo na, “kin ki gaya min me ke damun ki, ni kuma na san lafiyar ki kalau koda kika yi maganan suicide. Amma kullum ki tuna ke din muslma ce wadda ta yarda Allah subhana ke bayarwa kuma shi ke hanawa, sannan shi yayi umarni da mu yi wa iyayen mu biyayya.

Kina cikin soyayya, right?”

Na daga ido na dube shi bance eh, ba ban kuma ce a’ah ba. Na yi alkawarin ba zan kara maganar Dream Husband dina da kowa ba, zan yi abinda zai bani kwanciyar hankali kawai; Nemansa.

Dr. Ya ce “Aisha-Siyama forget him, face your exams, its your future, obey your parents, stop stressing your mental well being, face your reality. You are still young, yanzu ne damar da kike da shi na gina rayuwar ki kada ki bari damar ta wuce a banza cikin mafarkin da ba lallai ya koma gaskiya ba.”

Gyada masa kai nayi kawai, fatana ya sallame mu. Ya dubi Anti Wasila yace “yarinyar ki bata tare da delusions, bata tareda kowanne rashin lafiya na kwakwalwa, amma tana bukatar hutu sosai kamar barci mai tsaho don stress ya mata yawa sakamakon infatuations da ta sawa ran ta, in tayi barci sosai zata samu nutsuwar zuciya don haka zan mata allurar barci ne kawai in bata simple drugs that will relax her stress.”

Aunty Wasila tayi ajiyar zuciya tace Dr. Kana ji fa tana maganar suicide, kuma kana kira mata lafiya. Dr. Ya ce “then kada kuyi mata auren dole, tunda bata so, abinda yafi suicide ma mata suna yi akan auren dole, wasu su sanya kan su a prostitution ko barin gida. Don haka don Allah ku barta ta nutsu, ku bata dama ta manta da shi a hankali”. Anti tace.

“Dr. Tun zuwa na gidan mahaifinta take maganar mutumin nan da take so, ka taba jin an so gaibu?

Ana neman shekaru biyar yanzu, bata taba dainawa ba, don haka bana jin zata daina din ko barcin kwana dubu zata yi.”

Dr. Amir Yace.

“Siyama where is he? Have you ever meet him in person?” Hawaye suka cika idanuna suka soma digowa, sabida yadda yayi maganar cikin damuwa da damuwata da nuna concern.

“I actually don’t know Dr. I don’t know.” Dr. Ya ce ki bani izni in zama abokin shawarar ki a kan sa, wato komai kika ji ni zaki kira ki gayawa ba kowa ba, sannan kafin ki aiwatar da komai a kan sa ki fara shawara da ni, i’m with you Siyama.

Lafiyar ki kalau, amma kina fama da infatuation wanda kika dade da sanyawa a ranki har ya zama kina  mafarkin sa, a zahiri abinda muka saka a ran mu muka kwanta da shi, shi muke gani a cikin barcin mu. Amma babu wani mutum da yake zuwar miki a mafarki face imagination da kika dade da sanyawa a ran ki ya zamar miki (fantasies).

Zaki iya raba kan ki da wannan fantasy da infatuation din ta hanyar treatment din fatar baki kadai da zan dora ki a kai (counselling) don kada ya zamo miki lahani ga kwakwalwa.”

“Gashi kuma Dr. Bana bukatar cire MAFARKAN nan nawa a raina sabida ina jin dadin su, na fi so in cigaba da rayuwa cikin mafarkai na, sun fi min komai dadi domin suna debe min kewar jiran sa. Na tabbata ko ba dade ko bajima jiki na na bani zai zo ne, mafarkan da kake son raba ni da su suna taya ni jiran sa, ba ni kadai nake wannan wahalar ba Likita, ka yarda da ni ba koshin wahala nake ba kamar yadda kuke zato. I believe that our hearts are jointly connected internally.”

Dr. Amir yayi murmushi ya mike yana hada allura, ya gama fahimtar duk abinda yake son fahimta, (she believed her fantasies and infatuations) na shekaru masu yawa raba ta da su farat daya zai yi wuya, har sai in ta samu actualizing din su.

Ya gama hadawa ya dawo yace “bani hannun ki Siyama zan miki allurar da zata sa ki samu isashshen barci.”

Ai kuwa tunda muka shiga mota nake ta barci, Allah ya so ni gobe da jibi duka babu paper. Lallai barci Rahma ne kuma ni’ima ga dan adam, kuma yin sa da ban yi ba kwana biyu ya taimaka wajen birkita ni da ta’azzara infatuation dina.

Abba ya dubi Anti da ke ta kokarin shirya masa abinci “ina ‘yar taki ne? Tun jiya ban gan ta ba””likita ya mata allura tana barci” bata da lafiya ne” ya tambaya yana yamutsa fuska. Anti tace “lafiyar ta kalau stress ne na jarrabawa kawai shine nasa aka mata allurar barci don ta huta sosai”. Abba yace “but an fi son barci natural, yin allura don kawai ayi barci?””Likitan da yayi mata ya san abinda yake yi, wajen specialist (psychiatrist) na kaita, ko ba komai yanzu hankali na ya kwanta tunda na tabbatar Siyama bata da tabin hankali kuma bata da aljanin dare as well.  Imagination ne data dade da sakawa a ranta yake zamar mata mafarki.”.

“Sai tsabagen iya shege kuma ba!”

Inji Abba cikin takaici. “Ni kuma nafi kowa iya shegantaka dani take zancen. Ko lefe bazan mata ba.

Wai Umar ne Siyama bata so? Humm, duniya mai abin mamaki. Zuciya mugun nama mai kawace – kawacen banza.

Allah ka shirya min Siyama, ka fidda rabon shaidan daga zuciyar ta”. Anti ta amsa da “Amin, amma Abba don Allah likita ya roki a daga auren kada ayi a yanzu, a kara bata lokaci zai yi counselling din ta ta manta da wancan din”

“Aikin banza aikin wofi, kada Allah yasa ta manta shi koma waye. Ta dauke shi su tafi gidan mijin ta tare. Bani da burin Siyama tayi zurfin ilmi a hannu na, gidan miji zan kaita a wannan watan da zamu shiga.

Duk wani nauyi da Allah ya dora min nata na sauke, a yanzu aure kawai ya rage, kuma zan tabbatar a hannu nagari na damkata, ba ruwa na da shirmen ta.

In ya so tayi tayi gunduwa-gunduwa da Umar din ta kawo mini, karewar rashin so kenan dai ko?”

Anti kasa magana ta yi, don tsakanin uban da ‘yar bata san wa ya fi wani taurin kai ba. Ba mamaki in ya kasance gadowa Siyaman tayi.

Kwana uku ina bacci sai dai Anti ta tada ni ta bani ‘fresh milk’ in sha in koma, dama kuma cikin al’ada nake, wani zubin sai tazo da kanta ta kaini toilet ta taimakamin na canza Pad sabida nauyin barcin da ke kaina. Ranar da barcin ya sake ni na koma na karasa jarrabawoyi na. Wanda babu laifi na dan amsa wasu yanzu domin na samu nutsuwa sosai.

Farewell From Regent Collage

A yau mun kammala Regent College Abuja, kowa ka gani cikin farin ciki marar misaltuwa yake sai hotuna ake dauka da ‘yan uwa da iyaye da kawaye. Anti ce da su Nadia suka zo dauka na bayan mun yi sallama da Azima Ko’oje da sauran wadanda muke mutunci dasu, da alkawarin zan je gidan su Azima idan na huta, kai tsaye muka kama hanyar gida, amma sai Anti tace Dr. Amir yace mu biya ta wajen sa ya kara gani na. Ban ce komai ba, ko babu komai shine wanda ya wanke ni daga hauka a idanun ta.

“Aisha Siyama an gama jarabawa lafiya ko, ina fatan akwai improvement?”

“Alhmdulillah Dr., na dan tabuka ana karshe-karshen”

“To wane course kike so zaki yi yanzu a jami’a?”

“Babana ba zai barni ba”

“Sai aure kenan”

Na hadiyi miyau da kyar. Ji kake mukut.

“Kin kara yin mafarkin sa?”

Girgiza masa kai na yi alamar a’ah,

“I only enjoyed my sleep”

Masha Allahu Aisha, kin karbi maganar Baban ki da muhimmanci yanzu ko? Imean ta auren dan uwan ki?”

Shiru nayi ban ce masa komai ba. Shi da kan sa sai y ace.

“Prefer not to say?”

Na gyada masa kai da sauri, yace “to ya yawan tunanin har yanzu yana nan?”

Na ce a hankali “bana tunanin komai tunda na gama barcin nan, ni ina zargin ba allurar barci kayi min ba gaskiya, damuwar tayi nesa da zuciya ta sosai. Bana jin bacin bacin rai sam ko wata damuwa, sai an tada min maganar auren Ya Omar.”

Dr. Ya maida hankalin sa ga Aunty yace “Alhamdulillah, she has responded fully to the treatment made. Shawara ta karshe itace ku hakura da yi mata auren nan, if not, abinda ake gudu shi zai faru da Siyama wato, zata tabu.”

Aunty Wasila tayi zugum da ita, tace “Dr. Matsalar ba daga gare ni bane, ba kuma daga Umar bane, wallahi yafi kowa damuwa da farin cikin ‘yar uwar sa, Baban su ne matsalar, ba zai taba yarda da wannan shawarar ba, iknowhim kamar tafin hannu na. In yace YES to da gaske yana nufin YES din, babu gudu babu ja da baya, baya waiwayen abinda zai je ya zo.”

*****

Muna isowa gida Abba na dawowa, duk muka yi gare shi muna masa oyoyo, ya dube ni sai  ya ga na rame ga idanu na sun zurma yace “jinya kika yi ne halan?” Girgiza kai nayi ban ce komai ba. Anti ce ta ce “na gaya maka ai, tayi jinyar baccin kwana uku”, “to Allah ya kara lafiya, ya batun jarrabawa kuma sai yaushe za’a gama?””An gama yau”. Ta fada da fargabar abinda zai biyo baya.

Daidai sanda muka shiga cikin gidan duk muka zazzauna a leather seats na falon kasa. Abba ya bude ‘brief case’ dinsa ya fiddo (flight tickets) guda biyu ya mikowa Anti. “Ga nan, amshi, flighttickets din ku ne na tafiya Lagos gidan Adamu gobe, zaku hadu ke da matar Adamu ku yi sayayyar duk abinda ya dace na gidan Omar da Siyama, ku kuma hada mata lefe irin wanda duk take so.

Da na ce bazan yi mata lefen ba amma Ummati ta ki. Rana ita yau da an sakko masallaci daurin auren su insha Allahu a Mambilah.”

Ya kawodaya daga cikin ‘credit cards’ din sa na bankin GT ya bata “abinda ke cikin nan nan ina ganin zai ishe ku sayayyar komai, ayi komai na hankali da kula bana son almubazzaranci.”

Hannu bibbiyu Anti tasa ta karba tana fadin.

“A madadin Siyama Allah ya saka da alkhairi. Ni kuwa sai nayi kasa da kaina.

Da daddare na bi Anti dakin ta na sameta tana canzawa Nadia Diaper, fuskata ba walwala nace “Anti nikam ba sai na biki Lagos dinnan ba, kuje kawai dik abinda kuka zabo zai min dai dai”. Hawaye suka balle mini.

Anti tace “sabida bakya farin ciki ko sabida baki godewa kokarin Baban ki ba ko??”

“Anti….!”

“Siyama ki shirya kayan ki zamu tashi Lagos gobe da safe insha Allahu, zamuyi kwanaki uku na san zasu ishe mu mu gama abinda ya kai mu. Kwana daya lefe, kwana daya furniture da kayan kitchen da labulaye. Nasara ta san ko’ina a Lagos da inda za’a samu komai mai kyau, zata raka mu.”

Juyawa nayi kawai na fita ba tareda na kara tankawa ba, don na san duk abinda zan fada din tirjiya ce kuma ta nuna min bazata karbi kowanne uzuri na ba.

Na tashi da zazzafan zazzabi a safiyar washegari, zazzabi mai zafi sosai harda jijjiga, da kartar hakora, wanda yasa dole Anti ta barni a gida ta tafi sayayyar kayan aure a Lagos don bata isa keta umarnin Abba ba, ni kuma na shiga jinyar kaina da kaina don Abba ma ba ya gari daga ni sai Maryam Jamila. Ita take taimakamin da miko min duk abinda nake so ina daga kwance, ta bani paracetamol na sha naji dan dama-dam wajen azahar na dafa mana noodles muka ci nida ita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 12Sakacin Waye? 14 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×