Skip to content
Part 18 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Emotions

Sai ya kasance tun daga ranar dana gan shi a talbijin nake bibiyar sa, nake bibiyar komai nasa da wani irin emotion, yawanci na kan ga hotunan sa tare da sauran VOA TEAM na talbijin ko na radio, na kuma fahimci ba’a bangare daya yake broadcasting ba, yana yi a sashen hausa, yana kuma yi a sashen vedio na turanci.

Wata irin walwala ta same ni a kwanakin nan, ba abinda ke bani nishadi irin kasancewar Hamzah mutum ne a raye ba aljani ba ba jinnul Aashiq ba, na koma bani da abin yi muhimmi irin na dinga bibiyar shirye-shiryen sa. Kullum da sabon shirin da zai kawo mai matukar muhimmanci da kayatarwa.

Daga yadda yake gabatar da muhimman shirye-shirye a gidan radiyon da talbijin na VOA zaka fahimci dan gaban goshin su ne. Kusan duk wani shiri mai muhimmanci shi yake gabatar da shi. Watakila wannan ba zai rasa nasaba da zazzakar muryar da Allah yayi masa baiwar ta ba, mai wata irin sassarfar magana wadda ke karawa shirin sa armashi da jan attention din al’ummah, murya ce mai taushi da sanyawa dan adam nutsuwaka saurare shi koda baka ra’ayi, sassarfar ta kuma bata hana a gane me yake cewa cikin dadin rai. Sai take kara mata wani irin armashi.

Hamzah na tafiya da zukata da dama ba tawa nikadai ba, na gane hakan ne ta hanyar comments da yake samu na miliyoyin mutane a shafin sa na Twitter da na Instagram a duk lokacin da VOA suka saki shirin sa.

Babu cikakken bayani a kan sa a google amma akwai cikakken bayani na aiki da profession din sa a shafin sa na LinkedIN.

Matakin Digiri dai-dai har guda uku reras yake rike dasu akan aikin Jarida daga Jami’ar ‘Sussex’. He’s a Chevening Scholar wato wanda yayi karatun sa na Masters daga tallafin ‘Chevening’, yayi Ph.D daga tallafin ‘Commowealth Scholarship’, cikakken dan Nigeria daga jihar Filato (Jos).

Ya yi aiki na lokaci mai tsaho da British Broadcasting Corporation, yayi da Radiyon Jamani (Deustche Welle) kafin ya bari duka ya dawo uwar su VOA.

Wadannan sune muhiman bayanan dana samu a kan Hamzahn da zuciyata ta ki hutawa a kan sa, daga shafin sa na professionalism wato LinkedIn. Suka zame min ababen taya hira, ababen debe kewa, ababen saka nishadi, hotunan sa kuma suka cika wayata fam. Wadanda nake sauke su daga shafukan sa na yanar gizo. Murmushin sa kadai mai kokarin narka zuciya ta ne, wanda ke tafiyar da numfashi na na wucin gadi.

Na yarda ba abinda ya kai soyayya dadi a zuciya da ruhi. To ina ga inda take samun martani daga wannan masoyin?Gare ni dai, ni kadai nake ninkaya a koramar da zakin ta yafi na zuma, gardin ta yafi na madara.

Koda Aunty Wasila ta aikowa da Young Abba sakamako na na WAEC da NECO babu wani abin a zo a gani a cikin su ban damu ba, a yanzu kam ko diyar Qaruna bana jin ta rufa bayana a kwanciyar hankali da samun contentment na rayuwa. I’m feeling myself on top of the world of happiness and excitedness. Tunda kullum idanuwa na na kallon abinda suke so, kunnuwa na na jin sautin mutumin da suka fi son ji a duniya bakidaya, wani abu wai shi karatu na rantse baya gabana idan ba yadda zan mallaki Hamzah ba.

Uwar dakina Nasara Alkali, ta dade tana lura da sabuwar rayuwar dana fada, kamar bana cikin tamu duniyar, kamar a wata duniyar nake rayuwa nikadai, na zama addicted ga wayata ko bandaki zan shiga da wayar nake shiga, idan kuwa akan masai nake zaka sameta like ga kunnuwana ina sauraron Hamzah – Mawonmase.

Duk abinda nake ciki ashe aunty Nasara na lura dani. Yau da Young Abba ya fita aiki sai ta shigo daki na cikin shiri, a daidai lokacin da Hamzah ya kammala shirin sa na safe wanda yayi akan janyewar yajin aikin jami’o’i na kasar Najeriya.

“Mrs VOA, ko zan samu ki rakiyar ki zuwa Walmart Supermarket?”

Nasara ta tambayeni tana kada mukullan motar hannun ta, tayi shigar ta islamically kamar kullum ta hanyar yin rolling da bakin mayafi akan doguwar riga samfurin kasar Oman ruwan kwaiduwar kwai data ke sanye da ita.

Tunda Hamzah ya gama shirin dana ke saurare, ba matsala zan iya raka ta. Don haka nace Aunty bani mintuna biyu in dan watsa ruwa, nima ina son fita in motsa jiki na, yau kwana goma kenan ban je koina ba.”

“Sai sauraren Hamzah Mawonmase!”

Anty ta fada cikin kirjin ta har sautin maganar ta ya dan fito. Na juyo daga kofar toilet bayan na zari towel daga ma’ajiyar sa, nace “na’am Aunty magana kike yi ne?”

Ta girgiza kai tace “Oh! Ban ce komai ba fa. Yi maza ina jiran ki a mota.”

A gurguje nayi wankan na fito wani wajen ma kumfa bata fita ba, a haka na saka jacket wadda ta kai min har kasan guiwa da wandon Jeans baki. Na saka hijab wanda iyakacin sa kafaduna, na dauki wayata da ‘yar karamar jakata ‘Chanel’ na bi bayan Anti zuwa mota.

Nasara Alkali

(My second lifestyle influencer)

Muna kan hanyar mu ta zuwa  ‘Walmart Supermarket’ dake kan titin Riggs Road, South Dakota, inda a can Anti Nasara ke yin duk wani provision din kayan abincin mu dana amfanin ta. Anti ta dube ni da wutsiyar idon ta. Kafin ta maida hankalin ta kacokam kan tukin data ke yi cikin gwaninta. Sannan ta kira sunana cikin siga mai nuna muhimmiyar magana take son yi da ni.

“Sai yanzu na gane dalilin da yasa Abban ki ya zabi yayi fushi da ke har ya kore ki Siyama. Nima kuma ina gab da yi; fushi da kora.”

Na zaro  ido ina kallon Anti cikin tsoro da razanar maganar ta. Me nake shirin ji haka ni Siyama!

Aunty Nasara bata damu da reaction dina ba kan maganar ta, ta cigaba da cewa.

“As long as mace zata bari wani namiji da ba mijin ta na aure ba ya shiga zuciyar ta, ya shiga cikin rayuwar ta yayi kane-kane irin haka ya hana ta cigaba, ya hanata wani tunani bayan nasa, ya shiga tsakanin ta da iyayen ta, ya yi galaba a kan karatun ta, ya dauki ragamar zuciyar ta daga kan turba sahihiya, wannan mace macen sunan ta sorry domin mara hankali ce, kuma wadda bazata iya fighting da emotions din ta ba.

Maimakon hakan, it’s the emotions that drives her, not her own humble self, su suke jan ragamar ta tare da wannan namijin. Musamman wanda bata cikin rayuwar sa, ba kuma son ta ya ce yake yi ba.”

Anti ta dakata ta yi kwana ta dauki titin Walmart Supermarket, ta bar kalamanta na ragargaza ni, sannan ba tare da ta damu dani ba ko halin da ta jefa ni ta cigaba da cewa,

“Siyama kin dauki hanya ta ruguza rayuwar ki, kin bar emotions suna driving din ki. Kin bar ALLAH Siyama tunda kin bar koyarwar AL’QUR’ANI, bayan cewa sune kadai abinda idan ka rike komi na rayuwa zai zo maka da sauki.”

Jiki na bakidaya ya saki, gwuiwoyi na sun yi sanyi kalau. Buri na kawai Aunty Nasara ta dauki hanya dodar kai tsaye ta gayamin me nake yi har haka da har take tunanin na bar ALLAH na dau hanyar rusa rayuwa ta.

“Amsa ga tambayar da kike yiwa zuciyar ki a yanzu Siyama, yaushe rabon ki da karanta littafin Allah, yaushe rabon ki da yin sallahr dare don gayawa Allah bukatun ki da rokon sa a kan ya sassauta zuciyar mahaifin ki?

Siyama kin fadi WAEC kin fadi NECO amma ba abinda ya dame ki sabida kin saka soyayya a zuciyar ki, soyayyar da bata da madafa don kuwa Hamzah Almustapha na gidan Rediyon VOA; BA MUSULMI BANE CHRISTIAN NE (Ahlil Kitabi) dake bin Addinin CHRISTIANITY.”

Don haka in zaki shiga hankalin ki ki shiga, in zaki dawo hayyacin ki ki dawo. Ki kama Allah ki kama iyayen ki. Ki maida hankali wajen gyara kuskuren da kika yiwa mahaifin ki, ya fiye miki alfanu duniya da lahira akan bibiyar shirye-shiryen Hamzah dare da rana, ya fiye miki alkhairi ga cigaban rayuwar ki, ya fiye miki maslaha da Ubangijin ki.

Yara mata irin ki sun fi goma dana samu labarin sun yi riddah a kan soyayyar wannan mushrikin a Najeriya.

Don baiwar iya magana da ta halitta Allah yayi masa karshe, amma arne ne Siyama, ba addinin ku daya ba, ko kusa bai cancanci soyayyar ki ba. Siyama Gembu, ‘yar musulmai ce rainon musulunci.

Umar Faruq shine mijin da ya dace da rayuwar ki kamar yadda Abban ki ya hango miki, abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala da gwauron dutse ba zai hango ba. Shiyasa aka ce ta yaro kyau take amma bata taba yin karko.

Don haka Siyama a matsayi na na UWA ba MARIKIYA ba nake baki shawarar ki kama abinda zai amfane ki ki manta da Hamzah, ki manta da Mawonmase, har yanzu ke yarinya ce da take kan gabar gina rayuwar ta. Baki kai ga cimma komi a rayuwar ki ba. You are still a Teen.

Na sama miki islamiyyah school a New York na gama komai zan kai ki gobe, a tsayin watanni shidda kacal ake haddar Al’qurani, ta wasu musulman Canada ce Dr. Ismail Memon da dan sa . Shaykh Ibrahim Memon Madani, su suka bude ta a birnin Buffalo, New York. 

Kafin watanni shidda nake son ganin Hafizah Siyama a gabana, in ga sabuwar Siyama mai Qira’ar Madani, wadda iyayen ta zasu yi alfahari da samun ta, kasancewar ta mahaddaciyar Al’qur’ani.

Idan kin kammala wannan makarantar zan maida ke aji shidda na sakandire da sunan transfer daga Regent, ki sake zana jarrabawar kammmala sakandire sannan ki fara karatun Jami’a.

Wannan shine tsarin da na yi miki nake kuma fatan ki bani hadin kai a kan sa, ko in mayar da ke Mambillah”

Murfin Littafi Na Daya

Ban iya tsayawa kallon yanayin da Siyamar mu ta fada ba na ajiye Biron, ba don komai ba sai don nafi Siyama kidimewa. Abinda ban sani ba; Shin SIYAMA zata bi tsarin uwardakin ta Nasara don a zauna lafiya da ita? Ko kuwa a’ah itama zata bi sahun masu yin RIDDAH ne kamar sauran matan da aka yi ittifakin sun yi RIDDAH a kan sa? Tunda dai mun ga har fiya-fiya ta sha don ta tsira da shida fantasie din ta a kan sa???

Sanin hakikanin wannan amsar sai ita kadai ‘yar mutanen Mambillah; Aisha-Siyama Mamman Gembu. Don haka mu biyo Boddon mu-Siyamar mu a littafi na biyu don jin yadda zata wakana tsakanin ta da ‘Dream Man’ din ta.

Shin da gaske Hamzah kafirin ne ko kuwa shaci-fadi ne irin na Nasara don ta samu hanyar raba Siyama da emotions din ta???

SAKACIN WAYE? 2 TARE SUKE DA LITTAFI NA DAYA. TAKU HAR ABADA SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI).

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 17Sakacin Waye? 19 >>

2 thoughts on “Sakacin Waye? 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×