Skip to content
Part 19 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

LITTAFI NA BIYU

In kin ji tashin hankali, razani da kidimewar da suka same ni a wannan dan tsakanin da Nasara ta dauka tana magana to guda daya kenan. Na shiga abinda ake kira bewilderment8 na zuciya da kwakwalwa, na shiga coma ba don na kwanta a kwance ba, sai don kasancewar ilahirin gabban jiki na sun daina aiki na kame a kujerar motar dana ke zaune. Wani bangaren na zuciya ta kuma yana mai gaskata kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakin Anti na. Na yarda iyaka gaskiyar da kowacce uwa zata gaya min kenan, iyaka matakin da kowacce uwa tagari zata dauka kenan don tseratar da ‘yar ta daga fadawa halaka, shi Nasara ta dauka ta kuma ke aiwatarwa a halin yanzu.

Ban tashi tare da mahaifiya ta ba, amma sai Allah ya hada ni da wasu irin matan Uba nagari, wadanda irin su sun yi karanci a wannan zamanin da muke ciki, wadanda kullum burin su shine su dora ni a kan hanya kuma turba sahihiya idan na karkace, in kasance yarinya tagari abun koyi, abun alfahari gare su da mahaifi na.

Iyakacin rudani na shige shi a wannan ranar, rudanin da ya kusafidda ni a hankali na. Ba musulmi bane a ina ya samo sunan Sahabin Manzon Allah kuma Baffan sa sayyidina Hamzah (A.S)? Ina ya samo sunan shugaban halitta (Almustapha) a surname din sa???

Duka wannan ma idan an bi salasala ai basu da wani amfani a wuri na, ba kuma zasu amfana ni da komai ba. Tunda kuwa Hamzah bai taba sanin da wanzuwa ta a duniya ba, Hamzah bai ce yana son Siyama ba, Hamzah bai sanni ba…. A takaice ni kadai nake kida na, nake kuma taka rawa ta iri-iri a kan sa, cikin wata duniya ta fantasy and imagination wadda ban taba jin mai irin ta ba sai ni.

Amma kuma ina tababa hadi da waswasi a cikin al’amarina da wannan bawan Allah, tabbas akwai wani BOYAYYEN SIRRI wanda Allah kadai ya san shi, ya kuma ke nufin sa a kai na da shi Hamzan, in ba haka ba ta ina ya kutso ya shigo cikin mafarkai na, na rayu shekaru kusan goma ina mafarkin sa, na kuma gan shi exactly a talbijin yadda nake ganin sa cikin mafarki da imaginations dina?

“Ya Allah taimake ni kafin na haukace!”             Na fada a fili, cikin kama kai na dake neman rabewa gida biyu saboda sarawar da yakeyi mun, ina girgizawa da karfi ina kara girgizawa ko hakan zai rage nauyin da yayi min.

Anti tace mata da yawa sun yi RIDDAH wato sun bar addinin musulunci a kan Hamzah, wanda ke nufin ta san shi farin sani, ta kuma san duk abinda nake ciki a kan sa. Domin kuwa har zana shi na yi da pencil  na kafe a cikin  frame din gefen gado na. 

Sannan cikin waya ta da laptop dina duka hotunan Hamzah Mawonmase ne,  wadanda nake saukewa daga shafukan sa na social media, ga kuma kona mata girki dana ke tayi a kai-a kai tun daga lokacin da Young Abba ya mallaka min waya,  sannan a fili nake kunna muryar tasa sautin na tashi daga rediyo na, ko talbijin din gidan dake falo, in kura masa ido kamar tsohuwar mayyar data ga nama ko kuwa kamar mai shirin hadiye shi don SO. 

A zahiri duk wata uwa in dai mai kula ce akan al’amarin ‘ya’yan ta to tabbas zata yi saurin gano inda na dosa a kan Hamzahn VOA, ba wai labaran nasu nake kallo ko nake saurare ba, tunda kuwa in ba shi yake programme ba ai bana ko tsayawa in kalla ko in saurara, jiki na ma bakidaya ya nuna Hamzah kadai yake so da gani, daga yadda yake amsawa da kowanne tashin muryar sa a talbijin. Domin har wani dan kyarma (shaking) jiki na yake yi idan Hamzah yana gabatar da shirin sa. Balle wayayyar mace mai tarin ilmin addini dana boko irin Nasara Alkali, ba zai zamo abin mamaki ba don tayi saurin ramfo ni. 

Mahaifin ta tsohon Alkalin-Alkalai ne na jihar Katsina wato Chief Justice Alkali Sada Abdurrahman. Wadda kuma tayi dukkan karatun ta ne a kan kimiyyar aikin jarida. Sannan tayi kwasa-kwasai marassa adadi akan Islamic Studies. Don haka ban yi mamaki ba data yi saurin bin kwakkwafin halin dana ke ciki.

“Kada kiyi mamakin inda na san shi fa, kafin kammala karatu na a kasar Algers, na yi wani gajeren Internship da gidan Rediyon BBC, a can na san shi farin sani don a lokacin yana aiki da BBC Hausa ne a garin London, kafin daga can ya koma Radiyon Jamus (Deustche Welle), daga can ne kuma katsam naji shi a VOA”.

Aunty Nasara ta bani cikakken bayanin da ya wanke tarin tambayoyi na a kan inda ta san Hamzah Mawonmase har haka, har kuma ta san cewa ba musulmi bane kafiri ne. Kodayake kiristoci masu bin addinin Almasihu basa kiran kan su kafirai, tunda a wurin su sun yarda akwai Allah.

Koda muka dawo gida a falo na jabe kamar kayan wanki na kasa koda karasawa daki na. Kafafuwana sun sage iyakar sagewa har ta kai ga sun kasa daukar nauyin gangar jiki na su karasa da ita cikin daki. Anty bata kara bi ta kaina ba ta shiga kicin ta fara hada mana abincin da zamu ci da daddare. Irin abun nan tayi min na ko oho, mai nufin  “ya rage naki, ni dai na fita ko ba sabulu, tunda na sanar da ke abinda baki sani ba, yanzu zabi ya ragewa mai shiga rijiya.”

A haka Young Abba ya dawo daga aiki ya shigo gidan ya cimmani jabe akan dobuwar kujera. A kan kujerar gefe na ya ajiye brief case din sa, yana loosing tie din wuyan sa yana fadin.

“An Siyama – Siyama babu lafiya ne?” 

Aunty ta fito kitchen rike da jug da tambulan mai garai-garai mai cike da danyar madarar shanu mai sanyi ta nufe shi tana fadin,

“kyale Siyama ka ji! Zazzabin tafiya Islamiyyah take yi, na gaya maka gobe insha Allah zan kai ta Madania din New York, komai na shirin fara islamiyyar ya kammala kamar yadda na gaya maka tuntuni.”

Young Abba ya karbi madara daga hannun matar sa, ya ce “ke kam Nasara kullum kan ki a tukunya yake, maimakon ki neman mata hanyar shiga Jami’a ta hanyar gyara sakamakon ta da bai yi kyau ba, sai ki tsiri kai ta islamiyya har tsayin watanni shidda wanda ke nufin ita da sake jarrabawa sai nan da shekara mai zuwa, sannan a zo a yi batun shiga Jami’a? By then tana da kusan 22 years wanda da a nan kasar ne ta gama degree na farko.”

Inda sabo to Nasara ta saba da Boko-Akida na mijin ta Adam Gembu, don haka bata yi mammakin kalaman sa ba akan karatun addini, don haka bata ja zancen da nisa ba ta mika masa madarar a bakin sa, sai da ya shanye tas, ta ce. 

“A gani na duk matsalar da Siyama ta saka kan ta a ciki rashin kama Al’qur’ani ne. Tayi SAKACI da Al’qur’ani a matsayin ta na diyar musulmi. Wanda ya kama Al’qur’ani abubuwa basa cude masa irin na Siyama, ba ya fadawa halaka irin wadda Siyama ke ciki a yanzu, baya shiga matsala irin tata, abubuwa basa fin karfin sa, haka baya rasa mafita ga dukkan matsalolin sa balle har ya fada cikin fushin iyaye, duk inda mai Al’qur’ani ya fada sai kaga Allah ya bashi warwara ya kuma bashi mafita ta alkhairi nan da nan. Ya kuma kasance cikin albarkar iyayen sa da nasarar rayuwa da cigaba mai amfani. Siyama na cikin masifar da komawa ga Allah ita ta fi mata amfani”. 

Young Abba ya zaro ido yana fadi cikin kakabi “toh! Allah ya raba  mu da masifa, ke fa wani lokacin baki iya magana ba, don kawai ta fadi WAEC ne kike kira mata masifa? Sai a ka ce baza’a iya sakewa ba? WAEC din banza? Da fa a Nigeria ne biya zan yi a yi mata. Na fa san ki da maida allura garma, dan abinda bai kai ya kawo ba sai ki dauke shi gagarumar matsala meye masifa a faduwa WAEC?.

Abban ta kuwa har ga Allah ta fi shi gaskiya, da Allah ya bashi ikon zaba mata mijin aure bai ce har da auren dole ba, irin wannan maimakon a gyara zumuncin da ake son dabbakawa sai ya koma an lalata shi bakidaya, idan ta kasa yi wa Omar biyayyar aure shine ta fada halaka gun Ubangijin ta.”

A ran ta ta ce “umh! Ta ki zabin iyaye ai kuma ga inda zuciya ta kai ta, akwai halakar da ta kai soyayyar mushriki? Babbar halakar kenan wadda tafi ta auren dole, soyayyar wanda bai yarda Allah daya ne ba.”

Amma dai Nasara bata fada masa hakan ba, ta kafe a kan cewa sai na je Islamiyyah ko yana so ko baya so.

Ni dai ina jin su daga kwancen dana ke kamar sassakakken gunki, suna  ta rigimar su a kai na kamar ba masoyan nan masu kwantarw juna murya ba, daga karshe dole shi ya hakura ya sakar mata ya yarda zan tafi “DAAR AL – ULOOM” tsayin watanni  shidda kafin in dawo in koma sakandire ajin karshe. 

Young Abba ba da son ran sa ba ya saka hannu a kan takardar da mahaifi ya kamata ya saka hannu, ya kuma tura mata duk abinda ta bukata wanda za’a kashe, ba don komai ba sai do yana yaba kokarin ta a kai na ya kuma yaba da soyayyar data ke yi min, hatta kudin jirgin kasa da zamu bi daga Washington zuwa New York Young Abba ya tura mata a lokacin. Don dai kuma ta kyale shi ya zauna lafiya, ya kuma san Nasara da naci akan abinda ta yarda da shi, bata niyyar abu wani yasa ta ta canza.

Wani irin wahalallen dare a gare ni, wanda na kwana cikin sa ido biyu amma a kwance, ni da wanda ya gamu da lalurar paralyses bamu da maraba. Na rasa inda zan saka kaina da labarin dana ji daga bakin Anti na Nasara a kan Mawonmase, mutumin dana rayu ina so tun fara hankali na. A karshe na yarda da cewa dole in dauki duk abinda Aunty Nasara ta gaya min da matukar muhimmanci and act accordingly. Ko ina so ko bana so. Don na zauna lafiya da ita. Idan ta kora ni Mambillah na san ‘yar gidan jiya zamu koma ni da Ummati, Abuja kuwa Abba ba zai karbe ni ba tunda har yanzu dan sa Omar bai dawo ba.

Magana ta hankali da tunani kuma na san dole in raba zuciyata da wannan infatuation din. Ba zai yiwu in cigaba da dora zuciya ta a kan soyayyar  mushriki ba, zan koma ga Allah ba abinda ya gagare shi. Zan koma ga Allah ta hanyar bin tsarin Aunty Nasara, wato in tafi Islamic School, in kama Littafin Ubangiji mai tsarki, domin neman waraka daga soyayyar data yi wa zuciya ta katutu, zan fara haddar Al’qur’ani da tsarkakakkiyar zuciya, zan cire HAMZAH MAWONMASE a rai na ko ta tsiya ko ta arziki, zan kafa sabuwar rayuwa mai amfani wadda babu soyayyar kowanne da namiji a cikin ta bayan mahaifi na da Kawu na wato Young Abba, Adamu, da kuma DAN UWANA; OMAR FARUK.

“DAAR AL-ULOOM AL-MADANIA, NEW YORK”

Makarantar na nan a garin Buffalo din New York, United States, wadda larabawa guda biyu daga kasar Canada ne suka kirkira musamman don gina malaman musulunci masu tasowa da mahaddatan Alqur’ani (Islamic scholars and Huffaz) tun daga matakin farko. 

Zan iya cewa na shiga wannan makaranta da kafar dama, domin ko watan farko ban rufa a cikin ta ba duk wata damuwata ta yaye, zuciyata ta cika da haske, hasken dake cikin Alqur’ani, babu komai a cikin ta yanzu sai tunanin yadda karatu na yake guda na; yadda gobe zan bada haddar dana yi a class washegari da kuma sabuwar surar da zamu shiga bayan wannan, farin ciki ya maye gurbin damuwa ta, ya zamanto bani da lokacin kai na, bani da lokacin da zan zauna in yi tunanin banza da wofi, har in shiga cikin emotions dina na baya. Hakika na yarda Alqur’ani maganin komai ne kuma waraka ne ga al’ummah.

Na fara karatun sauran littafan addinin musulunci cikin nasara bayan hadda. Ba Hifzil Qur’an kadai muke yi ba muna daukan kwasa-kwasai a sauran manyan darussan addinin muslunci kamar kana cikin Birnin Madinah Al-Munawwarah. 

Sai da na rufa watanni uku Aunty da Young Abba suka kawo min ziyara, na cika da farin cikin ganin Aunty Nasara dauke da ciki. Shi kan sa Young Abba da yake kushe karatun nawa da farko yau da ya ganni cewa yayi 

“Anya wannan Siyama na ce-Boddo na ce? Kin saje da larabawan makarantar, kin nutsu da yawa  Siyama, babu wannan moody din dana ke gani a kan fuskar ki kullum, sai far’a da annuri kike, kin zama kamar diyar larabawan Qatar ba fulben nan ta Mambillah ba”. 

Dariya nayi sosai na ce “kai Abba ni da nake fama da hidimar hadda kullum, wane kyau zan yi? Ban ki ba in ka  ce weather din garin Buffalo ya amshe ni, amma bama samun hutu ko kadan. Alhamdulillah mun kammala haddar hizf na talatin yanzu”.

Na gabatar musu da kawata Thurayyah – Imaan wadda ta zo daga Egypt, mun wuni sur tare dasu cikin farin ciki da hirarraki na yaushe gamo, bana bukatar komai don komai muke bukata makaranta na yi mana cikin kudin da iyayen mu suka biya. Young Abba, ya gaya min zasu je gida Najeriya cikin watan nan amma bazasu jima ba, wai Ummati ce bata ji dadi ba.

Nan ne na dan shiga damuwa har damuwata ta fito fili, amma sai suka kwantar min da hankali cewa ai har ma an sallame ta daga asibiti, tana Abuja hannun Anti Wasila. Tayi fama da ciwon baya da kafafu ne. 

Jin tana gun Anti Wasila sai na samu dan nutsuwa, na san Anti Wasila zata kula da ita yadda ya kamata ba kamar a ce tana Gembu ita kadai a gidan ta ba.

Bayan tafiyar su muka koma cikin makaranta ni da Thurayyah. 

Cikin kwasa-kwasan addinin muslunci da muke yi sun hada da Usul-Al Fiqh (Principles of Jurisprudence), Tareekh ul Fiqh (History of Fiqh), Ulumul Qur’an (Sciences of Qur’an), Seeratun Nabawiyyah (Life and Battles of the Prophet SAW), Tawheed (Islamic Theology), Mantiq (Logic), Tareekh Al Falsafah (History of Philosophy) Tasawwuf (islamic mysticism) da sauran su. Nafi bada karfi na ga kwasa-kwasai guda biyu wadanda nake specializing a kan su wato; Islamic Mysticism and Islamic Jurisprudence (Tasawwuf and Fiqh).

Kafin na kammala DAAR AL ULOOM AL-MADANIA na zama ISLAMIC SCHOLAR (Malamar addinin Muslunci), wadda zata iya tara dalibai ta koyar da su ilmin musulunci da ilmin da ke cikin Al’qur’ani, harshe na ya kama larabci sosai wanda ke cakude da accent na turanci. Na haddace Al’Qur’ani mai girma a iya watannin da makaranta ta diba mana, na kuma sauke duka littafan dana ambata a sama, dama wasu da dama da ban ambata ba. Na rubuta littafi (project work) a kan Islamic Mysticism.

Ranar bikin kammalawar mu aka yi mana jubilation wanda aka nuna a gidan talbijin na Aljazeerah da CNN, na ga Aunty Nasara da tsohon cikin ta tana hawayen farin cikin nasarar data samu akai na, na canza rayuwa da tunani na positively. Ta kankame Young Abba lokacin da aka kira sunana na karbi Al’qur’ani mai girma da certificatedaga hannun shugaban makarantar mu Shaykh Isma’il Memon, wato shaidar kammalawa. 

Muka dawo gida Washington. Anti da Young Abba kamar su goya ni, Anti ta aika ma Ummati da Aunty Wasila cewa a yanka rago ayi min sadaqah. Na kammala haddar Qur’an. Daga Ummati har aunty sun sha mamaki da suka ji wai na haddace Alqur’ani cikin abinda bai gaza shekara ba.

To dan adam duk abinda ya saka a ran sa ya kuma yarda shine abin dogaron sa to hakika a haka zai tafi masa. A can baya na jingina soyayyar gaibu a raina, da kuma ta zahiri a bayan ganin dana yi masa a talbijin, daga baya na samu mai ankarar da ni cewa duka is a waste of time, kuma abinda ka likawa zuciyar ka shi zuciyar ke yin galaba da shi a kan ka.

Ba jimawa da dawowa ta gida Young Abba ya karbo min shaidar kammala Regent dina daga Abuja, da jarabawa ta da bata yi kyau ba, don haka na samu aka maida ni aji shidda na zana jarrabawar sakandire tare da dalibai masu fita a wannan shekarar. 

Cikin yardar Allah da tsayuwar zuciya waje daya da kuma ta iyayen gida na kwarai dake tsaye bilhaqqi a kai na, na samu sakamakon da zai ishe ni fara Jami’a a ko’ina cikin duniya.

A lokacin Ahyaan yaron da Anti ta haifa ma Young Abba yana gudun sa ko’ina, kullum muka yi waya dasu Anti Wasila sai ta kanga min kukan jaririn data kara haifa itama mai suna Hayatuddeen. Mu kan yi hira da Maryam -Jamilah da Shukrah-Nadiya. Ta kuma gaya min lokaci zuwa lokaci Ko’oje kan kawo mata ziyara ta wuni tana hira ta. Don haka ne sanda Aunty Nasara ta samu mai zuwa Abuja na yi wa Ko’oje aiken kayan sanyawa masu daraja akwati guda, don ba abinda Young Abba da matar sa Nasara suka raga min da shi na bukatun rayuwa sai Alhamdulillahi. Tsakani na dasu sai addu’ar alkhairi.

<< Sakacin Waye? 18Sakacin Waye? 20 >>

3 thoughts on “Sakacin Waye? 19”

  1. Auwal Ibrahim Karaye

    This is very interested. Sumayya Abdulqadir (Takori) is like no other. We are very proud of you may God continue to bless your knowledge.

    By Auwal Ibrahim Karaye
    Sign Language Interpreter

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.