Skip to content
Part 20 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

New VOA Staff 

Nasara ta duba screen na kwamfutar kan cinyar ta sosai, sakon email ne wanda ta fidda rai da shi ta kuma manta da shi, tafi shekara da neman aiki da gidan Rediyon VOA sai yau Allah Subhana ya yiwa aikin fitowa, suna kiranta interview na gaggawa nan da kwanaki biyu masu zuwa.

Mikewa tayi bayan tayi printing din takardar akan takarda, ta samu maigidan ta Adamu a dakin barcin su. Bakin ta kamar ya yage don farin ciki. Fuska kamar gonar auduga don smiling.

“Imagine Baban Ahyaan sai yau aiki na da VOA ya fito”

Young Abba yana daga kwance yace “wane sashe ne suka kira ki?” Tace “Sashen Hausa ne, VOA – Amurka, Hausa.”

Young Abba ya taya matar sa murna amma sai ya ce “the entire house will be missing Mama Nasara, kada wata budurwa mai zubin buzayen kauye ta ji labari.”

Dariya tayi tace “ai itama admission din ta ya fito da “George Washington University”, zata fara B.A dinta a Journalism.”

“Journalism kuma? Ba Data Science da kika ce zata yi ba?” 

Inji Young Abba cikin yamutsa fuska,  irin na rashin na’am da zabin ‘yar tasa. 

“Ke jarida ita jarida wato ko? Ku taru ku dinga saka ni a kwana in rasa yadda zan yi in yi muku karya?” 

Nasara tayi dariya sosai kafin ta daga kafada irin na ba ruwa na ta ce “abinda ta zaba kenan, a can baya na tursasa ta tayi course a kan abinda bata yi niyya ba, sai don in samu rayuwar ta ta canza, Alhamdulillah na ci wannan nasarar, wannan karon ba zan canza mata akida ba, ko me ta zaba shi zan yi mata.”

Sai ya zama mute, ya kasa cewa komai.

Aunty taje ta yi interview da VOA kuma cikin taimakon Ubangiji ta haye, ta zama daya daga cikin staff na VOA Hausa.

Ni kuma na fara zuwa daukar lacca a George Washington University, ina jin dadin darasi na na Journalism fiye da zaton ku, gani da babbar ‘yar jarida a gida wato Anty Nasara Alkali Sada, wadda ke kara highlighting dina komai kullum ranar Allah, don haka ba da dadewa ba na zamo cikin zaqaquran daliban sahun farko a tsangayar mu.

A wannan lokacin duk wata nutsuwa da duk wani buri dana ke nema a rayuwa na gama samun shi, ba abunda zan ce da Young Abba da mai dakin sa Nasara sai addu’ar alkhairi da nasara a rayuwar su. Allah kuma ya raya musu dan su Ahyan rayuwa mai tsayi da albarka yasa ya zamo mahaddacin Al’qur’ani.

A can gida Najeriya kuma Ummati ta matsa a kan su maido ni gida haka a yi min aure, kuma kafin Allah ya dau ran ta, shekaru na ashirin da uku duk tsararraki na sun ajiye ‘ya’ya a cewar Ummati. Kullum dai Young Abba cewa yake zan zo ne ta yi hakuri, ta bari in kammala digiri na ko shekara talatin nayi bazan rasa mijin aure ba insha Allahu.

Abba kam zuwa yanzu yafi son zamana tare da su Young Abba musamman wannan makaranta ta Huffaz da Anty tayi min sanadin ta. Don haka yace shi ya bar ma Young Abba ni, duniya da lahira. Allah ya raya kananan dake gaban sa.

Ko ba’a fada ba na san na ci darajar Al’qur’ani zuwa yanzu zuciyar Abba ta dan sassauta a kaina, duk da cewa Ya Omar bai juyo gida ba har zuwa yanzu, kuma basu ji daga gare shi ba ko da sau daya.

Wata ranar Asabar ina gida bani da Lacca, sai wani tunani ya zo min.

Kawai na tashi na kunna system dina na budo yahoo.mail na soma zana wa Ya Umar sako. Kasancewar na dade da haddace yahoo mail address din sa, wanda ba komi bane umargidadogembu@yahoo.com ne. 

Na fara da cewa;

“Ya Omar,

Daga zuciyar kanwa ma’abociyar nadama.

Ina fatan sako na ya same ka cikin amincin rayuwa. Idan hakan ya kasance, alhamdulillah.

Hakika duk abinda Allah ya tsara mana idan muka yi kyakkyawan duba a cikin sa sai muga cewa ubangiji na da kyakkyawar manufa na kasancewar sa yadda ya tsara shi. Na dauki al’amarin da ya faru dani a baya a matsayin hanyar da zata kai ni ga kyakkyawar rayuwa a gaba. Wato sai an bata ake samun sanadin gyarawa.

Ni Boddon ka, banida bakin da zan baka hakuri, idan sabida ni ka bar gida na roke ka don alfarmar zumunci ka dawo haka. Ka ji tausayin Abban mu. Ya Umar Boddon da, ba ita ce yanzu ba. Wallahi nayi hankali kuma na yi nadama.

A yanzu kam bani ba zaben miji sai wanda ubangiji ya ga dama ya zaba min.

Bani da wani buri a kan wancan tsohon burin nawa na baya, na dade da bashi baya ya zama Tarihin da ko son tunawa bana yi. 

Ka dawo haka Ya Omar don Allah ka ga irin cigaban da Boddon ka ta samu, ka cigaba da rayuwar ka yadda kake yin ta tare da Abban ka, (i stepped away to make Abba happy), tunda yace baya bukata ta in babu kai. 

Ka ji tausayin wannan Uba naka mai tsananin kaunar ka. Nima (i have found a new home and a new family) a gidan Young Abba, Abban ka na matukar bukatar ka. Ka taimakeni ka dawo Ya Omar don al’amuran rayuwa ta su daidaita, Abba yace bazai tafa farin ciki da ni ba sai ranar da ka dawo.

-Boddon ka mai rokon ka KA DAWO GIDA! KA DAWO GIDA!! KA DAWO GIDA!!!

Ina gama kammala rubutawa na duba nayi editing sannan na turawa Ya Faruq, ina fatan ko bai bani amsa ba to in samu ya ga sakon nan nawa. Na dade da burin aika masa sakonni ta mail Allah bai taba bani iko ba sai yau. Ko in ce ban samu nutsuwa ba a baya, kamar wadda nake ciki a yanzu.

80th Anniversary And End Of The Year Voa Party

A wani zangon karatu da ba zan manta ba da Young Abba yayi tafiya zuwa kasar Najeriya ne al’amarin ya afku. 

Daga ni sai Aunty da Ahyaan a gidan muna shan hutun karshen mako. Aunty ke gayamin gobe insha Allahu wato Lahadi suna da liyafar karshen shekara (End of the Year Party) nasu na iya ma’aikatan VOA tare da 80th Anniversary na VOA. Tace zamu tafi tare don zasu jima a wajen taron, bata son barin mu mu kadai, in ya so ko a mota ne mu zauna mu jira ta ta gama.

Washegarin ranar ina kokarin shiryawa da Doguwar riga wadda ita ce ‘casual wear’ din mu in zamu fita ni da Aunty, sai ko lullubin mayafi na rolling a wuya da saman kai da mayafin rigar duk da muka saka da muke yi, sai ga Aunty ta shigo daki na rike da kaya sababbi kar.

“We all have to wear our native attire today (yau duka kayan kasar mu zamu saka) sabida kowa shigar kasar su zai yi a wurin.

Ta mika min dinkakkiyar atamfa (Cote d Ivoire) ruwan zuma mai ratsin golden, wadda aka yi wa dinkin doguwar rigar fitted gown mai wani irin fasali da ya kayatar dani matuka tun kafin na saka kayan. Ko ina ta kai aka dinka mata oho. 

Na saka kayan data banin, kasancewar na dade rabo na da irin wannan dressing din sai na fito a wata kala dabam, hakika kala ta ce ta fulanin usli na Mambillah, wadanda suka samu zuzzurfan ilmin addini dana zamani, tamkar ‘yar tsana na koma don kyau. Aunty ta zauna akan stool da kanta ta gyara min fuska da serene make up kafin ta ce in shirya Ahyaan shima, zata je ta shirya ta dawo mu wuce.

Ina shirya Ahyan muna rera karatun Al’Qur ani nida shi kamar yadda na sabar masa. Har Aunty ta gama shiryawa cikin irin atamfa ta ta dawo rike da mayafin da yai dai-dai da zubin golden na jikin Atamfar ta miko min, ita kuma tayi amfani da ruwan zumar mayafi. Hannu na rike da Ahyan muka fito. Aunty ta bude mana motar muka shiga gaba ta ja motar a hankali muka dauki hanya.

Tunda Anti Nasara ta hau kan titin (330 Independence Avanue) inda nan ne babbar hedkwatar VOA dake cikin kwaryar birnin Washington D.C wato, Wilbur J. Cohen Federal Building, gabana ke wani irin mugun faduwa, yana lugude maras sassauci, maras kuma dalili. 

Haka kawai jiki na ke bani something weird will happen  (wani abu strange na shirin faruwa da ni a wajen nan), wanda zai juya duniya ta ta koma tamkar gare-gare abin wasan yara.

Abinda yafi kawai in kirkiri abinda zance da Anti zan koma gida a kan sa, don gujewa koma menene, sabida rawar da kafafuna ke yi da tsigar jiki na da ke tashi, amma na hanga na duba na rasa uzurin da zan bata na cewa mu koma gida, wai don kawai gabana na faduwa, domin wanna liyafar mai matukar muhimmanci ce a  garesu bakidayan su VOA family, domin ta hada da 80th Anniversary din VOA wato bikin cikar gidan talbijin da radiyo na muryar Amurka shekaru tamanin da kafuwa. Don haka gagarumin taro ne suka shirya wanda suka dade  basu yi irin sa ba.

A dakin taron da ake liyafar wato babban (conference hall)  na gidan talbijin da radio din VOA, ma’aikatan su ne zallah a ko’ina suna ta shige da fice don tabbatar da everything is in place kafin gama zuwan kowa, bakake da fararen fata, kowanne yayi shiga ta ainahin kasar da ya fito.

Kasancewar VOA suna broadcasting ne da 48 languages worldwide don haka ma’aikatan su sun fito ne daga kasashen duniya daban daban. Anti ta barni da Ahyaan ta shige ta nutse cikin staff  ‘yan uwan ta, an yi wa wajen decor iri-iri da tutar kasar Amurka da tambarin VOA (VOA Logo) mai kayatarwa da ban sha’awa.

 Liyafar, wadda sun shirya ta iya su ya su ne ‘VOA family’, wato shuwagabanni da ma’aikatan su kadai. Wuraren zaman kan su an kawata su yadda ya kamata, kowacce kujera like da sunan occupant din ta. An ajiye abin sha da fulawoyi iri iri da abuwawan motsa baki na alfarma a wasu wuraren har da (Barasa) ga masu bukata tun kafin liyafar ta fara.

Kafin kace meye wannan Anty Nasara ta bace min a cikin staff  ‘yan uwan ta, don seat dint a yana can ciki, mu kuma ta manta damu, sai na kama hannun Ahyan muka nufi can wani gefe da babu wadatar mutane muka zauna akan wata farar kujera mai farin tebir a gaban ta muna  fuskantar abubuwan da ke faruwa a dakin  taron daga inda muke zaune, amma hakanan gabana bai bar faduwar da yake tayi tun dosowar mu wurin ba.

Sun fara gabatar da shirye-shiryen taron kamar yadda suka tsara, ina jin komai amma bana fahimtar komai, sakamakon hankali na da baya jiki na. Ya tafi bakidaya ga amsar sababbin sakonnin dana ke ji a cikin jiki na.

A cikin tsare- tsaren su akwai karrama wasu daga cikin manyan hazikan ma’aikatan su da zasu gabatar duka a wannan ranar. Daga inda nake zaune ina ganin duk abinda ke wakana duk da cewa na kasa sakin jiki na a wurin, sakamakon rashin sabo da shiga manyan tarukan yan boko irin wadannan da kuma tashin da tsigar jiki na ke ta faman yi ta ko’ina.

Da dan adam ya hada sani da Allah da ko kusa ban yarda na na biyo Nasara VOA ba,  tun sanda na samu weird feelings dinnan a tare da ni. Da na nemi uzurin dana bata ta baro ni a gida kamar yadda zuciyata ta shawarce ni a farko. Amma da dan adam bai hada sani da Alla ba, kuma gudun kaddara guzurin tadda ita ne, sai ban isa in tsallakewa abinda Ubangiji ya shirya a kai na tun halitta ta ba.

*****

KARSHEN TIKA-TIKA!

Ya shigo Hall din da takun sa na sassarfa kamar koyaushe, haka nan yake takun sa gab-gab na karfafan maza, bayan ya yi wa motar sa parking ba dai-dai ba, kasancewar yana cikin saurin ya makara sosai. Wani dogon mutum, siriri, baki ma’abocin ingarman jiki.

Sanye cikin shadda Wagambari babbar kalar Army-Green, ya yi shiga ta cikakkun Black-Africans (Nigerians) wadda ta boye zahirin kamannin kabilar da ya fito daga cikin ta. Ta bashi suffar cikakken dan Arewacin Najeriya. Kai tsaye bazaka ce ga kabilar sa ba illa ka kira shi cikakken dan Najeriya. Baki dogo haka siriri, don tsayi har ya dan rankwafa, mai cikar gargasa a fuska da saman giran idon sa, mai fadin kirjin da ake yiwa lakabi da physique chest, ya sanya kwayar idanun shi cikin farin gilashi mai kara karfin gani kamar koyaushe zaka ganshi like da wannan gilashin a cikakkiyar fuskar sa, mai cike da gargasa da sassanyan kyau, mai dauke da siririn dogon karan hanci da idanu masu shape din Almond. 

A kafar sa takalmi ne sau ciki samfurin Ferfetch  (army – green), agogon dake daure a damtsen hannun sa na danyar azurfa ya nitse  cikin gargasar dake kwance saman fatar hannun sa shima Ferfetch ne mai zaman kan sa. Mutum ne ma’abocin iya dressing mai shiga zuciya da daukar idanu da bazaka so ka yi masa kallo daya baka maimaita ba.

Ta gaba na ya wuce da wata irin classy tafiyar shi ta sassarfa, yadda yake da sassarfar magana haka yake da sassarfar tafiya a zahiri, kai tsaye ya wuce zuwa high table, bayan ya barbade ni da kamshin turaren sa mai tsinka zuciyar duk wanda ya shaqe shi; SAUVAGE (By Dior) irin turaren dana tabbatar irin na Young Abba ne sak.

Saurin da yake yi yana da alaqa da kiran sunan sa da ake ta yi akai-akai ba kakkautawa a lasifika, wanda amon sunan ya karade ko’ina na hall din, camerori a kan sa tun shigowar sa, baka jin komai sai tashin sunansa daga bakin MC na taron …..HAMZAH ALMUSTAPHA MAWONMASE…… ‘Best VOA RADIO Broadcaster of the Year’. (Wannan shine award din da gidan Talbijin da Radio na VOA suka bashi).

Ya daga medal din sama ya jijjiga sannan ya yi jinjinar ban girma ga masoyan sa na duniya da gidan rediyo da talbijin na VOA bakidaya.

Kafin kuma a lika masa abin maganar a jikin rigar sa ya soma karanto “History of VOA…..cikin tsararren turancin sa mai amo (audible) mara gundurar kunnen mai saurare; shekarar da aka kafa ta, nasarorin ta da kalubalen da suka sha gamuwa dasu, kafin su kawo wannan matakin na madaukakiyar nasara, daga lokacin da aka kafa VOA a kasar Amurka  zuwa yanzu.

Wani abu tamkar ‘ignition’ ko kuwa chemistry din gravity ke bin ilahirin jiki na lungu da sako yana kassara ni, yana tono tsofaffin feelings tare matattun emotions na shekaru goma yana dawo dasu baya filla-filla kamar ana rewinding casette yana sake bankado su fili yana sabunta su ta hanyar sake refreshing din su, wadanda aka yi amfani da karfi (force) wajen binne su a kasan ruhi ba don sun mutu ba….. Lokacin dana daga ido ina kallon Hamzah Almustapha yau a gaba na……  Not in dream, not in radio, not in TV and not in imaginations….!!!

Amma abu daya ke amsa kuwwa a kwanya ta a wannan lokacin yana maimaita kan sa tamkar a lokacin “Nasara Alkali” ke sake fada mun shi da kakkausar murya dai-dai inda take cewa; Hamzah Al-Mustapha na gidan Radiyon VOA ba musulmi bane   Christian ne mai bin addinin Christianity.

Wato a yau na yarda ita soyayya ta gaskiya in dai ta hakika ce bata taba mutuwa bakidaya daga zuciyar diya mace no matter how bitter the experiences kuma komin tsufa ko gushewar shekaru, ko canjin da zamani ya kawo, sai dai ta suma ko ta shide na lokaci mai tsaho, musamman idan wannan soyayyar bata samu yayyafi ko martani daga wanda take son ba. Sai ko idan bata ga abin son nata ba ko jin muryar sa…..Amma bata taba gushewa daga zuciyar mace gabadaya.

Yau dai gani ga DREAM HUSBAND dina (in physical reality) a birnin Washington D.C din Amurka. A wani waje da ban taba mafarkin zuwa ba banda cikin Radio da talbijin dina. Wanda ke nufin kaddara ta da shi yanzu ta fara cakuda da ‘yar uwar ta, wata kaddarar ma ba’a soma ta ba tukunna, ban kuma san farkon ta balle karshen ta ba.

Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine Addinin sa, wanda shi yake haska ma dan adam komai na rayuwar duniya ya yi shi da kyau. Ya kuma banbanta tsakanin sa da dabba. Shi kam Hamzah na da ababe da yawa da mace zata so shi a kan su, kyawun surar sa ya shahara, duk da cewa appearance din sa kawai na sani ba inner self din shi ba. Amma kash! Bana son tuna kalmar nan ta BA MUSULMI BANE!

Zan fi yarda in Anti Nasara ta fada ne don ta tsokane ni, ko ta samu hanyar raba ni da emotions din sa cikin sauki a lokacin da take ganin bai dace ba. Ta ina za’ace wannan perfect handsome gentleman ba musulmi bane?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 19Sakacin Waye? 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×