Skip to content
Part 21 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

A fili na shiga furta.

“Aamantu Billahi Rabba! Wa bil Islama Deena!! Wa bi Muhammadur-rasulullahi SAW Nabiyyan wa Rasoula!!!”. 

Na jaddada imani na da addini na, da imanin dana yi da shi a kan harshe na da zuciya ta. Kada imani na yayi rauni a kan sa. Nima a saka ni a jerin masu RIDDAH. Na sake maimaitawa a fili don dai in samu wannan mushriki ya daina burge ni. Ya daina samun tasiri komai kankantar sa a tare da ni. Na yi amanna da cewa an halicci zuciya ta ne tare da kaunar sa, tunda ban taba sanin wanene shi ba, ban kuma taba ganin sa ba a zahiri sai yau. Balle a ce wani abu nasa ne ya dauki hankali na.

Ban kara sanin abinda ke faruwa a wajen ba face  sunkuyawa da na yi a kasan tebirin dana ke zaune cikin wani yanayi na sarkewar numfashi, kamar mai fama da ciwon Asthma, kwatankwacin irin shidewar dana yi a gaban Abba rana ta farko dana fara jin muryar sa a Rediyon Abban. 

Banbancin wancan karon da yanzu shine this time around ban fadi warwas kasa ba. A zaune nake dirshan a kan kujera ta. Because i learned to be stronger. Yau gani ga HAMZAH ALMUSTAPHA MAWONMASE in reality na kuma tabbata yanzu ne kaddara ta da shi zata fara aiki, yanzu ne komai zai fara warware kan sa… ya bada ma’anar mafarkai na a kan sa.

Wannan haduwar itace mafarin komai da ya faru tsakani na da shi. Farkon haduwar kaddarorin mu wuri guda…Tunda na baya komai ya zo min in dream and  in imagination ne. Jiki na na bani wannan haduwar bata nufin komai, face sharar fage ga tabbatuwar mafarkaina na shekaru masu yawa a kan sa……

Ban yarda wai ni kadai nake koshin wahalar nan ba, ban yarda ni kadai nake soyayya a cikin mafarkin sa ba…. Amma komai ya faru da ni a yau ni na jawo, tunda ni nayi SAKACIN tako kafafu na na zo har inda yake…..!!!

FIRST ENCOUNTER (HADUWAR FARKO)

Na dauki lokaci mai tsayi a haka a inda nake, kai na sunkuye akan tebir bayan wucewar sa ta gaba na da barbadeni da yayi da kamshin sa na turaren Sauvage (By Dior), in ka ganni a wannan lokacin tamkar wadda ta farfado daga maye, ko kuwa wadda ta farfado daga shidewar wucin gadi  sabida yadda nake kokawa da numfashi na a tsakiyar kirji na. Idanuwa na bakidaya sun rufe kan su ruf. Sun kasa budewa don tsoron yi masa kallo na biyu, sabida raunin da suka samu da ganin sa yasa bazasu jure abinda ke karakaina a zuciyar ba. Kada in je su nakasa a dalilin shaukin ganin abinda suka kwadaitu da gani shekara da shekaru daga mafarki zuwa ido biyu. 

Zuciyar kadai ke racing a cikin kirji na kamar doki a filin Polo. A karshe na yanke shawarar barin wajen kafin sense of presence din sa da yayi overlwhelming dina har haka yayi sanadin karasar da dan ragowar karfin zuciyar da na mallaka da ragowar numfashi na.

Na amince a baya cewa I’m now stronger and more powerful over my feelings, to why all these? Wannan rudun dana shiga daga ina ya samo asali? Bai kamata in bari ganin sa na zahiri yau ya karya wannan karfin zuciyar dana dade da mallaka ba.

I will continue to be stronger and fight my meaningless emotions a kan Mawonmase, kamar yadda Uwa ta Nasara ta koyar da ni. Don haka barin wajen shi ya fi min alkhairi da amfani. Don haka na mike cikin jan kafa na doshi hanyar fita.

Ko ganin abinda ke gabana bana yi a haka na fito daga conference hall din, da sauri – sauri gudu-gudu, na manta shaf da dan kani na Ahyan da uwar sa ta bani rikon sa, shi kuwa sai faman bina yake inda duk na jefa kafa ta yana kuka yana kiran suna na ganin na tafi na bar shi. Ahyan cewa yake “Aunty Siyama ki tsaya ni!”

Bai san cewa Antin sa Boddo-Siyama ta kurumce ta kuma makance a wannan dan tsakanin ba, don kuwa ko juyowa in kama hannun shi ban yi ba, na cigaba da tafiya don kunnuwa na bakidaya sun toshe da kururuwar sunan “Hamzah…..” wanda har zuwa lokacin da na baro hall din, bai bar yi min amsa kuwwa a kunne na ba kamar yanzu MC na taron ke sake maimaitawa…. “HAMZAH ALMUSTAPHA MAWONMASE! Best VOA Radio Broadcaster of the Year!”. 

Ban tsaya a ko’ina ba sai a jikin motar Anti Nasara. Ina fadi a raina bari in tuka kaina in bar wurin. Taimakon da Allah ya yi min shine mukullin motar yana hannu na don tun shigar mu ta riga ta bani, na bude mazaunin direba na shige na zauna a mazaunin Anti, da fatan yau zan tuka mota da kaina kota halin ka-ka domin in nesanta kai na da Hamzahn mafarki na, Hamzan dana dade ina burin bayyanar sa da son in gan shi a fili, ko na daina jiran tsammanin warabbuka.

Yau gashi ya bayyana a gaba na in physical reality, amma gashi jiki na, idanu na da zuciya ta sun kasa daukar nauyin ganin nasa, neman mafaka suke helter-skelter, don tsira da addini na da lafiyar zuciya ta, sai kawai na kifa kai a kan sityari ina maida numfashi. 

Daga bisani kuma na lumshe idanu na da sukai min min nauyi da wani irin yaji-yaji, na kuma zuki dogon numfashi na fesar a hankali cikin fatan samun sassauci daga dimaucewa ta. 

A lokacin na tuna ban iya tukin motar bama, balle na tuka na tafi gida na bar Anti a wurin. 

Ban taba dakacen rashin iya tukin mota ba sai yau. A can baya ban taba gwadawa bane sabida bana tunanin watarana zan yi, sabida tsabar tsoron accident da Allah yayi ni da shi, amma ashe komai daurowa take yi, yau naji a rai na zan tuka mota anyhow ko na iya ko ban iya ba, domin in samu in nesanta kaina da shi a reality, kamar yadda na samu na nesanta kaina da mafarkan sa, imaginations, emotions da infatuations din da suka zama abokan rayuwa ta a baya da taimakon Allah da karfin Al-qur’ani da support din Uwa tagari irin Nasara Alkali. Life is perfectly okay for me now bana maraba da duk abinda zai dagula ta, ina jin dadin rayuwa ta fiye da baya domin na fi samun kwanciyar hankali da gamsuwa a cikin ta, ina tafiyar da rayuwa ta dai-dai wa daidai babu tunanin sa babu mafarkan sa, babu komai, babu kowa a cikin ta sai abinda ke gaba na wato neman ilmi, don haka zan iya cewa HAMZAH YA ZO A LOKACIN DA NA RIGA NA HAKURA DA SHI, wato ya zo at a very wrong time. A kurarren lokaci.

Lokacin da bana bukatar duk abinda zai maida ni situation dina na baya. Lokacin da rayuwa ta ta samu daidaito. So I must run-away from him.

Ni na san babu alkhairi a cikin haduwa ta da shi (in person) sai fami ga wani tsohon warkakken gyambo. Wanda kuma bazai kare ni da komai ba a bisa ma’auni na hankali da tunani. Sai da na murza mukullin na lura da Ahyan dake gefe na daga waje wanda yaci kuka har ya gode Allah, sakamakon gudun da ya sha a kokarin sa na kamo ni kada in bace masa a dalilin saurin dana dinga yi daga hall din zuwa parking lot. Na bude masa kofa ya shigo da saurin sa har yana ajiyar zuciya ya kwakume ni. 

Zuciya ta ta karye ta tausayin sa, tana gaya mini kada in kuskura in yi gangancin tukin nan da na san ban iya ba, sabida wannan yaro da bai ji ba bai gani ba rayuwar sa amana ce a hannnu na, Dan da yake tamkar tsoka daya a miya kuma sanyin idaniya ga iyayen sa Adamu da Nasara. Dan da kafin su same shi sai da suka barar da dukiya mai yawa cikin jelen asibitoci ba dare ba rana tsayin shekaru shidda suna zarya gaban tebirin likita don neman samun haihuwar sa. 

Ba zasu taba yafe min ba idan na salwantar musu da rayuwar Da sabida dimaucewa da rudewar ganin wani DREAM HUSBAND IN REALITY, wanda ni kadai ta shafa da natacciyar zuciya ta mara mafadi. Duk da gaskiyar da Anty ta dade da gaya mini na lura ba abinda ya canza a masifaffen son da zuciyata ke masa. Komai lafawa yayi, komai raguwa ya yi albarkacin kama addini da nayi ka’in da na’in.

Jiki na yayi mugun sanyi ganin Ahyan yana kuka, iyayen sa basu saba yin biris da shi irin yadda na yi yau ba, shi dan lele ne ba na wasa ba a wurin iyayen sa, na kashe motar dana kunna na fasa tukin gangancin dana yi niyya. Na janyo shi jiki na na rungume shi sosai ina jijjiga shi cikin tausayin mu mu duka biyun, ba don mun zama marayu ba ko don mun rasa wani namu sai don cewa dukkan mu kafadar da zamu jingina a kai ko mu kwanta mu yi kuka a lallashe mu muke nema a daidai wannan lokacin, da wanda zai kara mana hope a rayuwa. 

Anti ce kawai zata iya rarrashin mu kuma tana can cikin harka kace-kace da abokan aikin ta bata da lokacin mu a yanzu. Ina gayawa kai na ba zan koma ciki ba ko da Anty Nasara zata kwana bata fito ba, zan jira ta a nan har ta gama mu koma gida. 

Sake gani na da shi ba zai haifar da Da mai ido ba. Sai na bude kofar bangaren da Ahyan yake yadda zamu shaki wadatacciyar iska sosai na dafe hannaye na a kan sityari. 

Sai a lokacin ne na fara nutsuwa, na koma hayyaci na, sai na lura ko da nayi kokarin tuka motar, to bazan iya fita ba, sakamakon an yi blocking bayan mu da wata tsaleliyar mota kirar zamani “GMC Terrain” baka wuluk da ita sai sheki da numafashi take yi, mota ce kirar jiya-jiya daga shahararren kamfanin (General Motors) dinnan na Amurka, an ajiye ta da wani irin wawan parking da yayi matukar karya doka. Wanda da gani zaka san cikin rashin nutsuwa mai motar ya yi shi.

Ko wane mahalukin ne da wannan parking din haka! Ni kadai nake ta sakin tsaki da korafi har ma da son in yi zagi, a kokari na na korewa kai na halin dimuwa (gigita) dana shiga na ganin Hamzah Mawonmase (in reality), na shiga kokarin maida nutsuwa ta da ganin ‘Dream Husband’ a fili na zahiri ya raba ni da ita bakidaya. Maimakon hakan, sai na maida kai ga jin haushin mai banzan parking din da ya tokare mu, na shiga jiran fitowar sa in yi “huce kan dami” a kan sa. 

Daidai lokacin da na hango Aunty tana tahowa gare mu tare da wata mace gajeriya kabila ga dukkan alamu abokiyar aikin ta ce, suna tafe suna magana har suka karaso gaban mu Aunty na cewa.

“Sorry Siyama, ina ta neman ku a ciki, ashe nan kuka dawo”. Ta fada tana shafa kan dan ta, tana tambayar sa abinda yasa shi kuka, kafin ta dubi wadda suke tare ta ce “Ga nan colleague dina aunty Joy, ku gaisa Siyama”. Cikin kokarin maida walwala ta hadi da farfado da gusashshen murmushi a kan fuskata, na gaida wadda aunty Nasara ta kira da suna Joy. Aunty Joy din ta ce “Mrs Alkali, (sunan da suke kiran Aunty da shi kenan) ina kika samo wannan kyakkyawar budurwa haka son kowa kin wanda ya san ba zai samu ba?”

Nasara tayi dariya, domin ran ta dadi yake yi a duk lokacin da wani ya yabi kyawun halitta ta musamman in ya alaqanta kamanni na da kama da mijin ta, ita kanta ta san mu din da duk zuri’ar mu masu kyau ne, wanda da ace don kyau a ke aure da Adamu Dalhatu Gembu bai zabe ta ba, sabida ita komai nata na hausawa ne, ta ce. 

“Diyar maigida na ce da na gaya miki ina riko daga Mambillah”.

Joy ta ce. “No wonder na gan ta fara sol ga hanci har baka kamar Baban Ahyan. In zaki bani, ina yi wa Jacob kamu” (Jacob din kanin aunty Joy ne da take riko anan kasar). Aunty ta yi dariya ta ce “wannan “Mari ce Babban KIFI”, sai babban KIFI watau “SHARK” kadai zan baiwa auren ta (sai mai gida da mota)”. Suka kyalkyale da dariya kafin suka yi sallama da Joy cikin tsokanar juna, tana cewa “kawai Nasara ki ce auren jari zaki yi da ‘yar ki, uwar zamani Nasara mai idon cin naira”, Aunty tace “na ji din, wa ya ki Naira da akwatunan lefe dozen? Ai sai wanda bai haifi Mari babban kifi irin tawa ‘yar ba”.

Nasara na kokarin shiga motar ta, bayan sun gama barkwancin su da kawar ta, sai ta lura da yadda ‘GMC Terrain’ dinnan tayi blocking din mu ta baya.  A fili ta ce “subhanallah”, sannan ta kwalawa kawar ta Joy kira wadda har ta juya ta tafi zata shiga tata motar tace, “Aunty Joy, motar wane dan rainin wayon ne wannan haka? Haka kawai zai bata mana lokaci ga maghriba ta kawo jiki zamu je gida mu yi sallah”. 

Joy ta dawo itama sai lokacin ta lura, tace “ku yi hankuri ku dan jira su, yanzun duk zasu fito ai, (it’s already 6pm closing time). Na fi kyautata zaton motar HAMZAH MAWONMASE ne, koda yake su biyu ke da irin wannan motar shi da Director Philip Carter”. 

Ina kallon yadda Aunty Nasara tayi maza ta kalle ni. Ko me ta tuna a lokacin? Ko meye dalilin kallon hanzarin data yi min? Hakika ta tuno wani abu, ta manta shaf inada tsohon scenario a kan Hamzah Mawonmase da bazata kawo ni VOA ba. 

Tayi maza ta dauke ido daga duba na ganin na kafe ta da nawa idanun, cikin kallon tuhuma mai tsanani, kamar ina tuhumar ta da jajayen idanu na kan cewa; “don me kika kawo ni na gan sa? Bayan kin taimaka min na manta da komai nasa? Kin yi nasarar raba ni da ‘infatuations’ dinsa?”. 

Cikin basarwa mai yawa Aunty Nasara tace “Siyama ina ganin mu koma daga ciki mu samu toilet mu yi alwallah mu yi sallah, dole mu jira sai an dauke motar nan tukunna”.

(Ni na san Aunty Nasara ta kalle ni da hanzari ne a lokacin don taga irin reaction dina, sakamakon ambatar sunan “Hamzah Almustapha” da kawar ta Joy ta yi a gaban ido na kuma cikin kunne na, aka kuma tabbatar min da cewa yana wajen taron nan. Ta hakan ne zata fahimci shin har yanzu yana nan makale a raina, har bayan tsayin shekarun nan, ko kuwa tayi nasarar cire min shi completely na huta ma kaina da infatuations din sa? Daga ranar data bayyana min cewa Hamzah Almustapha Mawonmase ba Musulmi bane Christian ne?).  

Sai dai kuma bata yi nasarar ganin komai a fuska ta ba wanda zai bata labarin abinda ke zuciya ta, kasancewar na sha mata mur, na daure fuska tamau domin haushin ta da nake ji ba dan kadan bane.

“Anti ba inda zan koma fa!” Na yi mata musun komawar data ce muyi cikin hall cikin gardama da gardandami ga rikici fal idanu na, a kasan rai na ina mai rokon Ubangiji kada ya sa na kara tozali da wannan bawa nasa daganan har gaban abada. Bayan a can baya addu’a ta kullum itace ta bayyanar sa a fili, ba don komai ba sai don saboda illolin da ganin sa ya haifar mun a zuciya, da ruhi har ma da gangar jiki na, na fami ga warkakken ciwo, da ya riga ya yi healing tun da jimawa. 

A yau ganin sa physically ya sa har ina neman shidewa. 

(Ashe na yi gudun gara…. na tadda zago ne a kan kin komawa hall) duk yadda Aunty Nasara ta yi ta fama da ni a kan hakan. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 20Sakacin Waye? 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×