Kafin Anti ta samu bakin kokawa na mamakin gardamar dana ke yi mata yau, Joy ma ta samu wucewa zuwa tata motar sai gashi nan ya fito daga hall din, cikin takun sassarfa na irin gait din sa (salon tafiyar sa), ga tsayi ga fadin kirji, ga wata extraordinary charisma a tare da shi, kai tsaye inda motar sa take ya durfafo yana tafe yana waya da harshen turancin sa mai amo (audible) da tsabtar (good pronounciation) kai ka yi tsammanin ‘Charles Dickens’ ne ya duro Najeriya.
Da sauri na bude motar mu na shige ciki, tun kafin ya karaso. . .