Skip to content
Part 22 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Kafin Anti ta samu bakin kokawa na mamakin gardamar dana ke yi mata yau, Joy ma ta samu wucewa zuwa tata motar sai gashi nan ya fito daga hall din, cikin takun sassarfa na irin gait din sa (salon tafiyar sa), ga tsayi ga fadin kirji, ga wata extraordinary charisma a tare da shi, kai tsaye inda motar sa take ya durfafo yana tafe yana waya da harshen turancin sa mai amo (audible) da tsabtar (good pronounciation) kai ka yi tsammanin ‘Charles Dickens’ ne ya duro Najeriya.

Da sauri na bude motar mu na shige ciki, tun kafin ya karaso inda muke, har ina tuntube da kofar motar saura kadan in ci da baka kamar mara gaskiya. Sakamakon haduwar da kwayan idanun mu suka yi, wadanda suka wani irin sarke miraculously, koko in ce unexpectedly domin hakan ya faru ne ba zato na babu tsammani. Na hangi wasu irin Almond-Shaped Eyes ta cikin farin siririn gilashin kara karfin gani da ke sanye a idon sa, wadanda sun fi kyau a zahiri sun kuma fi haske da daukar ido fiye da a hoto da kuma talbijin. 

Kasancewar kofar Hall din nake fuskanta lokacin da ya durkako inda muke, shi yasa kwayar idanun mu suka hade yana dosowa. Dole in fara neman tsari da wannan Hamzah, domin al’amarin sa da ni wanda ke faruwa bi da bi in an array kamar an tsara ya fara shallake dan kankanin tunani na. 

Ko kafin in shige motar mu kwayan idanun mu sun riga sun hadu. Na yi kokarin janye nawa kwayan idon amma sai naji tamkar magnet ya rike ta, na kasa dauke ido a kansa na lokaci mai tsaho, haka shima. 

Ina kallon yadda ya dan ja birki da tafiyar tasa, kafin kuma ya cigaba da tahowa amma wannan karon ya rage sauri. 

Hasken fitilun wajen masu kama da tsakar rana suka haska min Hamzah tar-tar, at the same time suka haskewa Hamzah Almustapha Mawonmase fuskar wannan bafullatanar halitta da ta sha bambam da sauran halittun matan da ke gilmawa a wurin, ga kuruciya ga kamewa, ta nuna cikakkar Fulben Mambillah Plateau, kuma dressing din ta duk da cewa ‘Nigerian Attire’ ne lullubin da ta yi ya nuna symbol na addinin ta da al’adar da ta fito. 

Mr. Hamzah was like; look at that familiar look in that innocent Muslim girl’s eyes, she’s looking at me with utmost familiarity, kamar ta sanni a wani wuri…. somewhere far away da ita kadai ta sani! 

Kallon da ke cikin idanun ta ba na yau bane, bi ma’ana, na kakkarfar sanayya ne. Amma a iyaka tsinkayen sa na ‘yan dakikai, shi dai bai iya gaskata ko tsinkayar inda ya santa ko ya taba ganin kyakkyawar fuskar ta ba. 

Hasken fatar ta, wanda bai yi kama dana turawa ba ko Asians ko Arabs ko kadan, haka bata yi kama da wadda suke tare ba wato, Nasara Alkali, wadda da ganin ta babu tambaya ita ka san bahaushiya ce. Tsayuwar karan hancin ta mai tsini kamar an dasa mata shi da hasken idanun ta shine ya rike maganadisun idanun sa a kan ta. 

Kafin kuma ya ankara ta janye idanun ta da karfin gaske daga kallon kudar da suke yi wa juna, bayan ta kare masa kallon tsaf, ta shige mota da saurin gaske har tana tuntube saura kadan ta fadi, ta rufe kofar da mugun karfi ji kake bamm!. Bayan ta sakar masa wata muguwar harara tamkar fararen kwayar idanunta zasa fado kasa a soya su cikin mai.

Already a lokacin ya iso inda muke. Ba shi kadai yayi mamakin yadda na rufe kofar motar ba kamar zan balla ta daga Anti Nasara har Ahyan zuwa Joy sun firgita. Aunty ta bi ni da kallo na mamaki da ayar tambaya tana cewa “wane irin abu ne haka?”. 

Ya karaso yana ta apologizing, bisa bata lokacin da ya jawo mana, tamkar ya durkusawa Anty Nasara don bada hakuri. Bayan kuma he’s her senior in age and at work (wato yana sama da ita a aiki da kuma shekaru) nesa ba kusa ba.  Wannan abu yayi matukar impressing Nasara.

Har sai da Aunty ta ji kunya ta hadiye duk wani bacin ran ta da fushin ta na bata mata lokacin da yayi tace “babu komai Mr. Hamzah, all is well”. Yace “suna ta kira na a loudspeaker kamar zasu karar da suna na, gashi kuma na makara, shiyasa nayi parking a rude. I’m very sorry”. Hausar bakin sa ras, kamar ta Bakanon da ya je Zamfara yayi shekara ashirin. ‘Yar kankanuwar In’inar ta kawata accent din sa sosai. 

Daga bayan mota da nake zaune ina jin su shi da Aunty suna magana akan wani abu da ya shafi aikin su, kamar wata tafiya ce zasu yi zuwa kasar Russia don dauko rahoton yakin nuclear da ake yi a can tare da Team din ofishin sa. 

A karshe suka yi sallama ya shiga motar sa, har ya kunna zai tafi sai ya hango Ahyaan a gaban motar Anti, yana waving dinsa da hannayen sa yana kuma yashe masa ‘yan kananan hakoran sa yiri-yiri masu kyau, yayin da ni nake zaune daga gidan baya.

Fitowa yayi ya fasa jan motar ya karaso barin da Ahyan yake, kasancewar tagar motar a sauke take. Hannu ya daga masa admirigly ya ce “Hi, Prince. Hi Little Angel. I’m Uncle Hamzah. Yaya sunan ka?” 

“Cuna na Ahyan Adam”.

Ahyan ya bashi amsa da ‘yar siririyar muryar sa. Cike da kaunar kyakkyawan yaron very jovial da shi abin alfaharin kowacce Uwa ya mika masa hannu suka yi musabiha, ya dan rike hannun Ahyan din cikin nasa ya ki saki, yana kallo na daga inda nake zaune a kujerar baya da kallon sanyin rai saboda ya san ya bata mana, yayin da nayi mugun sunkuyar da kai kamar baiwar da ta yi wa sarki karya. Bayan na zabga masa harara. Amma fa zuciya na harbawa.

The way yarinyar take acting take kuma behaving kamar ta dade da sanin sa farin sani, a cikin idanun ta akwai tarin sanayya, kamar ta san komai da ya shafe shi ba tun yau ba, kamar kuma tana fushi da shi mai tsanani, kamar bata so ta bude ido ta gan shi a gaban ta, abin ya matukar bashi mamaki, don dai shi ya san ko a hanya bai santa ba amma ya san wadda suke tare, bai kula ta ba. Ya dai sake kallon ta ta cikin gilashin sa. Kafin ya juya gun Nasara.

Suka cigaba da magana da Aunty a kan tafiya  zuwa Russia a sati mai kamawa, rokon sa take ya taimaka mata a cire ta cikin tafiyar a saka Joy Bakasa Yakubu madadin ta, sabida maigidan ta zai dawo daga tafiya a satin, bata so ya dawo bata nan. 

Abinda ya ce da Nasara shine baya jin hakan mai yuwuwa ne domin ya riga ya saka sunan ta cikin Team din da zasu yi tafiyar, kuma dai ta san muhimmancin dauko rahoton yakin nuclear a yanzu, it will be a great opportunity for her idan ta daure ta je suka kawo rahoton da zai burge VOA abu ne da zai iya kaita ga promotion. A haka suka yi sallama. 

Ya janye motar sa a hankali cikin tukin nutsuwa ya bata hanya. Itama ta ja motar mu ta wuce, ta karkato mudubin motar yadda zata ke hango fuska ta sosai tana cewa.

“Siyama are you alright? Irin wannan rufe kofa haka kamar kin ga mala’ikan daukar rai?”

Ta fadi hakan bayan ta karkato da mudubin gaban motar zuwa fuskata, yadda zata ji dadin gano ni sosai, alhalin tana tuki amma gulma na cin ta. Da murmushi tace,

“I hope yau kin gan shi ko? And there’s nothing special a cikin ganin nasa! Your  Radio Presenter. He’s that Mr. Hamzah, Hamzah Almustapha Mawonmase ne”.

“Umh!” Kawai nace ma Aunty Nasara. Don tabbas bani da amsar bata. Da ta san halin da nake ciki a zuci, ruhi da gangar jiki na da bata maimaita min wanene shi ba.

Eh, kwarai na gan shi yau kam, kuma hakika GANIN SA YA FI JIN SA!!! Ganin sa ya fi jin muryar sa a radio da ganin sa a hoton talbijin tasiri a tare da ni da saka ni cikin rashin nutsuwa da kaka-ni kayi.  

Abinda Aunty Nasara bata sani ba shine; the more naji sunan a kunne na, the more zuciya ta ke sake karbar sa, tare da yi masa masauki na musamman da shimfidar manyan kilisai a cikin ta. 

The more wani yayi kuskuren ambatar sunan a kunne na, the more nake kara zamowa highly infatuated a kan sa. Ya ke kuma kara yin kane – kane a zuciya ta. Musamman a wannan gabar ta rayuwa ta da na ke cikin shekaru ashirin da uku, a gabar da babu abinda yayi min saura rayuwa sai Da namiji a gefe na, wanda zan kira miji na mallaki na by my side, ni kadai. Wanda zai tarairaye ni in tarairaye sa cikin kauna da soyayyar dana ke mafarki. Mu kwana tare mu kuma tashi tare cikin mayafi guda a matsayin miji da mata. 

Kuma duk duniya na hanga, na duba ban ga wanda ya dace da wannan matsayin ba sai shi kadai. Unfortunately an ce shi din BA MUSULMI BANE!!!

Banda kaddara da sharri irin na zuciya me ya kai ni? Me ya kai ni sanya mushriki a kasan rai na har hakan ya zame min damuwa? Me zan yi da wanda ya kafurta? Me ya kai ni son wanda bai yarda da cewa Allah SWA guda daya ne ba?

Sai dai ni da kaina na san, da can da yanzu akwai banbanci. Ratar da ke a tsakani mai matukar girma da fadi ce. Banbancin da ke tsakanin da da yanzu shine; yanzu ina iya controlling emotions dina in gaya musu gaskiya sabanin da; lokacin da emotions din ke juya ni suna tuka ni yadda duk suke so, suna gaya min cewa, a duk yadda ya bayyana ina son sa haka, kuma a haka zan aure shi. I can now fight my feelings for him because i’m stronger than before. A yanzu ina iya banbance dai – dai da ba dai-dai ba, ina iya banbance abinda zai yiwu, da wanda bazai yiwu ba, a addinance da al’adan ce. Har ila yau, a yanzu ina iya gayawa zuciyata tsantsar gaskiya komai dacin ta; a koyaushe ina gayawa kaina cewa matsayin sa da nawa ba iri daya bane a wurin Allah. Ba shi da amfani cikin rayuwa ta tunda bai yarda Allah daya ne ba….

Duk abinda ya same ni yau, duk rudu, dimuwa  da kidimar dana shiga yau Aunty Nasara ce ta jawo min tunda ita ta jawo ni zuwa inda yake, alhalin ta san yakin data sha da ni kafin ta yi nasarar raba ni da imaginations din sa. Shiyasa har muka iso gida uffan ban ce mata ba.

Haushin ta nake ji sosai, haushi biyu ya tarar min, haushin Hamza bai kula ni ba, wanda ke nufin bai sanni ba, ni kadai na sha wahalar dreams and infatuations dina. Tunani na cewa we are sharing the same dreams and emotions ya bayyana karya. I’m the only one that occupies the feelings. 

Haushi na na biyu haushin Anty Nasara ne data yi min silar zuwa inda yake.  Don haka ita kadai take surutun ta har muka iso gida don Ahyan ya yi barci. Da ta gane i’m not in the mood na son yin magana dole ta rabu dani ta hakura tayi shiru itama har muka isa gida bata kara kula ni ba.

      “THE CHRONICLES OF A BEROM MAN” 

Tafe yake a kan hanyar sa ta komawa gidan sa dake cikin rukunin gidajen ‘Cielo Apartments’ a cikin kwaryar birnin Washigton D.C. Sautin tsohon mawakin Hausan nan ya kure a motar, a cikin wani baiti da marigayi Dr. Mamman Shata ke cewa;

“A rayuwar duniya kowa da kaddarar sa….”

Yana ji amma baya iya bin wakar yau kamar yadda ya saba duk da son da yakewa wakokin marigayin. Sakamakon zuciyar sa data yi nauyi da tunane-tunane. Amma a can cikin kwakwalwar sa yana gasgata kowacce kalma dake fita daga bakin marigayin mawakin, lallai ne a rayuwa kowa da irin kaddarar sa. Tasa kaddarar rayuwar kenan.

A lokacin ne wani abu ya gilma masa tamkar a majigi, hoton fuskar Bafullatanar yarinyar da ke tsaye jikin mota Acura ta soma yi masa gizo, tamkar wani shafi na shifcin gizo cikin idanun sa. Babban abinda ya sa shi tuno ta shine; Kallon fushin babu gaira babu dalilin da take masa, kallon sanayyar da ke cikin idanuun ta, hadi da kyawun surar ta da bai taba ganin mace mai irin sa ba sun taru sun tsaya masa a rai, sun hana shi tuki cikin sukunin zuciya yadda ya kamata. Sun hana shi tuki da mugun gudu yadda ya saba. Sun maida shi tensed.

Sai muskutawa ya ke a cikin kujerar sa yana sake muskutawa ko zai ji dadin tukin da yake yi, amma ya kasa jin kan sa dai-dai yadda yake ji a baya, ko mai yasa ya damu da irin kallon data ke masa? 

A rayuwar sa, mawuyaci ne ya yi wa yarinya kallo na biyu, amma ita wannan duk yadda take ci masa magani tana hararar sa tamkar idanun ta zasu fado kasa, kamar ta kama shi da gagarumin laifi, tana kuma faman kawas da kai daga barin kallon da suke wa juna, ga wani irin shan mur da ta yi kamar taga mala’ikan daukar ran ta, zai iya rantsewa yayi mata kallo har da na zarce ka’ida a fakaice ta can kasan kyawawan idanun sa. 

“After all she’s a Moslem girl Man, what’s your business with her? (diyar musulmai ce, meye hadin ka da ita?)” Ya tambayi kan sa cikin girgiza kai da cije baki. Kodayake duk yawan abokan mu’amalar sa a ciki da wajen Najeriya Musulmi sun fi yawa. Har ma a nan inda yake zaune.

Ba yau ya fara dating ‘ya’yan musulmi ba, musamman da yake su kan yi kuskuren dauka cewa shi din Musulmi ne kuma bahaushe, idan har ba shi yayi niyyar fada ba. Kallon musulmi suke masa. Sabida sunan sa da kamannin sa da accent din sa gabakidaya kwatakwata basu yi kama da background din sa ba. 

Bai san meyasa ya fi so a tafi a hakan ba, wato a tafi a zuwan shi Musulmin ne, baya kyamar Muslunci, baya kyamar musulmai musamman da ya kasance 80% na abokan huldar sa da abokan aikin sa musulmi ne, in ba wanda yayi masa farin sani ba babu mai iya banbancewa. Sabida baida wani appearance mai nuna addinin sa.

(A can kasan ran sa ya san; ka ce kai MUSULMI ne kawai ba karamin abin tinkaho da alfahari bane).

Shi kam meye hadin sa da al’ummar Musulmi bayan abokantaka ta aiki da ta mu’amala? Duk da cewa alaqar da musulmai ke yi da mutanen sauran addinai na matukar burge shi da bashi sha’awa, musamman yadda basa nuna kyara da kyama ga kiristoci, su ci tare, suyi hira tare, su yi kyakkyawar mu’amala ta abokantaka a tsakanin su.

Ya taba tambayar wani shaqiqin abokinsa Muhyidden Tokumbo Adesola, me yasa yafi son sa shi Hamzan duk cikin abokan su alhalin shi Christian ne shi kuma Moslem?

A lokacin Muhyideen Adesola ce masa yayi  “Addinin ka na gare ka, nima addini na na gare ni, Ayar Ubangijin mu ce”. Sannan ya jawo masa Ayar da larabci inda yace “Lakum Deenukum wa-liya Deen.”

Muhyiddeen ya cigaba  da yi masa karin bayani da cewa “Addinin mu na muslunci addini ne mai sauki da rangwamen gaske, hadi da adalci ga kowa.  Sabida rangwamen sa da adalcin sa ne ma ya amince mana auren matan ku na Ahlil Kitabi. Ka ga karewar mu’amala kenan.

Sama da komai Hamzah you are a very polite person with good Moslem behaviours. Da zaka muslunta da anyi namijin gaske a cikin addinin muslunci”. 

Maganar Muhyiddeen Tokumbo ta dade da tsaya masa a rai, ba tun yau ba in ya tuno sai ya maimaita ta kamar a lokacin Muhyiddeen ke yin ta, hakan da Muhyiddeen yace ya kuma kara saka masa sha’awar komai na al’ummar Musulmai tun daga halayya har dabi’a, shiyasa 80% na abokan mu’amalar sa da huldar sa ta yau da kullum musulmi ne.

Idan har ba ya je gida can Jos ko ya halarci zaman Church on Sundays ba, baya tuna shi Christian ne. Abinda bai sani ba kuma yake kishirwar sani har gobe shine; shin idan su Musulmai addinin su ya yarje musu auren matan Christians, su mazan an yarje musu auren matan musulmi?

Ya sa a ransa duk ranar da ya sake zuwa wajen Muhyiddeen Tokumbo, zai kara yi masa wannan tambayar don neman karin ilmi. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 21Sakacin Waye? 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×