Cikin mamaki da tsoro wannan karon nake duban sa, kafin in yi ta maza cikin rawar baki da raurawar zuciya na ce, "ka bani hanya in fita malam a cikin lifter fa muke" Hamzah ya gyara tsayuwar sa yace "ashe kuwa zamu kwana a lifter in baki gaya min inda kika sanni ba!"
Allah ya taimakeni wani daga waje ya tsaida lifter din, daga can waje kofa ta bude, nayi wuf na fice ta kasan hannayen sa ba tare da ya ankara ba lokacin da wancan mutumin yake kokarin shigowa. Ina fita shima ya fito daga lifter din muka jera. . .