Skip to content
Part 25 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Cikin mamaki da tsoro wannan karon nake duban sa, kafin in yi ta maza cikin rawar baki da raurawar zuciya na ce, “ka bani hanya in fita malam a cikin lifter fa muke” Hamzah ya gyara tsayuwar sa yace “ashe kuwa zamu kwana a lifter in baki gaya min inda kika sanni ba!”

Allah ya taimakeni wani daga waje ya tsaida lifter din, daga can waje kofa ta bude, nayi wuf na fice ta kasan hannayen sa ba tare da ya ankara ba lokacin da wancan mutumin yake kokarin shigowa. Ina fita shima ya fito daga lifter din muka jera.

Kafin duk mu ankara cewa ba’a downstairs wato hawan karshe lifter ta ajiye mu ba. Ta ajiye mu ne a hawa na goma wanda nisan sa bazai biyu da tafin kafa ba.

Amma dai da in koma cikin lifter din nan mutumin nan dana ke gudun sake haduwa dashi wata da watanni  helter-skelter ya kara kulle ni ya hana ni fita muna shakar iska guda, gara nayi ta bin stairs komai yawan su har nasamu na isa kasan koda zan kai dare ina sauka. 

Don haka na juya da sassarfa na soma bin matattakala da kafafu na, kirjina na duka, ga mamaki na sai shi kuma ya biyo ni a baya. Muka jera.

In ka gan mu a lokacin tamkar couple dake kan ganiyar sabon aure, musamman da yake shigar shaddah yayi, na gane cewa shaddah is his favourite attire, inda duk na cira kafa nan yake mayas da tasa akan stairs din. 

“Young Lady kin ki gaya min ina kika sanni? But the familiar look in your innocent eyes have said it all. Cewa kin sanni. 

By the way i’m Hamza Almustapha Mawonmase. Ko ya sunan kanwar tawa?”

Idanu na neman lumshe kan su suke yi ina zaburar dasu kan su bude sosai. Na yi masa shiru kamar da dutse yake magana, sai bin matattakala a jejjere nake ina sauka, shi kuma yana maida tasa kafar a duk inda na cire tawa.   

Yace “Kanwa ta, na hada ki da ALLAH ki tsaya!”

Cikin madaukakin firgicin jin ya ambaci “Allah” na dakata, tare da juyowa bakidaya na fuskance shi. Idanun mu suka sarke kamar ranar VOA Anniversary. Mamakina na kalmar “Allah” da ya ambata ne, so i’m shocked, ashe ya san Allah!”.

A hankali na dube shi da kwantattun idanu na, kwayan idanun suka nuna laushin da zuciya ta tayi, yayin da wasu irin kibbau kamar allurai suke fita daga cikin idanuna kai tsaye zuwa cikin ‘Almond – shaped eyes’ din sa. Nace.

“Me yasa zaka hada ni da Ubangiji na inyi abinda ban yi niyya ba? As far as i know, ban san ka ba  Mr. Hamzah!”.

Murmushi yayi, ya zagayo gaba na ya tsaya, murmushin da ya kara sanya ni shivering daga can cikin kirji na da kafafu na, “karya kike yi, zan iya rantsuwar da babu kaffara cewa kin sanni, wannan kallon ba na yau bane, ba na jiya bane, kallo ne mai tushe mai lasisi. Gaya min a ina kika sanni?”

Baki na da jikina duka suka soma rawa kasancewar Hamzah kara matsowa gaba na yake yi. Kusancin dake tsakanin mu ya zama bai fi na taku biyu ba, kamshin sauvage din sa ya kara birkita ni, ya fi ni tsayi sosai, and that chemistry  ya cigaba da aiki a ilahirin jiki na. Murya na rawa kamar yadda jiki na ma ke yi nace,

“Na gaya maka ban san ka ba, ka bani hanya in wuce dare yana yi min”, “Ki rantse da Allah baki sanni ba” Mamakin mutuminnan ya kusa zauta ni, na Allah da yake ta ambata. 

Murya na rawa, na tattaro duka courage din duniyar nan na kara a kan wanda nake da shi, don na ga cewa wannan ce dama ta ta karshe da zan san gaskiyar abinda Aunty Nasara ta fada a kan sa, abinda har gobe na ki yarda da shi a kasan raina, na kuma kasa samun wanda zai amsa min da gaskiya. 

“Mr. Hamzah zan gaya maka na san ka ko ban sanka ba, idan ka yi alkawarin amsa min tambaya ta guda biyu. Don Allah ba don ni ba!”

Gyara tsayuwar sa yayi ya kuma bani dukkan attention din sa, kafin yace “ina jin ki kanwa ta, kuma zan baki amsa to the best of my knowledge.”

Tsoro na kara mamayata, amma ina matukar son quenching curiosity dina yau, once and for all.

“KAI MUSULMI ne? Ko kuwa ka yi riddah ne daga addinin muslunci?”

Tambayoyin yarinyar sun zame masa tamkar job interview da dan adam ke son ya haye ko ta halin kaka for the survival of his future. Amma “karya” bata cikin dabi’un sa. Mutane da yawa sun masa wannan shaidar wato baya karya domin kare kai. Dalilin wadannan tambayoyin data yi masa ne bai sani ba. What’s her business with his personal religion? 

A sanin sa ba ruwan kowa da addinin kowa a kasar nan, su din, wato kiristoci sun fi musulmai ‘yancin yin addini kuma sun fi su gata a gwamnatin kasar ta Amurka. Ya rasa me yasa jama’a da dama ke mistaking din sa to be a Moslem (kuskuren daukan sa Musulmi) alhalin bai taba dandana addinin Musulunci ba. Sai ya cigaba da taka stairs kawai bai amsa mini ba. Sai ma tashi tambayar da ya jefe ni da ita.

“Mene ne RIDDAH?”

“Mr Hamzah kayi alkawarin amsa min tambaya ta to the best of your knowledge, bamu yi zaka rama da kowacce tambaya ba.”

Na fada cikin rauni, ina fatan abinda zai fito bakin sa ya karyata abinda aka fadamin shekaru kusan uku a baya a kansa. Ina fatan idan ya bude bakin yace min. 

“Ni musulmi ne Siyama haihuwar muslunci tashin muslunci kuma rainon muslunci. Ki maida min dukkan emotions din ki, da kika kwace min su (by force) daga zuciyar ki, su koma sababbi kar-kar a kai na.”

A haka muka taka matattakala ta kai kusan guda goma bai ce komai ba, ni kuma ban katsi hanzarin sa ba, sai da ya mula don kan sa ya ce,

“Why do you want to know my religion? Kuma me sanin hakikanin addini na zai kare ki da shi baiwar Allah?”

Kai tsaye na amsa “just to quench my curiousity about you.”

Sai bayan na fada nayi saurin toshe baki na da tafuka na, shikenan na yi subutar baki na gama gaya masa cewa na san shi din, ba yau na san shi ba.

“Kenan hasashe na gaskiya ne na cewa kin san ni!”

Na girgiza kai, kafin in bashi amsa ya katse ni da cewa;  “Kanwa ta, yaya sunan ki? A ina kika san ni?”

Fatar baki na na rawa da kakkarwa, sabida yadda zuciya ta da kanta take raurawa nace “Si-yaa-mah!”.

“Siyaam, na nufin Fasting, right?”

Cikin kidima na dube shi, ya fadi SIYAM da accent din asali, yadda larabawa ke fadin Azumi, har ma’anar kalmar larabci wato ya sani.

“Ya Allah! Who is this Man?” Ban san cewa a fili na yi furucin da ke ci na a zuci ba.

Zuwa yanzu mun isa hawa na karshe. Babu sauran steps. Motoci ne a gaban mu a jere wannan na wane waccan masu numfashi da walainiya na ma’aikata, na san wannan ne waje na karshe da zamu rabu inda daga nan kowa zai kama gaban sa. Gashi bai bani amsar dana ke matukar kwadayin ji ba.

“Siyaam, sai gani na biyu!”.

“Mr. Hamzah baka cika alkawari ba”

Na fada cikin ragaita, kamar in fashe da kuka, ji nake in ban ji gaskiyar abinda nake son ji ba a kan addinin sa, curiousity zai iya kashe ni a daren yau.

Bakar motar sa ‘GMC Terrain’ dake gaban mu yasa mukulli ya bude ya shiga, kafin ya sako kan sa ta taga ya dube ni a inda ya bar ni harde da hannuwa a kirji ina kallon sa idanu cike da ragaita, ruwa yana sauka akaina yaf-yaf yana jika ni amma kamar ba’a jiki na ruwan ke sauka ba. With utmost respect yace “ki yi min alfarma in kai ki gida, Siyaam, do me this privilige just once in life, don na lura ba ki da mota, ruwan nan yana kara karfi ina tsoron kada ya dake ki da yawa kiyi zazzabi Siyaam.”

Yadda yake furta SIYAAM din ainahin yadda larabawa ke furtawa babu harafin “A” din karshe ya karawa sunan nawa armashi da dadin ji a kunnuwa na, ya kara min jin cewa ashe sunana mai dadin gaske ne har haka mutane suke bata min shi, babu wanda ya taba pronouncing din sunan expertedly the way he did. Sai naji bazan iya tankwabe wannan tayin nasa ba. Duk da ban taba shiga motar kowane namiji a kasar nan ba Young Abba ba. 

Ji nake ba shiga mota ba, ko kai na ya ce in sare in bashi zan sare a wannan lokacin in mika masa sabida yadda ya girmama ni, ya kuma nuna damuwa da lafiya ta, in dai zan zauna kusa da shi yana tuka ni ai na samu abun rubutawa a DIARY dina yau. Na taba yin wannan mafarkin a can baya, na gani na zauna  a gefen sa yana tuka ni a mota. Watakila idan akwai wani cikin mafarkaina da shi da zai zama gaskiya to wannan ne kawai.

Ya bude min kofar kusa da shi na shiga na rufe. Cikin wata irin nutsuwa da kwarewar tuki ya tada motar  muka hau kan titi.

Sautin mawakiyar larabci Nancy Agram ya kunna a cikin motar. Hamza ba zai gushe yana kashe ni da mamaki da tu’ajjibin al’amuran sa ba. Kodayake as far as i know NANCY AGRAM ba musulma bace. Amma kuma ai balarabiya ce.

Satar kallon sa nake yana tukin sa cikin madaukakiyar nutsuwa da iyawa, cikin bin ka’idar tuki na kasar Amurka, bayan na gaya masa unguwar da zani. Komai nasa cikin tsanaki da gayu, na kara satar kallon nasa sai caraf! Ya kama kwayar ido na da tasa. Dai-dai ya sha kwana danja ta tsayar da mu, ya tsaya yana cewa,

“Siyaam, don Allah a ina kika san ni?”

Sunkuyar da kaina na yi ina wasa da yatsun hannu na. Yau ji na nake on top of the world gani tare da Hamzah Mawonmase a muhalli guda, har muna magana, har yana tuka ni a mota. What a lucky and blissful Monday!

Ashe dai binne tsofaffin emotions da matattun infatuations dina nake yi kawai da taimakon addu’a da Alqur’ani a watannin baya. Ashe dai Hamzah Mawonmase bai shigo rayuwa ta don ya fita a sanda nake so ba,  ashe Hamzah Mawonmase ba zai taba barin rayuwata bakidaya ba. Ashe sai in ban ga Hamzah bane ko ban ji muryar sa ba nake tunanin nayi escaping daga soyayyar sa.

“Ba zan gaya maka ba, sai ka amsa min tawa tambayar Mr. Hamzah. Kai Musulmi ne ko kuwa RIDDAH ka yi? After all, sanin addinin ka ba zai zame min gagararren abu ba, tunda kai din ba boyayyen mutum bane, ko a net na duba zan samu bayanin duk dana ke so a kan ka, amma na fi so ne in ji daga bakin ka zan fi gamsuwa, duk da ina da hanyoyin da inna bi cikin sauki zan sani ba tare da ya zame min abin wahala ba”.

Daidai nan danja ta bamu hannu, bai kara magana ba nima haka har muka zo kofar Condo din mu. Na murda marikin kofa zan fita, amma dana murda marikin kofar sai na ji shi gagau, a garkame. Wato ya rufe kofofin motar automatically. Yadda n ba shi ya bude min ba bazan iya fita ba. Sai na juya na dube shi da idanun bidar dalilin rufe min kofa. Alhalin gamu a kofar gidan namu.

Juyowar da idanu na basu fada a koina ba sai a cikin lumsassun idanun sa. Babu kuma wata gaba ta sassan jiki na da bata amshi sakon dake cikin idanun Hamzah ba. Looking straight into the peak of my eyes with hidden horizons cikin idon sa. A raunane yace,

“Na yi alkawarin amsa miki tambayar ki to the best of my knowledge; Ni Hamzah dan Addinin Christianity ne.!

Iyaye da kakanni na duka babu musulmi ko daya, they lived and died serving Christ. Amma na girma ne a cikin  musulmai na kuma rayu a North (Arewa) tare da aminina na kuruciya wanda musulmi ne, shine mai asalin suna Hamzah Almustapha ba ni ba. 

Na yi amfani da ‘primary certificate’ din sa na dora karatu na  a kai bayan rasuwar sa. Dalilin da yasa nake amfani da sunan sa kenan a makaranta har yau da sunan ya bini a profession dina.

Siyaam, i’m not a Moslem like you, but a devoted Christian, Catholic, from BIROM KINGDOM!”

Shock biyu ne suka tarar min a lokaci guda. Shock din ya zama kamar na lokacin farko da Aunty na ta gaya mun cewa Hamzah Almustapha ba musulmi bane. Na wannan lokacin bansan me yasa yafi huda ni har cikin bargo fiye dana wancan lokacin ba. Hakan ya faru sabida daga bakin sa maganar ta fito kai tsaye, kenan babu sauran kokwanto Hamzah is not Muslim. Akwai wasu attributes nasa dana kara laqanta a tsayin ‘yan mintocin dana yi tare da shi yau masu matukar kamanceceniya sosai dana Musulman kwarai. Gashi ya ce bayan kasancewar sa Christian ma Catholic ne, wanda sun fi sauran tsaurin addini.

-Baya karya.

-Bashi da girman kai.

-Ya san Allah, duk kalmar da zai fada sai ya hada da rokon ayi masa don Allah.

Murmushi na yi mai ciwo, ina jin duk wani feelings dina a kansa yana dissolving wato yana narkewa yana  kwaranyewa a kasa. 

Dan sauran hope dina na cewa Aunty tsokanata take yi, ko tayi ne don tayi galaba a kaina a wancan lokacin ya karasa bin ruwa. Na saka a raina wannan ce rana ta karshe da zan kara tuna kalmar “Hamzah” da sunan So, na kuma tabbata Ubangiji na bazai bar ni haka ba, a jihadin da zan yi wa addinin Sa, in sadaukar da soyayyar shekaru kusan goma saboda tsira da addinin Allah. 

Allah Zai dubi sacrifice dina don addinin sa ya musanya min da mafi alkhairin sa. Amma kuma me? Saukin kai irin na Hamzah Almustapha ya gama  tafiya da ni, sai naji ina yi masa kwadayin Musulunci. Irin su da a ce Allah ya yo su a musulmai, da anyi nagartattun mutane. 

I’m a muslim ba don na zabi zama Musulma ba, sai don an haife ni cikin musulunci. So being a muslem is never by choice. Allah ne ya zabe ni ya bani. He’s a Christian maybe because he was born into christianity ba shi ya zabarwa kansa ba shima.

Me zai hana in janyo shi a jiki in nuna masa hanyar tsira? Wannan ita ce soyayyar da zan iya yi masa ta hakika. But idan yana da interest a kan Musuluncin ba?  Abubuwa da yawa sun nuna ba yau yake tare da musulmai ba, da zai musulunta da ya musulunta tuntuni, tunda yace aminin sa ma da yake bearing sunan sa da suka tashi tare musulmi ne.

Jiki na yayi mugun sanyi, ban iya nace komai ba naga wayata dake cinya ta a hannun sa. Ya saka lambar sa a ciki ya kira ya ajiye min abata a inda ya dauke ta. 

Sannan yayi unlocking kofar ta bude. Da mugun sanyin jiki na yunkura na fice. Ko nagode ban iya cewa ba. 

“Sai gani na biyu…… Siyaam.”

Wannan “Siyaam” din da yake ta ambata ba karamin tafiya yake da imani na ba.

Ina kallo ya ja motar sa a hankali ya bar rukunin gidajen Condos din mu, sai naji kamar in bi bayan sa in ce ya dawo ya karbi addinin musulunci a baki na. Ba zan iya rayuwa cikin kwanciyar hankali alhalin ina ganin sa cikin bata ba.

                                         *****

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 24Sakacin Waye? 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×