Skip to content
Part 27 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Iyakacin abinda ya rubuta kenan, wanda yasa Nasara sakin wayar a kasa ta tarwatse. Cikin karaji tace “SIYAMA! Me nake shirin gani haka?

Karya yake bazai taba musulunta sabida ke ba, kin yi masa kadan, kin yi tsararo. Kafin ya gan ki ya ga dubun ki, saidai su su bar nasu addinin ba dai shi ya bar nasa a kan su ba. Kuma barin nasu addinin baya sakawa ya aure su. Me yasa kika kula shi? Na dauka tun a shekarun baya mun rufe chapter din Hamzah? Na dauka kin gama cinye jarrabawar ki a kan sa?

Kada soyayyar dake zuciyar ki ta rude ki ga aikata negligence (sakaci) da addinin ki”.

Ta sassauta murya kafin tace cikin curiousity.

“Exactly me ke rudar ki a kan wannan Mushrikin? Ni dai na san ba kyau bane, don bai kama kafar Omar ba, ba dukiya bace don ke ba ‘yar mutsiyata bace. Ba addinin sa bane don ke malamar musulunci ce mahaddaciyar Al’qur’ani. Ki gaya min ta ina wannan alaqar zata yiwu? Ta ina wannan hadin ya dace?”

Sai a wannan lokacin na magantu. Da dukkan karfin zuciya ta. 

“Shi yasa ai nace miki zan koma gida Mambillah in nemo Omar muyi auren mu, shine kawai solution. Ban ce miki zan auri Ahlil Kitabi ba. Ban ce miki wani abu na ruda ta a kan sa ba. Ban san me yasa kaddara take yawan hada mu ba. Duk iyaka kokari na nayi don in kauce masa a VOA. Amma sai in hadu da shi a inda ban zata ba.”

Na saka mata kuka mai cin rai itama, kwatankwacin irin wanda na yi wa Hamzah.

Aunty Nasara ta rungumo ni jikin ta tana bubbuga baya na cikin lallashi. Kafin tace “tafiya Mambila ba ita ce maslaha ba. Just ki manta da shi ki cigaba da harkokin ki, ki kuma yi blocking lambar sa daga wayar ki. He is my senior me at work ba don haka ba da na je har ofishin sa na yi masa gargadin kada ya kara kula ki, don bazaki hada mu da rigimar da in mun san farkon ta bamu san karshen ta ba.”

Ta kawo tsarabobin data yi mana ni da Ahyan daga Atlanta ta bani. Ta yi ta kawo min misalai masu gamsarwa mai nuna cewa ta san ina son Hamzah, amma in sawa zuciyata dangana da cewa alaqata da shi ba mai yuwuwa bace a matsayi na na cikakkar musulma haihuwar musulunci, rainon musulunci, da matsayin sa na kirista haihuwar Christianity. Ko bata fada min ba bana bukatar a fahimtar dani wannan, kuma na dauki komai tsakanina da shi a matsayin jarrabawa daga ubangiji, domin ya jarraba karfin imani na da addini na. Ina fata in samu cinye wannan jarrabawa da kyakkyawan sakamako.

Saidai kuma nayi – nayi in yi blocking din nasa na kasa. Sabida tausayi yake bani idan na tuna mutuwar kafirci a gare shi duk da kyawawan halayen sa wuta zai tafi.    

Tun daga ranar kuma kullum cikin turo min sakonni masu narka zuciya yake. Har da ayoyi na rantsuwa daga littafin sa Bible “PSALMS” na cewa ba zai hakura da ni ba a kan banbancin addini.

“Na amince kowanne obstacle ba zai rasa mafita ba, Siyam. Roko na gare ki shine ki bani dama in dawo gidan ku mu zauna officially mu tattauna, mu nemo mafita ga tarin banbance – banbancen mu, wanda shi ne abinda yake barazana ga cikar farin cikin kowannen mu a yanzu.”

“I believed ina son ki. I trust my natural feelings on you. Jiki na ya bani cewa akwai ‘ya’ya masu yawa kuma masu albarka a tsakanin mu, wadanda zamu samar daga tsaftatatcciyar hanyar aure, mu hada karfi wajen yi musu tarbiyyah”.

“Ban taba jin abinda nake ji a kan ki a kan kowacce mace ba, wanda ke nufin ke ce matar auren dana dade ina jira daga HEAVEN, wadda zata jagoranci farin ciki na ta kaunace ni saboda Allah. Give us a time to discuss and find lasting solution to our differences”.                       

 -Hamzah Mawonmase.

Jin cewa bani da niyyar amsa ko daya cikin tarin sakonnin sa kuma na ki zuwa VOA, na hakura da karatun nawa for the second time a kan sa, domin hakika na dauki nasihar Nasara mai kaunata da gaskiya da kuma zuciya ta ta Islamist, Nasara kan ce. 

“Ina kokarin nusar dake gaskiya ne kasancewar Hamzah bai fi sauran maza ba. Duk abinda ke a Hamzah, duk abinda yake burge ki da shi a kansu, sauran mazan musulmi ma suna dashi har wanda ya zarta nasa, tunda kuwa su sun yarda ALLAH Wahidun ne (guda daya ne bashi da abokin tarayyah) to suna da komai koda basu da komai na alfanun duniya sun rabauta, shi kuwa in ya mutu a haka fanko ne, wadanda za’ayi itatuwan wutar jahannama da su ranar gobe kiyama”.

Ire-iren wadannan maganganun na Aunty Nasara na kara frightening dina, su firgita ni su tayar da hankali na na dukufa rokawa Hamzah shiriya koda kuwa ba don mu yi aure ba. For his own survival a wurin Allah.

A wannan ranar ta Litinin sai ga Nasara da babban bako a ofishin ta. Director din department din su gabadaya na ‘Media and Publicity’. Mr. Hamzah Mawonmase.

Karo na farko da ya taba taka kafafun sa zuwa ofishin Nasara Alkali, bai ce a kira ta ta same shi a nasa ofishin ba, kasancewar a kasan sa take nesa ba kusa ba.”

“Ah! Wa nake gani kamar Director na Mr. Hamzah? Oga da kan sa! Ai da ka aiko in zo da na bar komai nake yi na zo.”

Nasara na fadin hakan ne cikin mamakin ramar data gani a tare da Ogan ta Hamzah, sati biyu baya sun yi meeting tare da shi he is healthy, vibrant and energetic, yau kuwa yayi kozai – kozai kamar ba shi ba, gashin kan sa ya cukurkude, kwatankwacin irin halin da ta baro Siyama a ciki.

“Wanda yake nema shine a kasa har kullum. Besides, ke Mama na ce yanzu.”

Ya fadi yana zama a kujerar dake fuskantar makeken tebirin da ya raba tsakanin su.

Nasara ta mike ta isa ga firjin ta ta bude, cikin karramawa ta juyo tana tambayar sa “Coke zan miko, ko ruwa koko Coffee ran ka ya dade?”

Girgiza kai yayi “duk ki bar su, ki sammin lokacin ki please. Na  zo ne takanas akan maganar ‘yar ki Siyam.”

“Ko baka fada ba na sani” Nasara ta amsa cikin murmushi. Dan fiddo ido yayi yana mata kallon ta ina kika sani?” Murmushin ta sake yi tace “ni da Siyama are more than matar Uba da ‘yar miji, ‘ya ta ce wadda haifar ta ne kawai ban yi ba.

So na san komai a kan Siyama, na san komai akan son da take yi maka tun bata hadu da kai ba. Bata kuma san ka ba. Wanda ya janyo mata matsala da iyayen ta, tun ma kafin ta san wanene kai. Dalilin dawowar ta hannun mu kenan. 

Na samu na ceto ta daga soyayyar ka ta gaibu, da wadda ta fara bayan ganin ka a raye, wadda bazata kai ta ko’ina ba sai cikin matsala da addinin ta, al’adar ta da iyayen ta. For Allah’s sake Mr. Hamzah, me kake so a tare da Siyama? 

Aure tsakanin ka da ita Haramun ne a addinin mu, da dai ace kaine macen ita namijin to babu laifi addinin mu yayi wannnan rangwamen”.

Hamzah ya kama kai yana jujjuyawa kwayar idanun sa sun kada sun yi jajir. Yace “koda na bar ta tayi addinin ta aure tsakanin mu haramtacce ne?” 

Aunty tace “kwarai da gaske”. 

“Mrs Alkali ki taimake ni ki gayamin wacece Siyam? Tarihin ta da nasabar ta, ki wayar min da kai a kan wannan MAFARKIN data ke magana a kai, gashi yanzu kema na ji kin yi magana kwatankwacin sa, wanda har ya saka ta batawa da Abban ta a kaina?”

Nasara bata san me yasa taji Hamzah ya bata tausayi ba, damuwar dake cikin idanun sa da muryar sa kadai ta isa,domin ta gano tsantsar kaunar Siyama cikin idanun sa. Sai kawai ta samu kan ta da warwarewa Hamzah labarin Siyama kamar yadda Wasila ta sha gaya mata. 

Yadda ta girma tana mafarkin mijin auren ta mai irin kamannin sa da muryar sa (fantasies), yadda ta bijirewa auren dan uwan ta da suka tashi tare har ta sha fiya-fiya don dai ta samu ta mutu akan ta auri wani ba wannan mijin mafarkin nata ba. 

Yadda abin ya kusa kaita ga tabuwar kawakwalwa, da yadda Babanta ya kore ta ta koma Mambila gun Kakarta. Zuwan su Mambilla yi wa Ummati sallama da daukota da suka yi zuwa U.S. Nasara ta zuki numfashi kafin taci gaba da cewa. 

“She then became highly passionate ga kallo da sauraren VOA. Inda anan ta gan ka. Bata fito ta yi min bayani ba na fahimci kai ne mijin mafarkin ta na shekaru masu yawa. Wato kai ne Dream Man din ta.

A wannan lokacin ta lalata karatun ta na Sakandire sakamakon ta bai yi kyau ba ko kadan. Dana fahimci halin da Siyama ke ciki, sai na soma tunanin hanyar da zan bi in ceto ta daga soyayyar da bata da ma’ana kuma ta zama barazana ga duk wani cigaban rayuwar ta. 

Na yanke shawarar kai ta makarantar addini a New York inda ta haddace Al’quranil Kareem, wanda ya taimaka mata ta gyara rayuwar ta, ta mike sambal a karatu, ta cirewa kan ta damuwar ka. 

Kuskuren nawa ne kuma ni na jawo komai, na manta cewa a VOA kake, na gayyace ta zuwa “End of the Year Party and Anniversary” din mu inda a can ta ganka a fili, na dauka zata dawo da bara bana, sai ya kasance ba abinda ya faru tsayin watanni da ganin data yi maka a fIli. 

Sai na dauka completely ta hakura, sabida na gaya mata cewa ba addinin ku daya ba. Bayan haka da wasu watanni sai kuma aka turo ta Internship nan wajen mu. Wallahi lokacin da ta gaya min cewa nan aka turo ta na shiga damuwar cewa zaku kara haduwar, amma ban nuna mata ba ban kuma zurfafa dauwar tawa a kai ba. Na sani komai Allah ya rubuta dan adam bai isa ya kauce masa ba. Gudun kaddara guzurin tadda ita ne.

Ku kuka san a inda kuka hadu da abinda ya biyo bayan haduwar taku, domin na yi tafiya zuwa Atlanta. Na dawo na samu diya ta cikin wani hali, wai zata koma Najeriya ta hakura da karatun ta. Bayan saura shekara daya ta kammala.

Siyama did not derserve all these traumas of love Mr. Hamzah, because she is pious, religious, (mai addini ce, mai yawan ibada ce), wadda ta yarda da Allah daya ne bashi da abokin tarayya. Addinin ka ya ce Allah uku ne. Wanda ku kan ku kun san kuna tafiya ne a kan abinda kuka budi ido kuka samu iyayen ku a kai, amma kun san Allah daya ne, sabida Allah uku bai halicci duniya da abinda ke cikin ta ba. Ba shi da abokin tarayyah.

Jesus, wato Annabi Isa (A.S) ba dan Allah bane, bawan Sa ne kuma Manzon sa, Mary wato Maryamu ba matar Allah bace, bayin sa ne da ya halitta tsarkakakku kamar yadda ya halicce mu yayi nufin su zama aya ga mutane ba don su zame masa abokan tarayyah ba. Don haka babu manufa a tarayyar ka da Siyama duk son da take maka ko kake mata. Ka bar ta ta tsira da lahirar ta, kada ta kaucewa addinin gaskiya. 

Ku yi wa juna fatan alkhairi zan kuma sa a canza mata wajen yin internship dagaVOA”.

“Kada ki yi hakan, in kika yi hakan baki yi mun adalci ba. Ki bar ni in yi tunani cikin tsanaki. Mrs. Alkali i must confess to you that i’m love with your daughter, son da nake jin zan iya aikata komai zan iya sadaukar da komai don na tsira da ita.

Ki bani kwana uku in samo mana mafita. Kiyi wa Allah kada ki raba ta da VOA kaddarar rayuwar ta na a cikin VOA tun haihuwar ta.”

Ya fada yana share hawayen da suka cika masa ido da hankicin sa. Hawayen tausayin Siyama. Ashe shiyasa take masa kallon jin haushi, kallon ya bar ta tana suffering shekara da shekaru a kan sa. Amma bai tashi bayyana ba sai a matsayin wanda ya kafurta a nata addinin. Siyama na da duk wata dama ta taji haushin sa, ta kuma nemawa kanta tsira daga soyayyar da zata raba ta da imanin data yi da addinin ta na gaskiya, koda kuwa barin karatun data wahala a kai ne, addini yana sama da komai.

“Ki yi min alfarma guda daya Aunty Nasara” Ya fada yana hada hannayen sa biyu cikin roko (pleadingly). Nasara bata ce komai ba amma yanayin ta ya nuna shi take saurare. “Ki roki Siyama ta cigaba da ansa kiran waya ta, ta kuma dawo bakin karatun ta, kada ta samu matsala.”

Nasara tace “zata dawo makarantar ta bi’iznillah amma ban yi maka alkawarin saka ta amsa wayar ka ba; it has no meaning. Kada ka hure mata kunne ta kara bijirewa iyayen ta. In fact, daga rana irin ta yau, bana so ka kara kiran ta Mr. hamzah. Ko ka yi mata sakon text. Don na lura yana daga abinda ke dada birkita ta, ya dugunzuma ran ta ga sa ta son komawa kasar mu.”

“Ki yarda da ni yadda zaki yarda da Musulmi dan uwan ki. Ba zan hure mata kunne ba, na san daidai kamar yadda kika san daidai, na san abunda ya dace na san wanda bai dace ba. 

Na kuma san addinin musulunci addini ne mai tsarki, don watakila na fi ki shiga cikin musulmai. Kamar yadda nace ki bani kwana uku, ki kuma rokar min ita ko sau daya ne ta daga kira na, don Allah Nasara.”

Sai ga Hamzah ya sauko daga kujera, ya aje guiwowin sa a gaban Nasara yana roko. Nasara ta tuna waye Mr. Hamzah a organization nasu bakidaya, and he’s her master. Sai ta hau rokon sa itama a kan ya daina durkusa mata, zata yi duk abunda yake so in dai shima zai tsaya a limit din sa ya kiyaye abinda zai ketara addini. Hamzah yayi alkawarin hakan, sannnan bayan kwana ukun zai zo har gida ya same ta, Baban Siyama yake son gani wato marikin ta. Nasara ta ce babu matsala.

<< Sakacin Waye? 26Sakacin Waye? 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.